ne abin,in kin ganta Zaki so ta kyakyawa ce kamar Hamidan Lele Ni suna min Kama sosai wlh.
Mimi Tace Ina so a kawo min ai taimako ne dama an kwace min Fadila tana can ya na iya,Dariya sukayi Kawai.

Su Anwar da su Ihsan duk sun fitar da matan da zasu aura matan ma sun kawo mazajensu wasu a dangi wasu Kuma a wani wajen Suka samu,shirye shiryen biki akeyi za a tafi Abuja asha bikin yaran Yaya Ubaidu Dana Senator Abbas.
Hamida sai Murna takeyi zasu tafi da Lele dama ba school jiran Exam suke yi,Maza hudu Mata Hudu za a aurar sauran masu tasowa ne sai Nan gaba.

Nabeel ya musu dinkuna na Alfarma,biki Saura sati daya Mimi tuni ta tafi can ita,Affa Kuwa Saura kwana Uku a fara ya tafi can
Su Hamida ana gobe za a fara Event Suka sauka a Abuja ita da Nabeel dinta.

Hamida ta kalli gidan senator Wanda har family din Ubaidu can Suka koma gaba Daya a gidan za ayi shagalin sabo da girmansa, Hamida an dau wanka ansha takalmi me tsini,Nabeel ta gani ya karbi key a hannun wani me aiki a gidan,masu Aiki sun daukar musu Jakar kayansu sunbi bayansu wani part da ba kowa Nabeel ya bude hadadden part yasha gyara sai kamshi da sanyi ke tashi Kawai,yace Pipina a Nan na zauna Sanda Ina gidan Nan,Gashi Allah yayi Zan shiga Nima ta furta,Kasancewar a jirgi Suka Zo ba gajiya Kawai kayan suka ajiye Suka fito zuwa wani part inda manyan suke iyaye kenan har Affa Yana can da matansu a Nan Suka kwashi gaisuwa sannan Suka tafi inda dangi suke suna Shiga katon Palo Hamida taga su Anwar maza da Mata ana ta labarin duniya ana Dariya harda dattijai dangi suna tsokanarsu,Hamida tana shiga suka hau ihu ga Shakira ga Shakiran Lele, Dariya Hamida ta saki ba shiri ta shiga ciki suna ta kallon dan cikinta.

Fatima tace Pipin Lele ashe an hadu da abin Hamida tace wlh Allah ya nufa suka dinga dariya,Lele ne ya shigo Suka Yi tsit ana Masa Sannu da zuwa Suka gaisa yace ana ta surutun shirmen ne,wajen Hamida ya karasa tare da Mata rada zanje wajen wasu friends Dina sai dare Zan dawo,a dawo lfy tace ficewa yayi abinsa mota ya hau,Suka Dora surutunsu ana ta abin dariya Hamida tace bayin Allah Zan zirarawa cikina abinci yanzu Ni bana jurewa a nuna min kitchen,ai Kuwa aka nuna Mata ta Shiga abinci iri iri gashi Nan abinda take so ta eba.

Akwai wani yaro Dan gidan Senator ne Fauzan baya son magana bai wuce 24yrs ba, duk gidansu yafi kowa kyau in ka cire Nabeel Wanda shi na daban ne amma Fauzan ya hadu sai girman Kai duk Family yafi su nuna Isa da mulki Yana Jin kansa,tasu tafi zuwa Daya da Nabeel,Nabeel sai yace ai yafi kowa hankali
Sai bayan an gama biki Suka dawo gida anji Dadi anyi zumunci biki ya kayatar an kashe Naira.

Bayan watanni Hamida cikinta ya tsufa sosai ga maitar Nabeel baya bari ta huta,tana kwance ta ya fara rabata da kayan jikinta wani dadi take karawa Yana ta buga harka Hamida tace marata ciwo take wlh tun safe Kamar Zan haihu,Nabeel bai ma ji ta ba sai da ya gamsu sannan yace ya shiga wata tara ne? Hamida ta fashe da kuka tace nace ma Banda lafiya kaki kulani wayyo Allah cikina ta dawo kasan bed,Nabeel ya rude ko wanka baiyi ba ya saka kayan baccinsa dogon wando da Riga ya sa Mata doguwar rigar Atamfa ya dauketa da tarkacen kayan haihuwarta da tace ta hada cikin Daren 12am ya tafi da ita asibiti ya Kira Mimi ya fada Mata ta taho itama asibitin.

Hamida tana ta faman kuka bata San inda hankalinta yake ba taga asibiti mutane duk gasu Nan ana hada hada tace ku tafi masallaci kuyi Sallah,duk inda aka wuce da ita sai tace su tafi masallaci suyi Sallah labour room aka shiga Hamida kuka takeyi tana zanyi Sallah Zanyi Sallah Kuma kuje kuyi Sallah.

Dama ita bata da juriya a ciwo ta cika asibitin da kuka Lelene ya jawo min Nakuda wlh Dana baiyi niiyar zuwa yau ba Lelene ya jawo shi,Mimi Tace ke ki rufe Mana baki ke baki da Hakurin ciwo,Kowa ya San haihuwa bazan iya ba Lelene mumnafuki bakin kwarto Nishi ta fara masu karbar haihuwa suna kanta, Ni bazan Haihu a gaban surukata ba,Mimi tace ai ke sai gyaran Allah duk haihuwa sai kinyi abin kunya,Hamida tunda wuya tayi wuya magana ma dainawa tayi har sai 1am Allah yasa ta haifo danta Namiji katon gaske me Kama da Nabeel,Mimi sai Murna,sai ga Hamida an dawo normal tun kafin ma a gyarata da kanta tace zatayi wanka,Mimi ruwan zafi taji akwai a toilet din tace,gashi dake private ne sai kamshi ke tashi kawai,Wanka tayi da ruwan zafi ta shirya kanta,Mimi ta bata wata Abaya baka ta shirya kanta ta fito Kamar ba ita ba,sai kunyar Mimi take ji tace Dan Allah Mimi Kiyi Hakuri,Dariya Mimi tayi tace ai ke Kam kinji kunya Hamida haihuwarki ta farko ma Haka Kika Yi Allah yasa ma operation aka Miki waccan.

Dakin hutu aka canja mata sannan Mimi ta hada mata tea me kauri ta sha,Nabeel Wanda yake rungume da dansa ya Gama Masa Addua Mimi Tace ya shigo ya shigo Yana Mata Sannu Hamida Suka balle da hira,Nabeel ne ya kalli bed din da Hamida take kwance ya zaro Ido tare da furta Mimi na Shiga Uku Matata zata mutu king jini ita kanta Hamida ana ta Hira bata San jini ya balle Mata ba Yana ta malala,sai ta fashe da kuka Jini Kamar an balle pampo Nabeel ya rude zai jefar da Baby Mimi ta karbe shi tace sauri ka Kira likita, Nabeel ya fita ya dawo da wasu matan likitoci tace amma an Bata tea ko?mimi tace ae Tace Watarana ba a bawa wacce ta Haihu ruwan zafi ta Sha sabo da idan me zubar da jini ce Yana Jin zafi zai balle Mata dama kadan yake jira.

Nabeel cikin karaji yace dalla malama ki daina Mana surutun Iska ki kula da matata wlh na rasata sai na daure ku,Kun San yanda nake sonta zaku min ganganci,Hamida tuni ta fara kokarin sumewa jininta Kawai malala yake Ummi tana dagata sai bul bul,Nabeel Hannu ya Dora a Kai ya fara kuka.




Saura na dare Inshaallah



AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮

56-60


Official

By
AsmaBaffa



Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM





Page naku ne

Herwwerhy
Ummu Lateepha
Ma'esha
Mrs Sadauki
Mrs Mukhtar
~•
~🥰






Hamida idonta Yana wani juyewa cikin kasalalliyar murya tace a Kira min Papa....kafin ta rufe baki tuni ta sume,Nabeel bai San Haihuwa ba sai yau sai kace mace ya dinga girgiza Hamida Yana kuka Hamida idan ta dan farfado sai tace Nabeel mutuwa zanyi,Lele ya rungumeta Yana kuka wiwi baza ki mutu ba,Hamida baza ki mutu ba anyi anyi ya fita yaki sai da babban likitan yazo yace ayi maza a kawo Wanda za a ebi jininta yanzu zamu bada Aron wani a asibin Nan in an eba Zaki biya mu namu,Mimi tace Dan Allah kuyi sauri yarinya zata mutu Kuna kallo Kamar ba private ba,Nabeel ya Mike ya Bude kofa ya fita fakal fakal ya dawo Yana ta Neman wayarsa alhalin Wayar ma tana hannunsa.

Su Ammar ya Kira da su Sale yace su taho asibiti jini ake so dama sunji labarin tana asibiti,Allah sarki Inuwa da Sale wasu Wanda suke mutunci Suka tattaro a daren Suka je asibitin,cikin gaggawa aka gwada mutum biyar duk lafiya suke Kuma yazo daya dana Hamida aka eba,already dama an Mata Allurori an sa Leda Daya na asibiti, Masu gyara dakin sun gyara shi neat har jikin Hamida Mimi ta cire kayan jikinta an goge Mata jiki tsaf da wives me shegen kamshi da nurses Suka kawo Suka taimaka aka gyarata suka kawo rigar asibiti wata bue doguwa aka saka Mata,Sannan aka ce Nabeel ya shigo lokacin ya daga hannu sama ba ruwansa da mutane Addua yake a fili duk su Sale suna ji.

Yana Allah ka bawa matata lafiya Hamida,Allah Ina sonta ya Allah ka barmu tare har tsufanmu Allah ka bata lafiya da tsawon rai,Yana ta Yi wani abin ma bai San me yake cewa ba,Mimi ta tattara kayan da Suka baci gaba Daya ta kaisu wani katon Rami a asibitin Wanda kullum wuta ci take a ciki a Nan suke kone duk wata najasa ta zuba a Nan sabo da kafin ace sun wanku za a Sha fama.

Nabeel ta samu a ciki ya zuba tagumi ya kafe Hamida da Ido,Har tausayi ya ba Mimi tace kaje gida kayi wanka ka dawo kaga yanzu wajen 3am ma Sai ka dawo da asuba Nabeel yace bazan iya ba wlh,Ina jaririn? Nabeel yace Ni na manta Wanda na mikawa ma shi wlh ohhh Inuwa na bawa sun tafi dashi gida nace a kaiwa Goggo Sara me aikinki sai ta Masa wanka ta gyara shi,Mimi tayi Murmushi tace Ashe akwai sauran dan Hankalin bai gushe ba,a Daren Suka Daura Mata jini Leda na biyu sabo da abin na gaggawa ne, ana Fara sa Leda ta biyu ga Allurai ta Sha sai ga Hamida ta dan motsa tana jujjuya Kai,Nabeel murna ta kamashi yace la'ilahaillahu Yana wani Murmushi Mimi tace kaji kunya dai

Da asuba jini na biyu ya Kare Hamida harda bude Ido wannan Karon tace Ina Lelena yace gani Nan Pipina ya rike hannunta ta damke hannun sosai tace ashe Zan sake ganinka,Murmushi yayi sai ga likita ya shigo yace Alhmdllh Yanzu idan zata ci wani abu a bata sai da anjima kadan Zamu Kara Mata wani,Lele yace Mimi a gida akwai farfesun da tayi ma ko ci bata yi ba,Hamida tace da zan samu nama da madara ta ruwa su zanci tana kwance duk da haka ba kwari a jikinta tunda jinin Bai wadaceta ba,a hankali tace da maltina,Nabeel jiki na rawa rigarsa ma ta bacci duk ta shafi jinin Hamida,Waya ya yiwa Habiba ta hado komai driver ya kawo ta,shi Kuma ya fita yaga inda ake siyar da abubuwa a asibitin Nan yaje ya lodo Mata su fresh milk,Madara peak,maltina,fresh yo,gasu Nan dai,ya dawo da sauri ya kawo,da Kansa ya hada Mata Madara da malt ya dagata Mimi ta Mikasa Masa ya bata tunda ta kafa Kai sai data shanye tas,ta dan kalli Lele idonta na lumshewa tace Naman fa? Yace yanzu za a kawo,ba a dade ba Habiba ta kawo ya zuba a plate ya fara Bata a baki tana ta cinyewa tana Shan Madara sai gata ta dan Kara karfi tace cikin sanyin murya Mimi kinji Ina iya daga hannuna,Sannu ana Kara Miki wasu Zaki iya mikewa ma ai jini haka yake,tace zata Yi fitsari Lele ya kamawa Mimi ta kaita tayi ta,tace Nabeel ya jiramu a dakin ba sai ka shiga toilet ba,Yace Mimi na fa San komai jinin Hamida ai jini nane mene in na gani,kofa Mimi ta kulle bata kulashi ba, wata kujera ta zaunar da ita duk ta wanke Mata jikinta da sabulu me kamshi sabo da ba Dadi ka zauna da me jinya da kazanta babu amfanin jinya,Nabeel karbo min wata rigar a wajen nurse sabuwa a sa Mata

Yaje ya karbo a ledarta Mimi ta shiryata tsaf Suka fito Nabeel ya taimaka Mata Suka kwantar da ita,Hamida a slow tace har na danji Dadi,Masu gyara ta Kira Suka sake gyara ko Ina Yana kamshi har toilet sannan Suka sake sa mata wani jinin,Mimi tayi Alwala tare da sallah,tana idarwa Nabeel yace zaije shima yayi wanka zai dawo Tace kasa habeeba tayi breakfast a kawo sannan ka taho da kayan bukata Dana sawarta yace to ya fita ya shiga motarsa zuciyarsa da sukuni,Yana zuwa gida gari ya fara haske ya fadawa Habiba abinda zata dafa sannan ya haura sama ya gyara bedroom din da Suka bari a hargitse da Kaya,Ya tube kayan jikinsa ya zuba a washing machine ya wanke su Kal ya shanya sannan yayi wanka tare da tsarkake jikinsa yazo yayi Sallah da azkhar Hamidansa ta Sha Addua,Kwanciya yayi ya huta amma bai iya bacci ba,Habiba tana gamawa ya kwashi komai ya koma asibiti Hamida tana ta sheka bacci jini na shigarta,Mimi ta eba abinda zata ci taci tace Nabeel yaci yace Mimi bazan iya ba sai naga abinda hali yayi ya sake Zama.

11am jinin ya Kare tana ta bacci su Ammar da Yan gidansu har sunzo dubiya sun tafi,su Sale sun dawo dubiya,sai da tayi bacci ta koshi sannan ta farka tana Bude Ido taji wani Dadi a jikinta sai gashi ta mike ta zauna da kanta,Nabeel sun shigo da likita sai Murna ya tafi wajen abarsa yace a kaiki fitsari ne?Zan iya zuwa da kaina fa, ta mike a hankali ta sakko Mimi Tace banda ruwa me zafi da yawa,Brush ta karba tayi tayi wanka sosai da sosai ta gasa dausayinta duk a hankali take komai sabo da bata gama dawowa normal ba,shirya kanta tayi ta fito tace an kawo min Kaya? Mimi tace ae a ciki ta Mika Mata doguwar riga Yar kanti marar nauyi me gajeren hannu ta saka ta zauna a bakin gadon ta kalli Lele da ya zuba Mata Ido tace ka Kira min su Karima a fada musu,Nabeel yace na fada musu dazu Ummi tana Hanya ma amma bance musu ga halin da kike ba gudun Kar hankalinsu ya tashi.

Mimi abinci ta zuba Mata taci da yawa sosai dankalin turawa da kwai Tasha tea taci nama ga Madara me kwakwa da malt,Taji karfi sosai tace bani wayarka,Nabeel ya Mika Mata ta Kira Sakina bugu Daya ta daga tace me jego ya jikin naji haihuwa,Tace Alhmdllh ku fitar da Ankon,ba Mimi ba har Nabeel sai da suka kalli Hamida tana fama da kanta a fitar da anko,Nabeel yace ke da ya kamata ki huta wanne bikin suna za ayi Kuma, Inshaallah Zan warke ne kafin lokacin Ina so zanyi,Mimi tace tunda tana so ka barta sai ayi a gidana tunda dama tafiya zanyi da ke,Lele yace ah tab a turo dai tsohuwa,Mimi tace ai dama ba riketa zanyi ba ta zauna da mu har na sati biyu sai ta dawo tare da Goggo ta kula da ita da yaron,to Nabeel yace badan ya so ba.

Sai dare Suka sa Mata na hudu suka ce daga shi an gama ya isheta dama sun gwada sunga kadan ya rage ya koma normal lokacin tuni Ummi ta iso sai lokacin Mimi ta Bata labari,Nabeel Yana wani corridor na hospital din su da wasu mazan Suma an kawo matansu,Nabeel yace Kuna ruwa suna ta dariya,wani yace ai Ni jini aka karawa tawa,Nabeel yace kaima? mutumin yace Naga tashin hankali,Nabeel yace Ni mamakin da nakeyi ka duba wannan Yar kafa ta Mata Yar bular kofa karama amma yanda jini dunkule dunkule yake fadowa,dayan yace Kai wani fa yayi dan botiki tari guda zaka ga ya Fado faf, Wanda Bai bi uwarsa ba ya shiga Uku dole mutum ya Shiga wuta cewar Nabeel,yace na Kara ganin darajar uwata Ni Kam,wannan yaron idan Naga ya batawa momynsa rai sai na karya shi Nabeel ya furta,suna ta dariya dayan yace Ina jaririn naka? Nabeel yace Yana can gida wajen me aiki ko ya suke ciki oho shi ya sani akan na rasa matata gwara shi ya koma dama ban Saba da shi ba.

Mimice tasa aka kawo jariri ance Yana ta kuka nono yake so duk da Haka an bashi madara,an Masa wanka yasha fararen Kaya sai kamshi yake kyakyawa da shi,Mimi ta mikawa Hamida tashi ki daure a bashi nono mu gani dama nonuwan sun cika sunyi bake bake har zafi suke Mata,Hamida tace a tambayi Lele na bashi? Ummi tace wacce irin Yar iskar yarinya ce kene Wai nononma sai an tambayi miji Ummi ta mike da kanta ta zuge zip din riga,Hamida ta saka hijab sannan ta shigar da yaron ciki Wai Kar a kalli nononta,Boyo ya Kare yarinya Ummi ta cire hijab din tace ki bashi Muna gani in da gyara a gyara miki,Duk da Haka Saida ta sa mayafi ta Kare sannan tayi Bismillah ta fara bashi Yana zuka ta fara mutsu mutsu da kafafu Wai zafi.

Ido ta rufe tare da daga Kai sama tana Jin azaba,Lele ne ya shigo room din ya sake sabon wankan shadda Fara Yana kamshi ya kalli Pipinsa yace zafi Wai? Kuka ta saki Kawai tana ba yaron tana hawaye Wai zafi,Lele yace to ba sai a bashi madara ba a huta,Mimi tace Naga uban da zai bashi madara kowa a haka ya koya in zata daure ta daure ai ganinka ne ya Sata sakin kukan shagwabar.

Nabeel zai zauna Yana Sannu zai daina,Mimi Tace fita wlh ko naci ubanka a dakin Nan yanzu zaka Zo ka damemu da fitsara,to ai yaron nake jira ta gama bashi na daukeshi,ba inda zaka da shi tashi ka fita,ba a sonsa ba ya fita.
Washe gari kwana biyu Hamida tayi waras sai dan abinda ba a rasa ba a ranar aka sallamesu Suka koma gidan Mimi gaba Daya,Yan Uwa da abokan arziki ana ta tururuwar zuwa Ummi ta tafi su Karima da Asiya suna nan,suna saman bed har me jego ana zuba Hira yaro ya ishesu da kuka an rasa dalili,Nabeel ne yazo gidan tare da Shiga dakin yaro Yana ta kuka an rasa ya za ayi da shi yace ko zafi yake ji naji Kamar zazzabi a jikinsa,Daukansa Hamida tayi ta mike tsaye tana jijjigashi yaki Shuru,Nabeel ya dauki dankwalin Hamida ya fara Masa fifiti sai yayi shuru idan aka tsaya ya saki kuka,yace ga ac nayi fa,da Alama
Showing 75001 words to 78000 words out of 133235 words