Hamida zata fahimce shi Amma Taki sai cika masa kunne ma da tayi da surutu sabo da bata magana a hankali,sai yace it's okay na Miki alkawari ni Kuma Indai kinje school Zan Baki dubu Daya kullum,duk ranar da kika je school to kizo Zan Baki dubu Daya cikin sauki ba tare da kin Sha wuya ba.

Zabura tayi da sauri ta juya ta kalle shi Suka hada Ido ta washe Baki tare da cewa Dan Allah da gaske kake?, Idan kina ganin karya nake Bari a fara Nan take ya zaro rafar Yan dubu dubu yace ga kudi kin gani,1k ya zaro ya mika mata yace mu Fara daga yau,a Nan nake Aiki kullum Ina wannan titin naku,Dubu Daya ta karba Hannu na rawa da karfi tace ka tabbata kayi alkawari? Yace ae ai ban Miki Kama da Yan karya ba,idan ka karya alkawari Al'quran sai na karya Nawa zanje dai school Amma sabo da kudi,Kuma tsakani da Allah bazan rufe ka ba bazanyi karatun ba bazan gane ba,duk Nabeel ya gaji da cecekuce yace naji Kawai kije school ki zauna a class har a tashi kizo ki karba 1k fine,Dariya ta kyalkyale da ita ta Kara wani kyau sosai dama gata me shegen kyau Kalar skin dinta me kyau baza ace Mata baka ba Amma Kuma baza a kirata Fara tar ba,Yar cif cif da ita sura me kyau komai nata dai dai Allah ya Mata Kira.

Da sauri tace da Dan uwanta Kai Sulaiman kake ko Sule na tafi school Allah ya taimakeka,ta tsani Sulaiman sabo da yanda yake dukanta sai taje makaranta dubunta Guda ta Bude tana tafiya tana kallonta Dan bakinta a washe da gudu ta kwashe har zuwa school.

Haka a class tunda ta shiga aji ta bude window gefenta ta kurawa waje Ido Haka malamai Suka barta sukayi darasinsu aka tashe su sabo da Hamida sun gaji da halinta Bata tsoron uban kowa ba kunyar kowa take ji ba bata Jin magana,Bata da rufa rufa komai ke ranta Kawai fada zata yi ko Mene,ko a gidansu an yarda ita bata karya.

Washe Gari ana tashinsu Nabeel ya manta da ita da gudu ya ganta ta taho wajensa hijab din a hannunta da takalminta Sandal duk a Hannu sai dai fes take ,Yana nunawa masu Aiki a motoci yanda zasuyi sai gata tazo da gudu tana dariya tace yawwa an taso mu a bani na tafi, Rana ta dameshi ya gaji yau sanye yake da kana Nan Kaya yayi kyau kallo Daya ya Mata ya zaro dubu Daya ya Mika Mata Tace na gode Allah ya biya ta sake arcewa da gudu da kallo Kawai ya bita tare da girgiza Kai yace Kauye kenan yaci gaba da uzurinsa Yana Gamawa ya tuka motarsa zuwa masaukinsa Hotel karami Dake kusa da kauyen,yana shiga room dinsa yayi order abinci sannan ya fada saman bed Yana huce gajiya,wanka yayi tare da Sallar la'asar ya kunna kallo Yana kallon ball har aka kawo Masa abincinsa yaci ya kwanta bacci ya kwashe shi.

Basma zaune take a dakinta me kyau tare da kawayenta suna ta zuba Hira tana Basu labarin Nabeel dinta abin kaunarta,cikinsu Amal tace Basma Angon naki yayi tafiya Wai kin shiryu ne an daina cutar samari,Basma tana Dan yanga ta manyan Yara tace wallahi Allah ya shiryeki duk Wanda na yaudara na Basu Hakuri sun yafe min yanzu Haka Ahmad ne Kawai Wanda ya Soni da gaskiya ai Kun San yayi aure wlh matarsa wajen nakuda ta rasu yanzu ya koma Dubai Karo karatu na rasa contact dinsa bare na Nemi yafiya yanzu Ni abinda ya dameni rashin Nabeel Kun San so kana so ka dinga ganin masoyinka a kusa,tafawa sukayi shegiya ko dai Kuna Dan romance ne? Basma ta yatsina fuska tace duk samarin da nayi da Ahmad Kawai nasan Yana min abubuwa masu sweet Amma yanzu na tuba sai dai da Nabeel zaiyi min Dana ji Dadi Kun San Body no be firewood,wlh Nabeel ko Hannu bai taba rike min ba sai kace Dan Kauye, gashi dai kyau karshe ga wayewa da komai ya hada Amma wallahi ko hannuna Bai taba rikewa ba,kunsan ko jikina na Dan matsa sai ya janye jikinsa gashi a Baki Yana ta nuna min kauna amma ba komai Allah ya kaimu ayi aure sai ya min Amma har ga Allah da kyar nake kaiwa Dariya sukayi suna tafawa.

Basma Tace ai Ni Ina son Namiji me class irin Nabeel,ga addini,ga tsoron Allah ba ruwansa da Mata sai Ni kadai,ai Yana bala'in so na,Kun San na yarda da kaina nice fa ware Baiko idan na rabi namiji ko Saura sati bikinsa a Rana Daya Ina rusa auren bare Kuma na tuba,nice fa da kaina nake sonsa ai ya shiga Uku ya Gama yawo,Nabeel na Gama sa Masa takunkumi ba wacce ta Isa shima bai Isa ba,inda Allah ya taimaka ma ban damu ba Kauye ya tafi aikin,wallahi tausayi yake bani Kamar Nabeel Dina a Kauye ga yanda yake bani labarin garin titin da yabi ta garin abin ba dadin ji,da ace birni ya tafi ai da na shiga uku sai Allah yasa Kauye ne ba wacce zai gani ta birge shi, Allah dai ya kaimu bikin yace in munyi aure ko Ina zaije kafata kafarsa.
Shewa sukayi Suka tafa suna ta Shan labarin Basma.

Tunda Nabeel yayiwa Hamida Alkawari kullum sai ya cika Kuma Bata kashe ko kwandala Tara kudin take ta Yi zata kafa jari ita dole sai ta Zama Yar kasuwa,Papa da Ummi da sauran Yan gidan suna mamakin yanda Suka ga Hamida kafin kowa ya tashi ta tashi tayi shara da wanke wanke da aikinta tayi Shirin school ta tafi Basu San ana Bata kudi ba sai mamaki suke Sulaiman yace ban yarda da yarinyar Nan ba Sam Ummi sai naje na duba makarantar,Itama Karima kanwar Sulaiman wacce ta Gama Degree an kusa bikinta ma tace makaranta take zuwa Allah yasa hakan ya Dore,Ummi Kuwa tabe Baki tayi Kawai Tace ummm sabo da Bata dauki Hamida a yarta ba,da yaranta Kawai take kula duk abinda Hamida zatayi tayi ba abinda ya shafeta ita Kuma Bata Mata mugunta Kawai dai Bata sa Ido akan tarbiyar Hamida sai ta yaranta,Wanda ya damu da inganta rayuwar Hamida Papa ne da Sulaiman babban Dan Papa.

Bangaren Hamida Kuwa da Nabeel sosai take Jin dadin kyautar Nabeel gashi kyawunsa Yana birgeta sai tayi ta kallonsa tana Jin Dadi,Ana taso su ta taho yau Kuma wata tafiya take Kamar Namiji ba ruwanta da wani ita macece,tayi sa'a lokaci motarsa ta yanko yau Bai Zo da wuri ba,Ganin motarsa fyalleliya da gudu ta bi bayan motar ta tana tura motar Dake tuki yake da slow zaiyi parking,Yana parking ya fito yaci uban kana Nan Kaya yasha kyau harda glass hadadde,Hamida ta kalle shi tana ta faman Dariya Kamar zararriya Tace Sannu da zuwa kyakyawan Dan Uwa,kasan ka Zama Dan uwana,Kyakyawan Oga Bari na goge maka motar kaga Nan ka shiga chabi Nan take ta zare hijab dinta tana goge Masa mota da sauri yace no...no Bari Zan kaita car wash,ai da ka Bari na goge maka Kyakyawa tana ta faman washe Baki yace no barshi a gabansa ta dawo ta tsaya tana wulwula hannaye tare da Sosa wuyanta yace Ahmm...mene ma sunanki?

Baki ta bangale Tace sunana na gaskiya Hamida amma da hausa Ana ce min Hamidatuwa,sunana na turanci Kuma Hamdy Amma zaka iya kirana da Hamida Hamdy Baby ae kwarai ehe yawwa,kallonta yayi Karo na biyu yanda take magana ba ko Jan numfashi ga sangarta da shagwaba Haka take magana,Hamida yace Naga dai kina zuwa school yanda nace yau harda bonus Zan Baki gashi karbi ya Mika Mata har 3k,ta kalleshi ta kalli kudin tace yau fa Weekend ba school gaisheka nazo Kawai Amma ka bani har dubu uku,yace ae Baki nayi ai kina yin abinda nace yanzu idan Naga kina kokari kina fahimtar abinda ake koya Miki Zan Baki kyauta Babba wacce tafi wannan,Me nace Dake Rannan? Tace kace idan nayi kokari Ina karatu zaka bani kyauta babba,Good ya furta tafi gida karki tsaya wasa,ta Kura Masa Ido yace I said Go, Tace Okay Sankiyu sir Wai Thank you take nufi,Fuska ya Bata yace ba Sankiyu ake cewa ba thank you Fadi naji,ta sake cewa sanki...kafin ta karasa yace no kalli lips Dina thank you,thank thank thank you,ta kasa ta sak cewa sanki..no,thank,Tace sank again ya gaji yaga dakikiyace ta karshe yace abeg go home tafi I'm tired.

Tana kallonsa Tace in tafi kace? Yace ae Yana yatsina fuska zata Kara Masa surutu ya daka Mata tsawa,Ta juya da sauri ta kalli ma'aikatansa Tace Kai kunci kwalabar gyatiminku dukan ku nasan ba a son ranku oganku yake bani kudi ba sai dai ku mutu wooooo....Kunga an bani dubu uku kwana Nan Zan iya siye kawunanku,Daya a ciki ya dura Mata mahaukaciya Tace wullu wullu tana ta musu gwalo ta arce da gudun tsiya..

Gidansu ta shiga suna zaune a tsakar gida Sulaiman Yana ta game shi da kanwarsa Tace mutum kullum yace a tafi makaranta Wai a Haka anyi makaranta ana gida kullum,ko Zama batayi ba ta sake Fitowa ta fice da sauri Kamar Namiji wajen kawarta ta tafi ta iske sun dawo daga kasuwa Suka zauna suna Hira, Tace yawwa Sakina na manta ban fada Miki ba Ina Yaya Sulaiman kin San yanda yake dukana sai naje makaranta? Sakina Tace ae Kamar yanda kuka Saba,yawwa Rannan ya biyo Ni Yana ta duka na Sai naje school sai muka bi ta wajen sabon titin da akeyi inda katafila suke? Sakina Tace na Gane

Ogansu na wajen ya dinga yiwa Yaya Sule fada yace a'a ba Haka ake ba karka sake dukanta Nan Ogan Nan ya dinga fada min kalami me dadiiiiiiiiii ta wani ja sanna taci gaba amma duk na manta abinda yace abinda na rike kawai a kaina yace kullum in naje school zai bani dubu Daya,Sakina Tace ke ki Bari Dan dan Allah? Wallahi Kuma Yana ta bani yau ma harda bonus,Sakina ta mikawa Hamida dafaffiyar Masara suna ci Sakina Tace dubu Daya a wata Kinga dubu talatin kenan,ai ihu Hamida ta kwala tace na Zama Hajiya kinga sai na Fado kasuwarku Nima Ina Saro Masara a gona Ina kaiwa kasuwa,tafawa sukayi harda shewa,ai ko Papa baya samun kudi haka gashi

yana da kirki gashi kyakyawa na sosai fari Kar da shi,Kin San fa Yaya Sulaiman duk dukana da yake nasan baici exam ba shima,ya akayi Kika sani? Sakina ta tambaya, Tace ke idan yaci jarabawa Zaki gashi ganshi a zaune a gida bashi da Aiki sai game babu aikinyi,ba Wani ilimi da yayi in ma yayi ban yarda ba,yanzu Baki ga kyakyawan Yaya yake ba Yana Dan lallaba Ni ba irin yanda ko a Gari ake min kallon marar hankali ba,Dariya Sakina tayi Tace ko dai son kyakyawan Yayan naki kike yi? Ba Wani so Kawai dai Yana da kyau ai nafi son dubu dubu dai Dariya sukayi suka dinga hirarsu sannan ta tafi.

Kamar kullum yau tazo sanye da Uniform an taso su da gudu ta karaso hannunta ya fara hangowa an manne shi da bandage bai ce komai ba Hamida tace Yaya Kyakyawa kaga hannu na kofar Hannu ce ta datse min yatsa,eyya sorry ya furta tare da zaro kudi ya Mika mata dubu daya yaci gaba da magana da ma'aikatansa sai taji yace hotel Zan koma Zan Yi wanka.

kusan kullum Hamida tazo sai taji yace wanka zai je yayi,Yana bata mamaki ko sau nawa yake wanka a rana oho, ta juya zata tafi sai ta juyo tare da kwala masa kira Yaya Kyakyawa agwagwa tana gaishe ka,Bai gane nufinta ba ya zaci shirmenta ne ba tare da ya dago ba yace kice Ina amsawa na gode,Dariya ta kyalkyale da ita bai sake ko juyowa ba itama haka ta tafi da sauri gida tana tuntsira dariya.



Littafin Nan ba a farko za a Sha Dariya ba sai gaba
Fans


AsmaBaffa
[6/28, 1:46 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮


3

Official


By
AsmaBaffa

Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



page naku ne

BASMAM GLAMOUR
MOM ABDALLAH
NAFEE
UMMU LATEEPHA
SA'ADATU TIJJANI
MMN UMMEE




Yau Monday yazo wajen leburorinsa sanye yake cikin shadda sky dinkin cif cif shi Yana jikin mota ya Kara waya a kunnensa Yana waya da Basmansa suna zuba love Hamida ta taso daga makaranta ta lallaba ta bayansa Wai zata bashi tsoro tayi Masa Cakulkuli da sauri ya juyo fuskara a murtuke Kamar an Aiko Masa da mutuwa nan take ta Shiga hankalinta taji tsoronsa sosai,waya yake Yana daga Mata hannu alamun tayi Shuru amma dariya Kawai take kamar itace take wayar,ta koma surutu tana to kayi hakuri Yaya kyakyawa bazan sake ba,Basma ta cikin waya Tace wace wannan? Yace no cikin yarana nane akwai wani me zubin Yan daudu to shi ya yazo,Basma taja tsaki tare da furta Allah ya wadaran halinsa, Hamida bada ita ake ba Amma sai dariya take haka Kawai.

Da sauri yace idan na koma hotel Zan kiraki ya datse wayar,Yana gamawa ya daure Fuska kamar an aiko Masa da mutuwa ya kalli Hamida Nan take ta nutsu yace yaushe kika Raina ni? Yaushe muka fara Haka da ke?Zaki zo ki taba min baya sa'anki ne Ni shashasha,Baki ta kumbura cike da shagwaba tace kayi Hakuri bazan sake ba,ka yafe min,Nan take yace ya wuce tare da zaro dubu Daya yace oya take jeki,Tace ya Naga kamar baka hakura ba ta furta da agwagwaba,yace na hakura karki sake Tace to,tafi to tace Zan tafi ai kaje dani Naga gidan da kake Zama dan Allah.

Bafa a gida nake ba a hotel nake Zama Aiki ya kawo Ni na kusa tafiya ma,Ina zaka tafi? yace can state dinmu Nan ba state dinmu bane Aiki ya kawoni Kuma aikin ma nayi tunanin zai dade Amma gashi mun kusa na kusatafiya gida,Kuka Hamida ta kece da shi ta Fadi a kasa ta fara birgima da burburwa tana Shure Shure ganin zata tara masa mutane

Yace ke..ke..ke tashi mene? no ..no..no.. stop crying ai ba yanzu Zan tafi ba da sauran kwanaki Kuma ko na tafi zandinga Aiko Miki da kudinki okay, sai lokacin tayi Shuru ta Mike tana share hawaye ta juya jiki a sanyaye tafi gida,yau Rai a bace tana kuka ta Shiga gida,Ummi ta samu da Papa ga Yar Ummi itama suna ta Bude kayan auren Karima ana gani Suka ga Hamida ta shigo da kuka,Sulaiman yace ke Kuma lfy? tana shesheka tace ba..ba..ba..Yaya kyakyawa ne yace zai tafi garinsu ba wallahi bana so ya tafi,Karima ce ta Mike ta dakko ghana must go ta kayan Hamida ta fito da ita ta bude kudi Yan dubu dubu da take Tarawa suka bayyana kowa ya saki salati

Wajen kayan Hamida ta karasa ta kwashe kudinta tas a hannunta,Papa a nutse yace Hamida a Ina Kika samo wannan kudi Haka? Ba tare da shakkar komai ba tace kawu wani ne ogan masu aikin titi yace Indai Ina zuwa makaranta kullum zai bani dubu daya har bonus ma yake Kara min da yaga Ina yin abinda yace kuma baka ganshi ba kyakyawa wallahi Kamar balarabe,ai kudin ma basu kenan ba akwai ragowa so nake na Tara na kafa sana'a mu Zama masu kudi bari na dakko wancen kudin na tuna da gudu ta nufi hanyar daki Tace ku matsa daga hanya Kar na kade ku,ganinta da gudu yasa Karima da Sulaiman Suka watse daga saitin Hanya ta wuce ciki sai gata ta Kuma Fitowa da dubu biyu da dari biyu,Tace wannan na jiya ne ya bani dubu uku,to Nan ya Naga dubu biyu da dari biyu Papa ya tambaya, Tace Yi Hakuri na manta na bawa Sakina a ciki Zan siya Masa kayan marmarni na Kai Masa sabo da mutuncin da yake min.

Kirji Ummi ta dafe Tace papa Ina tsoro karfa Yarinyar Nan ace Dangerous part dinta yake tabawa Yana Bata kudi ka tsawatar kar a samu matsala,da sauri Hamida ta girgiza Kai tace a'a..a'a wallahi ba abinda yake tabawa nawa Dangerous part Dina suna Nan lafiya ba abinda ya dame su,papa yace ki dai kula na fada miki, ai nasan Papa duk gidan Nan Kai kadai kake kaunata bari na kwashe kudina Kar ma a sace min barayi sun San kansu ehe ta furta tana kallon Ummi, ta kwashe kudinta tare da zubawa a wata karamar jaka tace yace ya kusa komawa garinsu ma Kuma bana so ya tafi.

Baki Suka tabe suna binta da kallo tana fita wajen Sakina ta wuce ta Bata labari Yaya Kyakyawa yace ya kusa tafiya ta fada da Kalar tausayi ta zuba uban tagumi tace zanyi kewar sa,Sakina tayi Dariya Tace kewarsa ko ta kudi? Tace ta Yan dubu dubu gaskiya nafi son kudin sai suka kwashe da dariya,Hamida tasa hannu a baki tana Murmushi, fita sukayi kasuwa ta siyo Masa abarba da Ayaba,sannan Suka je gona tare da tsinko masa lafiyayyun mangoro da yawa tace a hada Masa da goruba da giginya,Sakina tace na shigai Yan birni basa ci bare Namiji tace a dai hada da su na Kai Masa kafin ya bar gari Nima nayi Masa abin kirki yanda shima yake kyautata min yana bani kudi kullum ba irin Sulaiman ba da yake dukana kullum.

Haka Suka cika wata leda Viva da kayan marmari Suka tafi yau da Sakina za a aje ta Kai gaisuwa wajen Yaya kyakyawa.

Ai Kuwa Yana jikin mota a tsaye Yana latsa katuwar wayarsa Yamma tayi ya gaji sosai,da gudu Suka fyallo kayan Yana Kan Hamida suna zuwa Sakina tunda tayi arba
Showing 6001 words to 9000 words out of 133235 words