ma,a kunyace tace Ina yini Sannu,Yace Wai mene kike Jin kunyata? Murmushi tayi ta sake gyara hijab dinta tare da rufe fuskarta kusan gaba daya,yace Jannat tsakaninki da Allah baza ki fadawa Affa inda kike ba ko zai samu ya maidaki inda ya dakko ki kin San irin damuwar da yake ciki?
Kanta ta sadda kasa tana kallon yatsun kafarta hawaye ya dan Fara sakko Mata tace nasan ban kyauta ba Zan Koma ne..

Wata magana ce ta kawoni wajenki Jannat ta kalleshi kadan tare da maida kanta kasa tace to Ina ji,yace Ina sonki Jannat wlh tunda na ganki a Abuja naji Ina kaunarki in ba damuwa mu koma ni na yarda Affa ya daura min aure da ke,Zan rike ki Amana Jannat,Ina Matukar kaunarki,kullum da tunaninki nake kwana nake tashi,duk abinda kike so a duniya Zan Miki ko million Nawa ne Zan baki tunda Naga Kamar Neman kudi kike da jikinki.

Kallonsa tayi ya gyada Mata Kai yace wallahi ko Mene Zan kashe a kanki in ma ba a kasar Nan kike son Zama ba Zan tafi dake London muyi rayuwa a can,Jannat tayi Murmushi Kawai kanta har yau Yana kasa sabo da kunyarsa da take ji,yace ya Kika ce? a hankali tace kayi Hakuri Ina da Wanda nake so shine rayuwata,duk abinda nake nema a duniya ya gama Yi min,Ko Nawa ya kashe ya fada ni zan biya shi burina ki aureni Jannat kece rayuwata haba me dadin suna.

Jannat tace nidai kayi Hakuri wallahi ko duniya zaka bani bazan iya rabuwa da Abba ba,au sunansa Abba? Jannat tace ae,yace Allah wadaran Abba Kuwa ya cuceni Kika sani ma ko Dan Iska ne kike bata lokacin ki,ba Dan Iska bane Jannat ta hayayyakowa Fauzan da masifa ya zagi Abbakatinta, sorry ya furta
Bazan miki dole ba Allah ya bada zaman lafiya idan biki yazo kije kiga Affa dan Allah, Inshaallah ta furta,ya sake cewa Allah ya bani me so na Nima irin yanda kike son Abba,tace Ameen tana ta Jin kunyarsa,Kudi ya zaro Wanda bai San Nawa bane ya Mika Mata fafur taki karba tace na fada maka ni Abbana yana min komai,yace ai a madadin Affa na baki,karba tayi tace na gode ya Mata sallama ya tafi Yana ta dariya a mota harda cewa woo shege ni Yana driving dinsa.

Kullum suna wayarsu suna soyewa da Fauzan Wanda bata San shine Abbakati ba,har ranar da zasu koma hospital tazo,su Zee Suka ce zasu gaisa da shi idan yazo kofar gidan,Jannat tace ku bari zaizo musamman,Suka ce ba damuwa,Yana zuwa gate dinsu ta fito sanye cikin lace milk and Golden takalminta,mayafinta da jaka Golden,tunda ta fito yake kallonta ta cikin glass dinsa, ya dauketa Suka je ba bata lokaci aka ce su shiga,duk ga mutane nan suna zuwa da alama ziyara ake Shiga, ita dama tasan Hanya itace ke nuna masa Hanya dake katon asibiti ne sai da Suka Yi tafiya me nisa kafin su Isa wani bangare Wanda ka rantse a daji wajen yake wani katon daki Suka shiga,farkon shigarsu sai da Fauzan ya tsorata da irin marasa lafiyar da ya gani har idonsa yake rufewa bai taba zaton a duniya da marasa lafiya irin wannan ba.

Gaba daya wata irin halitta ce da su ta daban,wani me Kalar wani ciwon ma bai taba ganin irin ciwon ba,baza ka taba cewa mutanene ba,sai ka rantse Aljanu ne abin ba kyan gani ko kadan tsoro ne ya kamashi Addua Kawai yake a bakinsa.
Wata nurse tace Jannat an Zo ne ai ku Kuna layin masu sauki sauki kuje,wani daki Suka sake shiga wani gadon ruwa Jannat ta nufa Wanda Sam ba a gane wacce halittace macece ko Namiji sabo da gaba daya in banda Kashi sai fata a jiki,Kamar kwarangwal,gashin kanta babu ko daya,sai a wani gadon ruwa ake kwantar da irinsu in ba haka ba zagwanyewa zasuyi su rube a hakan ma wani wajen duk ba fatar ma Sai Kashi gashi nan ana gani an nade da bandage da auduka kowa sai wayyo wayyo Kawai ake ji,Jannat a gaban gadon ruwan ta tsuguna tace Mummy matar nan duk wayyo wayyo da takeyi sai data gane muryar yarta,bata iya magana sosa amma da kyar ta hada kalmar Jan..Jan...sai da ta huta tana numfarfashi ta sake cewa ki roka min Allah ya dauki raina na huta,Allah...Allah...ya Miki Albarka...Allah ya baki miji na gari...Allah ya tsareki da Sharrin duniya....Ni Kam nasan bazan tashi ba...shi...shi....shi...yasa nake so naji kinyi aure....
Jannat tuni zuciyarta ta karye ta fashe da kuka me tsuma zuciya,jin Haka matar tace Zan warke Inshaallah...ki daina kuka bani hannunki naji....Jannat tana kuka ta kamo hannun Mummy ta damke suna ta kuka a Haka.

Shi dai Fauzan tausayin Mummy ya kamashi kamar zaiyi kuka ga marasa lafiyar dake wajen ba me iya zuwa wajensu sai Mai juriyar gaske,Jannat tace Mummy ga mijin da Zan aura na kawo Miki shi yazo duba ki,Matar nan tace Alhmdllh daga yau na daina kuka ko yanzu na mutu Allah ya Gama min komai,Jannat ta kamo Hannun Fauzan ta hada Dana Mummy ta damke hannunsa tana sa Masa Albarka Wanda shi baya gane me take fada ko daya ma Jannat ke fada Masa abinda take cewa.
Mummy ta sake yin Mimimi da baki a haka magana take Yi Jannat ta fassara masa tace Allah ya maka Albarka,Fauzan yace Ameen Ameen Allah ya baki lafiya.

Masu kora ne Suka Zo suna cewa lokaci yayi kowa ya fita aka Kori kowa aka rufe wajen.
Wajen Doctor Jannat Suka koma yace Jannat I'm sorry to say mahaifiyarki ta cike iya kwanakinta Wanda aka gama kayyadewa in mutum bai warke ba zuwa wannan lokacin to an daina kawo Masa ziyara,Kawai kudin kula da ita Zaki ci gaba da turawa duk wata,amma bazan boye Miki ba,dakin da za a kaita sai me nisan kwana ke Fitowa daga ciki za a barsu a Nan ana dan basu treatment idan Allah yayi tana da nisan kwana ta warke idan kuma kwananta ya Kare to za a kiraki ku dauki gawa Kuma kin San komai tunda an fada Miki.

Jannat duk iya dauriyarta ta kasawa tayi hawaye ne ya balle Mata tace ba komai zanci gaba da Mata Addua da ace Ina raye Ina kallo uwata ta mutu gwara ta mutu a asibiti ko banza idan na tuna zan San nayi kokari Allah ne baiyi ba, Allah yasa ta warke yace Ameen,Fauzan Yana kallo yace Nawa ake biya duk wata? Yace dubu dari biyu,Nan take ya karbi accnt din asibitin,suna barin asibitin ya tsaya a bank ya biya na wata biyar,yace Zan tura wasu bayan biki ya Mika Mata tailer.

Godiya ta dinga Yi Kamar zata goya shi,kafin ya tashi motar Hannu yasa tare da goge mata hawayenta yace cry no more Inshaallah zata warke ai cuta ba mutuwa ba sai kiga me lafiya ya mutu marar lafiya ya mike karki damu Allah na Nan.
Tana ajiyar zuciya tace In...Inshaallah.
Kayan ciye ciye dana Sha ya siya musu yace sai Ina? tace muje Queens Garden sai na baka labarin a can I think is better, ba gidana ba?shedan Yana kusa Kuma ma gidan da za a kaini Zan gama kalle shi,yace farko Mama tace a gidamu za a ware Miki part ki zauna kafin mu koma gidanmu,ba damuwa cewar Jannat.

Wurin shakatawar Suka je ba mutane a ciki sai dai dai,Katuwar Sallaya ya shimfida musu suka zauna suna cin Shawarma da Ice cream tace Kamar yanda ka sanni Hannu ya daga Mata yace bari Mana mu gama ci,okay tace sai da suka gama sannan yace Ina jinki to Alhmdllh Yanzu naci na Sha sai ayi ta yi Ina ji start

Labari

Jannat tayi dariya tace
Babana dan asalin Bauchi ne shi kadai Iyayensa Suka haifa suna da arzikin dabbobi ya taso cikin gata su Suka daure Masa gindi yayi ilimin boko dana addini,bayan ya gama Diploma Iyayensa suka zabo Masa Mata a cikin dangin sabo da Babarsa Hajiya Saudatu da suke cewa Anne itace ta zabo Masa matarsa Talatu Yar yayarta ya aureta,bayan ya aureta Allah bai taba sawa sun Haihu ba har yaje matakin degree ya samu babban Aiki a NNPC lokacin Kuma mahaifinsa Yakubu ya rasu
Haka arzikinsaYana ta bunkasa

Babana Alhaji Usman Yakub mutumin kirki ne sosai da sosai akwai kyauta da taimako ga addini amma akan abinda mahaifiyarsa ke so ko yake so to fa idonsa rufewa yake Yi,danginsa kaf shi yake musu komai sai abinda yace daga nan ma da arziki yayi arziki sai ya tattara ya dawo da matarsa Hajiya Talatu da Mahaifiyarsa data rage Masa wato Anne,Anne sabo da tana son Talatu bata damu da rashin haihuwarta ba sai ma hanawa tayi tace baza a Mata kishiya ba,har Abbana ya koma England Karo karatu da iyalansa kaf yake tafiya Kuma suzo hutu

Watarana ya gama Phd ya dawo an Masa Karin girma arziki yayi gaba ya Zama kusa a kasar nan,Watarana da watan Ramadan yaje masallaci Jin tafsir da Yamma a Nan Abuja sai ga Yan agaji sun kawo wata budurwa amma ba yarinya bace zata Kai shekara 32 Suka ce wani yare ce a Nigeria can kauyen Ogun state suke Yan ta'adda sun kashe musu kowa a kauyensu sun kone Kauye Suma da kyar wasu Suka tsira ciki har da ita.

Ta shiga zaga gari gari Neman taimako tayi aikin wanke wanke da shara a gidajen masu kudi daban daban amma wahala da wulakanci ke korarta har Allah yasa ta samu aiki a Nan Abuja a gidan wani me kudi Nan ma wulakanci kala kala,ita Kuma babu abinda yake birgeta irin musulunci tunda yanzu ba dangi ne da ita da zasu hanata ba tana dai da Yan Uwa a Lagos Suma ba zumunci suke ba amma sun San dai juna ana gaisawa watarana.
Kawai sai tace zuwa tayi a musuluntar da ita Kuma a taimaka Mata da wajen kwana,Mummy Kyakyawa ce matuka fara babu Wanda bazai so ta ba,Nan take ta Musulunta a masallacin ta zabi suna Asiya Abba yace shi Kuma Yana sonta idan ta Amince zai aure ta.

Kowa yayi farin ciki ana ta yabonsa a Nan malamin ya nada Mata waliyyai Abba ma ya bada nasa lokacin ma Yan Uwansa maza sun Zo Watarana a Nan suke azumi sune shedu Nan take ya bada sadaki dubu hamsim aka daura Masa aure da ita.
Sai a ranar Anne taji da ita da uwar gidansa Talatu ai Kamar Abuja zata Kama da wuta haka suka dinga bala'i,Abba yayi ta bawa Anne Hakuri da matarsa yace kaddara ce, Bayan nan Suka Yi kamar sun hakura da komai, ya bawa Mummy part dinta daban.

Daga ranar Kuma Anne ta fara kishi da Mummy tare da Hajiya Talatu Suka hade kai basu da aiki sai zagin Mummy da wulakanci kala kala bata da katabus a gidan nan duk aikin gidan nan itace takeyi shekara daya ta samu ciki,Hajiya Talatu tana Jin labari taci kwalar Abba tace munafuki kaje kayi Mata ciki ni kaki kayi min wallahi bata Isa ba Nima sai na samu ciki,Fauzan yace tab hauka sai Mata

Jannat tace Anne tace kayi mata Kamar yanda ka yiwa Amarya ciki itama Talatu ai itace uwar gida itace ya Dace ka Fara yiwa yawwa yanzu sai kayiwa Talatu ciki itama,Abba yace ciki ai Allah ke badawa ya kuke abu Kamar jahilar,Anne ta fashe da kuka tace yau akan Amaryarka banza Asiya kake kirana da Jahila,Abba yace kiyi hakuri ba haka nake nufi ba,da kyar ya lallaba Anne ta hakura,watan cikin Asiya biyar Talatu ma ta samu ciki,Anne tace dan jakar uba yaji wuya da ace ban Masa kaca kaca ba ai dai bai Miki cikin ba,Talatu tace ai duk da haka bai birge ba tunda daga zuwanta zata rigani haihuwa.

Ana zaune masifar yau daban ta gobe daban har cikin Mummy ya shiga wata tara tunda suka ji labarin watan haihuwa ya Kama Anne ta saka Talatu a gaba Suka tafi Kauye Wai zasu je zaga dangi dan Kar ma su taimaki Mummy,gashi Mummy bata da kowa sauran a Lagos suke ba wani ma mutunci ne da su ba suna ganin su Yan birni ne basa harka da Mummy,cikin ikon Allah ranar da Mummy zata Haihu Abba Yana gida ya kaita asibiti tare da wata dattijuya me aikin talatu,ana zuwa ta Haihu lafiya kalau ba wata matsala har akayi suna Basu dawo ba,har Mummy tayi sati biyu sannan Suka dawo

Suna dawowa Suka ga Namiji ne ashe sabo da a garin da sukaji ana zancen Amarya ta Haihu ko saurarar zancen basuyi ba,Anne ko yaushe a karbowa Talatu maganin gargajiya take Wai duk dan ta Haihu lafiya sabo da Talatu Yar gidan Yayarta ce,sai ga ikon Allah lokacin da Talatu ta zo haihuwa sai aiki aka Mata aka Ciro jaririya mace.
Tunda taji sauki aka sallamota ta dawo sai tace bata San zance ba me yasa Abba ita bai Mata cikin Namiji ba,Kuma ta ya za ayi Amarya ta riga ta haihuwa bayan daga baya aka aurota,suna ta wannan, rayuwa tayiwa Mummy tsanani kullum sai kuka sai Addua Allah yasa ma tana zuwa makarantar Islamiyya sabo da ta kula da addininta.

Watarana Anne tace Mummy taje ta dama Mata kunu a kitchen tana shiga kitchen Talatu ta Shiga ta durawa jaririn Fiya fiya a bakinsa,sai da Mummy ta fito taga gawar yaronta bakinsa Yana ta warin fiya fiya,Mummy tayi kuka,Abba Yana zuwa ya tara Yan aiki ana bincike wata a ciki tace Hajiya Talatu ce ta ganta da idonta,Anne ta fashe da kuka tace idan yayi magana sai ta tsine Masa Abba Yana gani ya hakura Kuma shima bai damu ba sabo da yafi son Talatu tun asali duk abinda tayi bata laifi a wajensa Watarana ma yasan gaskiya amma sai ya take.

Cikin ikon Allah bayan wata biyar sai Yar Talatu ta kama cuta a ranar da aka kaita asibiti ranar ta mutu,Suka ce Mummy ce ta kashe Mata 'ya sabo da taga danta ya mutu a lokacin sai da Abba ya farfasawa Mummy jiki,Kaf Dangin Abba sun tsani Mummy arniya ma suke kiranta da shi, sabo da mutuwae yarsa ya saketa,bata San inda zata je ba sai Anne tace a bata boys quarters ta zauna ciki sai ta dinga musu wanke wanke da shara da aikin gida,Mummy ashe tana da ciki bata sani ba sai da ya saketa da sati daya ta fada Masa Abba yasan gaskiya sai yace shi wallahi ba cikinsa bane Sam,Anne da Hajiya Talatu suna zuga shi.

Tafiya tayi nisa kullum Mummy itace ke aikin gidan komai da komai ga duka ga zagi ga hantara ita Kuma sanadin cikin da take da shi na Abba shi yasa taki tafiya ta bar gidan,a haka cikinta ya shiga wata tara,lokacin Talatu ta sake samun ciki ya zube amma,Suka sake cewa Mummy ce mayya.
Daga nan Mummy ta Haihu da kanta a daki ta gyara kanta da jaririyarta Ni kenan nice,Allah yasa Abba duk wata Yana biyan Mummy kudin aikinta su take tarawa da kudin tayiwa kanta komai da me haihuwa ke yi har Tinkiya ta siya da kudinta aka yanka naci suna Jannat.

A haka na taso Mummy na raino na tana tara kudin aikinta har Talatu ta samu wani cikin yaron data haifa bai zo da rai ba har na shekara biyar lokacin nasan yanda Talatu da Anne suke dukana sun tsaneni sosai ko bangarensu bana zuwa amma duk da haka har bangarenmu suke zuwa su min duka,tace in munyi aure zaka ga inda Talatu ta yanka min duwawu da wuka,Haka Mummy ta samu makaranta me tsada ta sakani primary da Islamiyya me kyau,tun Ina Yar karama take koya min karatun addini amma bata Yi boko ba nice idan na koyo karatun boko sai na koya Mata,Muna haka har na shiga Secondary,a lokacin duk aikin gidan Nan tare mukeyi da Mummy duk sun sallami Yan aikin Mata,Abba Kuwa baya kaunata,baya kaunar ganina,Mummy har Kara ta kaishi wajen Yan Sanda amma abinka da me kudi ko fada basu Masa ba sai Suka ce Kawai ya barmu a gidansa muci gaba da Zama a matsayin yan aiki,lokacin Kuma Talatu ta Haifi danta Namiji,Mummy in kaga yanda ta lalace duk ta rame amma a haka ban rasa komai ba komai tana min Kaya masu kyau nake sawa makaranta me tsada.

Talatu da Anne suna ta Jin haushinmu har na gama Secondary Abba baya kaunar ganina karshe ma suka hanashi ya dinga biyanmu kudin aiki sukace kyauta zamuyi kudin aikinmu shine Zama a gidansa ,ranar da bazan manta da ita ba itace ranar da munyi girki da Mummy mun gama zamu ebi abinci dake dama abincin sai taga dama take bamu Watarana sai dai muci a boye,tana hanamu iba Muka tafi sai da Yamma bayan na gaji na tafi Islamiyya sai ta kawowa Mummy abincin ranar Mummy tayi mamakin ganin abincin da yawa,Haka taci ta koshi ta ajiye min nawa,na dawo daga makaranta Kawai na iske Mummy kwance tana murkususu,na fashe da kuka na fito na Kira masu gadi su taimaka min amma Anne ta fito tace duk Wanda ya ko kulani a bakacin aikinsa.

Da gudu na tafi na kirawo Abba,Ina kiransa da Abba ya kwada min Mari ya kore ni yace shi ba ubana bane, na fito Ina kuka na rasa wa zai taimaka min na fita na kirawo me taxi shi ya taimaka min na kwaso kudin da Mummy take Tarawa Muka tafi asibiti

Labarin Nan yanzu aka fara sai gobe Zan ci gaba kaga yanzu dare yayi yace no muje gidana ki karasa min a can,tace hadari fa yace
Showing 102001 words to 105000 words out of 133235 words