a gindin wata bishiya ba gida gaba ba gida baya ga yunwa da kishirwa kwanciya tayi tana kallon sama tayi flat tayi kuka tayi kuka tare da tsinewa Shehu ta daga hannu sama tace Ya Allah badan hali ba Allah ka nuna min hanyar da zan fita daga dajin Nan,Allah ka kawo min agaji yunwa da kishirwa zasu kashe ni ya Rahman ka ciyar dani

Mikewa tayi da kyar take taka kafarta haka taci gaba da tafiya sai data sake yini Yamma likis tana tafiya a cikin dajin sannan ta sake Zama a wata bishiya tana hawaye tana Addua tare da Kiran sunan Allah ta koma Kiran Lele,Nabeel,Yaya kyakyawa tun tana Yi ta koma papa da Yaya Sulaiman yunwa taci karfinta baza ta iya tashi ba.

Tana kwance taji wasu maganganu a kanta lokacin da kyar take gani dishi dishi taga wasu mafarauta su biyu da kayan harbinsu,a hankali tace ku taimaka min sace ni akayi daga wajen Yan kidnapping Allah ya kubutar dani,ruwa Zan Sha dan Allah,Wani a ciki ya tausaya Mata yace ai kin kusa bakin titi ma tashi ga ruwa hannunta na rawa ta karbi robar ruwan da ya Miko mata ta shanye tas,dayan ma ya bata tasa robar ta karbe ta shanye,wani a ciki ya zaro fura a cikin leda da yayi guzuri da ita ya mikawa Hamida ta karbe tunda ta kafa Kai a ledar sai da ta shanye tas duk yawanta bata rage ba tace bawan Allah bazan muku Kara ba ta jefar da ledar sannan ta koma ta kwanta sai data huta sosai taji karfi a jikinta ta mike tace ku nuna min Hanya naji garau yanzu na gode wayyo naga duniya

Suka ce muje sai mu saki a motar garinku,Tace na gode Suka tafi gaba dayansu tace amma dan Allah idan akwai waya a wajenku Zan Kira mijina ince na kubuta,dayan yace ki bari mu Isa bakin titi sai a Kira shi tace to suna tafiya tana basu labarin komai

Basu dade ba sai gasu a gefen babban titi Hamida murna Kamar zata yi me itace a gaba tana tafiya zungwi zungwi sannan Suka zaro waya ta karba tana Murmushi ta saka number Nabeel tayi dialing lokacin Nabeel Yana kwance Yana tunanin Hamida yaji wayarsa na Kara tunaninsa jami'an tsaro ne da sauri ya daga,Hamida tana Jin muryarsa yayi sallama ta kyalkyale da dariya Kamar yana ganinta tace Lele pipinka ce na fito Allah ya kubutar dani ka ganni za a sani a motar gidanmu ayyiriri Chaka lubaye chasss gani a bakin titi kaji karar motoci ta sake tuntsurewa da dariya tana murna,Nabeel ma har wani dan ihu ya saki yace yau yau zanzo garin zanbi flight gamu Nan zuwa.

Su dai Hamida dariya take basu ba takalmi ba mayafi a haka Suka sata a mota Suka biya kudin motar,dankunnen Gold dinta me tsada da Lele ya siya Mata shi ta cire a kunnenta ta mikawa mafarautan tace gashi ku siyar na baku kyauta sabo da taimakon da kuka min,kin karba sukayi Hamida ta dirgo daga motar bus tana rokonsu da kyar Suka karba sabo da sunga passengers suna jira,Hamida Yan motar sai tayata murna suke ta dinga basu labari kuwa Ana ta mamakin tabarbarewar al'umma makwafci wani baka San sana'arsa ba sai addua Hamida tace na yarda da shi sosai har sirri nake da shi ashe shima sana'arsa kenan.

Nabeel Kuwa sanar da mutanensa yake Kawai Yan Uwa suna ta tayashi murna,Ammar,Mimi,Affa da Nabeel Suka bi jirgi sai Adamawa,can Dangin Hamida ana ta murna ta bayyana,tana zuwa wanka ma botiki biyar ta Kai bayi kamar zata cire fatarta da gashin kanta sai da tayi fes fes dama Allah yasa ita bata Sha wahala a hannunsu ba wahalarta daya wannan tafiyar da tayi a daji gaba Daya kafafunta a kumbure suke,bata da kayan da zata a sa a gidan duk an tafi da su gidan mijinta sai t-shirt din Ummi ta zabi karama ta saka sannan ta daura zanin atamfar Ummi ta saka wata sabuwar Hula da Ummi ke siyarwa mutanen kauyen ba karamin Kyau tayiwa Hamida ba,sallolinta ta rama ana ta zuwa tayasu murna ko abinci bata samu ta ci ba sabo da mutanen dake turuwa Yan Uwa da abokan arzuka.

5pm su Nabeel Suka iso lokacin Hamida ta saka daron abinci a gaba shinkafa da Miya ga salat dinta a wani shegen plate an toza shi ka rantse mutum uku ne zasu ci,pure water a gabanta leda guda me sanyi,Papa ya siyo Mata wasu jelar kifi soyayye ta dora a saman abincinta hannayenta ta wanke ta zauna ta fara ci kenan taji muryar su Mimi da sauri ta wani ware murya ta amsa sallamarsu Wai Dan aji ta dawo fa da gaske,Har Affa sun shigo gaba dayansu palon Hamida ta bari da sauri ta fada tsohon room dinta Wai Kar aga Kalar abincinta da shegen yawa,mayafi ta yafa ta fito da farin ciki ta durkusa suka gaisa da su Affa,ta saci kallon Nabeel Suka hada Ido ita yake ta kallo zanin ya Mata kyau dake tana da hips ga duk jikinta luwai luwai ita ba me kiba ba Kuma ramamma ba,Signa ta Masa da Ido ya saki murmushi, Affa yace Hamida Kun Sha fama Hamida ta Basu labarin komai suka dinga mamaki wai Shehu ne ma,Affa ya kalli Nabeel yace kaga abinda nake fada maka shi yasa na hanaka Kama Doctor Ahmad da yanzu munji kunya Wanda baka zato shike aikata ma wani abin,kaga dai Shehu wa ya damu da shi an manta ma da shafinsa ashe Yana cikin Yan ta'adda ba
a sani ba,Mimi tace mugu bai da Kama ai wlh ai gashi nan rayuwarsa ta Kare shima dama dubunsa ce ta cika ta sanadiyyar Kama Hamida Suna ta zancen da Ummi da Papa,Ummi yanda take bada labarin Kamar itace aka sace.

Hamida bedroom ta koma ta fara cin abincinta sai Ummi tace jeka wajenta Man,ai dama kadan yake jira ya mike ya shige bedroom din Hamida ko Ina neat Yana kamshin turaren wuta,tana kasa a zaune tana hada kifinta da shikafa tana ci shi dariya ma ta bashi yanda take ci Kamar zata hada da hannunta, ba Bismillah Pipi? Hamida ta kalleshi tana Murmushi tace ban dawo hayyacina bane zo muci to idan mun cinye sai a Karo wani,rabon da yaci abincin kirki tunda aka sace Hamida,Sallaya ta shimfida Masa a kasan tiles din da Papa ya musu ba dadewa duk ya gyara gidansa sosai basu da makusa tun asali gidansu me kyau ne tiles ne Kawai yayi shi ba dadewa.

Zama Nabeel yayi suna facin juna ya dauki spoon din data ajiye a gefe ita yake ta faman kallo ta masa kyau ne sosai,Hamida ta tsaya da cin abincin ta shiga tambayarsa mene? nayi muni ko? Ya za ayi sai hakuri dama abinda nake ta Jin tsoro kenan Kar dan haskena ya dishe dama yaya abin yake,mazan yanzu Kunfi son kuga mace ta kashe titi da haske to ni kaga dama ba Fara bace irin kal kal na Sha wahala dole na dan hasken ya ragu amma sai ni naga da haske na ma.

Murmushi yayi ba shiri yace kyau Kika Yi wlh ban taba ganinki da single zani ba sai ya Miki kyau dake kina da shape rigar ma ta Miki cif cif masha'allah,Hamida tayi dan Murmushinta me kyau duk kunyarsa takeji ganin yanda ya kafe kirjinta da kallo ta sake kallonsa karo na biyu tace ya akayi da alama Naja'atu ta fara lafiya ko?ai kin san dokar sai Nan da 4months fa sannan Zan iya wani abu,Hamida tace ango ba harka ba shiri ya furta wlh karya kike kullum sai na latseki,Hamida ta rufe fuska ya fuske ya fara cin abincinsa yace ban son gulma kici abinci, Bude fuskarta tayi ta dankaleshi tace Lele me gemun gayu da saje,ke dai ki shafa idan zaki shafa da alama birgeki yake ki daina wani kinibibi cewar Nabeel

Hamida tace to Miko fuskar ya matso Kuwa ba musu ta wani sa yatsa ta dan dangwala tace haduwa dariya ya saki yace zanga ranar da zaki daina shirme yazu da yatsa shine har kin shafa har kin san ya hadu..

Hamida tace Lele Nasha mari fa a wajen ogansu kin fadawa su Mimi nayi,Lele ya bata rai tare da furta Allah ya Isa,Hamida tace cewa yayi fa ya sunana ai dai kasan nace na canja suna ko? Nabeel yace yes,tace sai nace Shakira kafin na rufe baki kaji wani uban mari Kai Lele duk Adamawa nasan baza a samu me iya Marin wannan ogan ba,sai da jiri ya kwashe Ni ba shiri na dawo Hamidata,Nabeel yayi dariya yace maganinki kenan,kaga tuwon dusar masarar nan dana ci kwana nayi Ina zawo kaga Kuwa wajen da ake bahaya tab gashi ana tsaye a kanka da bindiga Ni dai da dabara nake ko fitsari ne,Nabeel yace Allah yasa dai baki bude...kafin ya karasa tace Duwawu ai da dabara nake dan satile pant na dan rufe da rigar,Naga duniya nidai Allah ya shiryeni gaskiya na koma ga Alla.

Nabeel yana ta dariya,tace ai Kai kasan kanka Lele na shiryu pipinka ta nutsu da ace a baya ne ai da tuni a gaban su Affa Zan baje zancen duwaiwai amma kaga Kai kadai na fadawa Kai dinma dan na taba ganin naka ne shi yasa nake iya fada ma,Nabeel yace baki ganta ba sai nan gaba Zaki ganta,Hamida tace Fara ce na ganta tun yaushe Ina ta kallonta Sanda kana min abun nan,muci abinci ban son zancen abin Nan da mukayi Ina nadama,suna ta cin abinci itace ke cire Masa kayar kinfin tana sa Masa a gabansa Yana ci,idan salat ya Kare ta zuba masa suna dan hira sama sama,tace kalli kafata ya kalla ta tasa sosai yace sorry,tace Ni ban son Sorry din nan na bature sai naji Kamar ni ba a tausaya min, sannu to cewar Nabeel tace yawwa tana ta faman shagwaba tana kwabe fuska har Suka gama cinyewa tas taje ta Mike zata Karo yabi mazaunanta da kallo taje ta dawo kadan suka rage a abincin.

Su Mimi suna tsakar gida kasan bishiya suna cin nasu abincin su Hamida Suka fito ta dakko musu sabulu Suka wanke hannayensu Suka koma ciki ya Mika Mata mint chewgum shima yasa daya a bakinsa ta kwanta a saman bed Yana gefen bed din a zaune tace marata ke ciwo sama sama, maybe period zakiyi cewar Lele Hamida tace haka ne ma,Hannunsa ya daura saman mararta Yana shafa Mata a hankali ta lumshe Ido tana Jin sauki sauki sai ya Shiga latsa cikin ta fara dariya tare da buge hannunsa tace bana so kana so a kamamu ace wani abu muke,yace Ni rabon dana tabaki tun Sanda tsautsayi ya faru sai ki ta min wayo,hannunsa ta kamo tace karasa kwashe dadinka ka huta tunda baka San adani ba.

Dariya yayi ba shiri Albarkatun kirjinta dake tsone Masa Ido su ya fara shafawa Hamida ta mike zaune tace a gidan surukan naka ni bazan yarda ba yace to kizo mu tafi dake gida Kinga kin huta,idan Mimi ko Affa sunce sai na bik....bakinsa taji cikin nata Hamida ta fisge bakinta da kyar tace Naja'atu bata da lafiya zaka jawowa kanka ai yanzu dangerous ne a wajenka wannan wajejen ba abin ka kulasu bane,Nabeel yace Zaki sani ne yarinya lokacin nake jira sau biyar sai hudu kullum, fuskarta ta da danne da pillow yanda bazai ji ba tace Iskanci dadi Lele ya Zama nawa ahayye sai ma na sake zama wise a lokacin ne zan nunawa Lele ni din special ce.
Nabeel yaji tana ta wani kuskus bai San me take cewa ba,pillow din ya fisge suka hada Ido tace ta Fara dariya tana wani kunya,me kike cewa? Ya tambaya, Tace ba komai cewa nayi alasittiri bukwi .




Afwan jiya banyi posting ba.

Masu Sharhi kullum Ina Miko gaisuwa






AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

26-30

Official
By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM




Page naku ne

Aimana Haruna
Djamila
Anty Nice
Mamazee
Princess khadija
Mummy NEEMRAH
Ummu Sharhabeel
Ammin Samha
Farida Yusuf Bashir
Rahmat Saed
WasilaIbrahim
Maimuna Umar
Heendu





Hamida ce ta Mike tsaye ta gaji da halin Nabeel na tabe tabensa,Muryar papa Suka ji yace ke Hamida fito ku tafi dakin mijinki,Hamida ta zaro Ido tace papa a Hanya fa aka sace ni Yan Kai Amarya basu karasa dani gidan ba ai nayi tunanin sai an sake harhado Kan dangi a sake tafiya dani,Ummi tana ji tace ji sakarai Yan Kai Amaryar da sai da Suka karasa har Kaduna kwanansu daya Suka dawo sannan Zaki ce sai an sake kirasu sun tafi dake can din bakonki ne ko Nabeel bakon ki ne? Hamida ta turo lips tare da furta to azo a maidani dai dai inda aka saceni sai a daukeni a can ayi reverse a dawo baya, Papa yace ai ke Kam Naga Sanda zaki Zama mutum,Hamida kallon Nabeel tayi taga Yana lumshe Ido zaiyi bacci ta girgiza shi tace tashi Lele har kasa gabana ya Fadi yanda ake mutuwar Nan ta fuji'a haka Rannan wani daga kishingida ya wuce tashi gaskiya.

Dariya ta ba Lele ya gaji shi Kam,Mimice ta shigo tace ku fito mu tafi Mana flight zai wuce mu,Hamida da sauri tace to amma dake su Papa ne ta raina su,Ummi tana mamakin canjin Hamida wai Hamida ke biyayyar suruka har a fada Mata taji ba tijara ba rashin kunya,Lele ya za ayi ban dau wanka ba Zan shiga jirki Kar a rainani mutane suyi zaton ma Yar aikice wasu masu kudin Suka zo da ita daga wani garin,Dariya Nabeel yayi yace sa hijab har kasa sai mu tafi, haka ta saka hijab din Karima data manta shi a gida me Hannu har kasa yake ja,Nabeel yace Kamar zamu tafi da'awa Suka fito Hamida ta musu sallama,Ammar ya fito daga wajen Sulaiman yau rana ta farko Pipi za a Shiga jirgi,motar airport data kawo su ita ta maidasu suna zuwa airport ba bata lokaci suka shiga jirgi Hamida tayi Shuru bayan tayi Addua...

Nabeel fuskarta ya leka yaga bata kulashi ba duk surutunta yace madam lfy? Hannu ta taga Masa baza tayi magana ba sai idan sun sauka lafiya,Dariya taba su Mimi,Ammar dake bayansu yace Amarya? tayi shuru suna Dariya har su Mimi,Ammar yana tsokanarta Amarya ba magana a hankali tace da Nabeel ka amsa min Lele,Ammar ya sake cewa Amarya a kawo Miki juice? Nabeel ya makale murya yayi irin ta Hamida yace ae a kawo,Mimi tace Allah ya shirye ku,Affa yace manyan banza kun dami yarinya ku kuke Yi amma ni nake jiye muku kunya,Hamida dai bata ce kala ba har aka sauka daga jirgi sai data sakko sannan tace Alhmdllh

Driver ne ya daukesu ya wuce gidan Affa a kofar gate ya sauke Affa da Mimi yaja Nabeel da Amaryarsa zuwa gidansa Wanda ya gaji da haduwa komai sabo aka canja masu tsada,Driver yayi parking ta hango motocin Nabeel harda wasu sababbi ta kalle shi kawai a ranta tace Wai ni da ba komai ba a garinmu ana min Dariya ana min kallon mahaukaciya babu saurayin da ya taba cewa Yana so na ko da Wasa yau gashi nice Allah ya daga martaba ta,Wanda Kuma Suka fini ilimi da farin jini Ana ganin sunfi kowa basu samu irin mijina ba ko a nan na godewa Allah,Nabeel ne ya fita a motar tare da Bude mata ta fito ya maida ya rufe driver yaja mota ya tafi dama motar Affa ce.
A Palo ta zauna saman wata luntsumemiyar kujera ta harde kafa tana Shan ac,Nabeel ya haura sama yaje har yayi wanka ya shirya yaga baiga Hamida ta shigo ba sake fitowa yayi ya hangota tana maganganu ita kadai,kunne ya bude yaji tana cewa shike Nan ya Zama gidana yau sai kaji Ina bada address,inama za a dawo min da Sale me gadi da sai na kusa karasa shi da aiki ba irin Maganar da baice min ba ta wulakanci,gashi na koma Auntynsa dole bari na Kama kasa sai na mulki Sale

Kizo kiyi wanka ko sai nazo na daukeki Hamida mikewa tayi ta wani fuske ta wuce shi yace Bari inje masallaci, okay ta furta tayi sama dama gidan ba bakonta bane,bedroom ta zaba dama ta rigada tasan na ogan duk da cewar an canja komai na gidan,Dakin data ciki ta karewa kallo ya gaji da tsaruwa mamaki tayi ganin akwatuna guda takwas da alama na lefe ne,tana mamaki yaushe aka siya mata,wanka ta Shiga ta Dade ciki kafin ta fito tayi Sallah,taga har mudubi an shirya mata ta tuna su Ihalsan sunce sun shirya Mata komai a bedroom kafin a sace ta,Body lotion ta kalla da gani kasan me tsada ne ga kamshi Zama tayi tare da shafe jikinta da man sannan ta zauna a gaban mirror daure da towel fari ta gyara dogon gashinta sosai sannan ta Mike tana bude akwatuna daya bayan daya kayan sawa ne iri iri ga kayan makeup,wata sabuwar Atamfa ta zabo brown and Golden dinkin Riga da skert ta saka abinta sun amsheta sosai ta zuba kyau matuka,ta coka dauri jelar gashin data tufke tana reto a bayanta tayi kyau sosai da sosai ta kalli kanta a mudubi tana wani juye juye ta furta gaskiya ban yarda ba zai wahala ba daga kasar Ethiopia Muka samo asali ba,ba Yar Nigeria bace Ni daga kasar waje iyayenmu suka zo aka haife mu a nan na sani ma,tana shafa turaruka Nabeel ya bude kofarta tare da shigowa bedroom din,yaga yanda ta dawo wata balarabiya yace sai kace a Ethiopia,Hamida ta juyo da sauri tace ya akayi kasan asalinmu ko Papa ne ya baka tarihinmu Ni Kuwa ce min yayi dukkan zuriyarmu yan kauyen Adamawa ne Wai Yan Fulani amma da yawan
Showing 51001 words to 54000 words out of 133235 words