“Wane zance kake haka? Me yake damunka? Ina ce komai ya wuce ai, me kuma ya sake dawo da zancen mutuwa?, bana son wannan maganar karka sake”
Ya amsa mata kai yana murmushi.
“Ba zan sake ba Ammy”
Ya kwanta a jikinta kamar yadda yake mata a lokacin da suke cikin Kaduna idan yana gida tare da ita, babu ruwansa da girman da yayi kwantawa yake a jikinta yayi ta zuba shagwaba, kamar wani yaro. Kansa ya shafa yana kallonsa ita kam ba zata iya jurar rasa danta ba, zata haka for now domin ta san gaba ba zai dade ba, yadda yake da fushi ma wata kila da kansa zai zo ya fada mata ya saki Hurriya wata rana, domin zuciyarsa ba ko wace mace zata iya zama da shi ba, shi ma ba zai jure wani abun ba. Dan haka zata aje makamanta a gefe ta saka musu ido, gudun kar ta rasa ďanta kuma ya dauke ta a matsayin makiyiyarsa. Wannan ne abun da ta ayyana a ranta.
HAJIYA KALTUME POV.
“Daga min mana Ruma kafar nan ciwo fa take min amman sai ki rika dora min kanki nan kamar baki tausayina, gashi idan ina tafiya kamar zan yi dingishi haka nake yi, ina tunanin Egypt zan tafi a duba min ita, tun da nan sun gagara gane komai”
Ruma ta tashi daga kwancen da take a jikin Hajiya Kaltume ta kalli Khairy dake zaune tana gyara akafaitar.
“Yau ke da kanki kike gyara kafarki?”
“To ya zan yi? Ni tsoron fita nake yanzu, mutane za su fara kallonka saboda video nan da ya fita wata kila ma har a nuna ka ace ita ce”
Khairy ta fada kamar zata yi kuka. Hajiya Kaltume ta ce.
“Ke daina damar da kanki, abun ne dai kin riga min yi da kin yi shawara da ni da ba zaki aikata ba, ku yara ne ba ku san bandar kasa ba, sai ku rika gaggawa kuna son aikata abun da zai kaiku ya baro, gashi nan duk kin bi kin rame, kin tsallawa a madadin ita aka yi ma ta shiga damuwa gashi nan ma shirye shiyen aurenta kawai ake yi, ni damuwa ke damuwa abu ya taru yayi mana yawa, ni na rasa ina ma zan saka kaina na ji sanyi”
Hawaye ya zubo a idon Khairy.
“Da na san haka abun nan zai zama Wallahi ba zan aikata ba, kuma Wallahi ba ni na yada hotunan ba, ni dai kawai na nasa barazanar zan yada ne, shi ne yayi min shairi yace ni na aikata, gashi ya fadi zancen fyaden nan kowa ya ji, na muzanta Hajiya na ji kunyar duniya”
“Ba ke kadai ba, abun ya shafi kowa ai, da murna nake da Hurriya ce ta janyo sai gashi reshe ya juye da mujiya, ga abokiyar taya ni yakin tana can babu lafiya, ni na rasa ma ina zan kama, abubuwa sun tsaya min cak...! Ina tunanin shiryawa zan yi na tafi gurin Yaya Altine...”
Bata rufe zancen ba Alhaji Musa ya turo kofar falon ya shigo da sallamar fuska kuma babu annuri. Hajiya ta amsa Khairy ta sauke kai kasa tana jin kunyar hada ido da kanen mahaifin nata, ruma kuma ta gyara zamanta tana masa sannu da zuwa sai ya amsa yana zaunawa.
“Yauwa... Sannu dai Hajiya barka da gida”
Hajiya Kaltume dake jin kamar ya zo yayi mata albishir ne na ganin ya daidaita tsakaninta da Appa ta amsa masa tana murmushin karfin hali.
“Lafiya Kalau Alhaji Musa ya yaran?”
“Alhamdulillahi...”
“Maa Sha Allah...”
Sai kuma shiru ya biyo baya tun bayan da Hajiya Kaltume ta yi magana ta karshe. Khairy ta daga kai kadan ta kalleshi ta ga ita yake kallo sai gabanta ya fadi, ta mike tsaye zata bar falon ya katse shirunsu ta hanyar dakatar da ita.
“Zauna Ummulkhar maganar ai duk a kanki ne... Wato Hajiya dazun ni da Yaya mun tafi gidansu Hajiya Iyami, to ni ina daga waje saboda na dan ba su guri ne su gana, sai gashi ya fito yana fada min iyayen yaron nan ne suke son ganinsa....”
Daki daki Alhaji Musa ya jera musu abun da ya faru har zuwa karshe.
“A takaice dai yanzu shi yaron yace baya ciki idan ta samu wani ta yi aurenta”
Khairy ta fashe da kuka mai karfi daman ta saka ran haka, ganin yadda yaki ya daga wayarta tun daga lokacin da abun ya faru har zuwa yau da aiko musu da mummunan sako, Ruma ma kallon Khairy take cike da tausayinta domin ta san abubuwan za su mata yawa ne. Fasa auren na Khairy da aka yi ba daga hankalin Hajiya Kaltume ya jefata a tunani ba kamar jin cewar Alhaji Musa ya bawa Appa da Amma guri domin su gana sai ta ji kamar an watsa mata garwashi a zuciya.
‘Su gana kamar yaya? Daman ganawa suke a yanzu? Ko da yake ga zahiri tana ganin shirye shiyen auren Hurriya da ake sai dai ta ji labari yadda aka yi ko za'ayi a gurin ďanta Yasir idan ta shinshini gulma, be bawa Momy ta yi komai ba ita da take karkashinsa a yanzu balle kuma Ita da igiyar aure ta raba, yanzu hankalin Appa ya koma gurin Iyami kenan? Gashi har da zuwa da kanensa ko dai auren zai maida? Tun da yanzu ta samu lafiya kamar yadda ďanta ya fada mata tun kwanakin baya? Ita kam abubuwa sun ribchabe mata a yanzu komai ya shige mata hudu...’
Bata gama sakar zuci ba Alhaji Musa ya kira.
“Hajiya kin fahimce zancen nawa?”
Sai ta kalleshi kamar wata yar marainiya idonta na cika da hawaye, ta rasa laifin me ta yi abubuwa suka zo mata a haka.
“Na fahimta Alhaji Musa, to me zan ce kaddarori ne gasu nan sun rufe mu..”
“Shiyasa aka ce idan zaka gina ramen mugunta ka gina gajere, yanzu gashi garin yi ma yar'uwarki sharri kin kunyata kanki kin kunyatata kin bata sunan gidanku, ina amfanin haka?”
Hajiya Kaltume ta dafe kanta.
“Yara ne sai ka rasa gane me ke cin zuciyarsu batsa tsayawa su yi tunani”
A nan ya samu zaren zancen ya rufe ta nasa fadan yana karanta mata inda yake ganin abubuwan da yake yi ma yaran ba daidai ba ne.
“Komai dai aka yi uwa ake dorawa laifi, to na ji Allah ya yaye mana”
Ya tashi ya fice daga falon ba tare da sallama ba.
“Yanzu ni Hajiya Fatee zata yi wannan cin fuskar, ashe ko mutuwa na yi ita din ba mai rufa asirin yaya ba ne? Har zata kyale Fadeel ya aiko wai ya fasa aurenki? Ita Hurriya ba gata nan makauniya ba amman a haka da siraicinta da komai ta samu dan manya mutane ya aureta?”
Ruma ta share hawayenta ta ce
“Hajiya Saboda Hurriya bata aikata ba ne aka yi nata sheri aka ce ta yi, shiyasa Allah yayi mata wannan sakamakon, daman sakamakon masu hakuri mai girma ne, shiyasa yake da kyau mu kiyayi iyakokin Allah domin ba za mu iya jurar radadin ukubar sa ba, gashi yanzu tun ba ayi nisa ba ta fara ganin illar abun da ta aikata”
“Ke dalla can rufe mim baki, tun kamin a haife ki na san wannan! Tashi ki ba ni guri, daman ke da Yasir haka kuke kamar ba ni na haife ku ba”
Ta lalabo wayarta dake hannun kujera ta shiga kiran Hajiya Fatee....
Fadeel ya gyara mata fillon dake bayanta ta jingina da fillon tana runtse ido, ta cije baki alamar ba karamin ciwo take ji ba.
“Wayarki ce take ringing a miko miki?”
Ta daga mishi kai, sai ya tashi ya nufi gurin da wayar take ya dauko ya miko mata.
“Hajiya ce take kira”
Hajiya Fatee ta karbi wayar ta duba ta aje domin ba ta da kalaman wanke kanta a gurin aminiyarta a yanzu, ita ma ta kanta take.
“Wata kila ta kira tayi maganar auren da na ce na yanje ne”
“Shi ne ma, da dai ka yi hakuri Fadeel ka rumgume kaddara kamar yadda mijin Hurriya ya rumguma”
“Hajiya ko na auri yarinyar nan ba zan samu aminci da ita ba, daman can ba sonta nake ba saboda ke na nake son na aureta shi na dan kin matsa, kuma yanzu kowa ya ga abun da ya faru babu wanda zai so ta zama uwar yayansa fa, indai zata iya aikawa yar'uwarta haka ina da sauran mutane ko abokiyar zama? Amma Hurriya kaddara ce ta fada mata, ni Wallahi da wannan din ma be aureta zan iya aurenta yarinyar tana da kirki ai”
Hajiya Fatee ta sauke ajiyar zuciya ya hade yawu.
“Yanzu dawowa zaka yi da Afrah kenan?”
“Haka nake tunani Hajiya saboda akwai yara a tsakaninmu, kuma daman bata min komai ba haka nan kawai na turata gida ban san me ya zo kaina ba, yarinyar nan tana min biyayya sosai ke ma kuma tana miki kawai dai kin dauki karan tsana kin dora mata ne Hajiya”
“Tana yi fa, tana min biyayya gwargwadon hali, gashi nan ai na koma da ciwo, daman wanda be gode Rahamar Allah ba zai gode azabarsa...”
Ta karashe zancen da kuka.
“Wannan kuma wata jarabawa ce ta Allah Hajiya, wannan ciwon ai ba san minene ba ciki ya fara kumbura kuma kin ce ba ki son aje asibiti, gashi tun da muka dawo ciwon zuciya be barki ba, ga cikin nan naki tsoro yake ba ni, idan na ce zan tafi asibiti kuma ki ce ba haka ba, a nan gida kowa duk wanda ya zo ba hadin kai kike ba su ba kuma basa gane komai”
“Zan tafi ba yanzu ba, Fadeel lokacin da zaka kai ni asibitin zai zo, yanzu na hausa nake son gwadawa ina tunanin aikin jinnu ne, akwai inda Murja zata karbo min magani na fara sha”
“Toh Allah ya sauwake”
Ya fada tare da damuwa sannan ya tashi ya fice falon zuwa gurin kanwarsa Zainab da ta zo daga Neja take jinyar mahaifiyarta. Sai da ya fice sannan Hajiya Fatee ta daga kiran Hajiya Kaltume dake shigowa a karo na barkatai.
“Wallahi Hajiya Fatee kin ba ni mamaki, yanzu kina raye zaki bari ďanki ya juya ma Khairy baya? Kina raye Fadeel zai watsa min kasa ado? Ashe ke ba mai rike yarana ba ne ko da bana raye?”
“Na ce kar yayi Hajiya Kaltume amman ya nuna min ba zai iya auren Khairy ba, kuma kanen mahaifinsa ma da suka nema masa auren da kansu suka kira shi suka bashi shawarar ya canja wata yarinyar”
“Amman ai kin isa da shi, sai ki nuna masa hakan ba daidai ba ne kuma ki ce ba zaki yarda ya fasa auren nan ba, shi be san kaddara ba?”
“Ke kaddara kika sani ne? Na ce ke kaddara kika sani ne da zaki rufe ni da fada kamar uwata? Ki bar ni na ji da damuwata mana, kin san halin da nake ciki amman saboda rashin tausayi irin naki kike neman kara min wani”
Hajiya Kaltume ta nuna kanta.
“Ni ce marar tausayi yau Hajiya Fatee?”
“Idan ba rashin tausayi ba, miye na kira kina daga min hankali? Kaddara kowa ai rumgumarta yake, ke yarda kika yi da kaddarar auren Iyami? Na ce yarda kika yi? Gashi nan kin janyo min saboda ke zan mutu na barwa yaya abun kunya, saboda ke komai ya lalace min, babu kalar karyar da ban yi ba akan cikin nan, kuma duk sanadinki ne komai ya faru, ke da kike kishiyar ba a miki fyade ba sai ni yar rakiya, kuma ke Malam be miki komai ba sai ni kujera mai dadi zama, yanzu wai har kina da karfin halin kira kina min masifa, to ba zai aureta ba, kuma Wallahi ďana ya fi karfinki magani ba zai masa komai ko bana raye, karki sake kirana da wani zancen Khairy aure an fasa ba za'ayi ba, idan cilastawa gaskiya ki cilasta Alhaji Haruna ya maida ke mana, ko ki cilasta Yasir ya nemo mai aurenta a cikin abokansa sai ni da kika raina...”
Ta kashe wayar tana kuka sosai kamar ranta zai fita.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[1/2, 6:58 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
5️⃣3️⃣
“Wai yau ni zan kira Hajiya Fatee ta zage ni ta kashe min waya? Yau ni duniya ta yi ma zafi haka? Ashe rana zata zo da aminiya ta zata watsa min kasa a ido? Ta fada min ban yarda da kaddara ba? Yau ni Kaltume duniya ta yi ma daurin hohon goro?”
Rike take da bakinta tana maganar mamaki fal a zuciyarta, taya abubuwa suka zame mata haka? Ga saki ga auren Hurriya ga auren tata ƴar an fasa yau kuma ta kira kawarta ta fada mata magana marar dadi. Ruma ta kalleta kamar zata ce wani abu sai dai kuma ta san mahaifiyarta ba mace ce mai fahimta ba, dan haka bata yi kokarin furta komai ba, Khairy sai rusar kuka take kamar wanda aka yi ma mutuwa.! Ta sani ba wani son Fadeel take ba amman tana hangosa a wani tsani da zata hau ta tsira daga kallon da mutane suke mata kuma ta samu mafaka da zata fake daga zagi da bakinciki zuciya. Sai dai kuma a yanzu ta rasa wannan saboda Fadeel ya juya mata baya...!
“Da ma mutuwa na yi da ma ban kawo yau ba, rayuwa ta juya min Hajiya, yau ni ce aka fasa aurena, ni ce Appa yake fushi da ni, yau ni ce video suke yawo jama'a na tsine min, yau ni ce nake tsoron shiga cikin mutane, ni ma ni ce na mutu ba Salma ba?”
Hajiya Kaltume ta kalli yarta cike da tausayinta ta ce.
“Ki daina yi ma kanki fatan mutuwa Khairy fasa aure ba shi ne karshen duniya ba, ita kanta da hotunanta suka yadu a duniya ba ta rasa mai aurenta ba balle kuma ke da magana kawai aka fada akanki kuma ba kowa ya ga hotonki ba, abubuwa za su daidai ta Khairy ki daina fatan mutuwa dan Allah”
“Ba zaki gane yadda nake ji ba Hajiya, ba zaki gane ba shiyasa kike fadar hakan...!”
Hajiya ta daka mata tsawa kamar yadda take mata magana da daga murya saboda rashin kunya da bakinciki.
“Ni kin san yadda nake ji ne? Kin san abun da yake raina? Ke aurenki kadai aka fasa fa amman kike wannan haukar ni kuwa mahaifinku sakina yayi saki biyu, yanzu kuma me kika gama jin Alhaji Musa ya fada? Cewar daga gidansu Iyami suke alamar zata iya dawowa a koda yaushe kenan! Ga auren Hurriya babu wani shirye shirye da ake da ni, sannan mahaifinku ya juya muku baya, da yanzu shi zai shigo ya sanar mana fasa auren nan yana fada yana karawa amman ki duba ko shigowa nan baya son yi, rabuwata da mahaifinku da cewar babu ruwansa da yarana dawaimiyarku akaina zata dawo dan kasuwanci da na fara karyewa zai yi abun da na tara ya kare, kuma bakincikin bana tare da mahaifinku ba zai bar ni na cigaba da rayuwa ba, amman a haka dauriya nake so nake na rarrasheki kokarin kwantar miki da hankali nake”
Khairy ta tashi ta shige dakinta da gudu tana kuka, Hajiya Kaltume kuka take sosai kamar yadda kukanta ya saka yar autarta Ruma kuka.
“Hajiya ko zaki ma su Baba Musa da Baba Lawal a bawa Appa hakuri”
“Babu wanda zan yi ma magana Ruma, babu wanda be san abun da ake ciki ba amman ba su yi kokarin sasantawa ba, ba zan kai kukana a gurin kowa ba, Wallahi hakki ba zai taba barin iyami ba ba zata taba ganin daidai a rayuwarta ba”
Ruma ta dubi Mahaifiyarta cikin rashin fahimta inda uwarta ta dora.
“Hajiya Amma bata gidan nan fa, taya wannan issues din ya zama laifinta? Wata kila ma dai kisan da kika saka ka yi ma Hamad ne nake bibiyanmu...!”
Hajiya Kaltume ta kalleta ta sauri ta buge mata baki.
“Kul.... Kul... Kul... Kika sake furta magana irin wannan, kul... Zuciyarki ta sake raya miki wani abu makamancin wannan... Ni ban kashe Hamad ba ban kuma ce a kashe shi ba, su suka aikata a karan kanku dan haka babu zancen bibiyar hakki a nan, Iyami kuma ita ce silar komai tun farko dole na fadi haka, ke yarinya ce ba zaki gane abun da nake nufi ba, kuma ba zan bawa Alhaji Hakuri ba, ba kuma zan nemi kowa ya shiga maganar aurenmu ba, da yardar Allah sai Alhaji ya kawo kansa yana kuka yana rokon na yafe masa”
Ruma ta kalli Hajiya Kaltume domin ta gama fahimtar inda ta dosa, ta san kuma wanda yayi nisa baya jin kira mahaifiyarta ba zata taba fahimtarta a yanzu ba, dan haka ta share hawayenta ta tashi ta bi bayan yar'uwarta.
“Duk yadda za'ayi na gyara al'amurrana sai na yi sai dai na rasa komai
Showing 186001 words to 189000 words out of 215510 words
“Wane irin magana ne wannan?”
Ta daka mishi tsawa.

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63 Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72