Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[1/2, 7:00 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
5️⃣5️⃣
*Shafin nan sadaukarwa ce gareki UMMU FAISAK my albasa my tomato my pepper, jikar Iya kawar Amo da Hajiya Kaltume. Alherin Allah ya kai miki har a gadon baccinki*
*** *** ***
_Wallahi baka taba yin farinciki a rayuwarka ba Adam kamar yadda ni ma ba zan yi ba, ba zaka taba ganin haske ba, sai na bayyanama duniya abun da kake boyewa sai na hana ko wace mace aurenka, baka da zabin rayuwa daga yanzu har zuwa mutuwarka, idan ban auru ba ba zaka auru ba Adam..._
Yana gama karanta sakon ya dan dago ya kalli mutanen dake falon sannan ya maida kansa yayi mata reply.
_Mu zuba zuwa Khairy, ni da za a ga shege, kuma ni sai na auri macen da nake so nake ra'ayi amman ke ba zaki taba auren mijin da kike so ba, saboda kowa ya san me na yi miki kuma idan kika matsa asirin ba nawa kadai zai bayyana ba har da naki domin ke ma yanzu ya shafe ki kin ga sai mu yi jinya tare_
Yana bata amsa ya aje wayar ya cigaba da kallon tv rai a bace, Salim ya taso daga inda yake zaune ya nufo Adam.
“Ara min wayarka zan sauke app wayata ya ki sauke shi”
Without second though Adam ya mikawa Salim wayar ya tashi ya hanyar dakinsa. Salim ya zauna a gurin da Adam ya tashi yana.
“Akwai pin a jiki”
Adam ya dawo ya cire masa pin sin sannan ya shige dakinsa. Kai tsaye a Salim ya shiga whatsapp dinsa yana duba recent chat ne ga wani abun daga hankali ko bata rai ba, yana kokarin fitowa daga whatsapp din sakon Khairy ya sake shigo ta SMS.
“Mu zuba zuwa ni da kai shege ka fasa Adam”
Ya haka ya samu bin sakon ya karanta har wadda ta aiko masa da farko. Salim ya dan dago da mamaki kamin ya sake maida kansa, wannan ne karo na biyu da ya sake ganin wani abu da ya daga masa hankali a wayar Adam. Da kansa ya shiga dakinsa ya mika masa wayarsa sannan ya fito harabar gidan zuciyarsa na zafi. Domin ganin yakw yanzu ya zama loser shi ya fara son Hurriya amman abokinsa yayi masa overtaking duk kuwa da irin yadda aka bata sunan Hurriya, it pain him yadda abokinsa yayi betrayed dinsa. Number Namra ya kira domin sauke mata haushin dake ransa.
Namra ta share hawayenta sannan ta kalli wayar dake gefenta ta dauka.
“Hello”
“Burinku ya cika? Kun nani Hurriya kun bawa wani?”
“Wane irin magana ne wannan? Wa yake murna da wannan auren ne? Kai kanka ka san Hurriya bata dace da Captain”
“Bata dace da shi ba ta aure shi? Na yi zaton ma kina can gurin raka amarya ai”
“Zan aje wayar idan baka da wata magana mai muhimmanci, ina cikin damuwa ba zan yarda ka kara min wata ba”
“Baki da matsala daman saboda ba ke kika rasa ba”
“Idan har da gaske kake kana kaunarta me ya hana ka fitowa ka aureta kamar yadda Captain yayi?”
“Captain ne silar lalata komai, a duk lokacin da na yi masa maganar Hurriya ture min maganar yake, saboda yana min kallon wani dan iska, daga baya na fahimci sonta yake shiyasa kansa yake yi ma campaign”
“To kai miyasa baka kirkiri taka Jam'iyar ka yi takara da shi ba? Da ka yi hakan da auren nan yanzu be faru ba”
“Ban yi tunanin zai yi jihadin aurenta a haka ba, na dauka zai hakura da ita ni da shi duk mu rasa...kuma na yi tunanin da gaske din ta aikata sai bayan da gaskiya ta bayyana abun ya zo min a wani iri”
“Ya fika kaunarta shiyasa ta tari yakin gaba da gaba, gashi kuma daga karshe gaskiya ta bayyana cewar bata aikata ba, ka ga ya ci riba, kark sake kirana Salim”
“Ni zaki ce kar na sake kiranki?”
“Ubana ne kai? Alakar dake tsakanina da kai saboda Hurriya ne, yanzu kuma ta yi aure dan haka babu sauran wata alaka tsakaninmu, gaskiya Captain ya fada kana wasa da zuciyar mata shiyasa ko wace macen ka gani sai na nuna kana sonta, da farko ni daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, ai kara da ya hana ka aurenta hakan zai koya maka darasi”
“Ko kuma ya koya masa darasi ba, idan har aboki zai iya cin amanar abokinsa na kurciya ya karbe masa yarinyar da yake sannan ya datse alakarsu har ya nuna shi da bindiga kuma yayi masa barazanar rasa aikinsa me kike tunani? Dole shi ma hakki zai bibiye shi”
Namr taja tsaki ta yanke kiran. Daga ita har Salim Momy Hajiya Kaltume da kuma Khairy kwanan bakinciki suka yi a ranar duk saboda bikin Hurriya.
WASHE GARI...
Misalin karfe goma na safe Hurriya na kwace jikin mijinta yana gyara mata baki bayan sun gama cin abinci da breakfast da aka aiko musu daga Family house din su Captain.
“Tashi mu zagaya na fada miki yadda gidanki da dakinki yake”
Ta dan dago kamar bata son motsi, cikin siffar shagwaba da son kuka ta ce.
“Ni dai da ka bar shi, ba amfani tun da ba gani zan yi ba”
“Zaki taba ai, kuma idan ya bude zaki gani”
“Wannan idon abu ne mai wahala ya bude, Appa ya kashe kudi mai yawa akan ido, kullum kara rufewa yake ba budewa ba, yanzu kuma ya rufe gaba daya”
Ya dora gemunsa a saman kanta yana taba fuskarta.
“Zai bude Hurriya zai bude da yardar Allah... Ina ta shirye shirye akwai abun da nake jira ina son nan da dan lokaci zamu tafi Ethiopia akwai wani asibiti ido mai kyau zan saka a dubaki a can zasu Miki aiki kuma ina da yakinin Allah ba zai kunyata mu idonki zai bude”
Ta yi shiru tana sauraren yadda yake gangarawa da hannunsa zuwa gurin da bata tsammani.
“Idan kuma idon be budewa gaba daya fa?”
“Zai bude, ki daina fadar hakan ki yarda zai bude”
Ta zabura ta tashi zaune daidai da sauri ta ture hannunsa. Sai yayi murmushi ya cige baki ya kashe mata ido kamar tana kallonsa.
“Iya daga kafar na yau ne kawai, you better get ready for tonight...”
Ya rada mata a kunne sannan ya mikar da ita tsaye tana bata fuska kamar zata yi kuka, gaba daya sai ta ji tausayin kanta ya kamata.
“Kin tuna ranar da kike fada min na yarda dake na ce miki na yarda baki aikata ba, amman ban tabbatar ba, to anjima zan tabbatar”
Ji ta yi kamar kasa ta bude ta shige ciki tsabar kunya a yanzu ta fahimci inda zancensa ya dora tun a karon farko da yace mata zai tabbatar. Dariya yayi ya rumgume ta ta baya tana takawa a hankali har suka fita dakin. Kitchen suka fara yana fada mata abubuwan dake ciki wadanda aka siya gurin Khadeeja Candy, sannan suka fito suka shiga dayan dakin nan ma ya fada mata abun da ke ciki idan ya fada mata sai ya kai hannunta ta taba ta ji yadda yake da haka har suka fito harabar gidan nan ma ya rika fada mata yadda tsarinsa yake.
“Amman wata zata zauna da ni ko? Idan ka fita”
“Saboda me?”
“Zan ji tsoro ni kadai ai, kuma ban zan iya komai ba ai”
“Baki bukatar yin komai for now, kuma idan zan fita zan tafi dake gida gurin Ammy ki zauna idan zan dawo sai na dauko ki kamin su bar garin nan”
“Wani garin za su koma”
“Kaduna suke zama, ni ma ai da zarar lokacin da aka ba ni a nan ya kare can zan koma a zamu zauna, amman kamin mu zauna can sai mun fara tafiya ayi miki aikin idonki tukuna...”
“Da ace idon zai bude, kai nake son na fara gani Captain...”
Ya kwantar da kansa a kafadarta.
“Ba zan ce Aa ba, amman maybe zan zama mutum na biyu da zaki fara gani saboda iyaye suna raye”
Ta juyo ta saka hannayenta ta lalaba inda saitin fuskarsa yake ta rike fuskar.
“Kana karfafa min guiwa, kai kake fara yarda da ni kamin kowa, na jihadin lokacin da ka yarda ban aikata ba, kuma idan a rufe ido da kunnenka daga jin duk wani abun da za a fada a kaina, har ranar yau ta kasance, duk wata macen mai dacen aure a bayana take a yau...”
Ta yi dage ya duka mata da fuskarsa ta sumbanci shi a gurin hancinsa.
“We deserve each other shiyasa Allah ya hada mu a tare kuma ya tare duk wani abu da zai shiga zuciyata ya bata zamanmu har yau ta kasance”
Hawaye ya sauko mata.
“Ina kaunarka Yaya”
“Yayanki yana gida wannan mijinki ne, My Baby Pearl...”
Ya kwantar da ita a kirjinsa yana shafa bayanta. Cikin gidan suka dawo duk yadda ta so ta ki be barta ba sai da ya taimaka mata ta yi wanka, sannan shi ma yayi suka fito ita da shi suna daure da tawul daya, ita tana ta gabansa shi kuma yayi mata rumfa a baya, har gaban madubin dakin suka tsaya ya cire tawul din sai ta yi saurin juyawa ta rike shi dariya ya sa domin shi ma babu tufafin a jikinsa.
“Idan ba ni ba wa za a kawo w tsaleliyar budurwa kamar wannan kuma ya kyaleta”
Ta saka mishi haka, hakan ya saka shi dauko mata tufafinta ya taimaka ta saka sannan ya shafe mata jikinta da mai kyau ya saka nasa tufafin ya dauki hoda da kansa ya shafa mata ya saka mata man lebe ya saka mata turare sannan wasan ya canja salo. Be kyaleta ba sai da ya ga lokaci na tafiya tukuna ya shiga ya sake tsabtace kansa ya fito ya sumbance ta.
“Zan tafi na gaishe da su Ammy na san yanzu wasu za su fara zuwa ganin amarya kar ayi gulma da ni”
“Ni kadai zaka bari?”
Ya saka bakinsa cikin nata ya sake sumbanta tukuna ya sake ta.
“Mutane za su shigo yanzu ai”
Ya amsa ta sannan ya nufi wayarsa dake kara ya dauka ya duba mai kiran.
“Nafi'u...”
Ya furta sannan ya amsa kiran.
“Hello oga barka da safiya ya aikin”
“Sorry na kira ban sani ba ko kana cikin wani aiki”
“Go ahead”
“Hotunan nan ne aka sake yadawa tsakanin jiya da dare zuwa yau, kuma mun bibiye account din sai kuma samu an goge na alhani amman mun samu information din dayan da ya saka hotunan umarni kawai muke jira mu kama shi a Bincike ina ya samu hotunan”
“Irin wannan ma baku bukatar umarni na Nafi'u just do it ina yaron yake...”
“Kaduna... Ka yi duk yadda za'ayi ku kama shi please kuma ku bincike shi da kyau”
“Okay Sir”
Ya sauke wayar cike da mamakin mai kokarin hana su jindadin rayuwa a yanzu.
“Me ya faru?”
Ta tambaya domin jin yadda yake amsa wayar da kuma yadda yayi shiru bayan amsa wayar ya tabbatar mata da ba kalau. Kallonta yayi sai yayi murmushi ya nufo inda take ya saka zauna.
“Babu komai Babyna wani abun ne da ya shafi aikina”
“Ka tabbata?”
“In Shaa Allah”
Ya sumbanci gefen fuskarta yana kallonta wani irin sonta da son kwanciyar hankalinta ke fisgarsa. Be bar gidan ba sai da mutane suka fara zuwa daga yan'uwansa da na Appa da na Amma musamman wadanda ba garin suke ba.
CAPTAIN POV.
Ammy ta aje tea cup din dake hannunta tana kallon danta.
“To waye kuma da wannan aiki?”
“Za mu gane, kuma ko waye sai ya dandana kudarsa”
“Ko yar'uwarta ce?”
“Bana tunanin haka, saboda asirinta ya tonu, kuma bana jin Adam ne domin ya fada cewar ba shi ba ne ko a yanzu!”
“Ko ma dai waye ya kamata a hukunta shi a yanzu, domin ya wuce gona da iri kuma ba kai kadai ne da fadan ba har da na mu domin idan hotunan suka sake yaduwa har da mu za a taba”
“Mutum daya nake zargi.”
“Waye”
“Bana son fada, amman gaskiya zata yi halinta, and if i find out shi din ne, zan masa ba dadi”
“Zan yi magana da aka daddynka san fada masa a zafafa bincike ta bangarensa ma ko zamu samu wani abu, and ka kula da gidanka domin wanda zai iya yi ma Iyalinka haka zai iya neman rayuwarka ko ta matarka ko ma ya sake yin wani abun da zai zubar da kimarka, gashi yarinyar ba gani take ba be ma kamata a barta ita kadai a gidan ba”
“Na barta ne just for today and tomorrow saboda masu zuwa, amman bayan nan idan zan fita nan zan kawo ta sai idan na dawo sai na dauke ta mu wuce”
“A madadin haka ka rika kaita a gidansu mana ko kuma ka dauki mai kula da ita tun da ka ji ka gani zaka iya”
Ya dan yi murmushi.
“Nan din ma gidansu ne ai saboda gidanmu ne, Ammy kina son yarinyar nan fa ki daina boyewa”
“Au boyewa nake ma?”
“Idan ba shi ba, miye na danka mata key mota? Duk soyayya ta dake fa baki taba siye min mota ba, amman ita gashi kin siya mata sabuwa, sannan kika bada kayan bikonta”
“To ya zan yi? Na yi abun da ya kamata uwa ta yi ne, ba ni da wani zabin ne”
Yayi dariya sosai yana kallon mahaifiyarsa cike da farinciki.
“Ni dai tarewar ne a haka be min dadi ba, da dai ka hakura har idon ya bude da abun ya fi armashi gaskiya”
“A yanzu din ma babu abun da ya ragu Ammy, ina farinciki da matata kuma ba wai bana son duba idonta din ne a yanzu ba, akwai planning din da nake, ina son nan da two years....”
“What...! Baka da hankali ashe..!”
Ya dan bata fuska.
“Ammy ni?”
“Taya zaka auro yar mutane ka ajeta har nan da two yrs sannan a duba idonta? Wane irin plan ne wannan? Hummm uhmm you better not, karka kuskura gwada wannan, iyayenta ba za su yarda ba ai”
“Karkashin ikona take yanzu”
“Haka ake aure a garinku? Dan tana karkashin ikonka iyayenta ba za su yi mata abun da ya dace ba, gaskiya be kyauta ka ajeta a haka har two yrs ba ai sai ta wahala kara dai a gwada idan ma ba a dace ba ansa ba a dace ba ne amman ba wai haka nan kawai ba”
Yayi murmushi ya taso daga inda yake zaune ya zauna kusa da uwarsa.
“Kin gani ko Ammy kina son yarinyar nan Wallahi gashi kin damu da ita...”
“Ni shawara ce kawai nake baka, idan ta ni ne ka barta har sai nan da shekara goma ma babu abun da ya dame ni”
Side hug yayi mata yana dariya.
“Ammyna i love you so much...”
Ta yi murmushi kadan tana tabe baki.
“Ka ji da shi, ku yaran zamani sai dai abi yadda kuke so ba yadda iyaye suke so ba”
Ya sake yin dariya ya mike tsaye ya fice daga dakin, haka ya fito harabar gidan ya gaisa da mutane cousin dinsa mata suna ta tsokanarsa. Sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Nafi'u ya aika masa da wata number.
“So nake ka yi min hacking din account din da yake jikin number nan, ka duba duk wani abu da ke cikin chat din maybe zamu samu wani abu da muke nema, ka yi duk yadda zak iya ka duba komai na account din”
“Okay ranka ya dade”
**** **** ****
A WEEK da bikin auren Hurriya Amma da Gwaggo suka tafi Ummara tafiyarsu da kwana biyu Momy ta tafi tare da babbar ƴar Appa wato Sapna Momy kuma ta biyawa yarta Namra suka tafi tare duk kuwa da kasancewar ta taba zuwa ba sau daya ko biyu ba. Hakan kuma ba karamin taba ran Hajiya Kaltume yayi ba, a nan ta fara shige shigenta ko zata samu kamin Momy da Amma su dawo Appa ya daura aure da ita kuma ya juyawa Momy da Amma baya, amman yi take kamar tana shuka dusa, ga ciwon kafa ya sakata gaba amman ta kasa tsayawa ta maida hankali gurin neman lafiyarta kokarinta na yadda zata koma karkashin inuwar mijinta ne a yanzu. Bata da wani buri da ya wuce wannan kuma duk inda zata saka kafa ta gabatar da bukatarta za su karbi kudinta su ce za a mata aiki mai kyau kuma Appa zai juyo ya nemata haka ma aurensa da Amma ba za a maida ba. Babu abun da ke daga mata hankali a ciwon kafarta nan kamar yadda idan an bincika ake ce mata babu wani rauni ko wani ciwo a gurin amman kuma ita tana jin azabar ciwon da ko tafiya bata iya yi daidai yanzu. Tana shan wahala sosai gurin hawa da saukowa a stairs har bata son yin ko daya sai idan ya zame mata dole. Yau ma kamar kullum ta sauko tana ta wai wai wai da kafar har ta zauna. Yasir yayi saurin yanke wayar da yake ganin Hajiya ya aje wayar gefe
Showing 195001 words to 198000 words out of 215510 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66 Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72