knocked sannan ya tura dakin ya shiga to his greatest surprise sai ya samu wasu ne a dakin ba ita ba, gaishe yayi sannan yayi musu bayanin wanda yake nema.

“Wata kila an sallame ta mu ma yau aka kawo mu”

“Okay Allah ya bada lafiya”

Ya juyo ya fito, har ya koma motarsa kiran Salim da na wasu new numbers be fasa shigowa wayarsa, sai da ya shiga motarsa sannan ya kashe wayar gaba daya. Daga asibiti ya nufi gidansu Momy, ya san ganin Hurriya a wannan daren a bangaren Momy ba abu ne mai sauki a gareshi ba, bayan sun samu misunderstanding a dazun, and idan tace kar ya shiga dakin Hurriya ko kar a kirata be isa ya ce ba haka ba. Sai dai ya san karfin son ganin Hurriya saboda duba lafiyarta ba zai bar shi ya huta ba har sai ya ganta, shi be ma ga dalilin dauketa daga asibitin a yanzu ba a dawo da ita gida, ko dai daki aka canja mata, wata zuciyar ta hararo. A kokarinsa na neman amsa ya karfafaf kansa guiwa ya bude motar ya fito yana kallon windows din dakin na Hurriya. Tunawa da bata iya ganin komai a yanzu ya saka shi kara jin tausayinta. Hannayesa ya saka a aljhun wandonsa sannan ya taka ya isa gurin kofar dakin ta Momy ya danna door bell. Namra ta bude kofar falon, ganin Captain ya sakata mamaki sosai domin ta san ba shi da lafiya me zai zo yi a gidan by this time. Ta ja baya tana kallonsa without saying anything kamar ta yi arba da wani bako, Momy dake da remote ta aje remote din tana kallonsa.

“Wata fitinar ce kuma ta taso?”

Yayi murmushi ya sauke kansa kasa.

“Na je asibiti duba Hurriya ban same ta a can ba”

Momy ta dauke kai ta maida gurin Tv kamar bata san abin da ke fitowa daga bakinsa. Namra ta kalli Momy kana ta nufi kujera ta zauna.

“Hurriya bata asibiti if case you didn't know”

Ya maimaita yana kallonsu domin zuciyarsa na raya masa, wani abu akan rashin ganinta be yi ba a yanzu.

“She's not here either”

Ya kalli Namra gabansa na tsananta faduwa.

“Wani abun ya faru? Mahaifinta ya koreta ko kuma yaya?”

“Tana gidan Mahaifiyarta”

“Ina ne?”

Momy ta kalli Namra dake kallonta sannan ta kalli Captain ta amsa masa.

“Ban san gidan ba”

Ya kalleta da kyau sannan yayi murmushi ya ce.

“Zo muje waje ki ji”

Momy ta kalleshi cike da fusata ta ce.

“Babu inda zata je, ku fita waje ka tirsasa mata abun da bata sani ba? Ko kuma ka ce zaka daketa?”

Yayi murmushi

“Sai da safe Momy”

Ya juya ya fice ba tare da ya kara cewa komai ba, Namra ta bishi da kallon mamaki.

“Da ada ne zai yi kamar zai tashi gidan nan saboda bacin rai, amman ji yadda ya fita har murmushi yake”

“Ai dole yayi murmushi mana saboda ya san ya kulla min bakinciki da bacin rai, ba rantsuwa Hurriya zata yi ba ko kur'ane ta hade ba zai aureta ba”

“Amman Momy bata aikata ba fa sheri ne”

“Okay wannan ya wadatar dake kenan kin hakura da shi? Fine”

Momy ta jefar da remote din ta mike tsaye ta nufi hanyar stairs tana jan tsaki. Namra ya bita da kallo kamar na rashin fahimta kamar mamaki.

Ya dade a cikin motar sannan ya yi mata key ya fice daga gidan yana tunanin yadda za'ayi ya samu ganin Hurriya, da farko yana son na duba lafiyarta ne yanzu kuma yana sso sanin halin da take ciki jin cewar tana gurin mahaifiyarta, korarta mahaifinta yayi ko kuma wani abun ne ya faru...! Ya kunna wayarsa ya duba location din da aka turo masa, kamin ya kashe wayar kiran Ammy ya shigo masa amman ya ki ya daga already ya san dalilin kiran nata. Tafiya yayi mai nisa ta kusan barin garin Gusau sannan ya isa Lalan, ya kutsa cikin wata unguwa dake gurin ya shiga can ciki har ya isa gidan. Horn yayi wani soja ya fito rike da bindigarsa ya duba motar Captain ya sauke gilashin motar Soja ya sara masa sannan ya koma da gudu ya rika gate din shi da wani suka bude. Captain ya fito matarsa suka sake sare masa sannan dayan ya ba shi labarin yadda suka dauko Adam abun da ya motsa asibitin gaba daya domin sun tabka rashin mutunci a kokarinsu na cika umarnin shugaban na su.

“Ina yake?”

“Yana ciki gaba daya a firgice yake”

Captain ya wuce gaba suka take masa baya, a yayinda ya isa gurin kofar da aka saka Adam kuma sai dayan ya bude masa ya sare masa. Captain ya shiga dakin da shi kadai ne be da haske a duka dakunan da suke gidan. Sojan ya haska Adam dake zaune a kasa daga shi sai gundun wando idonsa daya a kumbure hancinsa na jini sai nishi yake kamar na mutuwa. Captain ya karasa ya duka a gabansa ya karbi wayar ya haska Adam da kyau sannan ya haska kanshi

“Ka gane ni?”

Adam ya kalleshi da ido daya ya kasa cewa komai, sai Captain ya kama hannunsa da ya rumgume a shimfida a kasa ya mike tsaye ya daga kafarsa zai taka hannun.

“Dan.... Allah.... Dan Allah.... Karka taka karaya ce a jiki dan Allah ka yi hakuri....”

“Na sani ai, ba ni na karya hannun ba? Kuma ga dauri a jiki na gani”

Captain ya kai kafarsa ya taka hannun mai karaya na Adam ya murza, sai da Adam ya kwala wani irin ihu ya kwanta a gurin kamar zai mutu. Captain ya dauke kafarsa ya duka saitin da fuskar Adam take yana kallonsa ya ce.

“Soja be san tausayi ga azzalumi ba Adam, wannan kadan ne daga bangaren aikin mu, na ce a aje min kai a nan na tsawon awa goma, kuma a gana maka azaba kala kala, sai dai ka ci albarka na fito duba Hurriya sai na yanke shawarar kawo maka ziyara”

“Dan Allah ka yi hakuri... Dan Allah ka yafe min.. Ka yi hakuri... Wayyo Allah mutuwa zan yi”

“Mutuwar ai nake son ka yi shiyasa na ce a dauko criminal irinka daga asibiti a kawo ka nan, ka ga babu wanda ya san gurin da kake a yanzu, idan na ga dama zan iya kashe ka a nan, na aje maka bindiga nace tare kake da yan ta'adda, idan na ga dama kuma sai na aje maka bindiga b tare da na kashe ka ba, na ce mum daukoka daga asibiti ne muka kawo ka nan saboda ka nuna mana sauran yan'uwan ta'adancinka, ko a hukunmance babu wanda zai tuhume mu, kaga na lalata maka rayuwa zama gidan kaso kuma ya kama ka, ko da ka fito rayuwa bata da amfani a gurinka”

“Me na maka? Me na maka? Ni fa Adam ne Adam Sarauta”

“Ni kuma Ni kuma Captain Jamal AA Turaki ne, sai yaya? Wannan be ji wuta ba ku gasa min shi da safe zan dawo”

Captain ya mike tsaye, Adam ya yunkuro yana kuka zai rike Captain ya kasa saboda azabar da yake ji a hannunsa.

“Ka yo hakuri dan Allah, me na yi?”

Captain ya juyo ya kai masa duka a baki.

“Mai tsada ka taba, ba ka ce kai dan'iska ba ne? Zan nuna maka na fika zama shege”

“Wallahi Wallahi ban mata komai ba”

Captain ya daga gira daya, sannan ya kunna wayarsa ya saka ta a plane mode, ya shiga camera ya kunna video.

“Me saka ka yi min karya to? Me yasa ka ce min tare kuke haduwa?”

“Na yi hakan ne saboda kar laifin ya shafe ni kadai”

“Ya aka yi hannunka ya kai ga jikinta? Har aka yi muku hotuna?”

“Hotunan an dauke su ne a lokacin da Hurriya takw bachi bata cikin hayyacinta, bata san an yi ba”

“Saboda me?”

“Magani aka saka mata”

“Kai ka saka mata maganin kenan?”

“Ba ni na saka ba, Khairy ta saka mata, ban san yadda aka yi Khairy ta saka maganin ba, ni dai ta kira ni kawai ta ce min na zo gata nan”

“Sai kuma ka zo?”

“Eh saboda mun shirya hakan da ita?”

“Saboda ka lalatawa Hurriya suna?”

“Aa ba dan a bata sunanta ba ne, ni ina son Hurriya ne tun farko, sai dai Khairy ta bata min suna a gurinta da iyayenta shiyasa sai ta ki saurarena, ni kuma na kasa hakura Khairy ce ta kawo shawarar na yi amfani da Hurriya kawai a wuce gurin, ta karbi kudi mai yawa a hannuna saboda ta samonin kan Hurriya, amman ban samu yadda nake so ba, ni kuma na biye mata ne saboda ina ganin kamar wannan ce kadai damar da nake da ita, shiyasa ta hada plan aka zo da Hurriya a gidansu Zuhura ta kira ni tace na zo, ko da na zo har sun cire nata tufafi, ni kwantawa kawai na yi aka yi mana hoto”

“Saboda me ka yi hotunan?”

“Saboda na yi amfani da su na yi ma Hurriyya barazana ta amince da ni, saboda Khairy ba zata iya kawo min ita na yi amfani da ita ba, tana tsoron ace ta yi hanya ayi ma Hurriya Fyade idan asiri ya tonu zata ji kunya”

Captain ya kai masa duka akai kamar wani criminal.

“Ka ji Jarumi yarinya tace bata yinka sai ka koma ta bayan gida kai dole sai ka yi amfani da ita ko? Ashe ma fyade ka tashi yi mata!”

“Saboda na rasa yadda zan yi ne, kuma ya nuna min bata so na kirikiri”

“Me ya hana ka? Ashe baka kai dan'iska ba”

“Babu yadda zan yi na samu kan Hurriya ne saboda bata saurare balle na fita da ita ko na ja ta wani gurin, Khairy kuma tana tsoro, shiyasa ta shirya wannan abun, bayan mun dauki hotunan sai kuma yadda zan yi amfani da su ya zama aiki, saboda Khairy bata son ace da wayar na yi amfani na yi barazana a gurin Hurriya ba, saboda tana jin tsoro”

Adam na kuka irin na karti da majina shabe shabe ya ke fadar hakan yana rike da hannunsa mai karaya.

”Nii kuma ba zan iya tunkararta kai tsaye ba, saboda ina tsoron kai ta fada a gidansu, gashi ban samu yadda zan yi magana da Hurriya ba, a lokacin ne na gane kamar wayo Khairy ta yi min, sai fadan ya koma tsakaninmu, na kasa daga nata kafa saboda zan bar kasa na tafi gurin masters sanadin haka mu ka yi fada, washe garin ranar da muka yi fadan na kirata na bata hakuri muka hadu a wani gurin and.... I... Rape her there.... ”

Captain be san lokacin da ya bude baki ba.

“Wait... Wa ka yi raping?”

“Khairy saboda ta ci kudina kuma ta kasa ba ni abun da nake so, sai fadan min take na yi amfani da hotunan, ni kuma hotunan ba su da amfani a gurina saboda ban samu damar kebewa da Hurriya ba, kuma ban san ya hakan zai faru ba”

Captain ya mike tsaye yana jinjina lamarin Ubangiji, bahaushe ya ce wanda Allah ke yi ma fada baya fada, all this plan akan Hurriya amman Allah ya kareta sherin da suka kulla be same ta ba.

“Wacece Khairy ma?”

Ya sake tambaya domin tabbatarwa.

“Yayarta ce, mahaifinsu daya a gurin Birthday Khairy muka hadu da Hurriya, saboda Khairy ce friend dita”

“To me yasa ka hadawa hotunan? Bayan ka samu abun da kake so a gurin Khairy? Akan me zaka cutar da Hurriya meye nata a ciki?”

“Ba ni na yada hotunan ba Wallahi, ban san waye ya yada ba, wata kila Khairy ce saboda ta ji haushi abun da muka yi mata, ta ce min sai ta dauki fansa, wata kila ita da yada hotunan”

“Me yasa ka amsa cewar tare kake da Hurriya? Why? Idan ma an yada me ye ribarka na amsawa”

Ya kasa magana sai wayyo wayyo yake yana kuka. Captain ya kama hannun ya murza.

“Ba tambayarka nake ba?”

“Wayyo....wayyo.... Wayyoooo..... Na yi hakan ne saboda kar nawa sunan na bace ni kadai, dan Allah ka sa a maida ni gida dan Allah”

“Za a maid kai, na samu abun da nake so ai ka saukakawa kanka, amman still zaka fuskanci hukunci...”

Captain ya tsayar da video ya mike tsaye ya fice daga dakin da Adam ke ta ihu yana neman ceto.

“Ku bar shi a nan DSS za su zo su dauke shi, ku babu hannunku a ciki, ko a office kar wanda ya amsa cewar kun je dauko yaron nan”

“Yes Sir”

Ya sara masa, sauran soldera din da suke waje mota biyu duka suka sara masa, sannan ya bude masa motarsa ya shiga ya rufe motar ya sake sara masa. Captain ya cire plane mode din ya shiga contact dinsa ya nemo wata number ya kira, after sun gaisa ya ce

“Mubarrak akwai wata yarinya da aka batawa suna, kuma abun ne da ku ya kamata ace kun yi Handel a yanzu, Lawyer na zai shigar da kara a gurinku cikin dare nan, please ina son ka tashi yaranka a location din da zan turo maka yanzu su dauki yaron, already na saka an dauko shi daga asibiti na san be kamata na yi haka ba amman na kasa hakuri ne”

“Me yaron ya aikata....”

Captain ya labarwa abokinsa abun da ya faru a takaice, sannan ya dora da cewar.

“Already babansa ya kai case din kotu saboda na karya masa hannu, na zubar masa da hakora so now i want you to cover me up...”

“Karka damu I know my job, ka turo Lawyer ka ya saka kara a gurin mu yanzu nan”

“Thank you”

Yana sauke wayar ya kira Lawyer sa Barrister Hauwa Zamau. Yana tukin motar yana fada mata abun da ya faru har ya isa gida.

“To a matsayin wa zamu shigar da karar?”

Yayi shiru yana kallon harabar gidan kakan nasa.

“A matsayin wanda zata aura, ina neman hakkin cin zafinta da yayi, abu ne kika sani duk wanda ya yi ta’adi ko kuma ya buga hotuna ko bidiyon tsiraici na mutum a yanar gizo ba tare da izinin mutum ba, to lallai irin wannan mutumin ya aikata laifi, and can be punished for Cyberstalking under S.24 of Cybercrimes (Prohibition, Prevention, etc.) Act 2015 of Nigeria or any law being in force in Nigeria..”

“Amman a yadda ka fada min ya amsa maka cewar ba shi ya yada hotunan ba”

“Wannan zai zo daga baya, a iya yanzu shi kadai muka sani da hotunan dan haka shi muke zargi, shiyasa muka shigar da karr gurin DSS saboda fadada bincike”

“Good point, i hope iyayenta ba za su ba mu matsala ba”

“I will fix that later... Ki aiko min da account number dinki yanzu nan”

“An gama ranka ya dade”

Ya katse kiran ya sauke wayarsa. Gallary dinsa ya shiga ya kama hoton Hurriya da ya dauka a dakinta ya duba.

“Mai tsada... Kin rike mutumcinki gashi abun da suke shirya miki ya koma kansu, ashe kaddarar mai yawa ce Allah ya takaita a haka, pretty girl with golden Heart...”

Magana yake da hotonta dake cikin wayar yana murmushi kamar ance masa tana saurarensa, kaunarta ta karu a zuciyarsa, a yanzu ya kara tabbatarwa ita din tabbas mai tsada ce...
Sai da ya turawa Barrister alert mai kauri tare da Nafi'u sannan ya fito motar, sai a lokacin ya lura bakin motoci dake gidan, kamin yayi wani motsi kira ya shigo wayarsa wannan karon Daddysa ne ya kira, ya amsa kiran da girmama da ladabi.

“Hello Daddy”

“Jamal kai ka aika aka dauki yaron nan daga asibiti?”

“Wane yaro?”

“Dan gidan Bashir Sarauta”

“Cewa suka yi na dauka?”

“Ka amsa min kawai ka dauke shi ko aa? Me ya fitar da gidan?”

“Na dauke shi, amman na yi covering case din yana hannun DSS yanzu”

“Why? Fadan nan ba naka ne kai kadai ba so ka cire hannunka a ciki ka bar ni da mahaifin yaron nan, ka zo gida yanzu nan”

Daddy ya katse wayar a take. Captain ya karasa ya shiga cikin falon, ga mamakinsa sai ya samu Salim a falon tare da wasu mata biyu, sau daya ya kalli gurin da Salim yakw zaune ya dauke kai zai wuce gurin Ammynsa dake tsaye tana kallonsa da waya a hannunta.

“Jamal.... Ina Adam...?”

Captain ya juyo ya kalleshi.

“Jamal....? How dare you call your boss like that?”

“Ba a office muke ba, baka da wannan ikon a nan, ina Adam?”

“Na dafa shi an cinye ka san ni maye ne”

“Kai ka aika da boys aka dauko yaron nan ina ka kai shi?”

“Taya ka san ni na aika aka dauko shi? Ka gan ni a gurin ne?”

“Mahaifiyarsa ta fada min yadda komai ya faru? Taya zaka aikata hakan Jamal? Ina hankalinka ya tafi?”

Captain ya taka ta isa inda yake tsaye, cikin wani irin isa da izza Captain ya ce.

“Bari na kira headquarter na fada musu Salim Sarauta ya shigo har cikin gidanmu ba tare da uniform ba, yana tukumar ogansa da sace wani wanda ban san da wanzuwarsa a kasar nan ba, kuma ka kira sunana kai tsaye with full of disrespectful, and you know yadda wannan abun zai taba aikinka”

Captain ya kara matsawa kusa da shi sosai.

“Ka san yadda Power take da karfi a Familymu, zan yi duk yadda zan iya na ga an cire uniform a jikinka, lastly ka san yadda bad ending yake karewa korarren ko da karami ne balle kai, and you know i can do it, so respect yourself....”

“YES SIR...”

Salim ya amsa masa dan dole yana kamewa guri daya, sannan ya hade yawu ya juya ya kalli matar da hankalinta yake a tashe ya ce.

“Mu tafi Anty Nabila”

“Mu tafi? Bayan ba mu san inda yaro yake ba? An zo an dauki yaro cikin asibitin yana cikin tsananin ciwo sannan ka ce min mu yafi? Mu koma mu yi me?”

Cikin kuka matar take magana, sai dayar dake gafenta ya amsa waya sannan ta kama hannunta

“Mu tafi Anty Nabila”

Sai da suka wuce sannan Salim ya kalli Captain ya juya ya fice daga falon cikin tsananin takaici.





Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman
Showing 141001 words to 144000 words out of 215510 words