Ammar yace yanzu ya motsa yatsansa baki gani ba wallahi,wayyo Dadi kasheni dan Allah? Ammar Dariya ta bashi yace Allah tace bari nayi sauri na dawo ta kashe Wayar.

Affa ne ya kalli Ammar yace Hamida ce ko? Mimi sai taji duk duniya bata da Kamar Hamida ta damu da danta matuka,Basma Kuwa karfe uku na Yi tace Mimi Naga an kawo abinci yunwa nake ji ta koma wajen kayan abinci ta ebi abinda ranta ke so taci ta shake cikinta,Mimi Kamar ta mareta haka taji,kafin magrib Hamida tuni ta dawo lokacin Kuma an gama komai na tafiya da Nabeel Paris,Affa,Mimi,Ammar da Alhaji Abbas sune zasu tafi,Hamida ganin an fito da Nabeel kamar an dauki gawa ta fashe da kuka tace wallahi mutum ba komai bane a wajen Allah dan Allah a tafi dani,Affa ya lallasheta yace ko sati baza muyi ba Inshaallah a gida zamuyi jinyarsa karki damu kije gida,Basma gidansu ma ta wuce abinta,Hamida ta koma gida ta tsaya a wajen su Inuwa suna jimami tace la'ila ha illallah Uncle Inuwa muji tsoron Allah mutum ba komai bane Hamida bata San Sanda tace Nabeel Dina sak gawa tana hawaye tayi cikin part dinsu ta fada bedroom dinta tare da fashewa da kuka ta kifa kanta a saman bed,su Affa Kuwa tuni sunbi jirgin Abuja daga can suka wuce kasar Paris







AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

9

Official
By
AsmaBaffa


Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne

Mom Aneesat
Tajrah
Ummeealgusawi
Alhamdulillah
J Jad kitchen
Aysher kabara
Asli Smasher
Anty Nurse Zaria
Real Maman Waleeda






Suna zuwa hospital suka wuce direct dama an San da zuwansu babu bata lokaci likitoci Suka karbeshi,Suna gama komai su Affa Suka wuce hotel gaba dayansu,Mimi da Affa room daya,Alhaji Abbas da Ammar ko wanne dakinsa daban,wanka sukayi tare da cin abinci sannan suka gama komai Suka koma hospital din ba dadewa Suka yiwa Nabeel aikin gaggawa aka gama cikin kankanin lokaci Already sun sa Masa robar fitsari, Bayan sun gama Suka canja Masa Yar farar rigar hospital din sannan Suka maida shi dakin Hutu sannan likita ya nemi ganin su Affa a Office dinsa.

Tsohon baturen tukuf su Affa ansha boko an koshi turanci Kawai ake watsowa ta ko Ina,Doctor din tsoho ne tukuf cikin harshen turanci yace Aiki yayi kyau ba wata matsala zuwa Nan da 14days za a sallameku amma sai yabi dokoki Indai baya so wata Matsalar ta faru,akwai wani liquid zamu baku kullum zai zuba a cikin ruwan dumi ya zauna a ciki kullum sau daya har tsawon 3mnths,banda sex sai After 5-6 mnths,ba fita sabo da ba a so yayi yawo ko driving ko motsa jiki daga kwanciya sai Zama sai ko Shiga toilet da ya Zama dole,bayan wannan ba wani abu da zaiyi,Kar abari yayi wani abu Wanda gabbansa zasu Sha wahala,Mimi har rubuta dokokin a jotter Kar ma a samu matsala,Bayan sun fito Suka Shiga inda Nabeel yake,aikin da aka Masa yasha wahala matuka duk ya fita a hayyacinsa kowa yaga Lele sai ya tausaya Masa,Alhaji Abbas ne ya kalli Mimi yace Fadila fa ta gaji kuka takeyi a kawota hutu wajen Mimi,kyaleta tukun sai Nabeel yaji sauki sai na maka waya a kawo min ita hutu,Alhaji Abbas yace ba matsala dama sabo da kullum ta ganni sai tace kawu Mimita a kaini wajen Yaya Nabeel,Murmushi Suka yi Kawai Jin Nabeel ya farka Yana kuka sabo da zafin da yake ji Yana Kiran Mimi dinsa,Mimi da sauri ta karasa Kansa tare da rike hannunsa tana cewa Nabeel dina gani,Ammar yana kansa shima ya rike hannunsa,Allurai Suka Masa ya koma bacci,Affa yace ah da Sauki ai in kaji mutum Yana iya kuka ma da Sauki,Sanda abin ya faru ai ko kukan bai iyawa,Alhaji Abbas yace duk Sanda aka Kama Wanda yayi abin Nan wallahi gidan sojoji za a fara kaishi duk azabar duniya sai an gana Masa kafin karshe a kaisu prison ko Yan Sanda bazan sa Yan Sanda ba a case din sabo da Kar su barsu a banza.

Ammar yace duk Wanda Suka Masa wlh sai an musu abinda Suka ma Nabeel,suna ta tattaunawa,Hamida tana gida ta rasa sukuni gashi har yanzu basu Kira ba bare ta samu number ko Ammar ne,wanka tayi tare da gabatar da Sallar nafeela ta daga hannu sama tana yiwa Nabeel Adduar samun lfy,Ranar Shehu ma cewa tayi ya bari sai an dawo da Nabeel taga lafiyarsa sannan za a ci gaba da karatu,tunda Suka tafi Bata da aiki sai nafeela,karatun Qurani,tasbihi tana Addua Allah ya bawa Nabeel lafiya.

Hamida Papa ta Kira Suka gaisa ta sanar musu halin da ake ciki,Yaya Sulaiman yace sai su Affa sun dawo zasu Zo dubiya..
Su Mimi kwanan su biyu a can Nabeel ya dawo hayaccinsa daga bacci ya farka Mimi ce kadai kusa da shi ya kalleta yace zanyi brush,da sauri ta kawo Masa wani bowl a ciki yayi sannan yace wanka,Mimi tace zasu zo su maka kasan Wanda ake maka daban Kuma nurses ke maka,kafin ta gama magana nurses maza sunzo Nan Suka saki wani labila suka masa wankan tare da canja Masa wata Yar Riga ta Hospital din fara dama simunce ba sa wando har watanni biyu haka,Alwala Mimi ta Masa a kwance yayi sallalolinsa sabo da ba damar tashi ko Zama bazai iya ba sai Nan da sati biyu lokacin da za a sallamesu,Abinci Mimi ta bashi yaci Kuwa da yawa yasha magungunansa sannan ya kalli Mimi yace Ina Pipi fa? Mene wani Pipi? Hamdy fa nace,Dariya ya bawa Mimi tace hmm Wai Hamidan ce Pipi Kuma? Wannan sunan Ina kuka samo shi? ko a Kira maka ita a waya? Kai ya daga Mata,Wayarta ta dauka ta Kira number Hamida,Lokacin Hamida tana kwance saman gadonta tana ta tunanin Nabeel,Ahmad sai kiranta yake taki dagawa,gajiya tayi da nacinsa ta daga da masifa yace dan wulakanci Ina Kira tun jiya kina shareni sabo da Farkan naki an yanke Masa abar,ai kamata yayi ma ku gane cewar Allah ne ya Nuna masa ishara,Tsaki Hamida taja tace Banda lokacinka ta kashe wayarta a ranta ta furta shi tunaninsa ai ya kawo kudi shike nan ya gama me wahalar zanyi maganinsa da kaina wannan ba mijin aure bane.
Kiran Mimi ne ya shigo da number Paris,tana ganin number kasar waje da sauri ta daga

Sallama tayi a nutse ta tsinci Muryar Mimi ce da ladabi ta gaisa ta sannan tace Mimi ya me jiki a sanyaye hawaye ya cika Mata Ido Nan take kuka ya kwacewa Hamida,ita Kam Mimi mamakin Hamida takeyi yanda ta fisu damuwa ma abin daure Mata Kai yakeyi,tun kafin a mikowa Nabeel waya tuni ya Miko Hannu a bashi ita
Mimi tace Lele ne fa yace a bashi ku gaisa ta Mika Masa Wayar ta mike ta bar Masa room din sai shi kadai

Hamida tana kuka tace Hello...Muryarsa taji tsab ba alamar Yana Jin jiki yace, Hamidatuwa Pipin Kyau,tana hawaye tayi dariya ba shiri tare da furta Ina Yini,Wai yaune Karon farko da Hamida ta gaida shi lallai an Fara hankali,tunaninsa ta katse Masa da cewa naji kayi Shuru ko jikin ne? Ya jikin da Sauki? Nabeel yace da Sauki sosai ba a taho da ke ba ga ranar ganin Duwawu a banza,ba shiri tayi dariya tace ba ruwana bazan sake kallo ba,Dan Allah ki ganta farar takashi gata a Nan ana barinta a banza,Baruwana ni dai dan Allah ka daina tuna min kunya nakeji ni,tunda kaji sauki Alhmdllh,Marairaicewa yayi yace me yasa Kika sa Ahmad ya kawo kudin aure? Mutumin da tun yanzu ya fara Miki gori shi kike so? Share zancen tayi tace yaushe za a sallameku? Nabeel yace Nan da 2weeks Inshaallah bakya son a Miki zancen Ahmad dinki ko? Yanzu kinfi son bakin duwawu akan Fari? Hamida tace ni dai dan Allah ka daina fadan harkar nan kunya kake bani,Jin tafi son Ahmad ya kashe Kiran kawai.

Hamida Kuwa Jin Nabeel tar akwai sauki sosai sai Murna tayi tsalle ta fada saman gadonta tana wani farin ciki ta mike ta fito ta ebo abinci a kitchen da yawa ta zauna ta ci ta koshi tare da korawa da ruwa.
Hijab dinta brown ta saka sannan ta fita wajen su Inuwa tace uncle Inuwa Lele yaji sauki sosai yanzu mukayi waya da shi har Wasa da Dariya muka yi,su Inuwa Suka dinka murna haka ta koma part din Mata Yan aiki ta iske su suna hutawa Hamida tace bayin Allah to ku tayamu godiya ga Allah Lele ya fara warkewa,gaba Daya Suka hada baki Alhmdllh,ficewa tayi ta koma bedroom dinta ta dauki Wayarta ta Kira su Papa ta fada musu Suma sunyi farin ciki, Doctor Ahmad ta Kira sabo da murna,ya zaci wani kudi ta samu yanda yaji tana Fara'a da murna Hadi da nishadi,yasan Kuma sunyi waya dazu sunyi fada,Hamida tace Yaya kyakyawa ya samu sauki sosai yanzu ya kirani har Wasa da Dariya mukayi,Nan take ran Ahmad ya baci Kamar zai cinyeta yace to shine abin murna haka ni na zaci ma wasu Kan kudi Kika danne tsaki Yaja tare da kashe wayarsa..

Tunda Hamida ta samu Number din Mimi kullum sai ta neme su an hada da Nabeel taji ya jikin har Suka kwashi 2weeks sai Shirin dawowa,Hamida ta zaci a gidan Mimi za a bar shi ta sa masu Aiki Suka gyara ko Ina na gidan neat,ranar Kuwa data kama zasu dawo bayan sun gama gyara gidan wanka tayi tasa sabuwar Abaya Arsh color tana jiran dawowarsu,Yamma likis sukaa sauka a Nigeria,a airport din Suka yi Sallah sannan Suka. Karaso gida Driver ya dakko su,Hamida tana Jin karar mota ta leka ta window na sama ta hango Nabeel shi ya fara Fitowa sanye da jallabiyya fara,Hamida ta Bude baki ganin yayi wani kiba ya Kara harske da kyau,Bedroom dinta ta koma ta boye a ciki,Sai da su Mimi suka Yi wanka ma tare da hutawa sannan suka zauna a dinning suna cin abincin da su Hamida sukayi me dadin gaske,Nabeel Yana ta zuba Ido Ina zai ganta sai kallon hanyar room dinta yake,sai ga Hamida an fesa kyau an fito,tunda yake bai taba sanin haka take da tsayi da kyau ba sai yau,Durkusawa tayi tana gaida Mimi da Affa suka amsa da fara'a Mimi tace Hamida wannan wanka Haka ko angon ne zai zo? Nan take annurin fuskar Nabeel ya dauke,Murmushi Kawai Hamida tayi tace Ina yini Yaya Kyakyawa da kyar ya amsa ya daure fuska,tace ya jikin da Sauki Kawai yace ya juya yaci gaba da cin abincinsa, bedroom ta koma abinta.

Alhaji Abbas Kuwa Yana komawa Abuja Basma ya rufe da fada kamar zai duketa yace mijinki na can kin San halin da yake ciki ko ki Kira kiyi Masa Sannu mahaukaciyar Ina ce ke dan uwanki mijinki kowa Yana Kiran waya yaji ya me jiki amma banda ke, Maman Basma tace to wallah Alhaji Nan su Anwar Suka ganta da wani Namiji Wai tsohon saurayinta ne ya kaita shopping suna yawon shakatawa da Aurenta gata nan,Alhaji Abbas yace hada kayanki ki koma dakin mijinki yanzu maza kibi flight,ba shiri ta tattara ta taho Kaduna ta tare da tare taxi ta shiga tana shiga taga mutum wani murjejen kato baki wuluk kusa da ita ta firgita sosai sai dai ta fuske tana yiwa driver kwatance yayi parking a kofar gidan Affa,gabanta ne ya yanke ya fadi ganin wuka fyalleliya a hannunsa kafin tayi magana ya soka Mata wukar a kirji ya zare ya sake soka Mata har sau Uku sannan Suka bude mota Suka jefo ta kofar gidan da kayanta gaba Daya.

Tana ta kakari bakinta kafin kace me ya cika da jini ihu tayi da karfi Sale ya jiyo ihun da sauri ya Bude kofa yaga Basma ce ihu ya kurma Yana Kiran mutane ya fada ciki da gudu su Affa,Hamida,Mimi da Nabeel duk Suka taho,Nabeel sai daga baya ya karaso sabo da an hanashi tafiya da sauri sai a hankalin idan ya warke,sabo da baya sa wando ma Sai jallabiya baya fita ko ina,kowa yaga Basma ce ai mata tuni sun rude da kuka Basma ta kalli Nabeel tace wasu ne a taxi ban San su waye ba....ka yafe min nayi ma abubuwa nice..nice..na sawa Hamida kwaya lokacin tana da ciki sabo da Kar...karrrrrrr....ta haifo yaron da rai kuci gaba da alaka,sa...sa..ta fara tari tace nice...nayi hayar Yan daba nasa su yanke maka gabanka sabo da na gane bani kake so ba baka sha'awata shine bana sooooooo.....wata ta samu itama....ka yafee....min...kishi ne yasa,Hamida kuka Nabeel Hawaye ya cika Masa Ido yace na yafe Hamida ma ta yafe,Hamida tana kuka tace a kaita asibiti waye marar Imani zai kasheta bata biyani dana ba,Ni ban yafe ba Dandana ta kashe min kowa yayi mamakin Hamida ba Imani haka,Hamida tace ni wallahi zuciya ce Allah Bai sa min ba amma ni idan nayi fushi bana sauka da wuri,sai da Kika Zo mutuwa Zaki ce a yafe miki Allah fa baya karbar tuban Wanda sai da mutuwa ta riske shi yaga mutuwa karara sannan zai ce zai tuba,sai kin tashi kin biyani dana da fadar dani da kika dinga yi Ina da ciki a kaita asibiti dan Allah karta mutu ta tashi a bi Mana hakkin mu,Kuma Yaya kyakyawa sai ya sakeki ko a lahira baza ki Zama matarsa ba Kar ma kizo Allah ya yafe Miki ki shiga Aljana a sake bashi ke a Aljanna munafuka wallahi walakiri sunfi karfin ki suna Nan taron dangi zasu Miki Matukar Kika je lahira hakkin Lele ma ya isheki.

Hamida ta juya tana Basma kinji kunya yanzu Naja'atun ma Sai a hada da ita a wajen kishi me tayi miki ku kaita asibiti Dan Allah Kar ta mutu sai ta biya mu hakkinmu Yasin bazan yafe ba bazan ji wani tausayinki ba,Affa yarsa ce ba yanda zaiyi haka Suka sunkuci Basma zuwa asibiti Nabeel ba halin ya bisu jinya yake,Hamida ta ganshi ya kurawa motar su Affa Ido tace muje ciki ko binta zaka yi? Kai har abada baza ka
Zama gwarzo ba,Nabeel shi kanshi ji yake bazai iya yafewa Basma ba.

Suna komawa Palo Hamida ta zauna tare da zuba tagumi tace oh ina ganin duniya bala'i,Yaya Mu hada kanmu Kar mu yafe kaji ko ance mun yafe muce bamu yafe ba,Nabeel ya kalleta yace Yar uwata ce fa jinina,ban sanki da Haka ba Hamida yaushe kika Zama marar yafiya? Ni sanda kina Kauye kinfi birgeni kina so na sai abinda nace amma yanzu gaba daya kin canja sai dai ki tafi wajen Dan iskan bakin saurayinki zance Nima kin kasa yafe min kince ke sai me bakar takashi kike so me na Miki dan Allah?
Hamida kwallace ta cika Mata Ido ta mike tare da shigewa dakinta saman bed ta fada ta fashe da kuka sosai bata son Dr Ahmad bata San ya zata yi ba gashi an karbi kudin auren sa.

Basma Kuwa tana can Rai a hannun Allah,ko da Affa ya Kira Yan Uwansa Bai fada musu me Basma tayi ba amma gaba daya da Yamma maza da Mata sun cika asibitin,anyi kokarin ceto ran Basma amma abin yaki sai cewa take a Kira Mata Dady da Mummy,Nan aka basu dama Suka shiga ciki Basma tana kakarin mutuwa ta fadawa iyayenta abinda ta aikata karshe tace dan Allah ku yafe min ku rokar min Nabeel da Hamida kafin a sakani a makwanci su yafe min,Alhaji Abbas da Mummy sai hawaye suke suna cewa baza ki mutu ba Inshaallah,Basma ta fara salatin annabi kafin ma ta Kai karshe rai yayi halinsa,masu kuka da kuka na yi Ana ta sanarwa dangi janaza,ko su waye oho, tunda yamma tayi baza a bari ta kwana ba,Haka aka karbi gawa sukayi gidan Affa gaba Daya dangi suna ta sauka a gidan Affa maza da Mata sai mutananen unguwar.

Sabo da Zaman tare Nabeel sai da yayi kuka amma Yana daki ba yanda za ayi ya iya fita,Yana kuka yace na yafe Miki Basma duniya da lahira,Mimi ce ta iske Hamida a Palo cikin Mata dangi tana ta kuka ita ma tana Allah sarki Basma Allah ka gafarta mata gata da kirki Wanda suke palo suna Allahu Akbar,Hamida tana shesheka tace munyi zaman mutunci Indai ba Ni na tsokaneta ba bata min komai,tsakanina da ita matar nan sai Alkhairi ,Bamu taba sa'insa ba da baiwar Allah nan,Muna zaune lafiya da ita baza ka taba Jin bakinta ba Wai Basma tace wani Abu a kanka Ina Sam badai Basma ba baza kaji ba,baiwar Allah ga hakuri, mace Yar gayu irin Basma,Dangi ana ta ai Basma ba ruwanta mutuniyar kirki ce duk gidansu ba me hankalinta basu San shegantakar data to afka ba,dama haka Mata suke Yi sai an Gama tsiya kala kala da mutum idan ya mutu sai ace ba a taba fada ba,ana yabon mutum,Ihsan ce ta shigo da katon Hijab da carbi,Hamida tace oh Yar uwa munyi Rashi Allah yaji Kan Basma mutuniyar arziki,Ihsan taji inda ake yabon Yar uwarta dama tasan Hamida sai ta fashe da kuka da fada jikin Hamida ta rungumeta,Hamida tana la'ilahaillahu kuyi hakuri Yar uwa munyi Rashi,Ihsan tana kuka tace Ina Yaya Nabeel?

Wallahi shi nafi Jin tausayi wayyo Nabeel shine abin tausayi rasa matar aure ba karamin firgici bane ga Namiji cewar Hamida Yan dakin Suka ce Allah sarki Allah ya bashi ta kirki wacce zata maye Masa gurbi,Hamida Bayan kujera ta zura kanta a hankali tace Inshaallah nice, nice ma dani za ayi in ta kallon Lele me Kyau ga runtumemiyar Naja'at Cass abinmu sai ta fito da kanta tana goge ido,matar Yayan Affa tace Yar Nan ya akayi kikan San Basma haka ne da Alama Kun shaku? Hamida tana goge Ido da Jan majina tace Aiki aka
Showing 36001 words to 39000 words out of 133235 words