yana ciki dan haka ta nufi gefen gadonsa ta zauna kusa da wayarsa, karanbani ya saka ta dauki wayarsa tana tabawa ta kawo haske amman bata bude ba sai an saka password, kamar zata cinye wayar haka ta kurawa screen din wayar ido tana kallon hoton Mama Rukayya dake jikin screen din ta yi masifar kyau ta sha makeup din zamani.

“Ke me kike yi da wayata?”

Ta dago da sauri ta dubi kofar bandakin sai kuma ta yi murmushi.

“Yayana hoton Mama Rukky ne a wayarka”

“To ya aka yi?”

“Ba ayi komai ba”

“Me ya kawo ki dakina? Gulma kika zo yi min?”

Ta washe hakora gaba daya ta manta da me kawo ta ma.

“Get out”

Ta mike tsaye tana dariya zata fice, sannan ta tuna dalilinta na zuwa ya juyo da ta dawo.

“Yauwa Yayana na tuna abun da ya kawo ni ma”

“Minene?”

“Gilashina da yake hannunka wanda na baka ajiya, tun da dadewa ka tuna?”

“Na tuna, ya aka yi?”

“Daya zaka ba ni please”

“Why”

“Zan saka ne”

“Wannan da yake idonki fa?”

“Shi ai shi ba wanda Appa ya siya min ba ne”

“Waya siya miki”

“Ni dai ka ba ni zan yi amfani da daya”

“Wallahi ba duba tun a lokacin da aka taba fasa miki gialshin na bincika ko'ina ban ganshi ba, ban san ya aka yi ya bata ba”

“Yaya ka sake dubawa idan ka gani ka ba ni”

“Okay”

“Toh, Yaya yau ka je gurin Mama Rukayya? Ko zaka je?”

Ya watsa mata wata kalar harara.

“Hurriya yaushe na fara wasa da ke?”

Ta fice da sauri tana dariya, a yanzu kam ta tabbatar Yayanta yana son kanwar mahaifiyarta, idan haka kuma ya kasance zata fi kowa farincikin domin dukansu tana sonsu. Bangaren Momy ta dawo ta shiga dakinta ta yi wanka sannan ta saka kayan bachi ta yi addu'a ta yi karatun suratul milk sannan ta kwanta.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[11/30, 9:45 PM] AMINA KABIR CAPS: *KHADIJA CANDY*


*3️⃣0️⃣*




HAJIYA KALTUME POV.

Kai ta daga sama tana karewa dakin kallo wanda ya kasance na kasa ne ko'ina sai kulli kullin yawu da aka sarkafa, sai mayan allunan karfe da madubai ga kuma ruwa a kasko da karya ga kwalabe ta ko'ina kana shiga gurin zaka fahimci wane irin mutum ne, balle kuma hancin mutum yayi arba da gawurtaccen kamshi turaren aljannu dake tashi har wani juyin kai yake sakawa. Cikin hikima Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana jin dadi, ganin take kamar ciwonta ya warke ma gaba daya. Yana shigowa cikin dakin ta gyara zamanta ta matsa baya tana kallonsa.

“Malam an shigo”

Ya zauna yana fadin.

“Da dai zaki kirani da Dan masani, ko na gangare zai fi Hajiya”

“Toh dan masani, sannu da kokari”

“Yauwa sannu dai Hajiya”

“Ya gidan ya iyali da komai”

“Komai lafiya kalau, Hajiya”

Ta dauko katon madubi ya dora a cinyarsa.

“Daman... ”

Zata fara bayani ya daga mata hannu, ya dangwalo yawun bakinsa yayi rubutu da shi, sannan ya kalleta ya girgiza kai ya maida idonsa a gurin madubin, ya fi karfin minti ashirin a haka sannan ya dago ya kalleta ya ce.

“Kanwar Kulu ta kawo ki nan ko?”

“Eh haka ne, can gidansu na fara zuwa sannan aka kawo ni nan”

“Na gani ai, kuma kin zo nan ne saboda mijinki zai kara aure, gashi kuma ya canja miki, ga danki yana son auren yar kishiyarki da ta fita, kuma kina fargabar kar ciwon da kika aika mata ya karya ta tashi mijinki ya ce zai dawo da ita, sannan kina yawan faduwa har ki ji ciwo a kafa har kika tsoron ko an miki ture ne”

Ta daga masa kai.

“Hakkun babu musu a maganarka take”

Yayi dariya.

“An fada mana komai ai”

“Haka nake so, yanzu so nake a hana ďana auren yar iskar yarinyar, kuma a hana mijina aure, sannan a dauke hankalinsa daga gurin kowa sai ni, idan da hali ma wannan matar da take tare da shi abokiyar zamana ita ma a koreta, sannan bana son mijina ya dawo da Iyami, kuma ciwon kafar nan ba turo min aka yi? Ni har tsoron faduwar nake ji kar naje na fada a inda be kamata ba kafar ta cire ko ta karye na shiga uku”

“Duk za'ayi Hajiya, amman sai kin daure kuma kin shirya domin ni bana aiki da wasa, ciwon kafarki kuma babu wani ture babu aljannu babu komai, daga Allah ne”

“Toh Alhamdulillah yanzu hankali ya dan kwanta, kuma daman ni ai haka nake so, yanzu miye abun yi?”

Ya aje madubin dake jikinsa gefe daya ya dubeta.

“Ina mai tabbatar miki da wani abu, tabbas mijinki zai dawo da abokiyar zamanki da kike tsoron ya dawo da ita, matukar baki tashi tsaye ba”

Hajiya Kaltume ta dora hannu a kai tana jin wani karin tashin hankali na kusantota.

“Shiyasa na zo gurinka ai, dan Allah a hana ya maido da ita”

“Za'a iya hakan ne kadai idan zaki iya daukar nauyin jini, amman muddin matar nan tana raye babu makawa sai ta dawo gidanki”

“Dan masani me kake nufi kenan?”

“Ni matsala ta bana boyo kuma duk abun da na gani ina fadawa mutum gaskiya, amman ina aiki na gaskiya, abun da ya fi kawai mu yi ma matar nan halbin kasko domin matukar tana raye Wallahi ina mai tabbatar miki mijinki sai ya sake zaman aure da ita”

“Dan masani babu wata hanyar sai kisa? Kar abun yayi min yawa?”

Yayi dariya.

“Ashe baki shirya kenan kika zo, baki shirya mallakar mijinki ba, kuma baki shirya hana kishiyarki dawawa ba, gaskiya ban ga wata mafita a nan ba bayan wannan, domin madubin nan baya kara kuma ya nuna min akwai sauran zama a tsakaninsu”

Hajiya Kaltume ta yi shiru na wasu dakiku sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

“To maganar mallakar Alhaji fa? Da kuma hana dana aure”

“Za a yi miki na mallaka zaki mallake Alhaji ki koma kamar uwarsa, karki damu da wannan amman fa zaki zuba kudi”

“Kamar nawa Malam?”

“A kalla za a kashe 50k”

Ta yi murmushi 50k abu ne mai sauki idan dai zata samu biyan bukata.

“50k ma matsala ba ne, zan bada fiye da haka ma, amman a duba idan akwai wani aiki mai sauki da ba sai kisa ba sai ayi”

“Bari kiji na fada miki, matar nan ma tana nan ta fara tashi domin wanda kika saka yayi miki aikin nan ya fara karya aikin, tabbas kuwa zata dawo cikin gidanki, kuma dawowarta yana nufin fitarki”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, fita ta kuma? Ai ni shi ne tashin hankalina, ta zauna ma ya na kare balle ita tana ciki ni ina waje?”

Gaba daya sai hankalinta ya tashi ta ji wani gumi na keto mata.

“Amman kana ganin idan an aikata aikin zai yiyu?”

“Me zai hana? Saboda hasarin halbin kasko idan be sameta zai iya fadawa akan jininta shakiki kamar danta ko yarta”

Hajiya Kaltume ta taba hannu biyu.

“Shikenan ma daman yarta ta isheni a duniyar nan, a aikata mata kawai ka ga aikata mata zai saka su ji tsoro su hana Yasir Rukayya, kuma zan huta nima hankali ya kwanta, amman ina lafiya idan aka ce zata dawo kuma ni na fita”

“Idan aka yi haka babu ita babu mijinki har abada”

“Toh yanzu yaushe za'ayi aikin”

“A yanzu ma idan kika bada kudi, sai a dauko kayan hadi a kira aljannu, cikin dare za'ayi halbi kin ga ruwan da yake cikin kaskoncan? A cikinsa za a halba idan aka gabatar da aiki aka yi halbi da dare kamin safe sako ya isar mata, amman fa tabbas idan be sameta ba zai fada akan yarta balle ma ita muke fatan ya samu”

“Akan samu irin haka ne, ayi ma mutum aiki kuma ya zama be fada kansa ba?”

“Ban taba samun irin haka ba, gaskiya wani lokacin ma akan fada ma mutum biyu da uwa da jininta, kawai ina tabbatar miki karfin aikin ne”

“Zan biya kudin, zan bada 200k gaba daya, ina son a hana dana aure kuma a janyo hankalin mijina a gareni sannan kuma a hana shi aure wacan yarinyar da yake hasashen aure a yi musu farraqu”

Dan masani na jin 200k ya ji ransa yayi wasai kudin wata gona da wani gidan kauye har da fili ma.

“Hajiya ni ko ina tabbatar miki, kuma na miki alkawari tsakanin yau zuwa gobe zaki tashi da labari mai dadi akan kishiyarki, na mallaka kuma akwai aikin da zan hana sai ki aiko ko kuma ki zo da kanki jibi ki karba, da zarar ya ci an gama da shi, a game da auren da zai kara kuma wannan ni an san aikin da zan yi, mai irin sunan yarinyar ma ba zai sake sha'awa ba”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi ya jinjina kai

“Haka nake so, so nake na mallake komai a gidan nan, ya zama be ganin kowa sai ni da Yayana, Hurriya ma ina son a cire masa ita a rai kwatakwata”

Ta saka hannunta a jaka ta dauko 200k ta aje masa.

“Idan bukata ta biya zan baka ninkin wannan, ni dai burina ayi aiki yayi”

“Aiki kam ya gama, tashi ki yi tafiyarki”

“Na Gode dan masani”

Ta mike tsaye tana jin kamar an yaye mata damuwarta gaba daya, tunanin kar ta daukarwa kanta hakki da yawa duk ya kau saboda ta ji ance zata fiya Iyami ta dawo. Bata bar garin ba sai da ta sake komawa gidansu Kulu ta yi musu alheri kowa ta bishi da 1k sannan ta shiga motarta direbanta ya kama hanya, suna mata addu'a bayan sun gama murna da jindadin kyautar da ta yi musu. Ta isa gida cikin farinciki kamar wata wanda ta aikin jihadi, tana shiga bangarenta ta yi wanka ta yi sallah sannan ta fito ta shiga Kitchen da taimakon Salma da Khairy suka gama girkin dare, sannan ta koma dakinta su kuma zauna a falo. Bayan gama sallah magariba ne yar yayarta ta shigo gidan daman ta kan zo jefi jefi idan an yi hutu. Hajiya Kaltume ta yi murna da zuwanta sosai daman suka sha hira a dakin kamin ta shiga da kayanta a dakin Khairy. Misalin karfe tara daidai Hajiya ta dauki abinci mijinta ta shiga bangarensada kanta ta kai masa, so take ta dawo da al'adarta ta kai masa abinci da kanta saboda ta samu damar tsare shi kuma ta tabbatar ya ci abincin idan ya saka maganin da bokanta dan masani zai bata. Sai dai gaba daya ya lura da yanayinta be sauko ba daga tsabanin da suka samu jiya, har yanzu fuska a daure take kuma tun bayan da ta gaishe shi ya amsa be sake ce mata komai ba, ita kuma bata yi yunkurin wani abu ba, har sai da ya fara cin abinci, sannan ta dawo gabansa ta zauna ta zuba masa ruwa.

“Wai Alhaji yanzu saboda dan tsabanin da muka samu jiya shi ne kake ta wannan fushin? Yaushe rabon da ka yi fushi da ni haka?”

Yayi kamar be ji ta ba ya cigaba da cin abincinsa.

“Ayi hakuri ranka ya dade a gafarci Kaltume, ban san abun zai zama haka ba, idan aure ne ayi ta yi kai zaka zauna da su ba ni ba, ita m Iyami Allah ya bata lafiya ka dawo da ita ta rike yaranta”

“Ameen”

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, sai ta ji kamar ta dauki murfin kular da yake cin abinci ta buga masa a kai saboda bakincikin amsawa da yayi da amin. Sai dai tuna abun da ta taka ya saka ta yi murmushi ta kawar da duk wani bacin rai daga zuciyarta... Sai da ya gama cin abinci ya sha ruwa sannan Namra ta kwankwasa kofar karamin falon nasa.

“Waye?”

Hajiya ya tambaya tana harara kofar a zatonta ma yar makiyiyarta ce.

“Shigo”

Appa ya amsa mata da kansa yana gyara, ta turo kofar falon ta shigo, ganin Hajiya Kaltume ya saka ta ji babu dadi domin tana son magana da Appanta private ne. Ta zauna kusa Hajiya Kaltume dake kallonta tana raya abubuwan da za su faru nan da yan kwanaki kadan idan ta mallake mijinta.

“Appa barka da dare”

“Barka dai Namra, ya kike?”

“Lafiya Kalau Appa”

Sai ta yi shiru.

“Akwai wata matsala ne?”

Ta dan kalli Hajiya Kaltume ta kalli Appa.

“Daman ina son magana da kai ne, amman zan bari sai da safe sai mu yi maganar kamin ka fita”

“Privacy kike so?”

Ta daga kai. Appa ya kalli Hajiya Kaltume kai tsaye yace.

“Kaltume mu shiga bedroom mu bar miki nan ko kuma ke zaki shiga”

Hajiya Kaltume ta dubi Appa da mamaki sai dai bata ce komai ba ta yi murmushi.

“Aa bari ni na shiga, Namra a kebe lafiya”

Ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi bedroom din Appa ta shiga ta rufe dakin, a nan ta samu damar yin kwafa ta cize baki.

“Nan da dan lokaci komai zai canja, ke ma idan baki yi hankali ba sai kin fi Hurriya shiga matsala ke da uwarki duk sai kun zama abun tausayi”

Ta zauna kan sofa tana matsa kafarta dake dake gwada son yi mata ciwo kamar jiya.

“Wai ni Alhaji zai cewa na ba shi guri zai yi magana da Namra, da dane ko fadar haka da ta yi ai sai yayi mata fada, amman ba komai duk a tafin hannuna zaku dawo sai na juya ku kamar waina”

Sai da Appa ya gama maganar da zai yi da yarsa sannan ya shigo dakin cikin wani yanayi na rashin yabo da fallasa ya zauna bakin gadonsa yana kasa wayar hannunsa, kamin ya dago ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.

“Tun shekaranjiya nake wani tunani”

“Kamar na me Alhaji?”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“Ina tunanin yaran nan ne da Iyami ta haifa, twins Hamid da little Hamad, tun da aka haifi yaran nan ban taba zuwa dubasu ba a matsayina an ubansu”

Hajiya Kaltume ta ji gabanta ya fadi irin faduwar da be taba yi ba, yau Appa ya fadi abun da bata kawo ran faruwar sa a nan kusa ba, lallai a yanzu ta yarda Malamin da yayi mata aikin ya fara karya shi saboda yana son ta ba shi kudi mai yawa ya mallaketa kamar yadda ya mallake Hajiya Fateee da bata ma son a fadi laifinsa. Babu wani abin da zata yi a yanzu da ya wuce ta boye komaia kasan zuciyarta, dan haka ta yi karfin halin murmushin da za a iya cewa ya zame mata na dole ne kawai ta ce.

“Toh Alhaji ai za a iya zuwa ka dubasu ai yaranka ne, ni zan iya raka ma sai mu tafi tare, ba wani abu ba ne”

Wannan karon ajiyar zuciyar da Appa ya sauke mai nauyi ce sosai.

“Ina jin nauyin hakan, saboda na juyawa yaran nan baya na ci amanarsu ba tare da sun min komai ba, ina tunanin zan dauko su amman me zan ce idan zan aika a dauko su? Kai....”

Ya busar da iskar data cika masa baki sannan ya tattare girarsa guri daya yana jin rashin dadin a abun da yayi ma yaran nasa da suka kasance jininsa.

“To ai ba abin kunya ba ne Alhaji, yaranka ne kuma idan acan baya ka yi kurkure yanzu ai gyara kake kokarin yi, karka dauki wannan a matsayin matsala dan Allah shirya ka je ka duba su ko kuma a dauko maka su”

“Ban gama yanke shawara ba tukuna, zan yi tunanin abun da ya kamata na yi”

Ya amsa mata sannan ya aje wayar ya hau saman gadon, ita kuma ta juyar da fuskarsa a dayan gefen tana kashe ido wani bakin kishi na cizon zuciyarta, sai a yanzu take jin ta yi daidai ta ya yarda a ayi ma Iyami halbin kasko domin bata san da wane irin zata sake dawowa gidan ta ba idan Appa ya maida ita gidan.
Kamin safiya ta waye Hajiya Kaltume ta matso saboda bokanta ya fada mata cewar idan yayi aikin da dare ya halba mata kamin safe bukata ta biya kuma ita ta yarda da hakan, sai da ta baro bangaren Appa ta dawo bangarenta take cin ciwon rashin karbo number wayar dan masani da bata yi ba, da yanzu sai ta tambaye shi ya samu yin aikin ko be samu ba. Kitchen din ta ta shiga ita da Ruma suna shrya abun karyawa, Khairy da Salma kam ana can wata duniya ana sharar bachi musamman ma Khairy da bata kwantawa sai ta sha abun da zai jefata a bachi mai nisa. Ita ma Ruma bata saba tashi da wuri ba saboda uwarsu bata koya musu tashin da wuri, sai dai yau ta tashi saboda tana da lecture 8 na safe. Suna shirya abun karyawar Hajiya Kaltume na tunanin kalaman da Dan masani yayi mata, kuma yanzu ta fara tabbatar da haka, domin a yanzu ta lura idan ta yarda ta fadi wata maganar akan Iyami Appa zai iya bata nata rai, balle kuma ace ya dawo, wata kila milkin da zata yi a yanzu zai fi an can baya, gashi yanzu ta haifi yara biyu maza ita kuma tana da
Showing 102001 words to 105000 words out of 215510 words