dabam, ina son Matata! Ni dai ina son ku san wannan”
Ammy ta saki baki tana kallonsa Momy kuma ta kasa rike zuciyarta.
“Namra ba kwantai ta yi Captain balle ka ce idan Hurriya ta mutu ba zaka aureta ba, kuma da yardar Allah Namra sai ta samu mijin da ya fi ka a komai, ina da rai wata rana sai ka zo kana fada min bakinciki da damar da ka yi na auren Hurriya, laifin ai ba naka ne kadai ba har da na Yaya”
Ta juya a fusace ta fice daga dakin tana barin kofar dakin a bude.
“Miye amfanin haka? Saboda wata yar iska wata bare zaka batawa kanwar mahaifinka rai? Matar da bata san gurin da zata aje ka ba saboda soyayya? Me ya shiga kanka ne Captain? Anya kai ne?”
Ita kam be ce mata komai ba har ta ci ta cinye.
HAJIYA KALTUME POV.
“Ya jikin nata Hajiya?”
Khairy ta tambaya. Sau Hajiya Kaltume ta yaye mayafin dake jikinta ta aje jakarta gefe.
“Jiki da godiya, amman kam Hajiya Fatee bata da lafiya sosai, yanzu ma daker ta yarda muka dauke ta muka kaita asibiti muna zuwa suka ba mu gado, ni ma kadan ya rage na fadi jiri sai kwasheni yake damuwa ce ta mana yawa Khairy ba ita ba ba ni ba, kara ita ta wani bangare, duniyar nan bata da dadi a gurin kowa yanzu sai azzaluma, tun da muka dawo kauyen nan Hajiya Fatee bata sake lafiya ba, sai kin ga yadda hankalin Fadeel ya tashi”
Khairy ta kwanto a hannun kujerar dake falon na Hajiya Kaltume tana fadin.
“Ni kaina bana cikin jindadi a yanzu”
“Ba ki da lafiya ne?”
“Lafiya ta kalau kawai dai zuciyata bata min dadi”
“Wake da dadin zuciya a yanzu Khairy? Ai sai idan abubuwa sun daidaita, ni kaina yanzu abincin kirki bana iya zaunawa na ci, abubuwa sun hade min? Ga sakin nan da Alhaji yayi min ko waiwaye gefena be sake yi ba, kamar wanda ya aje kashi... Ga Iyami a gafe damuwarta na son yi min yawa, yanzu ga Hurriya da gani magani suka yi ma yaron nan suka aura mata shi, kauyen nan kuma mun je mun tararda bakin labari, ban da ma karfin zuciya ai sai mutum yayi mutuwar tsaye ko ta gaba daya a take”
“Hajiya wannan duk saboda Amma ne, ita ta haifi Hurriya har ta kawo mana matsala a gida”
Hajiya ta hade hannu biyu ta daga sama.
“Saboda ita ne kuwa saboda ita ne, ni ko mutuwar Salma ai bana raba dayan biyu da laifinta a ciki, ga kamun da barayi suna yi mana shekarun baya saboda ita ne dai, ni kam yau da zan ga Iyami ai da hannuna zan kashe ta, duba ki ga Hurriya waya auri irin mijin da ta aura a yanzu? Duk cikin yayan Alhaji babu wanda yayi dacen miji irinta duk bayan cin amanar da ta yi min”
Maganar take zuciyarta na zafi sosai saboda bakinciki, kamin su dago kai su kalli juna jin tsayarwa mota har biyu a bangaren ana rufe gambun da karfi. Khairy ta tashi ta leka windows din Falon dake bawa mutum damar hango abun da ke waje, a take gabanta ya yanke ya fadi.
“Appa ne tare da Yaya kuma nan suka nufo?”
Ta saki curtains din ta dawo kusa da Hajiya Kaltume ta zauna zuciyarta da jikinta na rawa, Hajiya Kaltume ta maida hankalinta gurin kofar tana tunanin abun da ta yi domin a yanzu bata da tabbacin alheri zai kawo mijinta a bangarenta. Yasir ne ya fara turo kofar falon ya shigo sannan Appa ya biyo bayansa. Daga Khairy har Hajiya Kaltume faduwar gaba suka samu kansu har Appa ya zauna yadda Yasir yake karara Khairy ita kanta ta san akwai wani abu a kasa. Hajiya na son tambayar lafiya tana jin tsoron domin ta lura da yanayin Appa ba yanayi mai kyau ba, sai da ta dubi Yasir sannan ta kalli Khairy da yake harara.
“Wani abun kika yi?”
Khairy ta yi shiru jikinta ya hau kyarma zuciyarta na zillo.
“Umm Khairy... Me kike aikatawa Hurriya?”
Ras ras ras gabanta ya fadi irin faduwar da be taba yi ba, sai ta kasa amsawa kuma ta kasa daina kallon Appa fuskarta kuma ta kasa boye tsoronta.
“Me kike aikata ga Hurriya?”
Appa ya sake tambaya yana kallonta. Yasir ya mike tsaye zai nufi inda take sai Appa ya dakatar da shi.
“Dakata, ba abu ne na duka ba, wannan abun mai muni duka ba zai canja komai ba, ni kadai na san ya nake ji a raina, yaya ne dukansu ace ďaya ta aikatawa ďaya haka? Ya kamata na tambayi kaina me na yi?”
“Baka yi komai ba Appa babu ta inda ka gaza, dan Allah karka sakawa kanka tunanin wani abu”
Yasir yayi saurin fada yana kokarin kwnatarwa mahaifinsa da hankali. Hajiya Kaltume ta kallesu ta sake duban Khairy sannan ta ce.
“Duk lokacin da za'ayi ma Khairy hukunci a gidan nan ko duka saboda Hurriya ake mata shi yanzu kuma me aka ce ta yi?”
Yasir ya bude wayarsa ya kunna video ya mikawa Hajiya Kaltume, tana fara kallo Khairy ta fara hawaye domin ita ma tana jin abun da ake fada, sai ga Hajiya Kaltume rike da baki.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un sherin sa za'ayi ma Khairy kenan?”
Appa ya nuna ta da tsaya.
“Ban shigo nan falon na zauna dan na yi magana da ke ba, karki kuskura saka min baki a magana, duk wata asalin kiyayya da tsana da neman ganin baya ko kunyata wani daga gurinki ta samu asali, duk abun da Khairy ta aikatawa Hurriya a yau goyon bayanki ne rainonki ne, ke kika bude musu hanya ke kika nuna mata hakan, kin tsani yarinyar nan kin tsani uwarta, akan abun da Allah be haramta ba, kaina farau aure? Da a gidana kawai za a samu wannan tashin hankali? Ke ya kamata ki hada kan yaya matsayinki na uwar gida amman baki yi ba, sai dai ki nuna musu tsana da banbanci, yau duk wannan abun ya faru saboda ke ne!”
Ya maida dubansa gurin Khairy dake kuka.
“So nake ki karya ki banranta kanki kamar yadda Hurriya ta yi min rantsuwa bata aikata ba”
Ta girgiza kai tana saukowa daga kan kujera tana kuka. Yasir ta dafe kansa ya runtse ido sosai.
“Tir da halinki...! Tir da haihuwar ƴa irin... Tir da ke Khairy ba zaki taba ganin abun da kike so ba a rayuwarki.... Taya zaki hada kai da wani namijin a waje saboda cin ma burinsa ga yar'uwarki ta jini? Ki taimaka masa ya gaya rigar mutuncinta? Ko kawarki bata cancanci haka a gareki ba balle kuma Hurriya, karshenta gashi ya fadi abun da yayi miki hakan kuma be miki ba sai da kika yada hotunanta a duniya...”
“Na ji... Ni na hada kai da shi aka dauki hotunanta... Wannan gaskiya ne amman Wallahi Tallahi ba ni na yada ba, ban yadawa duniya hotunan Hurriya ba, Wallahi ban saka hotunanta a internet ba, bayan Adam ban turawa kowa ba Wallahi, akan wannan zan iya rantsuwa da kur'ane, sheri ne kawai yayi min”
“Amman kin karbi kudinsa da sunan zaki nema masa hadin kan Hurriya? Ta yadda zai samu damar Lalata da ita?”
Appa ya tambaya hopping to hear NO from her. Ta hade hannayenta tana kuka sosai.
“Na aikata... Ka yafe min Appa ka yafe min dan Allah? Dan darajar Hajiya... Ban aikata hakan saboda na kunyata ku ba, ban yada hotunan ba...”
“Lahaula wala kuwwata illabillah, Khairy karki kuskura ambatar sunana a gaban kowa daga yau, kar wata matsala ko matsi da kunci ya saka ki tuna cewar ni mahaifinki ne....”
Hajiya Kaltume ta saka Kalma shahada Yasir ya kalleshi da sauri Khairy kuma ta fashe da kuka mai karfi ta je ta gudu ta kama kafar Appa da tuni ya mike tsaye ya fara tafiya bayan ya fadi hakan.
“Appa ka yafe min dan Allah, na tuba ka yi hakuri dan Allah... Ka yafe min Appa”
Tsayawa yayi ya kasa tafiya kuma ya ji ba zai iya juyo ya kalleta ba saboda ta bata masa rai matuka.
“Bana bukatar ganinki”
Ya fisge kafarsa ya fice daga falon ya barta a gurin tana rusar kuka. Ta juya gurin Yayanta.
“Yaya Yayaya... Dan Allah ka bawa Appa hakuri dan Allah.... Wallahi Wallahi ba ni na yada ba... Sheri yayi min saboda ya hada ni da mutane ba ni na yada ba”
“Ko sa yaushe idan na yi magana akan abun da yarinyar nan take yi cewa kike ina matsawa yanzu ga abun da ta haifar, wani ya keta mutuncinki a banza kuma yanzu za a yada hoton siraicinki... Kamin mu shigo nan Appa kuka yake da idonsa miye amfanin ya ta saka ta mahaifinta kukan bakinciki? Miye ribar hakan?”
Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya fice yana kuka. Hajiya Kaltume ta mike tsaye tana kuka ta nufi gurin da yarta take kwance a kasa tana mulmula ta rikata cike da tausayinta.
“Ya yanke hukunci ne cikin fushi, ki yi hakuri Khairy zai sauko...”
Ta fara share mata hawayenta tana nata kukan.
“Amman da gaske yaron nan yayi miki fyade?”
Khairy ta daga kai wani sabon kuka na zuwa mata.
“Shiya hana ni farinciki da sakewa tun daga ranar har yau... Hajiya ashe haka ake ji idan aka yi ma mace fyade....? Bakincikin abun ya fi na mutuwa...”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un....”
Hajiya Kaltume ta fashe da kuka ta rumgune yarta.
“Ba a bar maganar nan ba, Allah ya isar miki ba zan kyale yaron nan ba... Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un wannan masifa ta mana yawa...!”
*** *** ***
Tsaye Appa yayi a dakinsa ya rumgume hannayensa a baya yana kallon sama. Fuskarsa da zuciyarsa babu komai a cikinta sai tarin damuwa da bakinciki, kokarin yake ya gano wani kuskuren da ya aikata har aka jarabce shi da wannan, wani abun kaddara ce kai tsaye domin gwada imanin bawa da zuciyar ko tana iya dauka, wani abun kuma ishara ce na wanin abun da aka aikata daidai ba ko kuma a can baya. Ya nemi guri ya zauna sai kuma ya ji kamar ya zauna a ruwa saboda damuwar da yake ciki hakan ya saka shi mikawa tsaye ya fara zagaya dakin. A yanzu ya gane tun farko yayi kuskure be tsaya ya zabe uwar da ta dace da yayansa ba, be duba dabi'u da hallaya ba, be duba mai addini ba kamar yadda Annabi ya koyar, duk ya tsallake wannan gashi yanzu dafin abun ya bibiyeshi. A dakin yayi sallah Azahar saboda jikinsa da yake jin ya sauya masa kamar ba na shi ba, wani abu mai kamar zazzabi yana rufe shi, zuciyarsa na ciwo sosai. Bayan yayi Sallah ne ya dauki wayarsa ya kira direbansa ya fada masa ya kimtsa mota za su fita yanzu, sai da ya mike tsaye sai jiri ya debi shi ya fadi kasa zaune yana ambaton Allah, can kuma ya sake yunkurawa ya mike tsaye sai gabansa ya rike kirjinsa yayi kamar an tokare shi da mashi, a nan sai da yayi ta addu'a sannan ya samu abun ya sassauta masa, a lokacin da ya fito ya shiga motarsa sai ya ji baya bukatar kallon bangaren Hajiya Kaltume domin ji yake kamar ita ta aikata haka ba Khairy ba, wani bangaren kuma yana ganin kamar da hadin bakinta, a yanzu ne yake mamakin kansa da be karasa mata igiyar da ta rage a tsakaninsu ba, ya kamata ya kabe ta daga gidansa ma gaba daya, sai a yanzu ne yake kara jin tsanar ta irin tsanar da be taba ji ba, nadamar shekarun da ya bata a tare da ita yake a yanzu, arzikinta ďaya yaran dake tsakaninsu ba dan haka ba shi kam da ko sunanta a yanzu ba zai sake son a ambata a gabansa ba. Har ya isa garin Maradum be ya tunanin komai sai irin zaman rashin ji dadi da Hajiya Kaltume ta yi da uwargidansa wato matarsa ta farko Maryamu uwar Sapna, an yi zaman da babu dadi ga fitina da tashin hankali kuma mafi akasari daga gurin Kaltume yake tasowa, kasancewar Allah ya saka zaman ba mai tsawo ba ne sai Maryamu ta bar mata duniyar.
“Ka nufi unguwar kuka tara...”
Ya fada kai tsaye domin a yau zuciyarsa yarta kadai take muradin gani, yar da ware dabam saboda sherin Hajiya Kaltume, idan ta gabato da bukata Kaltume sai ta tare ko yanke hanyar da za'ayi mata duka sai dai rabi. Yana daya daga cikin dalilin da ya saka bata marmarin zuwa gurin ubanta duk kuwa da kasancewarsa mai arziki domin bata jindadin gidan bata jindadin Hajiya Kaltume kuma bata jindadin yaranta, da ba su dauke ta a matsayin yar'uwa ba, har mantawa suke da ita. Ta gaban gidan aka faka da dalleliyar motar mai matukar kyau da daukar hankali, sannan direban ya fito ya bude ma Appa mota. Cikin jin zafin rikewar da zuciyarsa take ya fito motar yana kallon shagon dake facing din gidan sannan ya dauke kai ya nufi gurin da kofar gidan take. Ba laifi gidane da aka yi ginar bulo ba na kasa ba, sai dai ginin ya ji jiki ya goge saboda ya dade sumitin dake gidan ma duk ya fashe. Sapna na tsaka da surfen masara ta ji sallamar Appa, sai ta cire tabarya ta aje tana murna da farinciki ganin mutunen da shi kadai ya rage mata a duniyar nan.
“Laaaa Appa.... Appa kai ne yau....”
Appa yayi murmushi yana kallon yarsa dake daure da zanen da riga dabam. Ita ce babbar yarsa ita ce yayar Yasir amman wahala ta saka ta zama kamar ita ce kanwarsa ta biyu ma. Ta shiga dakinta da sauri ta dauko tabarma ta shimfida masa gindin bishiya, sai kuma ta ga kamar hakan be dace ba.
“Appa ko dai ka shigo falo?”
Yayi murmushi yayi bayanta suka shiga falon da ruwa ya taba silin kujerunta suka koɗe suka fara lalacewa.
“Tsaya Appa karka zauna”
ɗakinta ta shiga ta ɗauko zanen atamfarta ta kasan akwati ta shimfiɗa a kujerar a ƙoƙarinta na karrama mahaifinta, sannan ya zauna dai ta kwance ƙullin dake gefen zanenta ta cire dari biyu ta mikawa yaronta da ya shigo dauke da bokitin ruwa.
“Karbi Aliyu siyo ma Appa na ruwan gora a waje Appana baya shan ruwa sai na gora”
Yaron ya sauke ruwan da sauri ya leko dakin ya gaishe da kakansa yana murna sannan ya karbi kudin ya fice da gudu. Sapna ta zauna a kasa tana gaishe shi.
“Appa sannu da zuwa sannu da zuwa Appa”
“Sannu Sapna surfe kike yi?”
Ta yi shiru tana kallon kasa, bata son yace bata gode da abun da yake mata ba.
“Appa abun da kake aiko mana ne baya wadatar da mu, kasan yanzu Iyali sun karu ba kamar da ba, yanzu ba ni kadai nake ba ya kara aure ya aje can gumawa, gashi ba wata sana'a yake a yanzu ba, shagon da yake tsaro mutumen ya rufe shagon, kuma barayi sun hana noma, daman da shi ne muke samu muna karawa, shiyasa nake surfen dab abun da na samu sai na hada da abun da ya ba ni mu ci ni da yara...”
Appa ya sauke kansa kasa yana jin rashin dadi ta rashin adalci.
“Me yasa baki fada min ba Sapna? Kina da wani wanda ya fi ni ne?”
Ta girgiza kai.
“Ba ni da shi Appa kai ne uwata kai ne ubana ba ni da gata sai na Allah sai kai”
“To me yasa baki fada min ba?”
Damuwar ta bayyana a fuskar Appa har ta saka idonsa cika da kwalla, irinta ce a fuskar Sapna ita nata kwallar suna zuba.
“Gani na yi kamar ba a son zuwana gidan, bana jin dadin yadda ake banbanta ni ko dan ni ina kauye su suna birni ban sani ba, kuma idan na bukaci abu wani lokacin har sai na manta kake yi min Appa, duk da haka kana kokari da mu na aiko mana sa abinci duk wata, gashi ni ba ni da halin da zan maka komai, kuma ba ni uwar da zata maka godiya, wani lokacin ina kunyar bijiro maka da bukata nauyin ai sai yayi maka yawa”
Appa ya dube ta da kyau ya jinjina kai.
“Gaskiya ne.... Ke din nan ke da Hurriya da Yasir bana da kamar ku a ƴaƴa Allah ya muku albarka... Kuma da tsananin biyaya da tausayi a gareni”
“Amin...”
Ya amsa tana share hawayenta, Aliyu ya shigo tare da kanensa su shi da a falon suna ta murnar ganin Appa yau a gidansu, daman rabonsa da garin tun kamin a haifi Hamad...
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/27/2023, 6:05 PM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
5️⃣0️⃣
https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx
Appa ya maida ludayin furar ya matsar da shi gefensa ya gyara zamansa yana sauraren Hajiya Binta.
“Na muku addu'a sosai daga kai har ƴaƴanka, kuma zan cigaba da yi har zuwa ranar da za dawo da
Showing 174001 words to 177000 words out of 215510 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59 Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72