sake naga wannan iskancin a gidannan Kaine ma zaka Mata darasin wanka waye ya saka? Kai har wani wanka ka iya kalleka fa,Shehu yace wallahi Oga idan na nuna Mata sa janbaki ko Rihanna uwar dabbara jambaki ta gani sai ta yaba bare Namiji kalleta kyakyawa ai maza layi zasu dinga Yi,Nabeel ya hade girar sama data kasa yace wallahi ka koya Mata cin abincinka yazo karshe,Hamida tace dan Allah Malam kayi sauri bako zanyi,Shehu yaci gaba aka bar Nabeel a tsaye yaja kwafa ya shiga ciki ya gaida Mimi ya tambayi Affa tace Affa baya gida.

Tana gama karatu tazo ta wuce Nabeel Yana kwance yayi matashi da cinyar Mimi,Bata ce komai ba tace Sannu da hutawa Mimi ta wuce bedroom dinta ta fesa wanka sai gata ta fito Palo sanye da sabuwar Riga da skert na Atamfa sun kamata daf ta zuba uban kyau ba wata kwalliya tayi ba powder Kawai ta shafa sai eyeliner da maroon jambaki,gashinta ta gyara kawai ta Masa acuci ta yafa siririn mayafinta sky Kalar atamfar takalminta me dan tudu sabo Kalar kayan duk cikin darasin Shehu ne,tace Mimi nayi bako,Nabeel ya zaci da wasa take Mimi Kuma murna take tayi ta samu miji tayi aure can su huta,Baki Mimi ta washe tace Allah ya hada kanku yasa mijin aure ne,Hamida tace Ameen,Nabeel ya kalleta kamar zai kurma ihu, tana fita yace Mimi Zan wuce tace ka gaida matarka,Dan Allah ka rike ta amana yace Inshaallah tace ka biya Mata Umrah Allah hada kawunanku a ransa yace ba amin ba a fili yace Ameen ya fice.

Duk compound har garden ya duba ba Hamida ba labarinta motarsa ya shiga ya tuka da Kansa yayi waje Yana fita ya ganta a jikin motar doctor suna ta hira tana dariya har wani nutsuwa tayi duk haukar Nan bata Yi,kasa hakuri yayi ya fito cike da bala'i yace Malam I'm warning you for the last time don't cross my line a gain... don't ever in your entire life cross my line again,ka daina zuwa gidanmu ka daina kula min Mata,Na maka warning leave my wife alone yanda ya rufe Ido Yana masifa yaba Hamida tsoro amma ta maze,yace ke Kuma ki tuna yanzu ba yarinya bace ki Zama uwa da badan yaron ya mutu ba da yanzu raino kike,koma gida wallahi ko na farfasa Miki jiki yanda ya yo kanta da bala'i da gudu ta shigo gida,ya karewa doctor Ahmad kallo yace ka kiyayi kanka da Shiga gonata Zan maka abinda baka zato na fada maka,Ahmad yace Ina sonta ai Kai ba mijinta bane sabo da haka tace tana so na dole naci gaba da neman aure kuma bazan fasa ba,mu zuba Ni da Kai cewar Nabeel ya fasa tafiya ya koma cikin gidan.

A tsakar gidan yaga Hamida tana latsa sabuwar Wayarta kamar zai Mata kuka a nutse ba hayaniya yace Hamida me kike kika maida kanki why Zaki dinga haka? Me nayi? Yanzu ki duba yanda Kika fita ko kunya komai ana gani na surarki yanzu haka dai dai ne,da danmu Yana raye da yanzu fa ke uwa ce shayarwa kike yi,Ina sonsa Kuma aurena zaiyi Kai mene naka a ciki sabo da me kake so na daina kulashi? kasa cewa komai yayi haka ya sake hasala Hamida ta yarda baya sonta juyawa tayi ta tafi abinta.

Yau Nabeel ma tunda ya koma gida bai iya baccin kirki ba sabo da tunanin Hamida,washe gari da sassafe jallabiya Kawai ya zura ya taho gidan Mimi,ya iske Affa da Mimi sun fita ma wurin aiki, dakin Hamida ya kwankwasa bata zaci shi bane ta bude ya Shiga ciki baki ya bude ganin kayan sawa sababbi na alfarma iri iri tana shiryawa wardrobe,ya kalli kayan ya kalleta yace Hamida Indai akan kaya kike sonsa ki maida Masa Dan Allah Ni zan siya Miki ko mene,Ko kallonshi bata Yi ba taci gaba da shirya kayanta,Hamida I'm sorry na rokeki ki yafe min,na dade da yafe maka ka rabu dani kaje kayi rayuwarka nayi tawa,dan Allah ni Jahila wacce ba class dinka ba kaje wajen dai dai da ajinka Bai kamata ka zauna Kamar ni Yar Kauye kana kulani ba kamarka kana bani hakuri.

Fita yayi da sauri sabo da ji yake kamar zai mutu gaba daya ya rasa Jin dadin duniya tunda ya hadu da Hamida duniya ta daina masa dadi gaba Daya Kawai ya rasa me yasa yake jinta a ransa.
Haka Nabeel ya kasance kullum sai yaje wajen Hamida Yana rokonta ta saurare shi ma taki ko saurararsa tsakaninta da shi bakar magana.

Sati na cika Basma ta shilla kasa Mai tsarki Nabeel kamar an Masa bushara da Aljanna,so yake ya fito yanzu gadan gadan ya nemi auren Hamida shine Kawai kwanciyar hankalinsa,doctor Ahmad ba bata lokaci shi biyan kudi yayi ma aka zanawa Hamida waec da Neco,kuskuren Hamida ba Wanda ta fadawa a gidan ba ruwanta Harkar gabanta takeyi ita kuma Mimi dama ta daina shiga harkarta Affa ne Kawai ke kulawa shima Aiki duk ya musu yawa gashi Yana Shirin tafiya Uk Karo karatu.

Wani eatery Nabeel da Ammar suka shiga Lele sanye yake cikin kana Nan Kaya yaje zai Yi take away shi da friend dinsa Ammar,Ammar yace Lele kalli can kamar Yarinyar gidan ku ce da wannan doctor din,da sauri Nabeel ya kalli wajen yaga Hamida an kashe dauri cikin wani shegen lace harda maka tafkeken glass na Yan gayu tayi Matukar haduwa sai kace daga kasar waje ta sauka,Shi Nabeel mamakin wayewarta yake lokaci daya,Bai San dama tana ta kallon me akeyi a birni ba,a fusace ya nufi wajen Ammar Yana rike shi Yana Lele banda fada yasan zuciyar Nabeel,da karaji yace ba nace karka sake kula min Mata ba Kai wanne dakiki ne,Ahmad ya mike tsaye yace kai kullum ba abinda ka iya sai masifa,ai Mata lallashinsu akeyi a haka zata aureka ko iya kyau Mata suke so?,me ka Mata a rayuwa in Banda kaje kauyensu ka Mata ciki,nine na taimaketa Ni na maida ta mutum kalli kayan jikinta komai Ni na siya mata Kai me kayi Mata na inganta rayuwarta,ka kalleta duk kayanta da take sawa ko iyayenka basu iya siya Mata ba komai nine na Mata Kuma Ina Kan Yi mata,komai Ni na Mata,Nabeel Takaici ya kamashi yace kin gani kinji Kuma ji gori yake miki wannan ya isheki ki gane mutumin kirki ne ko kuwa,

Ahmad yace Kaine mutumin banza tunda Kai karuwa ka maidata,Hamida sai ta fashe da kuka tana nadamar surutunta da bata fada ba da ba Wanda ya sani,Nabeel yace wallahi ka sake ka Kara kiranta karuwa sai nayi maganinka,Ahmad yace oho ko karuwancin take haka Zan aureta Kai Kayi tunanin aurenta ne banza dabb.....kafin ya rufe baki Hamida ta kifa masa mari tace na daina sonka kazo ka kwashi tarkacenka,ta fige gyalenta ta jefa Masa da glass din tace ko wanne Dan iskan Namiji sai rashin mutunci duk na kirki sun Kare sai yan iska marasa mutunci,Nabeel Kamar ya taka rawar disco ya dauki mayafin yabi Hamida yace yi hakuri my love a rufe min jikin nawa ya yafa Mata ko kulashi shima bata yi ba ta Kara gaba tare da shigwewa taxi.

Tana shiga cikin gida ta zauna a palon Mimi ita kadai Nabeel ya tsaya a jikin kofa ya wani labe Yana kallonta tace na tsinewa kaina kafin kowa ya tsine min Ni Hamida Kabir Tahir na tsinewa kaina sau Uku,Dan ubana Wai ni dabba ce bazan hankali ba,wannan tun ba ayi nisa ba ya Kama gori,shi wannan Dan iskan Nabeel din Ni ya zanyi da su,jakantata ce Ni na jawa kaina yanzu da na nutsu nayi hankali ban fada an min ciki ba ai da na zauna lafiya to da yake ni awon igiya ce sai na fada, dole na gyara kuskurena ba ruwana bazan sake cewa Naga duwawunsa ba ko wani farar takashinsa ya karata can da abarsa yaje uwar Basma ma tayi ta kalla karewa,amma tsakani da Allah banyi abin kirki ba haka Kawai na dinga ta'adin baki Ina fadawa duniya naga duwaiwai to dana gani sai akai me in banda haukata shima da halinsa dan duwaiwan burar .....ta narkawa Nabeel ashar Yana jinta yayi Dariya a cikinsa kamar me,mikewa tayi tsaye tace tashi Yar Iska gantalalliya tunda bani da me min fada na dinga yiwa kaina kowa ya huta,Kuma Nabeel alfarmar Annabi na barshi.

Ido ya zaro waje ya Fado palon yace dan Allah Hamida karki min Haka,da wallahi kina so na kina girmamani yanzu me nayi Miki tunda dan iskan doctor din Nan ya shigo shike Nan ya canja kulaki,Harara ta watsa Masa tace sai kaga ana biki ma wallahi,gwiwowinsa ya zube a kasa ya kwantar da murya kamar zaiyi kuka yace Hamida please ya hade hannayensa biyu yace na gano sonki nake Hamida ban taba son wata ba a duniya sai ke,da ban gane ba sai yanzu na tabbatar Ina sonki Hamida fiye da kowa,kece farin cikina,bazan iya jure ganinki da wani ba,Tsaki taja ta Shige dakinta tare da rufe kofarta.

Haka ya gaji da jira ya fita jiki a sanyaye,Wasa Wasa Nabeel ya kasa cin abinci sai dai Abu me ruwa,Mimi taga duk ya canja kullum sai taga ya zauna Yana ta tunani abinci baya ci,duk ya rame sosai,Tayi tunanin rashin Basma ne ta tafi Makkah,Bmbata San me akeyi ba,Ya samu kwangila me tsoka amma ya kasa zuwa ayi aikin kudi zai samu miliyoyi na kirki,daga lokacin idan yayi ya Zama hamshakin gaske amma tunanin Hamida yasa Office dinma ya daina zuwa,idan yaje gidan Mimi ta daina Fitowa yana ganinta Sam dakinta take kullewa idan har yaga Hamida to Doctor dinta ne yazo ta fita kofar gida tayi zance tun Yana masifa har ya dawo ya gaza,ya zaci abinda doctor ya Mata na gori zata daina kulashi amma sai yaga ya lallabata sun koma sun jone.

Mimi ce ta tasa shi a gaba Nabeel Wai meke damunka mene ne ka fada min? Baka da lafiya kake boye min ko wata cutar ce ta kamaka,abinci ka daina ci nasan dai matarka Bata nan dole a nan zaka ci abinci me ya faru? Ya rasa inda zai sa Kansa in banda Ammar ba Wanda yasan zancen yasan Yana fadawa Mimi za a samu matsala,Affa Kuma yace sai in Nabeela ta yarda sannan zai aura Masa ita, ko me zaiyi Matukar Hamida bata sonsa bazai same ta ba,shi Kam rayuwa babu Hamida gwara ya mutu ma da yaga bakin ciki,Shuru yayiwa Mimi, Hamida tana jinsu tana kitchen kin Fitowa tayi,Mimi tace dan ubanka baza ka fada min meke damunka ba gashi Nan sai tunani kake Yi,Nabeel ya wayance tare da sakin murmushin yake yace ba komai fa Mimi a wajen aiki ne wata kwangila nayi asara,to ba Allah ne ke badawa ba Mene na damuwa haka,idan baka da jari ga gida na Nan na Kano nasan zai Kai Million hamsim yanzu tunda a g.r.a yake Kuma babban gidane sai ka siyar,wancan ma dana siya kwana nan duk ka siyar ka hada na bar maka,Ko a dawo da Fadila ta dinga tayaka Hira? Murmushin karfin hali yayi yace no ba sai an siyar ba,to kayi Hakuri ka fawwalawa Allah,Nabeel ya kalli Mimi yace hmm Kawai,rabon ma da yaga Hamida har ya manta sai dai ya hange ta a wajen Doctor,wucewa tayi da plate din Indomie tana waya da Saurayinta tace gashi na dafa Indomie zanci ka daina damuwa,Nabeel kamar ya kurma ihu haka yaji ta shige bedroom ta kulle,Mimi tana ta Murna tace Hamida doctor har ya siya Mata form din School of nursing yace kafin ayi biki zata Fara zuwa makaranta in anyi aurensu taci gaba a can kaga mun huta da Kaya,Affa Kuma ya amince ta nuna Masa komai da yardar sa akayi komai sun kusa kawo kudi ma,Bari naje na dakko ma form din ka gani Mimi ta tashi tana rawar kafa ta haura sama,Nabeel bai San Yana hawaye ba sai da yaji laima sannan ya shafa fuskarsa kafin Mimi ta dawo ya Shiga kitchen yayi sauri ya wanke fuskarsa ya dakko ruwan sanyi Yana Sha kamar bai damu ba.

A hannun Mimi ya gani ko karbar form din bai iya Yi ba,hankalinsa ya tashi da yaji za a kawo kudi,yace Mimi Kuma iyayenta sun sani? Tace yaro har yaje kauyen ya gaishe su da danginsa da komai Kai abinfa ba na Wasa ba ne wallahi yaje can itama Hamidan ana kawo kudi zata tafi can, Nabeel mikewa yayi yace bari na karbi number dinsa ma dinga gaisawa Mimi tace ya kamata,ya nufi dakin Hamida, Yana knocking gabanta ya Fadi ta bude kofa tace mene ne? Yace magana za muyi,Fadi a Nan,Hamida Ni kike fadawa haka? Kallon tara Saura quarter ta Masa tace da kasan yanda na tsan....kasa karasawa tayi kallmar ta Mata nauyi, daurewa tayi tace Malam ka fita Ni ba Yar Iska ba ce irinka,mashayin giya mazinaci ka cuceni ta fashe da kuka,a zahiri Hamida fakewa take da kukan an cuceceta amma har ranta kukan son Nabeel takeyi ta kasa cire shi a ranta tayi tayi ta kasa kullum kaunarsa karuwa take a ranta Kuma kullum son ganinsa take tana son kasancewa da shi amma dole ta hakura ta tursasa zuciyarta.

Durkusawa yayi har kasa a gabanta tana kuka,hawaye kamar ya zubowa Nabeel yace please Hamida kome kike so a duniya Zan Miki,matarka fa in ta dawo me zaka ce? Mufa musulmai ne Allah ya halatta min Mata Hudu,ya narkewa Hamida tace ka rike matarka Ni wallahi bazan.....bakinsa taji cikin nata Ido ta lumshe ta sa karfi ta ture shi tare da shigewa toilet ta kulle kofa barshi a Nan durkushe ya kifa Kansa a saman bed dinta,a toilet din ta durkeshi tana rusa uban kuka kasa kasa yanda bazai ji ba Kuma tayi ma kanta alkawari baza ta auri Nabeel ba duk son da take Masa, sai da Nabeel ya gaji da Zama sannan ya mike ya bar dakin ko Mimi baiwa sallama ba ya wuce gida direct.

Shigarsa gida ke da wuya ya fada saman bed dinsa ya kifa cikinsa da kyar ya iya tashi yayi Sallar Isha ya kwanta bacci ya gagari idonsa,In banda Hamida ba abinda yake tunani,da komai nata shi yake tunawa,Mimi a cikin dare ta Kira Ammar akan yaje yaji abinda ke damun abokinsa,Ammar yasan komai amma Kawai yace to,Bai je wajen Nabeel ba sai da safe ya iske Nabeel Yana kwance zazzabi ya rufe shi ko motsi bai iyawa tsoro ne ya kamashi,Bargo ya lulluba Masa.
Da sauri ya Kira doctor aka Masa gwaje gwaje hawan jini ya kamashi da karfi,an bashi magunguna da allurai an Masa Karin ruwa amma Nabeel babu sauki a abin nasa,Ammar duk iya kokarinsa yayi kasa hakura yayi yace mu tafi asibiti Kawai Nabeel yace bazai je ba,Lele so kake ka kashe kanka Kar ka manta Hamida yanzu Bata sonka gwara ka kyaleta ka fuskanci gaskiya ka rabu da ita sai kace Yar gwal,Nabeel baya iya Maganar kirki,Ammar yace to gaskiya Zan Kira Mimi,Nabeel ya girgiza Masa kai hawaye Kawai ya fara sakkowa Nabeel,tausayi ya bawa Ammar yace Kai Hamida kake so? Ya daga Masa Kai Wai ae,yace to tsaya naje na lallabota Allah yasa tazo ta kula da Kai,Ammar gidan Mimi yaje da sauri ya iske kamar kullum duk suna wayen Aiki sai Hamida,hankali tashe yace Hamida ga Nabeel can zai mutu sai abinda Hali yayi yace kije gidansa zai bar Miki wasiyya,Gaban Hamida ya fadi ta dora Hannu aka tace na shiga uku me ya sameshi yace ciwon zuciya,nayi nayi muje asibiti yaki yanzu ma kamar kakin jini ya fara Mimi ma ta tafi can kiyi sauri,Hamida tsalle tayi ta saki kuka ta fara tumami tana birgima Ammar ya saki baki Yana kallon ikon Allah yace ba kuka zakiyi ba kije ki bashi agaji idan Yana da sauran rayuwa to idan ya mutu duk munyi Rashi,Hamida ta daga hannaye sama tace bazai mutu ba...bazai mutu ba...in Allah ya yarda bazai mutu....bakin ka sari motar tantan ...bakinka ya sari tsohuwar tifa,tana kuka tace muje ka kaini,Ammar yace ni asibiti zanje karbo magani,mayafi ta figa ta Dora saman silk doguwar rigarta dark blue,ta fice da gudu takalman ma a Hannu ta eba,Tana Fitowa taga Doctor Ahmad dama sunyi zaizo ya fito da sauri ya ganta a hargitse.

Yace Honey lafiya? Da bala'i tace karka isheni dan Allah zanyi rashi,Ya sake cewa Hamida...karka dameni Malam ka tafi sai na kiraka a waya,Ahmad yaji haushi ya figi motarsa a ransa yace ki gama wulakancin wallahi Kika shigo sai na Rama Zaki Gane kurenki baki San waye Ni ba dama kwadayi ne ya kawo ni in aura na gurjeki.

Hamida Kuwa taxi ta shiga ta Masa kwatance kudi ta Mika Masa dubu Daya,yace Hajiya canjin tace na bar maka ta fyalla da gudu cikin gidan, dama tasan har room dinsa Kawai Shiga tayi lokacin ma duk ya jigata bai ma San me yake ba,Hamida tana hawaye kasa kasa ta ganshi cikin bargo,gefen fuskarsa dake waje ta taba taji mugun zafi Yana ta rawar sanyi,kumatunsa ta tallafe da Hannu biyu tace Yaya kyakyawa,tana fadan haka sai da yasan itace yaji wani sanyi a ransa duk da jikin da yake ji,yace sanyi nake ji kimin wani abin,Hamida tace ban San me Zan maka ba,Yana numfarfashi yace dumin jikinki dan Allah tace tab ba ruwana bamu da aure ai nayi hankali nida Namiji haihata haihata,wallahi... ba.. abinda Zan Miki kinji na rantse,Ya sake narkewa Kamar ransa zai fita harda tari, Hamida tsoro ya kamata,taji yace Hajiya Bilki me kosai tana bina bashin naira dari idan Allah yayi min rasuwa kije ki Bata,Ido ta zaro ta saki kuka,ya sake cewa sannan....Jamilu me dinki shima Yana bina dari hudu da hamsim ki bashi cikin abinda Allah ya hore min,...ya sake yin tari...muryarsa na rawa kamar zai sheka lahira yace Lawan kwalli me
Showing 30001 words to 33000 words out of 133235 words