shine Mana harda wani makale murya Yana min yanga Ni Kuwa na Masa gaja gaja na kashe wayata Wai harda tambaya what...Basma ni Nabeel kike zagi? Ni Kuwa zagi ta Uwa ta uba na Masa shine fa Kika ga ya tsorata yanzu Yana washe min Baki,kin San ni ban iya Fushi,Maryam tana ta mamaki sabo da ita tasan tabbas ta canja number Daya a number din Nabeel amma gashi Basma ta tabbatar ta samu Nabeel a waya, tunanin ko dai data ji Wrong number ne ta nemo wajen wasu Haka Maryam ta bawa kanta amsa.

Basma tace ai Nabeel ya shiga Uku Dani ya tsokano tsuliyar dodo yanzu Bari na kirashi da Daya layin Nawa na Raina Masa wayo,Wayarta ta zaro tare da Nemo number data Kira jiya,sai data Yi bugu biyu kafin a dauka sai taji an kashe an Kirata back,muryar Nan me Dadi ta sake dukanta Tace Nabeel ka daina wannan Iyayin kasanni na Sanka Ni ba birgeni kakeyi da wannan muryar ba ka fito min a mutum,Nabeel ya Gane muryarta Kawai Yaja Tsaki tare da kashe wayarsa lokacin Yana tare da ma'aikatansa Yana musu bayani akan wani aiki, Engineer kenan.

Adamawa state matashiyar budurwar ce ta sake fitowa sanye da uniform maroon and white wow kyakyawa da ita karshe,skin dinta chocolate me haske baza kace Fara Kar ba Kuma baza kace da ita baka ba,yanayin dirinta gwanin birgewa Haka fuskarta da komai nata me kyau ne, da kuka ta fito daga Dan kyakyawan gidansu na bulon siminti,kaf kauyen ba gida me kyan nasu gidansu na bulon siminti a sumulmule yasha paint green, ciki harda tiles zata Kai 19yrs wuyan Hijab dinta ya karkace Bari daya,jakar makarantar nata ta ratayota ta Gaban Dan guntun hijab din nata,tana gudu tana kuka matashin yayanta Yana binta da bulala suna ta gudu a Gari ana kallonsu.
Tana gudu tana magana wallahi bazan je makaranta ba,nace muku bana son makaranta Ni,ai ba Dole bane,ko dole sai anyi karatu ake samun ci gaba,Wanda yake binta da bulala yace wallahi dole sai kinje makaranta Dan ubanki,Ni bazan je ba wlh ka rabu Dani bana son makaranta Ni Kuma ko ka kaini sai na gudo,saurayin Allah ya bashi sa'a ya cafketa ya dinga tsula Mata bulala tana ihu amma tana kuka tana cewa bazan je makaranta ba Ni bana son makarantar ta sake kwashewa da gudu ya bita Ana ta kallonsu dama an Saba ganinsu kullum da safe sai ya rakota da gudu suyi ta gudu Amma baza taje ba,sai da ya Rakata har makaranta da bulala suna gudu tana ihu sannan ya dawo gida Yana masifa.

Wani dattijo da matarsa suna zaune a tsakar gida Yana bala'i Papa wannan Yarinyar
dole sai an dau mataki a kanta,ka duba girmanta mate dinta duk wasu sun Gama secondary da 3yrs Amma ita 21yrs har yanzu tana ss3 sabo da rashin zuwa makaranta gashi har yanzu Bata iya karatu da rubutu ba ko sunanta Bata iya rubutawa ba.

Sai lokacin Wanda aka Kira da Papa yayi magana yace Abita a hankali Dan Allah kaga bani na haifeta ba Yar Dan Uwa na ce marainiya ce Bata da Uwa da uba nine komai nata bana so ta kalle mu a wasu marasa Imani a kanta,a bita a hankali,Matar Papa Kuwa tana gefe Baki ta tabe Tace ai Indai Hamida ce zaku gaji wannan Yarinyar karshe ta lalace Matukar Baku bi shawarar Dana Baku ba to wallahi zaku Yi kuka,ku samu wani dattijo ku aurawa shegiya.

Tsawa Papa ya daka Mata Haba Mero yanzu idan yarki ce Zaki so Haka ta faru? to saurara kiji Hamida amana ce a wajena Kuma na dauka sai na sauke amana,dama ke kike gida ke ya Dace ki kula da tarbiyyarta amma bakya Yi,baki Mero ta tabe tace to shike Nan zamu gani ai,Tsaki Yaja ya fice abinsa da takaicin mero sabo da Sam ba ruwanta da Hamida tsakaninsu sai dai ta kallo duk da cewa bata takura mata.

Hamida Kuwa ko taje makarantar bata saurarar komai a makaranta kawarta guda Daya ce Sakina Kuma Sakina ita tuni ta gama secondary babarta take rakawa kasuwa tallan Masara dafaffiya.

Washe Gari da safe Haka Dan gidan papa Kanin baban Hamida kenan Wanda ke dukanta sai taje makaranta Sulaiman ya sake rakota da bulala suna gudu tana gudu tana bana son makaranta Ni bana son makaranta bazan je ba bana so,Yana dukanta tana gudu a Haka ya Rakata makaranta,Amma dukan ko a jikin Hamida,duk Sanda aka tashe su daga makaranta sai dai ta tsaya a Hanya tayi ta Wasa kafin tazo gida lokacin Islamiyya yayi Haka Islamiyya ma Sai ansha fama ake rakata da bulala itama ba abinda ta sani,Bata Jin magana.

Yau ba school Sunday Hamida ta shigo sanye da Riga da skert na shadda sun Mata kadan ma amma haka take sa abinta tana tafiya a hankali ta daga kai sama hannayenta suna harde a bayanta tana kalle kalle tana wani taku na gadara,Daga gidan ubanwa kike? Wacce suke Kira da Ummi ta tambaya,ko gazau Hamida bata Yi ba Kuma bata fasa kalle kallenta ba,dake nake Hamida daga Ina kike? Har gaban Ummi Hamida ta karaso tare da furta Ummi akwai Kuwa abinci,harara Ummi ta zuba Mata tare da furta ba abinda Kika sani sai yawon banza da tsayawa Kika Yi Kika koyi karatu da rubutu ya fiye Miki amma even ordinary Hami baki iya rubutawa ba bare a kai ga kin rubuta Hamida,daurin zaninta Ummi ta gyara tace ya kamata kiwa kanki fada,Hamida kisan me kike duk garin Nan a mahaukaciya suke kallonki ba a Miki kallon me hankali.

Dan baki Hamida ta turo tace Wai me Kika dafa ne Aunty dake ita in taga Dama Aunty take Kiran Ummi shi Kuma Papa tace uncle,Tsaki Ummi taja tayi tafiyarta abinta.
Kitchen Hamida ta wuce tare da eban abinci taci ta cika cikinta sannan ta kalli Ummi dake tace gasarar Koko tace ni Yar kasuwa nake so na Zama bana son boko bana kaunarsa ki fadawa mijinki,ko kulata Ummi Bata Yi ba itama Hamida ficewa tayi tana fito fiii fiiiii...sai kace tantiran maza.

Papa Yana shigowa Ummi ta kalli inda yake Jin Yana tambayar Ina Hamida ta Shiga,Baki Ummi ta bude tace wallahi kaine farkon lalata Hamida kana tunanin hakan gata kake Mata sabo da Kar ka takura mata bata da Iyaye sun rasu sannan Yar dan uwanka ce,abinda take so shi takeyi,abincin da take so shi take ci,gaba dayanmu koko muke Sha Amma Hamida shayi lafiyayye kake siya Mata kullum,Bata San babu ba,sutura me tsada ita kadai kake siya mata,duk yaranka na cikinka makarantar Gomnati sukayi amma Hamida makarantar kudi takeyi me tsada,bata cin tuwo sai abinda take so,Ni ban taba ganin dan an mutu an barwa mutum ya ba Yana Haka sai a kanka,kowa bai iya tarbiya ba sai Kai ai shike Nan gaka ga Hamida nan.
Tsaki Papa ya ja tare da furta kayan sawar Hamida kala Nawa ne kwata kwata? Sannan atamfar dubu uku sune masu tsada,ke da kike mace uwa kece me Basu tarbiyya ai yaranki kadai Kika sani,Hamida bakya sa Ido akanta ke wanne kokari Kika Yi sai burinki na aurawa ko tsoho ne Hamida,ko wanne Hali ta shiga ba ruwanki,yo me ya ruwana tunda Yarinyar mahaukaciya ce bata san ciwon kanta ba cewar Ummi,Tsaki Papa Yaja ya wuce ciki Kawai sabo da Yana da sanyin hali.



Ayi Hakuri da typing Error Basma ya kano ce na manta nasa Abuja bazan iya komawa baya ba fans.




AsmaBaffa
[6/28, 1:46 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮


2

Official


By
AsmaBaffa



Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne

ASMAU SANI
LATEEPHA
RUKEY MUAZ
NICE GIRL
HAJIYA ABOU
KHADIJA DANDUME
KHADIJA A HAMZA
HADIZA MUKHTAR







Basma Hamza Kabir shine cikakken sunan Basma,Yan asalin maiduguri ne kanuri,su biyu iyayenta Suka Haifa babbar yayarta Aunty Maryam sai ita, bayan sun taso cikin rufin asiri domin babansu babban likita ne sunyi karatun Boko sosai Yan Boko ne na gaske Aunty Maryam tana Gama degree ta samu mijinta Salisu,Salisu shima ya Gama degree baida burin aikin Gomnati ya samu Aiki a company na MTN Kano sabo da burinsa siyasa Kuma a cikinta yake Allah ya hada su da Maryam lokacin Maryam ta samu Aiki a ministry of health sannan aka musu aure.

Ana auren Maryam ba dadewa babansu ya rasu,bayan ya rasu da wata Daya Mamansu ciwon zuciya ya kamata itama ta bishi ya Zama sai Basma Kawai ganin Haka Yan Uwa suna son daukan Basma Salisu yace ta tattaro ta dawo kano gidansa zai hada ya rike ta zauna a hannun yayarta Maryam.

A Haka Basma tana zaune har ta Gama secondary school ta shiga University lokacin Maryam tana da yaranta maza biyu mace Daya,a yanzu Basma tana final year a University zasu zana final exam.
Basma abinda taga Dama shi takeyi Bata da takura ko wani Abu tana da ilimin addini sosai,Bata da wani Hali na banza sai son Wanda ya waye sannan me kudi,Bata da burin da wuce ta samu saurayi matashi kyakyawa me kudi Dan gayu me ilimin Boko,tana da kyankyamin Wanda Bai waye ba,ko baka da kudi Matukar ka waye to Basma zata je da kai.

Basma kyakyawace Fara tas Yar gata da mugun tsayi da kaurinta,tana da jsauray dai ita ba laifi sosai ta hadu ga iya daukan wanka ko a school maza na gasar kula Basma,Bata da kunyar zagin mutum duk girmansa Amma sai ka shiga gonarta.

Bangaren samarin Basma Kuwa duk Wanda yace Yana sonta Matukar Yana da Mata sai ta Masa karya zata aure shi Amma sai ya saki matarsa ta gida,wasu shashashun sai su Saki kuma sai Taki aurensu,akwai mazan da yawa an musu baiko wasu an sa Rana Amma Indai Basma ta sani Kuma suna alaka da Angon sai tayi amfani da kyawunta wajen wasu Wanda Basu da hankali tasa an fasa auren sun dawo suna Sonta karshe ta Kori mutum.
Gashi Kamar tsafi kowa Sonta yake Yi akanta sai mutum ya fasa auren budurwarsa sai ya sheka yaga ba kwaya,Basma Kenan.

Nabeel number da Basma ke kiransa tana zaginsa ya duba a Whatsapp yaga dalleliyar budurwa Yar gayu ita ma Basma sunanta sai dai ita tasa Real Basma,ita Kuma Basma Yar uwarsa Basma luv tasa Kawai,Takaici da nadama ta Kama Nabeel yanda anyi magana zai auri Yar uwarsa ba bincike ba komai yace ya fasa,Tsaki Yaja yasan da kunya ya koma yace ga Matsalar iyayensu zafi ne dasu gaba daya,Magana yayiwa Basma ta Whatsapp dama tayi saving number tana Hawa Online taga wani hadadden guy ta zaci wani ruwa biyu ne ko Dan wani Kasa ne,Nan take ta fara kaunarsa taga mijin da take mafarkin samu fadawa tayi a saman bed ta fara birgimar murna.

Aji ta ja sosai Bata kula Nabeel a time din ba,Lele uaga Shuru sai shima ya share da kanta ta dawo ta Masa magana Suka Fara chat Nan ta Gane tabbas ba Nabeel din school dinsu bane ,a hankali a hankali Suka Fara mutunci Suka fada soyayya da gaske takanas yaje har kano wajen Basma ta gama tafiya da Nabeel,zuwa Daya biyu yace za a kawo kudin aure,Haka ya dawo ya tasa Affa a gaba sai da aka Kai kudin aure ana bincike sai aka gano ashe ma Maman su Basma data rasu kawar Mimi ce sosai sun Sha zuwa Makkah tare a can Suka hadu, Nan aka Sa rana aka yanke biki Nan da wata tara Basma ta zarma da yawa sai love duk ta zake hakan yasa duk ta fatattaki samarinta sai iya Nabeel Wanda zata aura Kawai suna ta soyayya,Mimi suna ta zumunci da Dangin Basma,Wannan yasa Basma har gidan su Nabeel take zuwa ta danyi sati daya sabo da Mimi ke tursasata sai tazo,suna zuba love Nabeel ya samu babbar kwangilar aikin titi a Adamawa state a kalla sai ya kwashe wata hudu a can idan aikin Bai gamu ba sai ya Kai 5mnths.

Mimi ya samu a part dinsa yace Mimi banji dadin saka ranar auren Nawa har Nan da wata tara ba kusan 1year fa Mimi su Affa sunki ganewa sabo da bai so nayi auren sai karatu,Mimi danta ta kalla tace Nabeel ka rufawa kanka asiri ka rufa min kaga a hakan ma da kyar ya amince kayi auren to kayi Hakuri a haka 9mnths kamar yau ne fa,ko wata Matsalar ce? Kunya yaji yace ba komai to Mimi Allah ya kaimu,yanda kake addininka ka dage na Sanka ba Wasa,alcohol naga ka daina Sha ko? Mimi sai fa nayi wata uku ma ban Sha ba sabo da tana sawa Ina son aure Kuma Kinga Affa ba Yi min zaiyi ba shi yasa na hakura da Sha sai jefi jefi shima Inshaallah Zan daina gaba daya,yawwa Lele ai nasanka kana da tsoron Allah to ka Kara akan na da, Inshaallah Mimi ya furta tare da gyara kwanciyarsa saman kujera Yana latsa wayarsa.

Affa ne ya shigo tare da gallawa Nabeel harara yace kayi asara wallahi yaushe zaka tafi Adamawan? Gobe Inshaallah cewar Lele,baki Affa ya tabe yace Saura ka gano wata a can kace a fasa da wannan Dan iskan yaro marar Jin magana,Mimi tace wallahi ka daina iskance min yaro akan yaki komawa turai karatu so kake wani bala'in ya fada Masa kullum kana zaginsa kana ce Masa Dan Iska,Tsaki Affa ya ja tare da haurawa sama ya bar Mimi rai bace,Fadila ce ta dawo daga school da gudu ta Fado palon tare da fadawa jikin Nabeel Yana Mata oyoyo tayi wajen Nanny ta barsu ko Mimi bata kula ba.

Nabeel uban wanka ya hada komai tsab da sabuwar motarsa fara ya tafi wacce ya siyeta da kudinsa duk da cewa motarsa ba Daya ba,a wani Hotel karami kusa da kauyen yayi masauki,Yana can suna ta Aiki a wani babban titi Wanda ya ratsa ta wani kauye wannan titin yakewa Aiki da motocinsa yaransa ma'aikata suna ta fama shi Kuwa Yana mota Yana Shan ac,Sam Nabeel baison wahala ko kadan kana ganinsa kasan Yana hutawa.

Fitowa yayi daga motar hannunsa dauke da ruwan roba yasha farar shadda Yar ubansu yayi mugun kyau abinka da me kyau ya Gama hadewa kana ganinsa ba sai an fada ma ba kasan shine ogan,Hamida ce da gudu ta fito misalin 10am da uniform dinta hijab din ya karkace gefe tana gudu har kullum Sulaiman Yana binta da bulala Yana dukanta Yana dole makaranta tana wlh Ni baza Ni ba kome za ayi nace muku bana son karatu Ana ta kallonsu ta ci birki a Gaban motocin aikin Nabeel Tace wallahi sai dai kashe shi Ni ba inda Zan Dara daga Nan tana kumbura baki da sangarta,Sulaiman yana hankadata amma Taki tafiya,Nabeel Yana kallon ikon Allah baiyi Niyyar magana ba sabo da gadararsa,da kyar dai ya daga musu Hannu yace hey...hey Mene ne? Sulaiman da huci yace kana gani bawan Allah Wai Kamar wannan ta kusa shekara ashirin da daya amma baza taje makaranta ba har yanzu tana ta maimaita ss3 mate dinta duk sunyi nisa a university wasu sunyi aure to wallahi billahillahillazi la Ila ha illahuwa kaji rantsuwar musulmi sai taje school dole bazan taba bari ta lalace ba,Yar iskar yarinya Sulaiman ya sake tsulawa Hamida bulala ta saki Kara sannan ta daka yatsa sama tana girgigaza da kirji Tace to Ni Kuma na rantse da ubangin alarshi bazan je ba,Haka Kawai nace Ni bazanyi boko ba bana so bana so dole ne bazanje ba ni kam.

Sulaiman zuciya ta hangulo Masa ya fara dukan Hamida,Nabeel ne da muryarsa me dadin sauraro yace ya Isa tare da rike Sulaiman yace ai ba a duka,duka ai baya gyara mutum lallabata zakuyi,kafin ya rufe Baki Sulaiman yace wannan Yar iskar ce zata ji lallaba? Calm down karka sake dukanta Ni Zan Mata magana zata je school, Sulaiman yace ka tabbata? Nabeel yace yes of course,Zan gani ya koma gefe can,Nabeel ya danyi murmushinsa me Kayatarwa tare da kallon Sulaiman ya Dan daga murya yandazai ji shi ya furta don't worry I will talk to her.

Sulaiman a ransa yace kayi ma gani,Nabeel a nutse Yana birnancinsa yace me yasa bakya son zuwa school? Hamida tana Wasa da Hijab dinta cike da tabara tace wallahi Ni bana son makaranta,Allah bai sa min Sonta ba,ba kawaye bane ni da Makaranta na tsani karatu,ka ganni dakikiya ce bana ganewa ,ko an koya min bana ganewa,idan naje aji wannan Malam yace kaza wancan ma yace kaza sai na ji kaina Yana juyawa yuuuuuu ta fara juya kanta a baban Nabeel.

Yace to makaranta tana da amfani...kafin ya rufe baki tace ni nace Bata da amfani a kaina kaga ta turowa Nabeel kanta tare da fige hijab dinta da dankwalinta, gashi baki wuluk me tsayi da santsi ya bayyana tace daki kaji tana bubbuga kanta da Hannu Tace kaji Kara to Haka yake Kamar dutse baya jin komai a kulle yake ba fili ko daya a ciki da har Zan Gane ta furta tana maida hijab dinta.

Ka tambayi dan Uwa na wallahi na fada masa bana so,Wait wait Nabeel ya dakatar da ita yace ilimi Yana da amfani yanzu idan banyi ilimi ba Zaki ganni a wannan matakin? Amma kalleni kalli motata Ina da wasu da yawa a gida Kinga duk karatu ya bani sabo da Haka kije makaranta,Yana Magana ko kallonsa bata Yi wasanta ma takeyi tana kalle kalle sai da ya Gama tace Ni nasan kaina Allah bazan iya komai ba bana ganewa bazan iya ba ni gaskiya so nake na Zama Yar kasuwa anfi saurin samun kudi,gaka kaima kana ta business,No..no Ni ba kasuwanci nake ba ilimi ya kaini cewar Nabeel,duk yayi yanda
Showing 3001 words to 6000 words out of 133235 words