yi wannan karatun ba, gashi kuma saboda shi ka cika burinka tare da kai aka yi aikin idon da ka taba fada min cewar ka yi yar'uwarka alkawari”
Hurriya ta dago ga kalli Hamad ta mika masa hannayenta so take ya taba ta a karo na biyu ta ji idan da gaske dan'uwanta ne. Hamad ya kama hannun yar'uwarsa da ya fi Marmari fiye da kowa ya rike. Sai ta fashe da sabon kuka.
“Ni dai ina so ko da waninka ne aka kawo min a matsayin kai, zan karba kai ne kadai ka rage min farincikina ya cika, ni kadai ce na yarda baka mutu ba Hamad, amman duk haka ganinsa nake kamar ba gaske ba”
“Tun a ranar da da Captain yace min za'ayi wani aiki da yake son ayi tare da ni amman ba zai kawo aikin ba sai a lokacin da zan fara koyon aikin a wannan asibitin sai na kagara na ga haka, da na zo na ga fuskarki sai na ji kamar wata rayuwa ce ta same ni da ba zahiri ba, kuma ya hana ni magana a ranar har sai yau... Kuka nake Captain ya cutar da ni”
“Ban cutar da kowa ba a nan, ni kawai taimako na yi, kuma ba zan amsawa kowa tambaya ba sai a gaban iyaye”
Captain ya fadawa Hamad a tsawace, kamin ya rika fuskar Hurriya ya share mata hawayenta.
“Ya isa haka, yau aka bude idonki i thought hakan zai saka farinciki ba kuka ba, karki janyo min wata matsala please”
Ya rumgumeta a kirjinsa, ita kuma kamar ya karawa kukanta fetir haka ta ji sai ta kara fashewa da kukan sosai.
“Ina son na tafi gida ina son na ga iyayena idan suna raye...”
“Hakan ba zai yiyu ba, sai an dauki permission daga makarantarka hakan kuma ba zai yiyu ba sai da hujja, dole ka kwantar da hankali kamin mu yi tunanin abun da zai fi”
“Ba zan kwantar da hankali ba, 8na bukatar ganin Amma, babu ruwanka da rayuwata you lie to me azzalumi kawai, ka kira min Amma zan yi magana da ita”
Captain ya daka masa tsawa a karo na biyu.
“Ba zaka bar garin nan ba sai da izini, kuma ba zan kirata ba...! And control yourself Hamad na hadeye ka a zuciya Wallahi”
Yadda Hamad din yake ta fada ya kara tabbatarwa da Hurriya lallai dan'uwanta sai dai akwai abun da ita da shi ba su sani ba, waya kawo shi a garin nan? Meya saka ce ya mutu? Ta ya ya hadu da Captain? Kuma me yasa Captain ya boye mata gskiyar har zuwa yau? Ta dago kai ta kalleshi tana jin idonta yana wani dauri kamar zai like.
“Kira min Amma...”
“Toh zan kirata, amman yanzu ki min hakuri mu tafi masaukinmu kim ga Mama Rukayya da Momy Ikilima ma suna waje suna jiranmu! Sai mu magana a masauki zai fi kin ji”
Magana yake mata ta siffar rarashi yana shafa gashinta, sai ta girgiza masa kai ta lake kafadarta daya.
“Aa dan Allah ka kira Amma”
“Okay”
Ya ciro wayarsa ya danna number surukarsa ya aikata mata da kira. Wayar bata dade tana ringing ba Amma ta dauka tana sallama sai da ya amsa sallamar ya gaisa da ita sannan ya mikawa Hurriya wayar. Hurriya ta karba tana kuka
“Hello Amma...”
Hamad yayi saurin kara kunnensa a jikin wayar yana sauraren muryar mahaifiyarsa sai ya fashe da kuka.
“Lafiya Hurriya idon be bude bane?”
“Amma wata gaskiya zan fada miki mai kama da karya, Amma Hamad ne yana raye yana tsaye a gefena yanzu na yi magana da shi kuka ma yake yi Amma Hamad dinki yana raye...”
Amma ta yi shiru for some seconds sannan ta amsa.
“To ba Jamal wayar...”
“Amma baki yarda da ni ba?”
“Na yarda ba shi wayar..”
Hurriya ta mikawa Captain wayar sai Hamad yayi karaf ya karbe ya kara a kunnensa.
“Amma... Amma.. Amma...”
Nan ma Amma bata ce komai ba, domin ba muryar Captain ta ji ba, kuma ba muryar wanda ta sani ba ne, sai dai hankalinta ya tashi sosai tana jin kamar yarta ta samu matsala ne.
“Amma ki ce wani abu dan Allah Hamad ne...”
“Ba Hamad ba dai.... Ko waye kai dan Allah ka bawa Jamal wayar...”
Hamad ya dauke wayar a kunnesa ya mikawa Captain sannan ya nufi kofa zai fice hawaye na sauko masa, Hurriya ta yi saurin sakowa daga kan gadon tana kiranshi.
“Dan Allah karka tafi, dan Allah karka tafi Hamad inda da gaske kai din ne karka tafi dan Allah...”
“Jamal matarka bata da lafiya ne?”
Amma ta tambaya Captain ya sauke ajiyar zuciya.
“Lafiyarta kalau, kuma an yi aikin idon ya bude Alhamdulillah an yi nasara”
“To me yasa take min zan cen Hamad? Ko idonta ya fara ganin fatalwa ne yanzu kuma...”
“Da gaske ne Amma Hamad yana raye, akwai abun da baku sani ba, akwai abun da na boye muku sai a yanxu nake jin lokaci yayi da ya kamata ku san komai...”
“Kai ma baka da hankali ko Jamal? Dana Hamad ya dade da rasuwa...”
“Be rasu ba Amma Hamad yana raye....”
Ta katse wayar ji take kamar wasa suke son yi da hankalinta ko kuma dukansu ba su da lafiya ko kuma dai yana biyewa matarsa ne wata kila ta tabu.
“Ka ga abun da ka janyo ko? Ka kashe kowa a gurina kuma ka kashe a gurinsu...”
“Ban kasheka a gurinsu ba, ba ni na yi wannan ba step mother dinka ce ka tuna wannan? Ban fadawa kowa kana raye ko a mace ba, amman kai na fada maka suna a mace ne saboda ka rayu...”
Captain na kai aya kiran Appa ya shigo wayar Captain cikin girmamawa da mutuntawa ya amsa kiran.
“Lafiya kalau ya matarka?”
“Alhamdulillah an yi aiki cikin nasara Appa ido ya bude...”
“Alhamdulillah maa sha Allah ina take bata wayar..”
A madadin ta karba sai Hamad ya sake karbewa.
“Appa...”
Appa yayi shiru kamin ya amsa.
“Na'am waye wannan...”
“Hamad ne Appa Hamad ne...”
“Hamad na mu?”
“Eh Wallahi ni ne Appa wallahi ni ne ba fatalwa ba ne ban mutu ba”
“Me ka fada min na yarda kai ne? A ina ka hadu da Hurriya? Ina ka san Captain...”
“Ina karkashin kulawarsa ne Appa, ina tare da Captain kusan ko da yaushe, amman ku ya fada min kun mutu...”
“To ba shi wayar zan yi magana da shi....”
Hamad ya aje wayar akan gado domin bakin cikin abun da Captain yayi masa ba zai barshi ya sake hada hannu da shi ba. Captain ya kalli wayar sannan ya danne zuciyarsa domin ya san babba baya zama kamar yaro, kuma dole zai yi ma Hamad uzuri na halin da yake ciki a yanzu.
“Hello Appa..”
Iyami ce ta kirani tana kuka tana fada min wata magana da bata kama hankalinta ba, ni ma kuma bata kama nawa hankalin ba, shiyasa na kiraka sai kuma na ji makamancin abun da take fada min me yake faruwa.
“Labari ne mai tsawo Appa ba zai yiyu a waya ba, dole sai an zauna hakan kuma ba zai yiyu ba sai an dauki permission daga makarantarsu Hamad gudun lalacewar karatunsa”
“Hamad kake kira fa Captain...”
“Hamad Appa Hamad yana raye... Amman yanzu kamin uzuri zan tafi masaukinmu idan Hurriya ta natsu zamu yi magana... Zan kiraka na fada maka yadda komai zai gudana.”
Hankali namiji be taba zama iri daya da na mace ba hakan ya saka Appa ya saurare shi.
“Toh ina jira..”
Captain ya kashe wayar ya kalli Hurriya dake kallon Hamad kamar zata cinye shi tana hawaye.
“Kukan nan ya isa haka, ni da na san haka abun zai zama ba zan bayyana miki shi ba”
“Ni kuma sai na yi ta zama har zuwa lokacin da zaka bayyana ni bayan na ga yar'uwarta?”
Hamad ya fada a tsawace, Captain ko gefe da yake be kalla ba ya kama matarsa.
“Mu tafi Mama Rukayya suna reception suna jiranmu, daga can zan yi clearing kudin asibitin sai mu tafi masauki mu yi magana hakan yayi miki...”
Ta daga mishi kai.
“Hamad zai tafi tare da mu ko?”
Ya daga mata kai yana shafa fuskarta hawayen dake zubar mata yake jinsu har a ransa.
“Toh...”
Ya dauki mayafinta ya rufe mata kai sannan ya kama hannunta suka fito daga dakin.
NIGERIA....
Appa ya saka hularsa yana amsawa Yasir.
“Eh can zan tafi gurin Iyami na yi magana da ita, saboda na ji tana ta kuka abun ne da daure kai na rasa gane kan gadon labarin..”
“Ni ma na ji abun wani iri, maybe akwai abun da Captain din yake boyewa ko kuma Hurriya ta samu matsala ne? Yake biye mata...”
Yasir ya fada with confused.
“Amman na ji wata murya yake cewa Appa ni ne Hamad ne har da rantsuwa ni abun ya daure min kai... Shiyasa nake son na tafi gurin mahaifiyarta”
“Okay Aappa Allah ya tsare”
“Amin sai na dawo...”
A tare suka fito bangaren Appa ya shiga motarsa, Yasir kuma na nufi bangaren Hajiya Kaltume domin labarta musu halin da ake ciki. Shigarsa bangaren ta yi daidai ta cire mayafin da Hajiya Kaltume take tana sauke gajiya. Tana kallon fuskar danta ta san ba kalau ba, domin mamaki ne da daure kai a fuskarsa sai dai bata ce masa komai ba har sai da ya zauna.
“Lafiya.?”
“Wani abu ne mai daure kai Hajiya... Yanzu muna tare da Appa a gida muna duba kasafin kudin da suka shiga da fita na wannan watan bangaren Motocin Appa, sai Amma ta kira tana kuka wai Hurriya ta kirata da number Captain tana mata zancen Hamad, Appa ma be gane kan maganar ba sai da ya kira Captain din da kanshi sai wani ya karba yana cewa shi ne Hamad, Appa dai yayi magana da yaron kamin Captain ya karba ya ce idan sun koma masauki zai kira Appa su yi magana kuma shi Captain din ya fada ma Appa cewar Hamad ne, but labari mai dadi dai idon Hurriya ya bude”
“Hamad......!”
Hajiya Kaltume ta fada da karfi kamar zata rusa dakin.
“Karya ne ba dai Hamad ba, Hamad din da ya mutu? Hamad din da aka kashe? Yaushe zai rayu? Wane irin Hamad kuma? Wannan karya ne, an riga da an kashe Hamad ba zai dawo ba, wannan wai duk na minene Yasir? Duk na ganin bayana ne? Duk na son a ga karshena ne? An hana ni zaman lafiya da mijina, an fitine ni har sai da Alhaji ya sake ni, yanzu kuma zai maida Iyami, idon Hurriya ya bude, ta yi aure ta auri babban mutum, sannan n fasa auren tawa yar, mahaifinku ya juya min baya, na gagara neman lafiyata na gagara zaman dakina kullum bana gurin wannan boka bana gurin wannan malamin, amman har yanzu shiru, yanzu fa na dawo daga wani gurin, sai kuma ka zo min da labarin wai Hamad yana raye? Yaron sa aka kashe tuntuni? Yaushe zai rayu? Hamad ya mutu wani ne dai ya dawo yana son a kai ni gidan yari, burin Iyami ya cika... Shikenan tawa ta kare”
Cikin rashin fahimta da mamaki Yasir yake kallon mahaifiyarsa, be da dalilin daga hankalinta saboda Hamad ya dawo ba har da zancen gidan yare, above all ta gama fada masa tana bin malamai da bokaye.
“Ta ina dawowar Hamad zata saka a kaiki gidan yari idan ma gaskiya ne?”
Tana tambayarta ne a daidai lokacin da Ruma da Khairy suka sauko domin har dakunansu suna jin muryar Hajiya Kaltume saboda yadda take daga murya.
“Saboda ni na saka aka sace Hamad... Ni na saka aka dauke shi tare da Umm Ruman, Hurriya na ce su dauka sai aka yi kuskure aka dauki Hamad... Amman ban ce su kashe shi ba, Danja ne ya aikata hakan ba da umarnina ba..?”
“Waye kuma Danja?”
“Wanda na saka ya sace Hamad, a gidan Hajiya Fatee na hadu da shi.. Ni na saka shi aikin saboda ina son a karbe kudin Iyami ne da Alhaji ya bata lokacin da ya sake ta ya damka mata kudi da gida ga sarkar zinari ya siyawa Hurriya wannan ya saka na aikata... Iyami ta hana ni jindadi ta hana ni zaman lafiya ta saka na rasa komai daga zuwa aiki ta aure min miji sanadinta na rasa Salma ni na kashe yata da kaina... Iyami na ce a halbe sai aka halbe Salma ta cikin madunin Tsafi nan ma ni na saka mai aikin Nafisa ta kai ni duk saboda Iyami ne... Shikenan na lalace rayuwa ta ta kare...”
Kama ganin yadda take maganar yana murza jikinta zaka san bata a cikin hayyacinta. Khairy da Yasir ne mamaki ya cika su, Ruma kam kuka ta fashe da shi domin ta san asalin gaskiyar.
“Hajiya... Wannan maganar ba a cikin hayyacinki kike yinsu ba...”
Yasir ya fada tana tasowa daga inda yake zaune ya dafa mahaifiyarsa ta kai kasa tana kokarin cire riga.
“Ni na saka aka dauke shi Wallahi... Ni na ce a sace Hurriya su kuma suka dauke shi ina ta murna asirina yana rufe sai kuma ka ce min wai Hamad ya dawo? Gidan yari zan tafi kenan? Gidan yari zani Yasir?”
Ya rike rigarta yana kuka, ya dago ya kalli kenansa.
“Akwai wanda ya san wani abu a cikinku...”
Cikin kuka Ruma ta ce.
“Eh gaskiya ta fada, ita ta saka aka sace Hamad, kuma Hamad da ni duk mun ji muryarta lokacin da take magana da su, Har yake cewa Hajiya me na yi kika ce a kawo mu nan? Idan na dawo sai na fadawa Appa, sai ta fara fada tana cewa ya ji muryarta zai tona mata asiri, bayan ta kashe wayar ne suka buga mishi karfe akai kan ya fashe yana ta jini, Hamad yana ta ihu yana kiran sunan mutane har da ni, suka fitar da shi daga dakin suka bar ni daga nan ban san me ya faru ba...”
“Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'u ײ”
Yasir ya furta har sau biyu sannan ya mike tsaye ya rike bakinsa. Khairy kuma ta fadi zaune tana kuka domin bata taba jin wannan ba sai yau. Hajiya Kaltume kuma bata fasa tonawa kanta asirin abun da ta yi ba, tana ta firgar rigar jikinta da zanenta.
[1/5, 9:04 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
5️⃣8️⃣
*A duk lokacin da nake littafi sai an tambaye ni minene POV saboda ina saka shi a duka books dina, POV yana nufin POINT OF VIEW. idan wata ta sake tambayata sai na cire mata hakorin gaba 🥴*
HAJIYA FATEE POV
“Hajiya jikin ne dai?”
Fadeel ya tambaya yana taba jikinta cike da damuwa Hajiya Fatee ya dago ta dubi danta, cikin bakinciki da nadama ta ce.
“Ko da jikinki bana bukatar tafiya asibiti yanzu Fadeel, ku bar ni na yi abun kunyana a nan idan ma kasheshi saku yi ku kashe, bayan na tafi”
Afrah ta girgiza kai.
“Haba Hajiya ki daina fadar hakan, abun da ya same ki kaddara ce daga Allah, kowa da yadda Allah ya rubuta masa kaddararsa, zai iya samun kowa, Allah ya tsare mu da kashe abun da kika haifa, ko me kika aikata muna son rayuwarki kuma ina sonki a haka saboda kw mahaifiyar Fadeel ce ina son miJina ba zan taba tsanar mahaifiyarsa ba”
“Na yi abun kunya, sanar matar ďana ina ta ganin kamar kin tare shi daga gareni ashe sheidan ne yake ta min gizo da sake sake, dubi yadda na zama na janyo muku abun kunya”
Fadeel ya sauke ajiyar zuciya, tabbas idan har duniya ta san halin da mahaifiyarsa take ciki zai ji kunya ba karami ba, daga lokacin da na gane gaskiyar abun da take boye masa har zuwa lokacin da ta bayyana masa gaskiyar komai da komai be sake walwala ba, ba sake kwantawa bachi ya dauke shi ba, be sake kallon wani abu yayi dariya ba gaba daya farinciki ya kaurace masa.
“Zan tafi na bar muku abun kunya Fadeel, dan Allah ka yafe min kuma ka kula da yar'uwarta, ka fahimtar da ita ban kai aikata aka min cikin nan ba sai dan kaddara ta biyo ta nan”
“Karki damu Hajiya, Zainab zata dauko kuma zaki samu sauki ki tashi da yardar Allah, ko ma miya faru mu dai muna son rayuwarki”
“Mutuwata tafi rayuwata Fadeel bana fatan rayuwa idan ma na haihu lafiya, idan kuma ban haihu ba, kun huta karku fadawa kowa abun da uwarku ta yi, Afrah ki yafe min dan Alla..”
“Na yafe miki Hajiya Wallahi ni ban rike da komai ba”
“Allah ya muku albarka... Tashi ka tafi gurin aikinka, ga matarka nan ai ta isa tana kula da ni”
“Toh Hajiya”
Ya mike tsaye ya fice daga dakin. Kusan tun da gaskiyar cikin ta bayyana shi da yar'uwarsa suka ji cewar ba kari ba ne, cikin shege ne Hajiya Fatee ta yi Zainab ta bar gidan ta koma gidan kanen mahaifinsu kuma ta kasa komawa gidan mijinta saboda uwarta ta yi abun kunya, sai kulawar Hajiya Fatee ta dawo karkashin Matar Fadeel wato Afrah wanda ya maida ita gidansa bayan fasa auren Khairy da yayi daman ba shi da burin auren kawai yana biyayya ga cilastawar mahaifiyarsa ne. Matar da take zagi take cewa ta mallake mata ďa matar da saboda ita wannan mummunan kaddara ta same ta yau ita ce take kula da komai nata take mata komai kamar yarta, kusan a gidan ta tare ita da yaranta saboda kula da uwar mijinta.
A ranar da Hajiya Fatee ta yi ma danta da matarsa wasiya kuma ta roki gafararsu a ranar ta yi musu bankwana, a ranar ita da danta ba su kwana duniya ba, cikin dare nakudar data shekara ashirin da wani abu rabon da ta yi kalarta ta taso mata, idan Fadeel yayi yunkurin kiran wani ko kaita asibiti sai ta hana tana fadin ya barta ta mutu cikin gidanta domin ta san cikin nan ba zai barta ba, daga karshe da ya ga wahalar ta yi yawa sai ya dauko mota kamin ya saka ta ciki ta ce ga garinku ita da danta. Rufin asirin da take rokon Allah yayi mata na mutuwa cikin gida ta samu wannan an karba mata, kamin safe fuskar Fadeel da Afrah ta kumbura sosai saboda kuka. Haka Afrah ta rinka rusa kuka kamar uwarta ce ta mutu tana matukar jin tausayin mijinta da ya rasa uwa da kuma tausayin Hajiya Fateen. Sai yafiyar Allah take roka mata, wani kukan ba tashi a gidan ba sai da yarta Zainab ta zo ta fara nadamar
Showing 201001 words to 204000 words out of 215510 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68 Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72