zillo ta durkusa a kasan guiwoyinta ta dafa kasa. Hajiya Kaltume ma kuka take ta nufi yarta ta rika hannunta da niyar rumgume sai Ruma ta buge hannun Hajiya Kaltume ta nufi mahaifinta tana kuka ta rumgume shi yana hawaye, kusan kowa a gurin sai da yayi hawaye.

“Su ba mu gawarsa mana to mu gani, idan da gaske ya mutu su ba mu gawarsa mu gani Wallahi be mutu ba, boye shi suka yi Hamad yana nan da ransa”

Hurriya ce take maganar tana kuka, Gwaggo ta rikota ta rumgume tana kuka.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻*HURIYYA*


𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya kin daukar kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


𝐏𝐚𝐠𝐞 5️⃣

Hurriya first lost her sight a jikin Gwaggon, before ta yi going blank aka kwasheta ita da Amma sai Asibiti. Amma aka wuce da ita dakin haihuwa Hurriya kuma aka kaita Emergency. After 49hours of labor Amma ta haihu tagwayenta biyu duka maza. A madadin ta yi murnar ta haihu ta samu yan biyu sai murnar ta koma mata ciki saboda tunanin Hamad bata da wani kuka sai na Hamad. The following day aka sallamo ta daga asibitin bayan sun mata dinki kuma sun dorata akan maganin da zata rika sha na hawan jini sannan suka hana ta wankan ruwan zafi domin jinin nata ya hau sosai irin hawan da ba dan Allah ya kawo sauki ba, da abu ne mai wahala ta fita lafiya.

Har lokacin Hurriya tana asibitin Hajiya Binta na jinyar tare da taimakon Rukayya, kwananta biyu bata san inda kanta yake ba a asibitin, kamin ta farfado sai kuma ta zama so weak sai da ta sha drip da manyan allurar sannan ta samu sauki, the following day ita ma aka sallame ta two days after an sallami Amma. Wani abun da ya bawa kowa mamaki ciki har da Momy kuma ya daurewa Amma da Hajiya Binta kai shi ne, kin lekawar Alhaji Haruna a asibiti ko gida da sunan duba Amma ko kuma duba yaran da ta haifa masa, yan'uwansa na nesa da na kusa duk sun je duba twins din kuma sun je duba Hurriya wasu ma ba su samu labarin abun da ya faru ba sai a da suka je barkar twins. Sai dai Appa be bar rashin zuwa duba yaran da kowa ke musu lale da zuwa duniya, ya hana shi kyautata musu ba, duk wata hidima ta ya kamata uba yayi ma yayansa Appa yayi tun daga kan tufafin mai jego Amma har na jaririnsa, sai dai Amma bata yi taron suna ba, duk kuwa da kasancewar ba ayi taron gaisuwa a gidanta ba, an yi zaman makoki a gidan Appa kuma an masa sallatul ga'if wato sallar da ake yi ma gawar da bata kusa. Ta ko'ina Appa ya karbi gaisuwar mutane ana ta jajanta masa. All those days, hour's Hurriya a daki take rayuwa, domin bata son ganin kowa, idan zata yi alwala sai ta shiga bathroom ta yi idan ta yi sallah ta kwanta, bata son ayi mata gaisuwar Hamad, bata fitowa idan mutane suka tambayi ina take, idan kuma aka shigo sai ta rufe kunnuwanta bata sauraren kowa, she's the only one da ta kasa yardar Hamad ya mutu, ranar sunan yaran ma sai da ta saka kowa kuka, domin ihu take ta yi me yasa Amma ta sakawa little one din Hamad yayan kuma Hamid.

“Amma da baki saka Hamad din ba, Wallahi Hamad be mutu ba, karya suke yi Amma dan Allah ki cire, ki saka masa wani sunan ba Hamad ba”

Tana kuka tana rokon Amma a canjawa jaririn suna, Amma ta aje Little Hamad ta kama Hurriya ta rumgume.

“Hurriya dole mu karbi wannan gaskiyar, tana da daci amman dole ne mu karbi kaddara, duk yadda kike son Hamad na fi ki sonsa domin ni na yi nakudarsa na haife shi, una jin fiye da yadda kike ji”

“To me yasa kika sama Amma? Why? Why?”

Amma ta girgita da karfi tana kuka.

“Saboda ya mutu Hurriya, baki daya Allah ya karba ya bamu biyu ba? Toh sai mu gode masa, yadda ya so haka yake aikatawa, Hamad ya tafi tafiya ta har abada ya kamata ki karbi wannan, wannan shekarar haka ta zo mana”

Hurriya ta saki jikinta sai ta lankwasa ta yi baya Amma ta sake ta ta fadi kasan carpet din. Ita kam ta kasa yarda dan'uwanta ya tafi ya barta, fadan da suke yawan yi yake damunta a yanzu, why take ramawa idan yayi mata abun? Ko wane motsi yana tuna mata da dan'uwanta ne, bata taba sanin tana kaunarsa ba sai a yanzu da baya kusa da ita, ina ma ita aka dauka ba shi ba haka take yawan ayyana a ranta. Kusan kowa a gidan sai da yayi kuka kuma aka kasa wanda zai rarrasheta sai Yayanta Yasir, domin shi kadai ya fahimci manufarta kuma ya mara mata baya cewar Hamad be mutu ba, domin karbar gaskiyar cewar ya mutum shi ne ƙarya a zuciyarta.


****   ****     ****    ****

“Hajiya ki yi haƙuri dan Allah, bana son ina musa miki akan abubuwa, amman yaran nan da Iyami ta haifa nawa ne, idan ina buƙatar ganinsu ba sai na jira wani ya ba ni shawara ba, ayukan ne sun min yawa a yanzu amman da zarar na samu lokaci zan je na duba su, idan suka yi ƙwari ma aka yayensu ɗauko su zan yi na dawo da su gidana domin zuciyata ta fi amintuwa da haka”

Hajiya Binta ta kalleshi tana mamakin yadda yake ita bude baki ya musa mata a duk lokacin da ta yi masa maganar zuwa duba Twins din da Amma ta haifa.

“Tsoho me yake damunka? Wani lokaci ne baka da shi akan iyalinka?”

“Hajiya kin san kasuwanci ba daya ba, kuma idan ina son ganin yaran nan ni zan je da kai na, ina cw dai na sauke duk wani hakki na uba?”

“Toh baka bukatar ganinsu kenan? Haka kake nufi? Toh ni da nake bukatar ganinsu zan tafi, ko miye ya rufe maka ido ka kasa taka kafarka gidan Iyami Allah ya yaye maka shi tsoho, yau sati daya da haifa maka yan biyu kyautar Allah amman ka kasa taka kafarka ka duba yayanka”

“A gaishe su, Hajiya zan leko in Shaa Allah, kuma idan kin tafi ki fada mata next week Hurriya zata dawo zan aiko da mota a dauke ta saboda makaranta”

Yana maganar yana mikewa tsaye abun da be saba yi ba, ko magana Hajiya Binta take masa baya iya daga kai ya kalleta tsabar biyaya amman a yanzu duk ya canja mata, abun da be yi mata da kurciya ba a yanzu da girma ya kama shi yake canjawa. Baki saki Hajiya Binta ta fi danta da kallo har ya fice sannan ta girgiza kai hawaye na cika idonta.

“Allah ka shirya bawan nan naka, Allah ka karya duk wani abu da aka yi masa Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Ta rafka uban tagumi tana kokarim ganin bata bar hawayenta sun zubo ba, domin ta san illar zubar hawayen uwa ga ďanta. Appa har ya isa gida bw daina ganin laifin Hajiya ba, ganin yake tana kusa masa cikin al'amurran da be kamata ta saka kanta ba, shi dai aka haifawa yara to damuwa kuma na me tun da har be ce ba yayansa ba ne, kuma yayi musu duk wata hidima da ya dace uba yayi ma ƴaƴansa. Ba ta inda ya ji sayin kamar ta gurin da Hajiya Kaltume take taba masa ita ma tana dorawa Hajiya Binta laifi, tana bashi gaskiya na kin son zuwan da yake.

“Gaskiya Hajiya ba a haka, ai sai ta saka maka ido ta gani, ina laifin bayan duk wata hidima, kuma yara idan suka yi wayo ai sai ka dawo da su nan gurin Momy ta cigaba da kula da su, tun da tana da masu aiki ba daya ba za su rika musu komai”

“Ni ma haka na gani, amman ta kasa fahimtata sai laifina take gani, gaba daya ta rufe ni da fada”

“Toh ya ka ayi, sai hakuri ka san bata hada Iyami da kowa ba a gidan nan, duk dai abun da yayi dalili ya raba amman dai Hajiya bata dauki kowa sukarta ba sai Iyami, wai ni yaushe Hurriya zata dawo ne Alhaji”

Tana maganar ya aje kofin ruwan dake hannunsa ya amsa mata.

“Next week, na fadawa Hajiya idan ta je ta fadawa Iyami zan aiko da mota a daukota saboda makaranta”

Hajiya Kaltume ta dan tabe baki tana shafa zanen atamfar dake jikinta.

“Makaranta ma ai bata jira Alhaji, yanzu kan sai dai a canja mata makaranta a maida ita Government School, ko ba komai ta dan rage kewar Hamad dan na san abun zai yi da damunta, amman idan ta koma wata makarantar sai ta samu sabin kawaye kewar zata dan ragu, kuma ka ga yanzu private school ai duk an yi nisa da karatu sai dai ta Gwafnati ita ce za su karbe ta ko dan lalurarta”

Appa yayi shiru kamar mai nazari, idea Hajiya Kaltume na cewa a saka ta wata makarantar ta government be masa ba, sai dai ba zai iya nuna mata haka ba.

“Ko kuma a kaita wata makaranta, amman makaranta government bata cika kyau ba, bayan kuma ga duka yan'uwanta a private suke, kuma kudin biya makaranta ai akwai shi ba babu ba”

“Ba shi zaka duba ba, yadda Hurriya take da kokari a makaranta ko'ina zata iya karantu, kuma zata gane kamar sauran yan'uwanta daman kuma ta fi su basira, ni dai gaskiya shawarar da nake baka Alhaji a kaita government schools kuma bana son ka musa min akan haka, kai fa ka san Hurriya kamar ƴa take a gurina, yadda ba zan so abun da zai cutar da Ruma ko Khairi ba ita ma ba zan so abun da zai cutar da ita ba”

“Shi ke nan, tun da haka kike so, za'ayi, Allah ya tabbatar mana da alheri”

Fuskar Hajiya Kaltume ta fadada da murmushi.

“Amin Alhaji na, Allah dai ya kara rufa asiri, ya kara wadata”

“Ameen”

Ya amsa cikin rashin dadin rai da be isa ya nuna a fili ba. Abun ku da makirar mace haka ta rika jan sa da hira tana tabo bangagori da dama na kasuwanci, sai dai be yarda ya fada mata abubuwan da take son sani ba, sai dai ta fahimci wasu bangarorin da kuma har ta nuna masa sha'awar na son fara kasuwanci. Appa ya saka dariya.

“Kaltume ina zaki iya kasuwanci crude oil? Kina mace? Wannan kuma ai sai mu maza”

“Hmmm Alhaji ka manta karin maganar da hausawa suke cewa duk abun da namiji zai iya mace ma zata iya? Ai mata ma kansu ya waye yanzu ana damawa da su sosai akan crude oil a yanzu”

“Amman yan boko Kaltume ke da ko primary ba ki yi ba ina ke ina wannan kasuwanci? Da ma dai Nafisa ce tace zata yi ba zan musa mata ba, domin ita tana kasuwanci sosai ta san kan kasuwanci domin shi ta karanta kuma mahaifinta ma kin san waye shi ba sai na fada miki ba, amman ke Kaltume ina ke ina wannan kasuwanci?”

A take fuskarta ta canja domin ya tabo mata inda bata so, dauko zancen Momy ya ce ta fita wani abu, bayan kuma ya gama yaga fuskarta cewar ko primary bata yi ba. Alhalin kuma gaskiya ya fada haka ta yi rayuwa rayuwar kauye ba arabi ba boko sai talla kamin ya aurota.

“Alhaji na ga dai kai ma ba kasuwanci ka karanta ba, amman kake kasuwancin nan gashi nan kuma yanzu ka koma dam bokon har turanci kana ji”

Appa ya cire gilashin idonsa yana dariya.

“Kaltume ni fa na yi boko kuma na yi zurfi kawai dai rayuwa ce ta yi tsanani kuma kasuwancin ya fi tsaya min a rai shiyasa na watsar, na fara kasuwanci kuma da yake arzikin a nan yake kin ga a yan bokon ne a karkashina, amman ke Kaltume da ko sunaki ba zaki iya dubutawa ba Allah cutarki za ayi”

“Ga yayana zasu min komai”

“Matan dai ai kin san aure za su yi, Yasir kuma abu ne mai wahala ya rike kasuwanci domin na lura hankalinsa ya fi karkarta a bangaren aiki, bayan nan ma kasuwancin Crude oil yana bukatar kudi mai yawa sai mutum ya tsaya da kafarsa”

“Zan dan hada abun da yake hannuna na ga zai kai nawa, sai ka kara min da wani haba Alhaji ina matar Alhaji Haruna Mai Yadi ai wannan kasuwancin ba zai gagara ba”

Tana maganar har da wani daga masa gira kamar wata tsohuwar kasuwa. Appa dai yayi murmushi ya girgiza kai. Sai da aka kira sallah azahar sannan ya fita gidan ita kuma ta fito daga bangarensa ta nufo nata tana tunanin yadda zata zama daya daga cikin attijiran matan jihar Zamfara idan ta fara kasuwancin, bayan kasancewarta matar Alhaji Haruna Mai Yadi, so take ta mamaye ko'ina ta sha gaban Momy a yanzu, ta yadda ita kanta Momy sai ta yarda Hajiya Kaltume ta fita komai. Ta shigo falonta cikin yanayi na farinciki da jindadi ta tararda duka yaranta suna zaune falon suna hira ban da Ruma da tun da ta dawo ta ware kanta daban take rayuwarta ita kadai ba tare da sauran yan'uwanta ba, haka ma ba ta sake kusantar mahaifiyarta ba, a baya kuma ba haka take ba ita ce yar autar Hajiya Kaltume kuma ita ce shagwababbiyar yar rikon jakar Hajiya.

“Hirar me kuke yi?”

“Yadda zamu tashin garin nan idan Allah ya nuna mana bikin Maama”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi.

“Gaskiya ne, za ayi biki na ban mamaki daman wasu daga cikin abokan mahaifinku ba su san ma ya taba aurar ba”

Maama ta saka dariya

“Hajiya wake maganar auren Sapna auren kauye kuma tun kamin Appa yayi suna, aurena dai za'ayi aure na ji da fada da zai tashi hankali media ya zama topic of discussion a Gusau”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi kamin ta bi kowa da kallon.

“Toh Allah ya nuna mana, shi ma angon na ki na lura ai dan son riya ne”

“Wallahi haka yake, yace aurensa na farko auren hadi ne shi kuma baya son matar aka masa dole shiyasa be wani bada jiki ba, amman aurena ko hmmmm”

Duk suka dariya. Khairi ta ce

“Yaya Maama yana sonki Wallahi da alama kan waccan matar tasa zata sha wahala a hannunki”

“Kar ma ki ji yadda yake zaginta ni har tausayi take ba ni”

“Ba a tausayin mata ai Maama raba kanki, kina shiga gidan nan idan ta samu sa'arki waje za ayi da ke, wai ina Ruma?”

Hajiya ta karasa tana tambayarsu yar autarta domin ta zagaye falon da kallo bata ga Ruma ba. Salma ta ce.

“Hajiya kin san Ruma tana dakinta fa, yanzu ta mai da kanta aljanna bata son mutane ko kadan”

“Oh ni wannan yarinyar”

Hajiya ta nufi hanyar stairs, sai da ta yi kamar ta shiga dakinta sai kuma ta nufi dakin Ruma ta tura kofar dakin ta leka, zaune ta hangowa akan studied table dinta tana rike da wani textbook tana karantawa.

“Ke...!”

Ta juyo ta kalli Hajiya Kaltume. Sai ta shigo cikin dakin ta maida kofa ta rufe ta nufeta tana fadin

“Wai ke wani sabon iskanci kika kirkira yanzu da rainin wayo? Sai ki ware kanki dabam kina rayuwa kamar wata mayya?”

A take idonta ya cika da ruwan hawaye.

“Bana son gidan nan Hajiya, na fada miki ina son na koma gurin Hajiya Binta da zama ko Anty Farisa”

“Babu inda zaki je, babu gidan uban da zaki zauna idan ba zaki iya rayuwa a nan ba sai ki hadaye zuciya ki mutu”

Hajiya ta fada cikin bacin rai sannan ta juya daf da zata kai hannu ta bude kofar dakin Ruma ta mike tsaye ta ce.

“Har yanzu Hajiya gani nake kamar ba ke bace, na san baki son Amma amman kisan kai Hajiya kisan kai? Baki ga yadda suka fasa masa kai ba, ko'ina jini yake, still kuma suka karbi kudin nan gurin Appa, Hajiya mamaki nake yadda zuciyarki zata iya aikata haka, kullum sai na yi mafarkin Hamad abun da na gani ya kasa fita a idona ni kam ina ma ba ke ce uwata ba...”

Hajiya Kaltume ta juyo a fusace ta nufo Ruma gadangadan, tana isa gurin da Ruma take tsaye tana hawaye Hajiya Kaltume ta dauke ta da mari ta rufe ta da duka.

“Yaushe wuyanki yayi tsauri haka har bakinki ya iya furta kalamai irin haka? Dan ubanki fuskata kika gani tare da mutanen ko kuma gurin kika gan ni?”

Cikin kuka Ruma ta soma bata amsa.

“Amman sun yi magana dake lokacin da suka dauko
Showing 12001 words to 15000 words out of 215510 words