kulla mata munafurci na gaskiya da karya. Closet ta nufa ta dauko doguwar riga ta zuba ta dauki dankwali ta daura, sannan ta dawo gurin gadon ta kama hannun Hajiya alamar tana son ta tashi su tafi. Murmushi kawai Hajiya Binta ta yi ta mike tsaye domin ta san babba baya biyewa yaro ayi ta jayayya balle kuma Hurriya da bata son musu. Suna fara sauko stairs din Momy da Namra suka dago suna kallonsa a takr Hurriya ta ji wani iri ta kasa daga ido ta kalli kowa har suka sauka.

“Hajiya sannu da zuwa”

Momy ta fada dan babu yadda ta iya, if not ba zata gaishe da surukarta ba saboda bata zauna a falon ba, bata jira an kira mata kowa ba ta shige dakin Hurriya.

“Sannu da gida Nafisa, ya yaran?”

“Lafiya Kalau, ya tsufa”

“Gashi nan muna ja”

Namra ta gaisheta cikin muryar da ke nuna an mata dole.

“Hajiya ina wuni”

“Lafiya Kalau”

Ta amsa sannan ta zauna. Namra ta tashi ta shiga Kitchen ta dauko mata lemu da ruwa da dan abun tabawa ta aje mata. Ruwan kawai Hajiya ta sha shi ma dan kar Momy ta ce bata sha komai na ta ba. Bata wuce minti talatin a falon ba ta ce zata tafi.

“Da wuri haka Hajiya, na dauka nan zaki wuni, na ga idan kin zo har yamma kike kaiwa”

“Irin wacan tafiyar kai tsaye daga gida nake fitowa zuwa nan, amman ta yau daga wani gurin an fito sai na biyo nan na duba ku”

Duk suka mike tsaye ganin Hajiyar na ta mike tsaye.

“Allah ya saka da alheri mun gode ai a haka ma, bari na kira Alhaji a waya ina jin be san da zuwanki ba”

“Aa ba bukata na fada miki ba zuwan da na saba ba ne, ko bangaren Kaltume ma ba zan biya ba, sai dai wani lokacin”

Ta kalli Namra
“Namra an kammala karatu kuma sai mu ji shiru”

“Sauran Service, mun kusa zuwa”

“Aure nake magana, ga Khairiyyah ana ta maganar duk dai be turo ba amman ke mun ji shiru”

“Ni ma ina kusa Hajiya”

“Toh Allah ya nuna mana, kuna da labarin Musib da Miwan”

Wannan karon Momy ce ta amsa mata da kanta.

“Eh muna waya da su, suna kusan dawowa shi dayan ya gama nasa karatun ma, dayan ne ya rage”

“Allah ya taimaka ya sa a ci amfani”

“Amin”

Ta wuce gaba suna mata Allah ya tsare hanya, Hurriya ta biyota har gurin motarta ta direba ke ja ya kai ta duk inda take son zuwa. Kamin ta shiga motar ta juyo ta kalli Hurriya

“Karki yi wasa da abun da na kawo miki, kuma ki cigaba da hakuri Allah ya miki albarka”

“Amin Hajiya, na gode”

Ta shiga motar Hurriya ta rufe mata motar tana daga mata hannu har suka fice, sai da ta juyo zata shigo falon sannan gabanta ya fadi.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Ta furta domin faduwar gaba ne da bata saba jin irinsa ba, kuma na zata iya fadar dalilinta na faduwar gaban ba, sai da ta ja dogon Numfashi ta sauke sannan ta shiga falon, kallo daya ta yi ma Momy da Namra ta maida kanta kasa bata sake kallonsu ba har ta haye sama ta shige dakinta.
Namra taja tsaki tana wani hura hanci.

“Gaba daya yarinyar nan ta fita raina, Allah kadai ya san me ta fadawa Hajiya yanzu kin ga tana zuwa bata ko tsaya an kiraki ba ta shige dakinta, ta sauko tana min maganar yaushe zan yi aure wata kila ta fada mata karyar ina mata wani abun shiyasa har take tambayar yaushe zan yi aure”

Momy ta tabe baki.

“Komai zata yi, su je su yi ta yi, gida ne dai ba a isa a kore ni ba, ni har wata magana na ji a gurin Hajiya Mardiya”

“Wace Hajiya Mardiya?”

“Matar Alhaji Shamsu dan masanin tsafe, wai Alhaji zai hada shi da Kaltume tana son ya fara sana'ar crude oil”

Namra ta daki kirji.

“What? Hajiyar?”

“Ita fa, ni ma nace ko dai ba ita ba tace min ita ce fa, wai har sun fara maganar ma, ita ma mijinta ne ya fada mata”

Dariya ta subucewa Namra irin dariyar nan dake dauke da mamaki.

“Hajiya so take sai ta take ki Momy, saboda yanzu daga ke sai ita yanzu, Amma bata nan ganin take kishi ya koma tsakaninku”

“Ai ba zai daure ba, ni fa ina da degree a fannin kasuwanci, ita kuma ko primary bata yi ba, kin tana ganin mace da irin wannan kuma tace zata fi ni? Sannan ni arziki na na ubana ne da na gada da kuma nawa da na nema tun yana da rai har bayan ransa, ita kuma yar talakawa ce kamar Iyami, duk arzikin da zata samu ba zai kaiwa ba, domin ita zata samu ne ta karkashin Alhaji ni fa? Kuma kin ga karatun da na Musib ya tafi yi a waje saboda na saka shi cikin ragamar kasuwancina ne, domin idan mu ne yau gobe ba mu ba ne, ita kuma yanzu zata fara kuma dan ta be sha'awar kasuwanci, dana kuma yana da gogewar hakan”

“Ita ma Hajiya ina zata iya da kasuwancin Crude oil? Tana mace kuma ita da bata yi karatu ba?”

“Ai a duniya yanzu babu kasuwanci dake saurin kawo kudi kamar crude oil shiyasa take son ta fara, amman ina nan dake sai ta koma ko abun da zata daura ya gagareta, ai Iyami ma yanzu ishara ce agareta, ciwon na kwantar da ita ta rasa komai daman can da Alhaji ake tutiya yanzu kuma ba a tare, shiyasa rayuwar talauci bata yi ba Wallahi, ke yanzu kina ganin idan ace Iyami wata shegiyar attajira ce a gidan nan akwai wanda ya isa ya wulakanta mata ya? Kuma kin ga wannan abun da mahaifiyarta akatau a duk lokacin da na kalli yarinyar can ko uwarta na tuna da wannan sai kimarsu ta kara raguwa a idona..”

Bata kai zaren zancen ba ta yanke saboda kukan wayarta ta ji, ta juya ta dauki wayarta dake gefe tana ringing, ganin number da ta yi appearing a gaban gilashin wayar ya saka ta yi murmushi

“Captain”

Ta yi shiru still tana murmushi kamin ta sake fadar.

“Alhamdulillah, Okay maybe ta jefa wayar wani gurin ne”

Cire wayar ta yi a kunneta ta mikawa Namra.

“Karbi Captain yana son magana dake”

Namra ta mika hannu ta kara ta kara wayar a kunnenta.

“Hello”

“Ina wayarki”

Ta juya ta kalli stairs.

“Tana daki”

“Me ye amfanin waya idan ba zaki yi yawo da ita ba?”

“Sorry”

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kokarin sauke fushinsa yake yana kass da numfashinta ya daidaita bugun zuciyarsa.

“Ki shirya yanzu ki tafi Mall ki samo min wasu abubuwan i will send you the list”

“Okay”

Ta cire wayar a kunnenta tana murmushi, ta mikawa Momy.

“Wato idan kana son ka ga tashin hankali a duniyar nan ka batawa Captain rai, wai ya kira ni be samu ba, kuma fa ba zai wuce one missing call ba, shi da baya jera mutum kira ma, amman a wayar nan ina jin yadda yake ta huci”

“Wani lokacin kuma fa, idan namiji yana son mace, idan ta bata masa rai ya fi fusata fiye da kowa, ya kamata ki fara sabawa ai, iyayensa ma hakuri suke da shi ta wani bangaren ina ganin kamar har da laifinsu fa, saboda tun yana karami sun nuna masa basa son bacin ransa, shiyasa idan ransa ya bace abun yake masa zafi sosai saboda be san bacin rai ba, ko kuma ki ga abun kadan ya taba shi, su kuma hankalinsu duk ya tashi”

“Akwai haka amman Momy na fi yarda da abun har da hallita, duba ki ga yadda Hamad ma yake yi a da”

“Haka ne kuma, to sai ko hanzarta kar ki kara bata masa ran domin na lura kwana biyu nan hankalinsa yana karkata a kanki”

Namra ta yi murmushi ta nufi saying

“Ke dai Momy kina son canja manufar komai”

“Saboda ina fatar manufar tawa ta faru ba”

Ita ma dai da murmushin kasaita ta yi ta kana ta amsa wata wayar.

“Wa'alaikussalam”



*** *** ***

Sanin halin dan'uwanta ya saka bata wani ɓata lokaci ba shirya ta dauki jakarta, atm wayarta da kuma key mota ta fice. Lafiyarta da kamar minti ashirin da biyar Captain ya sake kiran Momy.

“Captain ta dauki wayar ya dai kuma ta tafi”

Momy ta bashi amsar tambayar da take kyautata zaton zai tambayeta.

“Eh mun yi waya da ita ai, an gama abincin rana”

“Ina tunanin an gama kam, ban leka Kitchen din ba, amman na san an isa gamawa zaka zo ne?”

“Aa ina da aiki da yawa ba zan iya zuwa ba, amman zan aiko mota yanzu a karba min a zuba a kula a bawa Hurriya zan turo wanda zai dauketa”

“Direba zai iya kai maka ai ba dole sai ita ba”

“Momy we have trust issues here, shiyasa ba ko'ina muka cin abincin ba, sai inda muka yarda, kin ga wanda zan aiko ma ban yarda da shi ba, amman idan tare da na gida ne i know I'm safe”

“Okay ka aiko shi yanzu”

“Okay Thank you”

Momy ta mike tsaye tana kiran masu aikinta dake kitchen, sai da suka shirya komai aka zuba masa a coolers masu kyau ta saka plate da spoon a karamin kwado. Hurriya na zaune dakinta mai aikin Momy ta shiga kiranta.

“Momy tace ki shirya ki fito yanzu nan da mayafinki zata aike ki”

Huriyya ta sauko daga kan gadonta ta nufi gurin da dogon hijab dinta yake ta dauka ta saka ta cire flat shoes ta saka ta bi bayan mai aikin da ta dade ta sauka masa. Ko da ta sauka Momy na tsaye dinning sai wani sham kamshi take tana yi ma masu aikinta fada. Hurriya ta tsaya a daga gefe sai da Momy ta gama fadan ta juyo sannan ta yi magana.

“Momy gani, Inna Shatu tace zaki aike ni”

“Ga abinci nan da zaki kaiwa Captain, ki jira direbansa ya iso, sauran kuma idan kika tafi ki yi karabanin bata masa rai ki dawo ki ga yadda zan ci ubanki na yi kasa kasa dake a gidan nan”

‘Shi dai wannan mutum suna jinsa kamar wani sarki’

Ta fada a ransa a zahiri kuma sai ta amsa da toh, ta nemi guri ta zauna har sai da direban ya iso, sannan mai aikin ta daukar mata kayan aka saka a motarsa. Mutumen da ya bude mata gidan baya ta shiga Soja ne dake sanye da uniform dinsa Complete, tana zaune cikin motar shiru tana kallon titi har suka isa. Tun a bakin gate din gabanta ya fara faduwa sakamakon arba da ta da fara da soldiers rike da makamansu, tafiya suka yi sosai ciki sannan suka isa wani bangere da aka ware dabam da sauran bangarori, daman gurin part part ne, a gurin da take ma part part ne. Fitowa yayi ya bude mata motar after ya faka, ta sauko kafafuwanta ta fito ta dauki kwandon shi kuma ya rika coolers din ya wuce gaba ta bi bayansa, gabanta sai faduwa yake saboda tsaron dake gurin, kusan wannan shi ne karo na farko da ta taba arba da sojoji da yawa haka. Wani gurin ya zagaya da ita dake bayan wasu manyan gine gine dake gurin suka isa wani part da aka kawata da furannin daga gaba. A nan din ma akwai masu tsaron wasu kuma suna ta aikin da takardu wasu da system. Can ciki aka wuce da ita ya lasa wani gurin kofa ta bude sannan ya matsa baya yayi mata alama da ta shiga.

Captain ne zaune a kujera cikin katon office din yana mikawa wani files din dake hannunsa. Mutumen ya karba ya tsare masa sannan ya juya ya fice, shi ma wanda ya riko mata cooler sai da ya tsare masa sannan ya aje, da zai fita kuma ya sake sare masa, yana fita kofar ta rufe kansa. Hurriya ta dago idonta kadan ta kalleshi sai ta yi sa'a ita yake kallo daga inda yake zaune sanye da uniform dinsa complete abun da bata taba gani ba, ita bata ma taba sanin soja ne ba sai yau. Da sauri ta maida idon har da dan rufesu kwarjininsa na yau ya fi na kullum wata kila saboda yau yana sanye da kakin na soja ne, dake karawa ko wane namiji kawarjini balle shi da Allah ya wadata da six-packs.

“Baki iya sallama ba? Baki iya gaisuwa ba?”

“Assalamu Alaikum ina wuni”

Ta hade sallamar da gaisuwar a lokaci daya ta fada da sauri, har lokacin tana rike da basket din ne tun da be bukaci ta aje ba. Ya aje pen din hannunsa ya mike tsaye ya zagaya ya fito daga gurin table din ya nufi wasu kujeru da suke can gefe visitors chair ya ware daya ya ja baya.

“Zo nan ki zauna ki ci”

Ta fara tafiya tana rike da basket din, ta ci? Ita? Ko kuma dai bata ji daidai ba? Maybe nufin yake ta aje. Dan haka da ta aje basket din ta ta dauko coolers din ta kai gurin ta aje.

“Na kai”

Ta fada, ba tare da bari sun hada ido ba. Ya mata banza ya cigaba da aikin da yake. A nan ta soma fahimtar manufar.

“Ni fa na ci abinci”

Ta fada kamar a shagwabe.

“Saboda ke na saka a kawo abinci nan, ina nan aikin ya min yawa kowa aiki yake yau, amman my mind was telling me kina can baki ci abinci ba you must eat...!”

Ya karasa a tsawace domin tana kokarin bata masa rai ne kawai, matsawa ta yi baya a zarane ta dan saci kallonsa tana bata fuska ita dai ta san yana neman ja mata matsala ne kawai a gurin Momy, kamar zata yi kuka ta ce.

“Na ci abinci fa”

Ya tsaya cak daga aikin da yake, ya dubeta. Kamin ya saka hannunsa aljihu ya ciro pistol dinsa ya aje kan table.

“Bana maimaita magana, kina cikin headquarter soliders ne you should be careful...”

Yana aje bindigar ya mike tsaye ita kuma ta fadi zaune jikinta na rawa kamar mazari, ta bude cooler ta fara zuba abincin wani na zubewa saboda tsoro. Ficewa yayi daga office din ya barta daga ita sai bindigarsa dake kan teburin aikinsa. Ta daga plate din ta dora a cinyarsa tana ci tana kallon bindigar, daman tana jin ana fadar soja basu da imani yau ta tabbatar. Captain be dawo Office din ba sai da ya dauki lokacin da yake kyautata zaton ta isa cinye abincin. Ta mike tsaye da sauri.

“Na cinye”

Ya kalli plate din sannan ya kalleta. Yanayinta so innocent da raunin dake tattare cikin kyawawan idanuwanta, suka saukar masa da tausayinta, fiye da wanda ya ji a lokacin da ya mareta Namra ta fada masa makauniya, fiye da wanda ya ji a lokacin da aka dauke dan'uwanta, fiye da wanda ya ji a lokacin da ya same ta tana cin abinci a kitchen din Momy irin cin yan yunwa tana kuka, fiye da tausayinta da ya ji a lokacin da ya ji maganar Momy da Namra akanta.
Dauke kai yayi ya nufi teburinsa ya bude wani guri daga kasa ya dauko box din gilashin da ya taba bata a lokacin da ya fasa na ta, a yanzu yana son ya bata gilashin ne da ya siya da hard earned money, da hannunsa a England, as an apology na marin da yayi mata a lokacin da yayi zaton tana sane ta bugu kirjinsa.

“Cire gilashin idonki”

Cikin wata muryar data fi kama da shagwaba da kuka ta ce

“Idan na cire hudu zan gani, bana gani komai sai da shi”

Kansa ya daga sama, yana addu'a a zuciya, na neman Allah ya kara masa hakuri da juriyar iya controlling kansa, domin babu abun da ya tsana a duniyar nan kamar musu. Hannunta ta kai ta cire gilashin ganin kamar zata bata masa rai a rashin aikata hakan, bayan kuma Momy ta gargadeta, a take kuwa ta ganin komai da kyau hudun da take tsoro ya mamaye idonta, da can tana ganin dishe-dishe idan ta cire gilashin sai dai bayan tafiyar da dan'uwanta daya tilo yayi ya barta sai idanuwan suka kara lalacewa saboda kukan da ta sha, da kunnuwanta take auna sautin takunsa har kwakwalwarta ta sanar mata yana tsaye a gabanta. Tsakiyar cikin kwayar idonta yake kallo, ya sani ko da zai saka wuka ya barka cikinta, ko ya dora mata bindigar da take tsoro a kai ko yayi mata dariya ba zata shaidar abun da ta gani ba, domin ita ta rasa wannan ni'imar. Kansa ya sauke kasa ya busar da iska bakinsa a hankali.

“Alhamdulillah”

Ya furta da nuryar da shi kadai sai muhallinsa za su ji, domin shi ya samu abun da Hurriya ta rasa, daman kuma hausawa sun ce mutum dan tara ne be cika goma ba, Allah ya mata gomai ya rage da ido, shi ne kadai tawaya a gurinta. Kamar an kunna wuta haka jijiyoyin idanuwanta suka sanar da kwakwalwarta dake raba sako, ta karbi sakon hoton fuskar Captain dake tsaye a gabanta hannayensa kuma suka zagaye tsakanin dama da hagu na kyakkyawar fuskarta. Dauke hannunsa yayi bayan ya saka mata gilashin sannan ya karbi na hannunta a lokacin da hawaye suka sauko a idonta irin saukowar da wanda yayi arba da su a fuskarta zai tausaya mata. Ya nade gilashin ya dora a kan teburinsa ba tare da ya kalli hawayen da suka zubo mata ba.

“Direba yana waje yana jiranki”

Daga haka be kara cewa komai ba ya fice daga office din, gafen hijabinta ta saka ta share hawayenta, sannan ta nufi gilashinta ta dauka ta cire wanda ya saka mata ta maida nata sannan ta nufi kofar ta bude. Taku daya biyu kamin ta yi na uku wanda ya kawo ta ya nuna mata hanyar da za su ba, ba wanda suka zo dazun ba. Ba musu ta bi bayansa har suka isa gurin motar ya bude mata ta shiga ta zauna, shi kuma ya shiga mazaunin tuki yayi ma motar key, amman shiru shiru ta ji yaja motar sun kama hanya ba, bata ankaro ba aka bude back seat inda take zaune, Captain ne ya shigo cikin motar ya zauna, tana kallonsa ta yi saurin maida idonta kasa, sai ya kai hannu ya dago fuskarta
Showing 96001 words to 99000 words out of 215510 words