“Ke ba ni labari ya aka yi Hurriya ta bar gidan?”

Sai da Khairy ta kalli kofar falon dan tabbatar da Yayansu ba zai shigo ba sannan ta fara bata labaran abubuwan da aka yi bata gidan.

HURRIYA POV.

Jerowa suka yi suna tafiya yana ta yi mata nasiha a matsayinsa na yayanta.

“Wallahi Yaya duk yadda kuke tunanin abun yake ba haka ba ne, ni bana munafurci ko zancen Abban su Husna ni da ita kawai na san na yi magana kuma maganar karatu kawai muka yi sai take ce min lokaci yana kurea na fada mata Appa nake jira, ban san yadda aka canja zancen ba abun har ya kai mahaifinta ya samu Appa da maganar”

“Wacan ya wuce, komai ya wuce yanzu kawai ina jan hankalinki ne akan rayuwa, duk wani abun da kika san zai janyo miki magana ko ya bata tsakaninki da mutane ki daina kuma ki gujeshi, ina yabonki Hurriya shiyasa idan aka fadi cewar kin yi wani abu nake musawa ko na yi mamaki saboda na san ba halinki ba ne, dan Allah ki natsu ki daina duk wani abu da be dace ba”

“Ba zan sake ba Yaya ba zaka sake jin an fadi wani marar dadi kaina ba na maka alkawari”

“Yayi kyau, in kin shiga ciki ki ce ina gaishe da Momy”

“Toh Yayana na gode”

Ta wuce ciki shi kuma ya juyo ya dawo bangarensu sai dai be shiga ciki ba ya shiga motarsa ya bar gidan. Sai da Hurriya ta maida kofar falon ta rufe sannan ta lura da Husna dake zaune akan sofa tana sanye da farar abaya. Da gangan Hurriya ta dauke mata kai zata wuce Husna ta yi saurin riketa tana dariya.

“Fushi kike yi da ni saboda ban zo ba kwana biyu?”

Hurriya ta cire hannunta daga jikinta fuska a daure ta ce.

“Ba saboda haka nake fushi dake ba, ina fushi da ke ne saboda kin hada ni da iyayena, abun da kike yi sam be dace ba Husna saboda na yarda dake na saka nake fada miki sirrina ashe fitarwa kike gashi nan kin yi sanadinyar da Appa ya koreni a gidan nan yau na dawo, kuma kowa a gidan nan yanzu ya tsane ni yana min kallo da munafuka”

“Innalillahi ni kuma, dan Allah ki tsaya mu yi magana ta fahimta Wallahi ban yi miki wani sherin ba, kuma mahaifina be zo gidan nan da wata manufa ba, dan Allah mu tafi dakinki mu yi magana...”

Hurriya ta tsaya kallonta kamin ta gyara tsayuwar gilashin idonta ta nufi stairs, Husna ta rufa mata baya, dakin suka shiga suka rufe sai after sun zauna Hurriya ta fada mata abun da ya faru.

“Innalillahi, Wallahi Hurriya ba ma ni na fadawa mahaifinmu ba, Umma ce ta fada masa kuma ita ma ta yi hakan ne saboda tana tausayinki, su a nufinsu idan Appa ya amince sai su dauki nauyin karatun har ki kallama ganin kamar ba a son ki yi karatun, ni ma kuma ban san suna da wannan manufar ba sai bayan sun aikata Umma take fada min wai Abba ya samu Appanku da maganar be amince ba, sun ma yi rabuwa marar dadi, dan Allah ki yi hakuri kar ki mi dawowa fahimta baibai, ban shigo ba shiyasa ban san abubuwan da suka faru ba”

Hurriya ta sauke ajiyar zuciya, daman ta raya a zuciyarta cewar kawarta ba zata aikata mata wani abun da zai jefata a damuwa ba da ganganci.

“Amman Hurriya ke da kika samu komawa gidan Hajiya meyasa kika dawo nan?”

Nan ma sai da Hurriya ta fada mata abun da ya faru, ciki kuwa har da rumgumar da Khairy ta yi mata a yau.

“Eh gaskiya kara da kika dawo, kuma ko yanzu ki yi taka tsantsan, saboda su ya saka bana son yawaita shigowa gidan nan, yanzu kuma gashi kin fada min abun da ake kallonki da shi kuma na san ni za a kalla a matsayin mai tayaki”

“Su suka sani, ai Allah yana shaidata”

“Haka ne, kin ma san abun da ya kawo ni wai?”

Hurriya ta girgiza kai tana kallon Husna.

“Wani abokin yaya ne yace kin san shi sunansa Salim ya ce min har kun yi magana amman ya rasa ya zai shawo kanki, shi ne ya zo jiya saboda ya gan mu tare lokacin da kika je gidan kuma ya tambayi Yayana ya fada masa ni kawarki ce sosai, tare da Yaya ma suka saka ni a gaba wai yana son na lallabaki na karkarto da hankalinki ki fahimce shi, shi ba da yaudara ya zo ba...”

Hurriya ta mike tsaye ta dafe kanta tana yawuta a dakin.

“Ni kam na shiga uku, mutumen so yake ya ballo min wasu ruwan kuma? Yaushe na samu na rabu da Adam shi kuma ya kuso yana son haddasa min fitina, na yi magana da shi na fada masa cewar ni bana sonsa kuma fa ma Yaya Namra yake so daga baya ne ya dawo guna”

“Duk ya fada min, amman yace ke ce baki fahimta ba, ko kuma yayarki ce take son bata lamarin amman shi tun farko ke yake so, kuma Hurriya ni fa ina ganin idan da gaske yake kuma aka bincika yana da halin kwarai sannan aka dace kina sonsa kawai ki aure shi ki huta da wannan gidan, albashi idan zaku yi aure sai ya miki alkawarin zai barki ki yi karatu”

Hurriya ta dawo ta zauna.

“Ni be min ba, kuma na fada masa gaskiya wata kila ma saboda shi ne na ga Yaya Namra ta canja min, sai ta yi zaton ko ina kokarin kwace mata saurayi ne, kuma fa tana son shi, ni gaskiya bana sonsa ni babu ma wanda nake so yanzu”

“Shi kuma yana sonki sosai Hurriya da ace zaki ba shi dama dai zaki saurareshi, ya ce min ma zai zo gobe”

“Dan Allah kar ya zo kar ya hada ni da mutane, ki fada masa kar ya zo dan Allah, Husna kin san halin da nake ciki ki fahimtar da shi mana”

Ta karasa tana cikin son yin kuka idonta na tara ruwan hawaye.

“Zan yi magana da shi, zan fada masa yadda zai fahimta, yanzu ya maganar karatunki”

“Ni dai yanzu ki tashi ki tafi kar ace na shigo da ke a daki muna gulma”

Husna bata da wani aiki a yanzu da ya wuce ta taimaki kawarta dan haka ta mike tsaye ta yi mata sallama, cikin tsoro Hurriya ta raka falo, hankalinta be kwanta ba har sai da Husna ta fice. Sannan ta dafa zuciyarta kamin ta sauke hannun ta koma dakinta, sallah ta yi ta fito falon ta zuba abincin rana ta ci.


****    ****    ****

Karamin filo ne a hannunta ta rumgume shi sosai a kirjinta, kalaman da Momy ta fada mata dazun take tunanin, suna kokarin dorata a wani tsani da bata taba hawa ba, zancen ana son su fahimci juna ita da Captain ta tsaya mata a rai. Yana da kyau da za a so shi, yana da cikar halitta da duk wani abu da ake so a jikin namiji, sai dai ganin yadda tsarin rayuwarsa yake ya saka bata taba ayyana ma kanta kaunarsa ko sau daya a zuciyarta ba. Ta dago ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan Salim ya saka ta dan yamutsa fuska kamar ba zata daga ba, can kuma ta kai hannu ta dauka.

“Hello”

“Namra ya gida, ko da yake yayarmu ya kamata na ce”

“Haka fa, lafiya kalau ya aiki?”

“Alhamdulillah, alfarma na kira na roka kamar yadda na saba yi, kanwar nan taki dai na kasa hakura da ita, na gwada ko zan iya amman na kasa”

“Toh yanzu kuma me zan yi?”

“Lallaba min ita zaki yi, yau ma zan shigo gidan kuma tare da dan'uwanki In Sha Allah”

Har zata tambaya ta ce wani dan'uwanta sai kuma ta ji bata bukatar hakan, domin ya nuna ba ita yake ra'ayi ba, dan haka be kamata ace ta shiga hancinsa ba.

“Okay zan yi kokari, amman daga wannan ba zan sake ba gaskiya, baka fada min ya kuka kare ba a wacan karon”

“Idan na zo zamu yi maganar”

“Okay”

“Thanks”

Ta cire wayar kunnenta tana hautsina fuska, kamar zata ji haushinsa kuma sai take ganin babu dalilin haka. Aje fillon tayi ta sauko saman gadon,

‘Babu wani lalaba ta da zan yi, yarinya ta nuna vata yinka dole ne, ai maganin namiji mai shegen ruwan ido kenan da son mata’

Ta fada a ranta kamin wasu zantunka su fara zagayar kwakwalwarta, yanzu da Momy ta fada mata kudirin da suke da shi akansu ita da Captain sai take ganin wata kila canja mata ne Allah zai yi da son Salim da ta fara, ya bata wanda ya fi shi komai, dan murmushi mai kyau ne ya kawata fuskarta, ta mike tsaye ta nufi kofar dakinta ta bude sai da ta shiga dakin Momy ta duba bata ciki sannan ta sauko kasa domin ta san idan bata dakinta to tana kasa ko bangaren mahaifinsu ko kuma ta fita daga gidan. Tun kamin ta karasa saukowa stairs ta ji fadan da Momy take yi ma Hurriya har da rantse rantsen abun da zata mata idan ta sake zuwa kai tsaye ta bude mata kuloli ta zuba abinci.

“An gama abinci ban zubawa mijina ba, ni ban zuba ba sai ke ki zuba ke gaki issashiya ko? To ba zan daukar miki wannan ba, daga yau sai yau karki sake bude min kula ki zuba abinci ki jira sai na diba, ai na fada miki nan ba bangaren Iyami ne ba, wannan rashin tarbiyar da kuke ni ba zan dauke shi ba”

“Ki yi hakuri Momy, hakan ba zai sake faruwa ba”

Hurriya ta fada cikin muryarta mai sanyi, dake nuna tsantsar nadamarta. Momy ta sake daka mata tsawa.

“Idan ma ya faru ke ce a matsala domin kanki zaki jawa bala'i”

Hurriya ta ji kamar ace zata iya gyara komai kamar bata taba ba, amman ba dama domin mai afkuwa ta afku, cikin tsananin damuwa ta nufi stairs tana tambayar kanta.

‘Wai haka ko wace ya take fuskarta matsala a gurin kishiyoyin uwa, ko kuma ita ce ta fita dabam?’

Bata da mai amsa mata tambayarta kamar yadda ita ma bata san amsar ta ba. Namra ta bita da kallo har ta haye sannan ta sauko.

“Abinci ta zuba?”

“Eh saboda iskanci da rainin wayo, ni kaina ban zuba ba amman ta zo ta bude warmers ta zuba abinci”

“Wani sabon iskanci ne ta kirkiro kuma yanzu?”

“Oho mata ita zata sha wahala ai”

Momy taja kujera ta zauna, Namra ma ta ja nata kujerar ta zauna, sannan Momy ta fara zuba abincin.



A bangaren Hajiya Kaltume kuwa tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira, Malam rashin samun wayarsa ya saka ta kira kawarta.

“Ikon Allah, hausawa suka ce dan halak kaki ambato, yanzu fa nake son kiranki na tambaya size din Khairy na talkami”

Hajiya Fatee ta fada daga dayan bangaren bayan ta amsa wayar kawarta Hajiya Kaltume.

“Hmmm ai ni wani abun ne na ji da ya so daga min hankali, kuma dai be daga ba shiyasa na kiraki”

“Me ya faru?”

“Wai anya baki tunanin Malamin nan yana tayar da aikin da muke ba shi ne saboda ya bukaci wani abu?”

“Ah touh Hajiya na ga cikin nan naki fa an kwantar kuma ya kwanta daga baya abu ya tashi, har kika ce ya bukaci wani abu agareki, ni na ma manta ban tambayeki me ya bukata ba”

“Hmmm wannan maganar kuma ai ta wuce Hajiya Kaltume ciki kuma ya koma ya kwanta yadda ake bukata, ke dai yanzu me sa kika kira ni kuma me ya daga miki hankali tukuna bari mu ji na ki”

“Salma ce ta dawo dazun, bayan ta huta take min hirar wai mahaifinta yana son kawarta”

“Maa Shaa Allah Salma an dawo? Hajiya miye abun mamaki a maganar? Maza ko uwarki aka ce su aura ai aurenta za su yi, balle kuma kawar yarsu, ke maza fa ba su da kunya, ina ce Iyami ma ai yarinya ce kuma ya aureta ko kin manta”

“Amman ke Hajiya baki yi mamaki ace Alhaji yana zancen aure a wannan lokacin?”

“Daman namiji mai son aure aure ai ba zaka iya hana shi ba, halinsa ne ke dai yanzu ba kin mallake shi ba ai duk wanda ta ji zata iya kawai ta zo”


“Aa, ina tunanin na gama da komai sai kuma wannan ya taso, na bar shi yayi aure ya kwaso mana wata ita ma ta zo ta hana mu zaman lafiya? Kuma tace zata zuba nata yaya? Ai kara ma Iyami da wannan yarinyar da take karama sa'ar Salma fa kuma kawarta, ni ban gama yarda ba shiyasa hankali yake kwantawa wani bangare, kuma na kira Malam wayarsa bata shiga ba, sai dai kuma ina mamaki idan har gaskiya me yasa Malam be fada min ba? Bayan kuma yace duka aikin da yayi yana bibiyarsa duk lokaci? Ko dai ya kwance kullin ne shiyasa har haka take shirin faruwa”

“Hajiya ki kwantar da hankalinki, idan ma ya kwance aiki wata kila akwai abun da yake bukata ne kamar yadda yayi min, sai ki ba shi karki zo ganin yadda yake min aiki a yanzu, ko jiya sai da ya bani maganin da zan saka a nama yanka tara na bawa Fadeel ya ci, kuma tun kwanan baya da ya fara min aikin nan Wallahi na fara ganin gaske, domin yanzu gidana yake cin abincin dare, na safe kawai yake ci a can shi ma kuma na san ya kusa dainawa, ga maganar auren nan har zumudi yake a yanzu ba kamar da ba”

“Idan kuwa haka ne, ai babu adalci a ciki, bayan ya fada min yanzu babu kowa a zuciyar mijina sai ni, sai kuma ace ya kwance aiki, idan ma wani abun yake so sai ya fada kai tsaye ba sai ya kwance ba”

“Ina ganin zai fi kyau ku yi magana da shi ki ji koma minene, ni kam Wallahi sai sam barka, yanzu har jinsa nake kamar wani dan'uwana”

“Zan yi magana da shi”

“Okay, kamin ki manta minene size Khairy”

“Hajiya zan saka ta turo miki daga baya, yanzu kam bana iya gane komai”

“Kar fa ki saka kanki a damuwa, komai zai warware”

“Ina fatar haka...”

Ta sauke wayar da tunanina kala kala a ranta.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[11/23, 4:50 PM] AMINA KABIR CAPS: *KHADEEJA CANDY*


PAGE 2️⃣4️⃣


Tun da Hurriya ta shige dakinta bata fito ba, har Magariba, bata son Momy tace ta mata wani abun ba daidai ba dan haka ta kebance kanta a dakinta, da dare ma bata ci abincin dare ba saboda bata fito ba, ta inda ta samu sa'a abincin da ta ci na rana be yi saurin narkewa ba, dan haka bata kwana da yunwar rashin cin abincin dare ba. Da asubar fari ta farka ta yi sallah sannan ta dora da karatun kur'ane har sai da rana ta fito sannan ta yi azakar ta hau gadonta ta koma bachi.

Tara da rabi ta sake farkawa, a kasale ta sauka saman gadon ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin bakar atamfa mai ratsin blue. Ta dora dankwalin a kan gado ta zauna gaban madubi ta gyara gashin kanta ta yi farkin dinsa a baya, sannan ta shafa hoto kadan abun da ba al'adarta mai ma dan ya zame mata dole ne take shafawa, amman a yau da yake ranar jumma'a ce ta ji tana bukatar yin kwalliya. Ta dauki turare ta mai kamshi ta fesa, sannan ta dauki man baki zata shafa sai ta tuna karyawa zata yi, hakan ya saka ta mayar ta aje ta koma saman gadonta ta kwanta tana duba agogo dakin dake nuna karfe goma daidai. Sai dai duk da haka bata son fita ta karya a yanzu ba dan bata jin yunwa ba sai dan bata son tsaba dokar Momy, sanin kanta ne Momy bata karyawa da wuri idan ta  fita ta taba abun da Momy ta aje ba tare da Momy ta ci ba bata san iya hukuncin da zai biyo baya, dan haka ta kara minti talatin akai sannan ta fito kanta a sake babu dankwali gashin kanta sai sheki yake. Masu aikin Momy kawai ta samu a falon dayar na kallo dayar kuma na saka turaren wuta.

“Dan Allah Momy ta gama breakfast dinta?”

“Wane breakfast kuma Hurriya breakfast tun yaushe har an wanke komai, na rana ma kadan ya rage a gama”

Hurriya ta ji babu dadi.

“Dan Allah Inna Shatu idan kuka gama abinci ku rika zuba min nawa dabam, ba sai an hade da na gida ba”

“Toh Hurriya”

“Yauwa na gode”

Ta nufi hanyar Kitchen kamin ta karasa ta ji muryar Namra a stairs tana kiranta.

“Me zaki yi a Kitchen Hurriya?”

“Tea zan hada”

“Saboda jindadi ko saboda me?”

“Ban samu breakfast ba, shi ne zan hada tea”

“To ki jira abincin rana ya kusa karasawa ai,
Showing 75001 words to 78000 words out of 215510 words