a tabarmar

Murtala yace Anne baiwar Allah ga iya tuwo da Miya,Sanda hakoranta na karshe turmi zai fice tace Murtala sa kibiya ka banbro min shi,Amma matar Nan Haka ta soye min Gilala ta,ba komai Allah yaji kanki amma tooooo na dai Yi shuru amma da kyar ne idan ba a fara Jibgar Anne a kabari ba,watakil tana can an Mata butar Malam,Fauzan yace ka Fadi Alkhairi ko kayi Shuru,Murtala yace an gama Oga amma gaskiya Anne zai wahala ta tsallake siradi,Jannat ce ta fito ta rako wasu Murtala ya Mata gaisuwa,Fauzan kuwa suna hada Ido ya kashe Mata Ido daya saura kadan tayi dariya.

Da rana ana ta kawo abinci kala kala Hamida ta tashi ta koma wajen Abinci duk wani abinci me dan dadi sai ta juye a wuri na daban,a kitchen take buya taci ta cika cikinta sai ta fito ta zauna idan ance abinci tace sai anjima,Kunu aka kawo na daka lafiyayye Hamida ta mike ta karba tayi can wajen wata Amarya a gidan dake gidan yawa ne,a can tayi Sallah ta Sha kunu ta koshi ta dawo kusa da su Jannat tayi malaho harda sadda Kai,Jannat tace Aunty tun safe baki ci komai ba ga aikin juye abinci da rabawa kina ta Yi ki samu ki sa wani Abu a cikinki,Pipi tace hmm wa zai baka cin abinci a babbar mutuwa irin wannan,Ni kaina iyayena nake tunowa sai tsusayin Anne ya Kama Ni,idan aka yi mutuwa dole sai kaji ba dadi bazan iya cin komai ba kyale abincin Nan jannat.

Tana zaune taga makwafta sun kawo Dambu me rai da lafiya Yana tiriri tace bari a juye sai a hada da na dazu a sallami bayin Allah,Jannat tace Sannu Pipi Muna godiya tace ai an zama daya,tana karba tayi kitchen da dambu plate Guda ta zuba taci ta koshi ta rage ta dawo ta rabawa wasu da Yamma gaf da zasu tafi sai data Kara cin dawake sabo da Hamida ita laulayinta cin abinci da yawa take yi, da su Fauzan suka tattara suka tafi Abuja,Jannat sai da akayi Uku ta dawo,Fauzan ya dakko abarsa a airport Yana ta zumudi kwana Uku baiyi komai ba,Bayan Yan kwanaki suka Shiga bikin su Zee dukkansu sun shiryu,anyi biki na gagara ko wacce an kaita dakin mijinta.

Hajiya Amatullah tun tana damuwa har ta hakura da auren Mummy suna zaune lafiya sai dan abinda ba a rasa ba,Mama Kuwa shiri suke sosai da Jannat.
Itama Jannat ta shiga University.
Bayan wata shida Hamida ta haifo yarta mace kyakyawar gaske taci suna ummussalama kyakyawar gaske Kamarsu daya da Lele wata biyu tsakani Jannat ta haifo twince dukkansu Mata zuka zuka,Fauzan sai Murna duk ya rasa inda zai da kansa ranar suna aka sa musu Fuad da Fudhal.

Bayan shekara biyu Mummy cikinta ya tsufa sosai ba a dade ba ta haifo 'yan biyu itama duk maza,Jannat sai Murna take tayi kannai,ba Wanda bai taya Mummy murna ba,lokacin Pipi ta gama degree abinta,Jannat ma tayi nisa,Arzikin Nabeel ya Kara bunkasa,ga Affa yayi retire Lele shike komai na gidan,Fadila ta girma ta shiga primary 5,Fauzan lokacin Jannat ta samu wani cikin shima arziki sosai ya bunkasa,kowa Yana cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali sai abinda ba a rasa ba kasancewar dan Adam baya rabuwa da jarabawa kala kala ta rayuwa.

Aslam Yana yawonsa ko Ina sai rigima,yau Sunday Nabeel Yana gida babu inda yaje,Pipi tana kitchen tana tsantsarawa me gida girki kamshi ya cika gida,Aslam ya shigo da gudu su Fuas sunzo Mum Yana Jan rigar Pipi,to je ka fadawa Dad,da gudu ya fita har da faduwa Lele yace sai ka Fadi baza ka taho a hankali ba sai kace mamanka a Kauye,Aslam yace cikin gwarancinsa Fu'as ne ya Jo,sai ga su Jannat sun shigo tare da Fauzan da yaransu abin sha'awa,Hamida tace Alhmdllh sai ku tafi min da Aslam,da gudu ya fada bayan Nabeel yace Daddy ni wajen Mimi zanje,Fauzan yace wa zai dauke ka dama ka damemu da kuka.
Zama sukayi suna ta hira anci an koshi a gidan Suka yini.
Suna kallon news suka ji an Kama wata Mata Yar asalin Niger tana safarar miyagun kwayoyi,ana hasko matar suka ga Hajiya Talatu ce ashe ,an yanke Mata hukuncin daurin Rai da Rai a kasar China.

Hajiya Talatu duk abinda ta kwashe na Abba ya Kare ta kashe su wasu sun damfareta millions of Naira karshe shine ta koma safarar kwayoyi da ragowar kudin Abba.
Yaranta biyu mace da Namiji Kuma aka dawo da su Nigeria.
Su Nabeel na gama ji Suka dunguma hukuma aka shigar da komai sai da aka tabbatar kannen Jannat ne sannan aka Basu yaran,Mimi ce ta karba zata rike su,Affa sai Murna ya masu Yara zai rike ya samu Lada.

Ita Kuwa Talatu sai kuka sai nadama gashi abinda ta tara cikin kankanin shekaru sun Kare, karshe anyi gidan yari da ita,dama China su akan harkar kwaya basa dagawa kowa kafa kisa suke yi,Talatu tun tana kuka har ta daina,ta fita a hayyacinta gaba daya.
Basma ware Baiko Kuwa ta hada kungiya guda ta mata itace shugabar Mata ta gidan yari sai abinda tace da Mata ga zalunci,duk ta addabi Yan prison kowa ya tsaneta a ciki.

Wata tantiriya aka kawo gidan yari wacce ta gagara ita Yar daba ce ta gagari ware Baiko a Iskanci tana zuwa Basma ta mata wani kallon banza,ai Kuwa matar ta Kama Basma Ware Baiko ta lakada mata dukan tsiya ta farfasa mata jiki,sai Murna akeyi ana Allah ya kara.
Yan matan Basma ne Kawai suka ji haushin dukan Basma da akayi sabo da gaba dayansu Yan matan sunfi su ashirin Lesbian sukeyi,Basma duk amfani take da su a boye a prison din.
tunda ma'aikatan suka gano sai aka dauketa aka maida ta prison din Lagos acan ake cin ubanta gaba daya wahala tasa tayi ladab Kamar ba ita ba,tana zaune sai kace an tonota daga cikin toka kanta ko dankwali babu ta rakube a jikin wani karfe ga aikin wahala,a wajen ta tsuguna tare da fashewa da Kuka abin gwanin tausayi tana na cuci kaina sai ta sake rushewa da kuka,Wata Igbo me karfin tsiya tazo ta sharara mata Mari ta bata aiki taki yi ta zauna tana uban kuka,Kafa Igbo tasa tare da yin ball da ware Baiko ta sake rushewa da kuka ta rarumi cuttlas ta tafi aikin sassake ciyawa tana bawa Igbo hakuri ba shiri ta fara aikin tare da wasu yaran matan Suma.

Pipin Lele ce ta dau wanka ta fito tana jiran mijinta a jikin galleliyar mota,Daya Yar tana kafadarta, Lele ya fito tare da Aslam rike a hannunsa sun zuba gayu wata dalleliyar mota Suka shiga driver yaja su tare da tafiya yawon shakatawa.
Jannat Kuwa da Fauzan suna Bedroom suna zuba Hidima Kamar zasu kashe kansu.



(END) karshe

Nan na kawo karshen Ware Baiko Allah yasa muyi amfani da darasin Dake cikin wannan Novel

Kuskuren da muka Yi Allah ya yafe Mana.

Masu sharhi Ina Matukar godiya da jinjina

Wanda ban bawa page ba ayi min afwa na gode

Sai Allah ya kai mu mun hadu a sabon Novel

🥰💕🥰🥰zanyi missing naku fans

Copy By Zainab Butalawa




AsmaBaffa

Showing 132001 words to 133235 words out of 133235 words