Babbar rigarsa ya cire ya juyo ya dauki wayarsa ya amsa kiran dake shigowa.
“Ranka ya dade barka da yamma”
“Barka dai Allah yasa akwai labari mai dadi”
“Akwai ranka ya dade, duk mutanen da ka aiko mana da sakon sunayensu mun kama wasu mun bincike su wasu kuma mun musu barazana a waya sun goge posting din sun bada hakuri, sai dai dukansu sun ga horunan ne a wani gurin ne suka kwafa suka yada abun, su ma kuma duk mun bisu mun saka sun goge kuma sun bada hakuri, mutum daya ne ya ce mana wani ya turo masa hotunan da bayani shi da aka turowa da kuma mu da ya fadawa mun bincika account din sai muka samu an goge account din.
“Na gode sosai already a nan mun riga mun gane wanda ya aikata abun, daman dai bukatar mu a batar da hotunan daga internet, thank you so much, zan tuntube anjima”
“Thank You Sir”
Ya sauke wayar Adaidaita lokacin da mahaifiyarsa ta biyo bayansa ta daga bangaren Daddy. Kallonta yake yana rike da wayarsa har ta karaso inda yake tsaye tana murmushin takaici.
“Congratulations ka yi aure Jamal, ka auri yarinyar da haukan ka yake nuna maka kana sonta, alhalin kanka ka wulakanta, makiyi zasu mana dariya su maka, ka zama abun kwatance a cikin sa'ainka da friends dinka, saboda ka auri makauniya kuma yarinyar da a yau idan na bude data na zan iya ganin siraicinta, wani ya rigaka taba jikinta, yarinyar da mahaifiyar da kuma kaf danginka ba a maraba sa zuwanta amman a haka farinciki kake kana jindadin ka samu mata, a daura aurenka a cikin gida, daga mahaifinka sai masu aikin gida sai uban yarinya, kai da ya kamata duniya ta san ka yi aure labarin aurenka ya cika kafafen sada zumunta sai gashi ya kare a karamin gida kamar wanda ya aikata sheri”
Ya rage tsawonsa ya zauna akan gado.
“Ammy na san baki son yarinyar nan, ba zan iya sakawa ki so ta ba, amman dai ina son ki sani ni dai ina kaunar yarinyar nan irin kaunar da ban taba jin ina yi ma wata mace ba, kuma jifanta da kike da kalamai marasa dadi ni kike gogawa bakinciki domin ita din matata ce a yanzu”
Ta kara yin murmushi tana daga gira.
“Haka ne Romeo uban soyayya, matar ka ce tabbas babu wanda ya isa ya goge wannan, ni kuma uwarka ce na fi matarka karfin ikonka a kanka, kuma har abada ba zan taba karbar Hurriya a matsayin suruka ba, ba zan taba sonta ba”
Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi ta nuna shi da yatsa.
“Jamal ni na haifeka ka nuna min karfin soyayya, mahaifinka kuma ya nuna min karfin iko, ni kuma a yau zan nuna maka karfin hakki...”
Da kakkausar murya ta fada masa haka ta juya ta fice daga dakin. Captain ya soke kai kasa damuwa na baibaiye shi.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
[12/21/2023, 11:29 AM] AMINA KABIR CAPS: *HURRIYA*
4️⃣7️⃣
Bayan kwana biyu....
After ya yanke kiran da ya shigo daga Ethiopia, cikin rashinya sauko da kafafuwansa ya sauko daga kan gadon cikin rashin kuzari, ya saka bedroom slipper dinsa ya nufi kofar falon ya bude ya fita. Downstairs ya sauko ya nufi falon kakarsa Hajiya Nene ya zauna a kusa da kakarsa yana gaisheta. Sai ta kai hannu ta taba jikinsa ta amsa.
“Lafiya Kalau Jamal ya karfin jikin?”
“Alhamdulillah”
Ya kalli Ammynsa dake zaune sanye da doguwar rigar abaya kanta babu dankwali.
“Ammy ina kwana?”
“Lafiya Kalau, ka ci abinci?”
“No zan ci anjima”
“Haka ka sabawa kanka da wannan dabi'ar baka son cin abinci? Saboda ka daga min hankali ne?”
Ya kasa daga ido ya kalleta.
“You fake it ko Captain? Tun ranar da mahaifinka ya bar garin nan baka sake sakin jikin ba, abinci ma baka son ci”
Ko bata fada masa kai tsaye ba ya fahimci abun da take nufi.
“Ammy an faking ciwo ne? Bana yin komai saboda na daga miki hankali. Tashin hankalin tashin hankalina ne”
Ya kalli wayar hannunsa ya mike tsaye.
“Bari na amsa wannan kiran”
Ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo
“Da gangan yake wannan abun”
“Da gaske ba shi da lafiya, na taba jikinsa yanzu da zafi sosai, ki kalli idanuwansa ki gani yaddda suka sauya alamar zazzafi yana damunsa sosai kuma ya rame sukuninsa duk ya sauya, Turai karki zama irin sukunan mana masu kishi da matan yayansu”
Ammy ta juyo ta kalli In-law dinta.
“Ba kishi nake da yarinyar ba, Allah ya tsare ni ba zan taba zama daya daga cikin irin wadannan iyayen ba, kawai ba ma the same team ne, ke ma kuma kina goya masa akan abun da kowa ya san ba daidai ba ne a gidan”
“Miye ba daidai ba? Goyo masa akan abun da addinin be haramta ba? Ko kuma son abun da danki yake so? Ke ce ba daidai ba, tun a ranar da aka daura auren yaron nan baki bar shi ya fita ko'ina ba, kin tsare shi a gida kamar mace gashi nan kin haifar masa da damuwa”
“Idan ya fita ma babu inda zai je, already yayi received email daga gurin aikinsu sun aminta sun ba shi sati biyu ya huta, to me zai fita yayi a waje?”
“Namiji ne shi fa, yana da abokai yana da guraren zuwa da yawa yarinyar nan ma tun da aka daura aurensu ba ki barshi yaje ya ganta ba, Turai duk wanda zai so ďanki yana bayanki ne, domin ke kika haife shi ke ya kamata ace kin fishi son abun da yake so, ba shi kanwa ko yayar da zai ti shawara da ita akan Matsalar rayuwarsa ke ce uwa da ke zai yi shawara a komai, yanzu kuma kin juya masa baya kika kokarin cilasta masa ya zaba tsakanin rayuwa da mutuwa”
“Hajiya abun da yarinyar nan ta yi yayi tsauri da yawa, ko da kuma bata aikata ba ni bana sonta bata cikin irin jerin matan da nake son Captain”
“Saboda dake za'a daura musu aure ko ba da Captain kuma ke zaki zauna da su ba Captain ba, ko a gidan karuwai ya dauko ta tun da har ya nuna yana sonta ya kamata ki so ta kema, balle kuma har igiyar aure ta shiga tsakaninsu ai zance ya kare, tarewar ki a nan ba zai hana Jamal ya gana da matarsa ko ta tare a gidansa ba, na san duk saboda shi ne kika aminta ki bi mijinki”
Ammy ta bata fuska sosai tana jin ta wani bangaren kamar bata kyautawa danta ba, sai dai ita ma kuma ba su kyauta mata ba, sam bata son Hurriya a matsayin suruka.
“Ba gori nake miki ba, amman lokacin da Aliyu ya gabatar mana ke a matsayin matar da zai aura, ba mu ce masa fa wanda muke so, sai kuma karba muna murna da addu'ar alheri, mu dai muradin mu ya auri wanda yake so ba wanda mu muke so ba, so da yawa mu kan ki abu ya zame mana alheri, kuma mu so abu ya zame mana sheri”
‘Gorin dai kike min Hajiya’
Ta fada a ransa a zahiri kuma sai ta mike tsaye ta dauki hijabinta dake gefen kujera ta saka ta fice daga falon. Sama da haura zuwa dakin da Captain yake, tana tura kofar dakin ta ji karar unkurin aman da yake daga bandakin dake bude, tsantsar soyayya da kulawa irin na uwa sai ta karasa gurin da sauri hankalinta a tashe.
“Da gaske baka da lafiya ashe”
Ta taba wuyansa zuwa kansa ta ji shi da zafi sosai, da kanta ta kunna lap ta wanke masa baki kamar wani karamin yaro.
“Mu je asibiti yanzu”
“Zan iya kira likita ya zo gida ya duba ni”
“Aa asibiti zamu tafi”
Ta cikin tsananin razani da tsoron kar wani abu ya samu danta. Sakinsa ta yi ta fice daga bandaki da sauri. Tawul ya dauka ya goge fuskarsa idonsa har wani ja suka yi alamar jikinsa ya saki saboda Fever, haka ya fito bandakin yana jin aman kamar be gama yi ba, kofar bandakin ya rike yana jin yawun bakinsa na tsinkewa. Sai ga Ammy ta shigo tare da Momy Ikilima
“Mu tafi ga direba can a waje”
“Ammy ba wani ciwo ba ne da zaka daga hankalinki ba”
“Ban taba baka umarni ka aikata a take ba tare da ka yi min musu ba, haka last time na ce maka zamu tafi England a duba lafiyarka baka yarda”
Ammy kamar zata fashe da kuka take maganar. Ganin haka ya saka shi nufar gurin da ya aje wayarsa ya nufi wayar ya dauka.
“Mu tafi”
Gaba ta saka shi, kamar wanda zai gudu sannan ta bi bayansa ita da kanwar mijin nata.
“Zan iya tuki ba ni key”
Ya mikama Direban hannu, direban ya kalli Ammy. Sai ta girgiza masa kai.
“Ka bari ya kai mu ina zaka iya tuki yadda jikinka yake da zafi nan”
“Ammy ciwon nan be kai yadda kike tunani ba, zan iya tukin nan da kaina”
Ya rufe baki yana karkata dubansa ga motar Salim da ya faka kusa da wata motar gidan. Captain ya bude motar zai shiga Salim yayi hanzarin bude tasa motar ya fito.
“Captain...”
Be amsa shi ba kuma be fasa shiga motar ba. Ammy ta kalli Salim din ta kalli ďanta.
“Salim ne”
“Na san shi ne Ammy mu tafi”
Salim na isowa gurin ya gaishe da Ammy da yar kunyarsa kunshe a aljihu.
“Lafiya Kalau Salim”
“Fita zaku yi?”
“Eh Captain za mu kai asibiti”
“Ba shi da lafiya ne?”
“Eh”
Salim ya kalli Captain din da baya son kallon gurin da Salim din yake tsaye ya mika masa hannu.
“Hi”
Captain ya kalli hannunsa ya kalli fuskarsa, sai ya amsa masa ba tare da ya mika masa hannun ba.
“Hi”
“Come on mu bar abun da ya faru ya wuce mana, ba yara ba ne mu, mun samu rashin fahimta kuma mun hau dokin zuciya, amman ba zan bari wannan abun ya lalata alakarmu ba, we're friends for more than 15yrs now wannan dan karamin abun ba zai bata alakarmu ba, na san na yi ba daidai ba a wani gurin kai ma kuma ka zafafa I'm sorry”
Salim ya sake mika masa hannunsa a karo na biyu, sai dai wannan karon na neman kawarda fadan dake tsakaninsu ne, ba irin na dazun ba da yake na gaisuwa. Wannan karon ma sai da Captain ya dade yana kallonsa hannunsa sannan ya mika masa nashi hannun ba tare da yace komai ba. Ammy ta yi murmushi.
“Ko ku fa, amman ace mace zata shiga tsakaninku kamar ba maza ba? Ban jidadin abun da ya faru ba kuma daman ina da kudirin na shirya tsakaninku”
Still Captain be ce komai ba, Ammy ta bude baya ta shiga tare da Momy Ikilima dake yaba yadda Salim ya fi karfin shaidan ya kawar da girma kai ya kawo kansa. Direban ya ja motarsu zuwa asibiti Salim kuma ya shiga motarsa ya bi bayansu. Sai da aka fara diban jininsa aka auna bayan likitan yayi masa tambayoyi sannan ya ba shi gado domin har yanzu akwai gajiya a tare da shi kuma yanayin jikinsa ya tsananta sosai. A take aka saka masa drip Ammy ta tare a dakin tareda Salim hankalinta a tashe ta fita dakin tana sanar da Daddy. Momy Ikilima kuma ta koma gida dare da direba domin sanar musu halin da ake ciki da kuma dauko wasu abubuwa da ake bukata. Sai dakin ya zama daga Salim sai Captain da idonsa yake rufe hannunsa kuma yake sanye da cannula.
“I'm so sorry akan abun da ya faru, gaskiya ta bayyana yanzu kuma za a yadawa duniya cewar Hurriya bata aikata ba”
“Matsalata da kai ba akan Hurriya ta aikata ko bata aikata ba ne, so please sunanta ya fita daga bakinka, matsalar sa muka samu saboda na karya hannun Adam ne so mu yi magana akan haka kawai”
Salim yayi ya dan tabe baki.
“That's right... Adam yayi abun da kake bukata an turawa mahaifinka video kai ma kuma na turo maka ka duba whatsapp dinka”
Captain ya bude idonsa ya kai hannunsa na hagu ya ciro wayarsa ya bude whatsapp dinsa, suna ganin Salim ya fara budewa kamin ya sauke video kiran Daddy ya shigo wayarsa ta whatsapp video.
“Daddy”
“Hi Jamal... Yanzu Ammynka take fada an baka gado a asibiti, haka ne... ”
“Eh amman da sauki ba yadda take daga hankalinta ba ne...”
Salim ya juya ya fice daga dakin, yana rufe kofar dakin Ammy na kawowa bakin kofar dakin, ganin Salim sai ta fasa shiga ciki.
“Ina son magana da kai Salim”
“Okay Ammy, zamu iya yi a nan ko sai mun tsada”
“Idan muka matsa zai fi”
Ya fara takawa ita ma ta taka sai suka jera suna tafiya.
“Amman ina son na sake yaba maka ne akan kokarin da ka y na kawar da komai a ranka, kuma ka bawa Captain hakuri duk da kasancewar ta wani bangaren ka fi shi gaskiya, na jidadin haka domin idan baka yi ba na san Captain ba zai taba iya aikata abun da ka aikata ba, ka san halin abokinka”
Salim yayi murmushi.
“Nasan halin kayana Ammy ba sai kin fada min ba, shiyasa ai na bada hakurin da kaina, ni kuma na fahimci ban kyauta ba ta wani bangaren and be kamata na bar yarinyar kamar Hurriya ta raba ni da Captain”
“Good na jidadin dawowarka sosai, daman ina neman wanda zai taya ni fadan nan domin ni kadai nake yakin nan a gidana, Engr yana goyon bayan Captain yan'uwansa kuma basa son fada masa gaskiya saboda Engr, yau ma Hajiya Nene fada ta yi min tana ganin kamar kishi nake da yarinyar nan ni kuma ba kishi nake da ita ba i just can't find any reason da zai saka na so ta, i know da cousin dinka aka aikata abun nan amman ko da ba gaskiya ba ne ai wannan abun ba zai shafe a idon duniya ba”
Ya tsaya daga tafiyar da yake.
“Why are you telling me this Ammy?”
“Bari na tambaye ka tsakaninka da Allah... Shin zaka iya auren yarinyar nan a lokacin nan?”
“Ba zan iya ba, ko a gaba balle a yanzu na jinjinawa Captain yayi kokari kuma yayi jihadin da ba kowa sai iya ba”
“To me yasa ba zaka taya ni fada masa gaskiya ba? Ka lurar da shi ta wani gurin da kurakurai suke mana”
“Idan na yi hakan zai bata alakarmu da shi ne akwai, ba zai fahimta ba kuma sai yi tunanin na zo ne saboda na daga masa hankali na hana shi zaman lafiya da Hurriya ko sonta yadda ya dace”
“Cikin Hikima zaka yi Salim, wannan taimako a gareni da kuma shi kansa abokinka, Wallahi bana son auren”
“Amman an riga an daura ai Ammy meyasa baki hana ba kamin a daura”
“Babu wanda ya sanar min da cewar za'a daura, mahaifinsa ya shigo gida ne kamar haka ya sanar mana sun je jaje kuma yin nemi aurenta an ba su har an daura, yarinyar da bata gani ma amman idonsa ya rufe ya rantsa sai ya zauna da ita”
Salim ya sauke ajiyar zuciya ya saka hannayensa aljihu.
“Yarinyar nan bata cancanci Captain ba ko kadan ko da kuwa bata aikata ba, ya kamata ya lura da yadda duniya take kallonta a yanzu, amman kin san Captain ba a masa daidai, kawai dai mu saka masa ido zai fi”
“Kai ma dai ba zaka iya ba kenan...! Babu wanda yake iya fahimtata”
Ta cige baki tana kallon wani ward din dake facing dinsu, Salim ma gurin yake kallo sai dai kowa da kalar tunaninsa. After Salim ya fice Captain ya tashi zaune
“Ina fatan dai ba wata matsala ta ja rashin lafiyarka ba?”
“Aa rashin lafiya ne kawai babu wata matsala Daddy”
“Ma Sha Allah, daman ina da niyar kira na maka albishir sai kuma Ammynka ta sanar da ni ciwonka a take tawun giwa ya take na rakumi”
“Akan Adam ne?”
“Ka ga video ne?”
“Aa zan sauke kenan ka kira ni, amman Salim ya fada min Adam din ya aikata abun da ake bukarta ya aikata”
“Ya aikata yayi kamar yadda muke bukata, mahaifinsa ya turo min da video, domin ya kara kira bayan ya tafi gurin mahaifin yarinyar be yi nasara saboda na yi waya da shi na fada masa duk irin magiyar da za su masa kar ya aminta da su, sai kuma ya dawo ni ma yana rokona sai dai ban bashi wata amsa ba bayan wanda ka bashi, kuma na tabbatar masa a jibi Monday za a shiga kotu, sai gashi yau ya turo min da video”
“Na jidadin hakan Daddy thank you very much, da goyon bayanka ne na samu wannan nasarar, zan yada video, na san hakan zai wanke yarinyar nan ko da ba gaba daya ba, zata yi farinciki idan ta ji i wish ni zan fada sanar mata ma saboda na mata wannan alkawarin”
Daddy yayi murmushi.
“Yaron
Showing 165001 words to 168000 words out of 215510 words
CAPTAIN JAMAL POV.

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56 Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72