ransa yace me hali baya fasawa dama yasan Hamida kafin ta dawo normal sai ta shiga school dole yace dole na kaita school a week din Nan.

Hannunta ya rike ya jata palon sama ya bar su Anwar suna ta dariya,paper ya dauka ya Rubuta mata sunan bank U.B.A yace me ake cewa wannan a turanci yanda ake ABCD kin tuna? tace ae yace to fada naji karanta maza,Hamida ta karbi takardar ta gyara zamanta a kujera harda harde kafa tana karkada kafafu ta karanta abinta da Hausa tace Uba Kamar baban mutum Uba amma ba Ubana ba gaskiya wannan ai wayon ka zagi banana ne Yana kabari Kuma ta kwabe fuska,harara ya watsa mata yace bani school Zan kaiki shehu baya aikinsa Kuma wlh a primary Zan saki cikin yara,Hamida ta fashe da kuka yanda bata son makaranta za a maidata baya tace Allah Zan dage Shehu ne Ni kwalliya yake koya min,Nabeel yace ai dama wannan ba malami bane korarsa zanyi na kaiki school suyi ta zaneki a can.

Hamida tace ai ya bani assignment na mathematics bari na kawo ka koya min Dan iskan maths din Nan ne me Find X wlh na gaji Ni bana iya nemota,Nabeel ma anyi rashin sa'a a duniya bai iya maths ba a school da kyar yake tsallakewa,sai yayiwa Hamida wayo yace tab Nemo x ai sai anje Taraba Hamida tace Allah dama acan take? Yace a school can ake kaimu a motar makaranta idan Muka ganta a cikin yayanta sai ta ba kowa daya shike Nan mun samo ta,Hamida tace dan Allah ka rakani,Ihsan tana da ita kije ta nemota ta miki assignment din dama yasan Ihsan ta bala'in iya maths, Hamida tace to gobe kafin su tafi zata min.

Hamida ta bar zancen Assignment ta Mike zata tafi
Yace ki zauna ki tayani hira tace a'a Ni dai bacci zanyi ,Kai ya jinjina yace Wai me yasa yanzu Kika tsaneni ne kin rainani fa? Hamida tace ka manta Sanda ka dinga wulakantani kana hantarata Kai da matarka ka mareni ka zageni duk sabo da kaga Kalar Dausayina bani da daraja sai yanzu gwara na auri Wanda banga Kalar tasa ba baiga tawa ba,ka je ka auri Virgin dinka ba ruwana,Nabeel yace haka Kika ce? tace ae ta juya tayi tafiyarta,tagumi yayi Kawai tare da furta ya Allah ka kawo min agaji Yarinyar Nan Bata San son da nake Mata ba tun farko Allah ka ganar da ita,Allah ka shiryi Pipi

Fitowa yayi ya ganta zaune kusa da Anwar da wayarsa tana tura film Wai zata kalla,Nabeel yaja kwafa ya wuce ciki shi duk ya matsu su tafi Abujansu ya huta,Har ya kwanta ya sake Fitowa ya leko palon yace wai bakusan ku kwanta bane dare yayi,Muhseen yace Kai Lele duk Nan fa Zain ne da mata kannenka mun girmeka amma sai wani Raina Mana hankali kake yi,Tsaki Nabeel yaja ya koma bedroom Hamida bata ma San me yake ba hankalinta na Kan waya amma tana jinsa,room din Mimi ya shiga ya iske ta tana gyara Kaya yace Mimi kice Hamida taje ta kwanta tana can tana sakin layi wajen su Anwar,Allah sarki Hamida bata yi surutun komai ba ma, Mimi tace me Hali baya fasawa sai tayi tunanin gaske ne tace naga ta fara hankali fa Kai wannan Yarinya Mimi ta sauka da sauri tace Hamida zo.

Hamida mikewa tayi tabi Mimi Sama,tana Shiga bedroom Mimi ta rufeta da fada Lele yana zaune Yana murna,Mimi tace Zaki je kiyi zancen Duwawun da kika Saba ne wallahi ki kiyaye Ni,Hamida tayi rau rau zata Yi kuka tace wallahi Allah bana fada tun yaushe na daina tun Sanda Kika ce na daina kula Yaya Nabeel na daina fadan komai Kuma Ina kiyayewa na gane gaskiya na gane ba mutunci na bane sai fa yau kadai Kuma daga Ni sai Nabeel na fada Kuma ban ambaci takashi ba wallahi Kawai dai nace Naga tasa yaga tawa Kuma ai shine Yace Yana s....Nabeel ne yayi sauri yace jeki Kawai duk ya hana aji karshen zancen Hamida sabo da Mimi Kar ta ji,tana Jin yayi Shuru taci gaba sai yace Yana so...da sauri ya dan bigi mudubin Mimi da Hannu ya saki Kara,Mimi tace maganinka kenan gashi Nan kayi famu,Hamida ta rufe bakinta da tafin Hannu sabo Dariya taci karfinta Wai yayi Famu kamar dan kaciya,Mimi ta kalleta tace fita ja'ira duk abin fitsara kina ciki kaima fita munafuki,Hamida tana sauka daga last steps ta juyo tana kallonsa shima Yana sakkowa a ranta tace sai na Rama,Tafi ta shiga Yi Masa tana wakar da akewa Yan kaciya a kauyensu Wai Lele takwa takwa....ah Lele takwa takwa...Yan Palo Suka kece da dariya kamar me,Nabeel shi kanshi da kyar ya shanye dariyar sabo da Kar ta Raina shi da yawa,fisgota yayi tare da murde hannunta ya kwace Wayarta ya wuce masallaci.

Washe gari da wuri duk Suka shirya Suka tafi har Anwar sun ga alama kamar Nabeel son Hamida yake shi yasa Suka hakura Kawai,gidan ya dawo sai iya su ya su Yan gidan sai Fadeela da aka kawota hutu,bayan komai ya lafa Nabeel ya samu Affa a room dinsa yace Affa ka canjawa Hamida teacher wlh in Banda kwalliya ba abinda yake koya Mata bata iya komai ba,Affa yace naga hakan nima Inshaallah gobe Zan kawo Mata wata Zainab babbar mace ce me hankali in yaso sai a sata a Islamiyya bana so ta shiga secondary ss3 bata San komai ba rainata student zasu yi a dinga wulakantata Kai kasan Yan makaranta,yace hakane kam yace yawwa kaima ka dinga dan koya Mata abubuwa,Nabeel ya sake cewa to amma Affa Ina son Nabeela dan Allah ka aura min ita,Affa yayi Murmushi yace bayan ka gama wulakantata Lele,dama Ina sonta Affa lokacin ban gane sonta nake ba tun farko,bazan baka ita ba kaje sai Zama yayi Zama ka Fara Mata gori wani dan abokina Zan bawa ita.

Nabeel sai yaji haushi yace Affa kafi son bare da ni? Affa yace kwarai tunda baka ganin darajarta ba ai gwara a bawa me hankali Kai ka hakura ka auri Yar uwarka Fatima ko Ihsan munyi magana da su Yaya mun yanke hukunci Hamida Wanda ta zaba zata aura,Nabeel yace Ni bana son su gaskiya da na auri Fatima ko wata gwara na Kare rayuwata a haka,Affa yace Kai ka sani kuma,Nabeel ya sake cewa please Affa,Affa yace karka dameni Lele tashi ka bani waje Hamida ko ta aure ka kana da tabbacin zaka Haihu sannan ma idan baka warke ba fa ya zakayi da Yar mutane wajen bukatar Aure? Nabeel yace Inshaallah ma Zan warke Nan da 5-6mnth Affa Ina da karfin jini,gwara Yar uwarka inda zaka samu rufin asiri,Nabeel yace ita Basma da aka aura min ita kalli fa abinda ta min Haba Affa,yace to dawo da daya Basma ka aura,Nabeel yace Ni duk me Suna Basma bana kaunarta yanzu, to tashi ka bani waje Allah ya hadaka da ta kirki amma ba Hamida ba.

Mikewa Kawai Nabeel yayi ya fice cikin bacin rai,Hamida bata San me akeyi ba karatunta take Yi sosai wajen sabuwar malamarta Aunty Zainab ta fahimci Hamida a hankali take bi da ita tana koya Mata har abubuwan rayuwa sannan tana zuwa Islamiyya sosai,kwana biyu taga Nabeel Sam Bai da walwala,kullum baya fara'a da sauransu Kamar yanda aka Saba,Sabgarta ma ya daina shiga kwata kwata,hakan yana damun Hamida sosai tayi zaton ko wata cutar ce kuma,tana so ta tambaye shi amma ba fuska.
Karatunta takeyi sosai ta nuna bata damu da shi ba amma a zahiri hankalinta na wajensa.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya zancen auren Nabeel ya kankama tabbas ranar arba'in din Basma za a aurawa Nabeel wata matar,Hamida sai ana gobe ta tsinci labarin,Kamar tayi hauka kasa daurewa Hamida tayi ta dauki biro da takarda ta Kira Shehu a waya tace mu hadu dan Allah a bayan gidan Affa,Shehu 5pm yace ta fito yazo,bayani tayiwa Shehu tace abinda yasa bazan rubuta wasikar da kaina ba nafi son rubutun kwari Wanda yafi Nawa kyau,Hamida ta shiga fadawa Shehu abinda zai rubuta a takardar har ya gama tace sa ayar tambaya a can,Shehu ya saka,Tace sa coma again,Shehu yace to ya saka ta karbi paper ta Masa godiya ta koma gida tana shigowa room dinta ta wuce ta saka a sabon envelope ta manne ta kaiwa Mimi tace gashi inji wani mutumi yace a bawa Affa,Mimi ta karba tace bai fada Miki sunansa ba tace ae yace shima aikoshi aka yi ya kawowa me gidan,Mimi tace to idan ya dawo Zan bashi Hamida tace to ta juya ta koma palo.

Kwanciya tayi tare da yin rub da ciki tana rubutu da karatu Nabeel ya fito shi fa Ammar,dama sun gaisa Ammar ya kalleta yace Sannu da karatu tace yawwa ta dago ta kalli Nabeel,yaga tayi kyau taci kwalliya cikin wani material black me adon red Riga da skert shi kanshi Ammar sai da ya kafeta da Ido sabo da ta fita ba karya,Haka suka wuce suna barin palon Hamida ta ajiye biro ta dafe kanta tare da lulawa tunanin Nabeel,a hankali tace dole in shiga in fita Ina Zan bar wannan inyi ya da zuciyata wallahi Matukar ba a Mana aure ba sai na bar gidan Nan har abada.

Zuwa dare Affa ya shigo bayan ya nutsu Mimi ta Mika Masa envelope ya bude tare da zaro takarda ya warware ya fara karantawa kamar Haka



Kuyi Hakuri da wannan




AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

16-20


Official
By
AsmaBaffa



Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM





Page naku ne

Ummu Abbah
Maman Raiz
Mrs Aleeyu
Sadiya Muhammad
Fatima Abubakar
Ummu Shafa'at
Maman Humaira mk
Rabiatu Maharazu
Ummu Ilham
Roukayya Bello
Ummisalehmuhd2
Najida Aliyu Bicca
Dr Zainab Abdullahi
Umma Khursum
Zainab
(Queen Hernah)
Zainab Shehu
Maman Humaira &ikhram
Mk Hussein
Maman Kadi






Affa karatu ya fara Assalamu alaykum
Bayan dubun gaisuwa me yawa tare da fatan Kana lafiya tare da iyalanka baki daya,Ya yaron wajenka da jiki? to Allah ya kashafe,na Kira wayarka bata shiga sakamakon Matsalar Network da muke Fama a Kauye.

Ba wani abu ne yasa na rubuto maka wannan Sako ba sai wani arziki da muke nema a wajenku dan Allah idan babu damuwa me zai hana a bawa Nabeel danka auren Hamida sabo da mu rufawa juna asiri tunda yaron nan shine ya aikata Mana ba daidai ba,da farko Kuma kace shine zai aureta bayan ta haihu,Ina neman wannan Alfarmar ,nasan Kai mutum ne me adalci da sanin ya kamata Ina so kayi shawara da Yan uwanka idan Kun Amince ko a waya ku Neme Ni,ko Hamida ita bata cancanta ta Zama matar Nabeel ba? Indai akan halayenta ne Hamida Inshaallah zata canja Inshaallah kuma kaga alama ta fara canjawa,babban rufin asirin da zakuyi Mana mu iyayenta shine ku aurawa Nabeel ita da Kun gama mana komai a duniya.
Dan Allah karku aurawa Nabeel wata face Hamida na rokeku ku rufa Mana asiri Kamar yanda Allah ya rufa muku,sai naji daga gareka
bissalam
Sako daga Alhaji Isah Tahir marikin Hamida

Mimi tana ji tace Alhmdllh dama abinda ya kamata kenan dama Nima abinda na yanke dan naga Hamida Ashe tana da hankalinta rashin tsayayye ne ya jefata a wannan hali amma gashi yarinya sai hankali take Ina goyon baya Kuma Lele yana sonta gwara a musu aure su karata dama shima Lelen ai Watarana irin halinsu daya da Hamida,Affa ya kalleta yace Kika ce da akan ya auri Hamida Zaki bar gidan Nan,Mimi tace na janye ba gwara ni ba Kai da ya Mata ciki kace love ne,Affa yace Nima naji wa'azi na ajiye akidar Bokon Nan Naga aya a gidana ba ruwana yanzu sukayi dariya,yace yau Zan fada Miki abinda Baki sani ba Kinga abinda Nabeel yayi ko to Nima Sanda Ina matashi na aikata,Sanda naje karatu turai shekarata goma bana Sallah daina yin Sallah nayi Kuma giya Nasha sai dana aureki na daina Shan ta ruwa na koma Shan alawar giya,Mimi ta zaro Ido waje tace yanzu dama duk alawar nan da Naga kana Sha giya ce? Affa yace ei ai in baki manta ba Sanda nake zuwa zance ma Zaki ga na bare alawa na jefa a bakina har kike cewa na San Miki sai nace Miki sai naje shopping Zan siyo Miki taki daban ai wacce nake Sha giya ce Baki sani ba.

Mimi tayi salati tace da nasan hakane ai bazan aureka ba wallahi,Affa yace aikin gama ya gama yanzu ko sakinki Kika ce nayi wa zai aureki a zamanin Nan da Mata Suka cika duniya yan matan ma ya Suka kare haka Zaki hakura mu karasa zuna,ke dai tunda Allah ya shiryeni ki godewa Allah amma Ni abinda nayi Nabeel baiyi ba,Mimi ta rufe baki da hannayenta yace shi yasa Kika ji nace love ne a zahiri ba haka nake nufi ba naji zafi dannewa Kawai nayi na tuna Nima nayi amma Ni bata samu ciki ba na tabbatar da fadar Allah duk abinda kayi sai an maka shi yasa ake so ka dinga hangen baya da gaba nayi nadama wallahi.

Yarinyar nan Hamida Bata San tarihinmu ba Kuma ki duba Nabeel ya Mata ciki amma taci gaba da sonsa idan Nabeel ya rasa Hamida ai har abada bazai samu me kaunarsa haka ba, nan gaba zata san asalinmu Inshaallah itama ta Zama jininmu.

A ranar Affa ya kira Yan Uwansa yace su taho jibi da Shirin daurin auren Nabeel da Hamida.
Bangaren Hamida Kuwa Papa ta Kira tace idan Affa ya kiraka ko me yace kace ba matsala karka ce baka San zancen ba,papa yace wani abin Kika kulla Kuma ke Hamida ki kiyayeni,Dan Allah Papa Kawai ka amsa haka yace to Kawai.

Sai 11pm Affa ya Kira Papa Bayan sun gaisa yace Naga sakonka Kuma nayiwa Yan Uwana magana sun amince jibi Inshaallah zamu Zo da Shirin daurin auren Hamida, Nabeel zai aureta Kuma mun dauki nauyi komai ba abinda zaku siya,Papa yaji dadi duk da bai San me Hamida tayi ba ya amsa da murna harda godiya.

Yana Gama Wayar Nabeel ya Kira ya sameshi a bedroom Nan ma ya Kira Hamida tazo,Hamida gabanta Yana ta faduwa ta durkusa a gefe can ta rakube Kamar ta Allah,Affa yace Papa ya turo wasika gashi ku karanta ya mikawa Nabeel ya karba ya karanta tsaf sabo da farin ciki bai San Sanda ya washe baki ba,Hamida ya mikawa ta karba a nutse,Nabeel yace Zo a karanta Miki baki wani iya karatu ba Zaki bata Mana lokaci,Hamida ta taso sum sum ta dawo kusa da Nabeel ya fara karanta Mata rai rai Nabeel harda kari yace kinji yanda Papa ya yabeni yace Ni mutumin kirki ne na daban ne a cikin mazajen duniya,ya sake duba takardar ya dago ya kalli Hamida yace kinji yace gani da nutsuwa gentle man,Hamida tayi Murmushi tana sauraron zuki ta malle tace to Papa bai iya karatu da rubutu ba Kamar Ni haka yake, Affa yace to in ba shi ba wa zai rubuta,tunawa tayi zata tonawa kanta asiri tace Yaya Sulaiman ke Masa rubutun ai.

Nabeel takardar ya kalla tare da kafe rubutun da Ido Yana karantawa a fili Yana cewa a bawa Nabeel auren Hamida badan komai ba sai sabo da hankalinsa da kamewarsa da nutsuwa,Alhaji Al-amin danka Nabeel ne kadai zai iya saita Hamida ya bata ingantacciyar rayuwa,Affa yace Miko min takarda dama yanzu uwarka tace kaima irinku daya da Hamida,Hamida an nutsu a dole ta kirki,Affa yace Hamida ya Kika gani kin Amince kina son Nabeel?

Hamida tayi kasa da kanta tare da rufe Rabin fuskarta da hijab a hankali tace Affa ya tsaya nidai na Kara kallonsa idan ya min? Mimi tayi dariya tace duk kallon da kika Masa sabo Zaki sake yanzu,Hamida ta boye Fuska tace to abinda kuka ce yayi bani da zabi,Affa yace kin tabbatar? Hamida ta daga Kai wai ae Affa yace mashaallah za ayi komai Inshaallah,Kai Nabeel ka kawo kudin aure da za a bawa iyayenta,Nabeel murna ta isheshi yace million Nawa?Mimi Tace kaima fa Nabeel Zama da Hamida yasa ka zama wani iri tashi kuje,a tare Suka fice,suna fitowa a steps Nabeel ya rungume Hamida tare da sakinta yace wannan na Kai kudin aure ne,anjima kadan zanyi na Engage dana daurin aure da Kuma na Kai kayan lefe,Hamida tace duk a yau? a'a bada ni ba matsa dan Allah na wuce,Nabeel shi duk zatonsa bata sonsa ganin bata murna bai san itace ta Kai wasikar ba.

Bayan Hamida ta shiga room dinta Papa ta Kira a waya,yace Hamida Wai wanne Sako ne Affan naku ne ke cewa yaga sakona mene? Hamida tace sai na Zo kauyen papa Zan fada maka, Papa yace to Hamida na yarda da ke,Shirin biki Kuma Affa yace za ayi a Nan kauyenmu gidana sai ki kokari gobe ki taho gida,Hamida tace to Papa,sunce su zasu Miki komai Hamida tace to Papa sai na Zo,Yace na sanarwa kawarki Sakina kin San tayi aure ta Haihu ma,Hamida tace ta fada min a waya,to shike Nan sai goben ki taho da wuri,Hamida tace to Inshaallah.

Washe Gari da sassafe Hamida tayi shiri tsaf zata koma kauyensu,Mimi ta kawo Mata kaya duka English gown ne masu tsadar gaske kala biyu Wanda zata sa da biki sai wani arnen lace tace wannan da shi za a kawo ki dakin mijinki to Hamida tace tare da yin godiya duk tayi wani sululu haka bata da karsashi,shi Nabeel Yana kula da ita Kamar kaunarsa ce bata Yi haka yake gani,takalma da jaka masu tsada Mimi ta shirya Mata tsaf tace Nan gaba zamu hada lefe ko kina dakin mijinki Inshaallah,Affa ya hada Mata uban tsaraba iri iri yace taje ta rabawa Yan Uwa.
Nabeel ne ya fito zai rakata mota driver ne zai kaita har can a zukekiyar
Showing 42001 words to 45000 words out of 133235 words