dakko Ni daga Kauye a can gidanta na zauna da Affa yaga Ina da hankali shine ya 'yanta Ni na koma 'yarsa na dawo gidansa da Zama Ina karatu na,Ta kusa basu Dariya Wai aka 'yantata sai kace zamanin da ake bayi.
Mimi ce ta Kira Hamida bedroom,tana zuwa tace zauna Mana,a kasa ta zauna da labadi,Mimi tace ki yafewa Basma dan Allah,Hamida tace haba Mimi sai kace nice kanwar fir'auna ai wallahi tun kafin a tafi da ita asibiti na yafe Mata komai Allah ya yafe Mana,Ni me tayi min ma Yar hantara ce da dan tsawa wannan ai ba wani Abu bane na yafe har ga Allah,Mimi tace Alhmdllh yanzu jeki dakin Lele ki kula da shi lallai yasha magani kinji,Hamida tayi dan damm sabo da gaba Daya yanzu tsoron kebewa take da namiji amma haka tace to bari naje,ki bashi abinci in yaci yasha magani,to Hamida ta sake cewa tace amma da kunya na ebo abinci a gaban mutane na wuce,akwai kitchen a sashensa kin manta ba abinda babu ki dafa Masa a can,Hamida ta sake cewa Mimi kukan mutuwar fa Kar a karasa Dani? Mimi tace Naga dai ranar da zaki hankali au dama duk uban kukan Nan da kike ba na Allah bane? Mimi ni fa Indai Kika ga nayi kuka to Allah akan yaya Nabeel ne ko wani abu da ya dameni a Rai na,amma zuciyata a bushe take ni kafin kiga abinda zai sani kuka sai ko In Lelenki ne.
Sabo da ban taso da iyaye na ba ban sansu ba ma Ni ko kalarsu ban taba gani ba ko yayeni ance ba ayi ba iyayena Suka rasu,Mimi sai taji tausayinta tace sorry dole ki Shiga wani hali ki hada Masa ruwan dumi Wanda zai iya Zama a ciki kin San maganin da ake zubawa ai a ciki sai ya shiga ya zauna a ciki Hamida tace irin na me Jego? Mimi tace ae,tace to ficewa tayi ta nufi sashen Nabeel.
Nabeel yayi zuru Yana tunani yaga Hamida ta shigo,sai data ga Lele Yana cikin damuwa sannan zuciyarta ta karye tayi kukan gaskiya da gaskiya ita aduniya in ana so aga Hamida a wani Hali to ace Lele ne ya samu matsala,a kasan bed din ta durkusa tana goge hawayenta ta kalli Nabeel tace Leluwan Kamshi...Nabeel ya harareta yace tunda bakya so na ki fitar min a room,Hamida tace mutuwa akayi Babba Addua zamuyi Mata,kin yafe Mata ne? Kai ta daga masa kawai,tace kasha maganin naka? Kai ya girgiza mata,Yana kallon Hamida sai yaji damuwarsa ta yaye wani farin ciki Yake tsintar Kansa in tana kusa da shi,sai da ta juya zata shiga kitchen tace Yaya Danyen jegon da Sauki? tana fada ta Shige kitchen bata jira amsarsa ba,tana Jin muryarsa yace a'a ai ba tambaya zakiyi ba kice a bude Miki ki gani,Hamida daga kitchen tace Kai Lele ko kunya.
Hada Basma akayi tsaf aka kaita makwancinta gaba daya gidan Affa ba masaka tsinke,ba Wanda yasan me Basma tayi ko a dangi sai iya iyaye ne Suka sani Suka rufe zance tunda an yafe,sai dare Hamida ta gama Masa girkin tuwon danyar shinkafa tayi miyar danyar kubewa ta Sha kifi, ta hadawa Nabeel ruwan maganin a toilet tana ta zirga zirga Yana binta da Ido ta fito tace na hada ruwan zafin me jego,kallonta yayi ya murmusa Kawai ya wuce toilet,ganin Ana ta cin abinci a gidan ta zuba tuwon a flask ta kawowa Mimi har dakinta ta iske Yan Uwan Mimi Mata makil a dakin ta gaishe su sannan ta Kira Mimi gefe ta bata harda rada Mata tuwo nayi karki bari a cinye Miki suje suci shinkafa ta kullum kullum,Mimi tace to Kai dakin Affa,Hamida ta kai dakin Affa ba kowa duk suna kofar gida a Nan ta ajiye ta koma dakin Nabeel taga har ya shirya cikin brown jallabiyya ya dauki gajeren wando zai saka Wai sai yaje wajen zaman makoki , Hamida tasan a dokokin likita Banda sa wando,tace karka sa wallahi baza ka bi doka ba dan Allah karka sa,tsayawa yayi Yana kallonta ta Masa kyau bai ma San kyanta ya Kai haka ba,yace sai na sa tunda Ahmad kike so bata da amfani a wajena,Hamida cikin dakewa tace please Yaya karka karya doka ka Mata Addua a daki Dan Allah ba sai kaje ba,nasan zuwa zaka Yi,duk duniya ko Mimi bata gane abinda ke damunsa sai Hamida tun kafin ta fara hankali ko kallo ya Mata tasan me yake nufi Yana tunani ta kwace wandon ta maida ma'ajiya tace Jego fa kake zata Yi waje ta tsinci muryarsa yace abincin fa, dawowa tayi ta fara serving dinsa yace harda yin wani tuwo? Me jego ai sai da tuwo ta furta ba tare da ta kalle shi ba muryarsa taji yace dan Allah karki auri Ahmad,mikewa tayi ta fice abinta ya bita da kallo Kawai.
Tana fita wanka taje tayi ta canja kaya tayi Sallar Isha sannan ta take cikinta da shinkafa da Miya harda salat ta sake sabon hijab ta fito cikin Yan makoki a palo,tayi jugum tana jan carbi, ana ta fadar halayen Basma na kirki Hamida tana cikin su Ihsan ka rantse dama a gidansu ta taso,Fatima kanwar Basma ce ta Dora hannunta a cinyar Hamida tace naji su Daddy suna cewa idan mutuwa ta lafa ranar arba'in din Basma za a daurawa Nabeel aure da Ihsan ko Ni wai,Hamida bata San Sanda tace Innalillahi wa inna ilayhirrajun ba,Mene ne Yar uwa? Hamida ta wayance tace Basma ce ke Fado min sai naji gabana ya yanke ya fadi,wata tsohuwa dake kusa da su tace Yar Nan haka mutuwa take mutum Yana Fado ma zaka ji gabanka ya Fadi sai hakuri duk mu na hakane kowa jiranta yakeyi,Hamida kuka ya kwace Mata za a aure Mata Lelenta kuka na sosai takeyi ana ta bata Hakuri ana yar Nan haka mutuwa take sai hakuri,Hamida Sam bata mutuwa take ba ta Lele takeyi tashi tayi ta koma bedroom dinta,Yan Uwan Basma dattijai Suka ce wannan Yarinya ta shaku da wannan baiwar Allah.
Hamida saman bed dinta ta fada tana kuka sai ga Kiran Doctor Ahmad tsaki taja sannan ta daga yace ya Hakuri? Tace Alhmdllh,Allah yasa ba Murna kike ba ta mutu ta bar Miki mijinta,Takaici ya Kama Hamida dama kadan take jira tace na fasa aurenka kai zo ka karbi kudin aurenka wallahi bazan aureka ba ko sama da kasa zata hade ka turo a karbar ma kudinka,Hakuri ya fara bawa Hamida tace bazan hakura ba na gaji da zarginka kazo ka karbi kudinka wallahi ko na rotse ma kai banza Jaki,Dr yana gadara shi llikita ne yace da ilimi na da wayewata da kudina babu Yar da zata zageni na aureta ko wacece wallahi na barki har abada Ni da Zan rufa Miki asiri fa zaki zageni, gobe zanzo da kaina na karbi kudina,Hamida waya takashe tace maza zo ka karba dan me bakar takashi na huta da Kaya.
Washe gari Ahmad ba mutunci ba kunya ana zaman makoki Affa ya zaci gaisuwa ma yazo amma ba Wanda ya gaisar Yana zuwa yace kudin aure na za a bani dana kawo na fasa yarinya bata da tarbiyya Wanda ya Mata cikin shege yaje ya aureta,su Papa da Sulaiman sunzo suna wajen,Ummi tana ciki wajen Mimi,Affa ya mike tare da rike hannun Ahmad yace muje gefe Ahmad ya fisge hannunsa ya fatalar da hannun Affa gefe yace dalla sakeni cikin dubban mutane yace kaje ka aurawa danka Wanda ya Mata cikin shege ta Haihu a bani kudina na fasa,mutane aka fara gunaguni,Alhaji Ubaid yayan Affa shi ya mike tare da kwashe Ahmad da mahaukacin mari Ahmad ya daga hannu zai rama Sulaiman ya tashi ya Masa wani mugun naushi a Fuska Nan take jini ta hanci ta bakin Ahmad,Su Anwar yayan Kanin Affa Dana yayan Affa Suka Mike zaratan maza sunkai su goma Suka yiwa Ahmad laga laga sai da kyar aka kwace shi,Muhseen shi ya zaro kudi masu yawa yace Nawa ne kudin Affa? Affa yace dubu hamsim ne,Muhseen yace kacal wannan ai kudin Yar budurwar akuya ce,Nan ya irgo kudi ya sawa Ahmad a Aljihu tare da tankada shi gaba gaba Daya family din tsabar hadin Kai Shuru sukayi Suka fuske Suka nuna Basu San ma zancen ba aka ci gaba da zaman makoki.
A Haka sai da labari ya Isa wajen matan cikin gida Mata Basu San Kan zancen ba Suka dinga tsinewa Ahmad,Nabeel zai je dakin Affa kenan ya tsinci zance Nan take farin ciki da murna Suka cika Masa zuciya Kamar ba matarsa ce ta mutu ba,Wanda Suka ganshi ranar cewa sukayi yaron Nan da tawakali yake,yaro yayi tawakali.
Anwar duk kwanakin da suke a hannun Hamida suke karbar Abinci duk sun santa ba Wanda bai santa ba,dama Anwar shi ya Santa yayi mamakin ganin wayewarta da hankalinta sai yaji kaunarta tana shigarsa shi Kam ya samu matar aure,Kowa in ya shigo sai dai kaji ana Ina Hamida bata Zama sai hidimar dangi takeyi dama gata ba kuya ai ta sata girke girke tayi suna ta Zama wata star Mata da maza Hamida Kawai,Muhseen ne shima fa yaji kaunar Hamida tana Neman kamashi birge shi take ga abin dariya,Ihsan ya Nemo yace Ina Hamida kice ta dafa min Indomie da kwai,Ihsan tace to ta Fara Neman Hamida,Yayinda Hamida ke dakin Nabeel tana hada Masa tea,Ihsan dakin tayi knocking, Nabeel yace come in, ta shiga tace Sannu Yaya Nabeel tace Hamida kizo inji Muhseen ki dafa Masa indomie,mugun tsoron Nabeel suke sabo da baya Wasa da kowa baya sabgar kowa,muryarsa taji yace get out baza ta dafa ba kowa Hamida, a girki zata Kare da aiki ku dama baku iya samun waje ba,Ihsan ta fice ba shiri,Hamida ta Mike zata fita yace wallahi kina fita zaki ga true color dina koma ki zauna yau ba inda Zaki,shike Nan kowa ya saki aiki ga masu aiki Nan,Shuru Hamida tayi ta dauki tea din ta Mika Masa ta koma gefe ta kwanta a kasan tiles,mikewa yayi ya koma saman resting chair yace hau bed din ki kwanta Kuma kiyi bacci,Fuska ta kwabe yace ba abinda Zan Miki Ni kin San Banda lafiya,tunawa tayi sai ta haura saman bed din ta kwanta ba Bata lokaci bacci ya kwashe ta,Shi Kuwa Yana gama Shan tea din ya fice tare da sa key ta waje ya kulleta gam ya koma dakin Affa ya kwanta a saman bed.
Ba Wanda bai nemi Hamida ba an rasa Ina take,dare har la'ar tayi Sallah Kawai tayi ta koma baccinta sai magrib ta tashi ta nufi kofa tare da murda handle taji gam gam,komawa tayi ciki tayi Alwala tare da yin Sallar magriba har Isha tayi ta mike tayi lokacin Anwar Yana so ya ganta su danyi Hira ya samu ya yada Manufa amma Nabeel ya boyeta, Muhseen ma ya nemeta Shuru ba a ganta ba har sai da sukayi bacci 11pm sannan Nabeel yasa key tare da Bude dakinsa tana gani ya bude tayi sauri zata fita ya riko hannunta ta fisge tare da karawa gaba.
Washe gari sadakar Uku Allah yasa duk mutane sun watse sai iya dangi, matasa su Anwar suna zaune Kawai
Sai ga Ahmad tare da kannensa su biyar matasa sun tsaya akan mutane yace zuwa nayi a bani dukkan kayan sawar da na siya Mata,Hamida sai ranar taji me ya faru tsaf ,wata ce ta shigo tace gashi can mutumin jiya ya dawo za ayi fada again, kofar gidan Hamida ta fito ta kalli Dr Ahmad,
Mata sun fita suna ta kallo,Ahmad Yana ganin Hamida yace yawwa rigar ma dake jikinki tawa ce a hado min kayan Dana siya Miki akwai dubu biyar biyar dana baki sau hudu,Banda su ice cream da snacks duk Ina son kudina,Hamida ganin ba wasu mutane duk su Affa basa wajen ma Sai yaransu,tace zakkar Soyayya ka fitar nayi tunanin ma cikon kudin ka kawo min ai baka gama biyana ba Nike binka bashi ma,ba Kaine a zuciyata ba in ba kirana kayi ba ko tunawa da Kai banayi,kudi da Kaya Kuma Allah ne ya rubuta Kaine zaka siya min Kuma ka bani kudi Nasha Alawa,kudinka Alawa ma Nasha da su kaga basu da Albarka ya zaka Yi Allah ya rubuta.
Ahmad yace tonon asiri ai ya Kare Miki ke da kikai cikin shege,Hamida tace danayi cikin ubanka ne ya min ta daga hannu biyu ta zageshi tace sharri zaka min sabo da zaka fasa aure kace nayi ciki Kuma tunda ka min kazafi sai na dakko ma Yan Sanda sai munyi Sharia da kai kayi min kazafin ciki, Hamida a ranta tace yo ko banza ai na kafa tarihi a dangina nice na Fara cikin shege Kuma banji kunya ba,? ke malama a hado min kayana,Hamida ta girgiza kai tace bani da lokacin ka dan tukunyar babarka kullum ka dakko bakar Fuska kazo duk a banza Zan fito.
mu a jikin maza Allah ke fitar Mana da arzikinmu Kuma Allah ya baka har da kaso na a jikinka dole ka bani sabo ba yanda za kayi rabona na ci hakkina nane Allah ya baka ajiya,shawarmar ma na zaci wani dan faten yakuwa ne haka,da nasan ba fate bane Zan bika ba ai ni na zaci faten yakuwa ne, ficika baza a baka ba iya kudin aure ne an baka Kuma kayanka wallah akan na baka gwara na yayyafa musu fetir na kone su.
wannan har wani kudi ka kashe,ni Murmushi million Nawa nayi har ce min kake na iya murmushi idan nayi sai kace Murmushi na Kai kosar da Kai yake kaji ba sai kaci abinci ba karka dauka ban San karya kake ba kana tafiya zaka narki abinci.
Lele da ace ya warke da tuni ba sai buzunka ba,Kuma wallahi kana magana Zan sa ko wacce mace a gidan makokin Nan sai ta lakace ma tabilallen hancinka,Su Anwar suna ta dariya Hamida tayi Masa tas Kuma yayi shuru,kannensa matasan samari sunga Yan hutu masu kudi Shuru sukayi,Ahmad yace kuyi Mata dukan kudina suka ce mudai Yaya ba ruwanmu wallahi baza ka ja Mana ba daga Haka sukayi tafiyarsu,Muhseen ne ya mike ganin haka Ahmad ya fada motarsa yace akwai magana a gaba sai na hanaki zaman lafiya a duniya ai Zan ganki a hanya Watarana,Nabeel ne ya fito sanye da jallabiyarsa dark blue,ya kalli Ahmad yace Indai haka kace to ka tanadi likkafaninka,Muhseen kafin kyafta ido ya sace Masa tayar mota da wani karfe,Anwar da Zain Suka fisgo Ahmad daga mota sai ya Shiga basu Hakuri,Muhseen dama dan kwaya ne Kamar Allah ya aikoshi haka ya dinga jibgar Ahmad sai guduwa yayi a million ya Sha kwana Ya bar motar a Nan.
Anwar yace wannan anyi jahili marar mutunci sai kace jahilin Kauye,Nabeel yace Wai doctor ne,please karku sake wani ambatar doctor jahili dai cewar Anwar.
Nabeel ne ya nufi cikin dangi zai zauna a saman carpet din da suke,Hamida tasan ba short a ciki sabo da lalurar, tace Yaya Nabeel matsowa yayi da kunnensa saitin bakinta yace fadi a hankali ta rada masa Banda wawan Zama mutane na sintiri a layin Nan ato,Murmushi yayi yace tafi gida kinzo kinwa your love masifa Ahmad dinki, gida tayi tafiyarta,Anwar ya kalli Muhseen yace kai gaskiya sauri zanyi na fadawa Yarinyar Nan Ina sonta,Muhseen takaicin Anwar ya kamashi yace ku duk bakuwa idan kuka ganta sai kunce Kuna so to ance an Mata miji,Anwar yace ko kaima kana ciki ne? Zain yace gaskiya beb din ta hadu Kan bala'i komai Excellent gata social ba ruwanta da wani Jin kai,Anwar yace Ina kaunar hancinta da kalar lips dinta wow,gata doguwa skin dinta me Jan hankali tana da Fara fara amma me dan duhu duhu haka,Anwar yace sai kaga gashinta ma,Nabeel hade rai yayi Kamar yau ance Mimi ta mutu tunda yazo wajen yaki magana hirar duniya Bai ce musu kala ba karshe ma tashi yayi ya koma cikin gida.
Bayan an sallami baki Saura iya family din su Affa Yan Mata da maza da dare sun cika palon damkam wasu a kasa wasu a saman kujera suna ta hira Hamida tana ciki amma bata sa musu baki a hirarsu sai dai duk Wanda yayi magana ta kalleshi,Nabeel Yana dining shi kadai Yana cin abinci,Mimi da Affa suna bedroom.
Sale ne yayi sallama tare da neman izini ya shigo palon daga kofa yace ance ana sallama da Shakira,Kallon kallo aka fara wace Shakira Kuma a dangi ba wacce ta mike sai aka ga Hamida ta mike tace Uncle Sale kace Ina zuwa aka kwashe da dariya gaba daya palon har Nabeel ya dara yaushe ta koma Shakira basu da labari.
Ita kanta Hamida sai data ji kunya,Anwar yace Shakira a Ina aka samo sunan? Hamida tace Nick name nayi sab...kafin ta rufe baki Nabeel yace sunan arniya ce fa mawakiya,Hamida tace ni Ina son abina Malam Shehu ne yace idan na waigo Zan kalle shi sai yaga kamar Shakira,su Ihsan dariya harda jefar da waya,Wanda yake kiranki fa? Nabeel ya tambaya tace me voters card ne Wanda Affa yace naje nayi tana da amfani shine yazo kawo min,tana fada ta fice ta tafi karbowa Yana kofar gida a Kan lifan
Suna gaisawa ya bata voters card ta dawo gida,tana shigowa Nabeel yace mu gani,Mika Masa tayi yaga ansa Shakira Kabir Tahir,Kai ya dafe yace Hamida Oh my God yanzu dan kanki ya kwance Shakira Kika je Kika sa? Kowa ya fara dariya,Yace dole sai an canja wata,Hamida tace Ni Allah bana so ni na canja suna na tashi daga Hamida ta furta da shagwaba,Nabeel a
Showing 39001 words to 42000 words out of 133235 words

Sharhi pls
AsmaBaffa
[6/28, 1:47 PM] Sis Asma: 🔮🔮WARE BAIKO🔮🔮
10-15
Official
By
AsmaBaffa
Ware Baiko Sadaukarwa ne ga
AIDA MAMAN TASNIM
Page naku ne Yan kirki
Safiyya Nabebe
Ummulkhair
Maman Alamin
Habeebah Heebat
Maryam T Baliya
Maryam

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14 Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45