itama ta fara tsanata sanadin hakan ta gudu da cikina kuma ba gidansu ta koma ba sai taje wani gurin daban domin na aika nemanta a gidansu aka ce bata zo ba, daga lokacin ban sake sakata a ido ba, sanadin hakan nayi aure na auri Mardiya yanzu kuma ga wannan amaryar da na yi, kuma ta inda na tabbatar da wannan itace tana da ƙanwa Maryam wacce ta yi magana da ita a yanzu”

Zayyan yayi shiru yana nazari, tabbas ɗan'uwansa bazarawa ya aura kuma ƴar sokoto idan be manta ba kamar Mai Martaba ya taɓa faɗa masa ƴar tsohon soja ce bayan haka kuma sunanta Namra.

“Amman kai baka sake ta ba?”

Abokinshi ya tambaya.

“Idan na saketa mi zai sa na zo yanzu na ce matatace”

“Lallai akwai jan aiki, ta yaudari Abdallah kenan”

Zayyan ya faɗa yana zuba hannayensa a aljihu.

“Ka min wani lamani mana Asim, ka haƙura har a gama walimar nan sai na samu Mai Martaba na faɗa masa”

“Na aminta”

Ya faɗa zuciyarsa na mugun bugawa. Daga Zayyan ɗin har Friends ɗinsa ruɗani suka shiga da tunanin yadda haka zai faru da kuma halin da ko wannensu zai shiga idan ya samu labarin abunda Asim yace.

Ko da suka koma ciki wani malami ne yake wa'azi akan haƙoƙin mace akan mijinta. Zaunawa suka yi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, ta ɓangaren Asim kuma yana jin zai yi ganganci idan har ya kuskura cewa Namra matarsa ce tun da yasan har ga Allah ya sake ta, sai dai what yasan tana da cikinsa ta bar gidan, and yana ganin kamar wayo ne Zayyan zai masa a zasu iya taushe maganar idan babu wanda ya sani amman idan aka ji dole a tsaya a bincike.
Wani irin abu ne ya fisgi zuciyarsa sai kawai ya miƙe tsaye ya ɗaga kujera da yake zaune ya jefar dan kawai hankalin kowa ya dawo gurinsa. A take kowa ya juyo yana kallonsa kasancewar yana can baya ne, sojoji kuma suka yo kansa da gudu, sai ya kware baki yana ihun.

“Wannan matar ta yi aure kan aure ne, matatace Namra matatace”

Ba kowa ba ne yake jin abunda yake faɗa sai waɗanda ke kusa da shi, sai dai kowa zai iya fahimtar faɗa ne yake, kamin sojaji su buga masa bindiga a ƙwari (knees) ya faɗi a gurin sai wani ya aika masa wani mugun shuri a ciki kamin su miƙar da shi tsaye su banƙareshi su fita da shi, babu wanda yace uffan har Zayyan da yake abokinsa.
Bayan an fita da Asim, Zayyan ya miƙe tsaye ya ƙarasa gaban Mai Martaba ya kai bakinsa dai-dai kunnensa yayi masa raɗa.


NAMRA POV.

Kaganin komai take kamar a mafarki, a kujerar da take zaune kawai a abar kallo ce, yau itace ake yi ma walimar aure da ɗan sarki, kuma sarkin yana zaune yana kallonsu. Wasu hawaye ta ji sun zubo mata masu sanyi, kamin hankalinta da dubanta ya karkata kan hayaniyar da take hangowa.

Wani irin mugun faɗuwa gabanta yayi, tasan yana nesa da ita amman idonta ba zai mata gizo ba, tabbas Asim take hangowa, sai dai bata iya jin abunda yake faɗa.

‘Miya kawo shi a nan?’

Itace tambayar da ta fara zuwa mata a zuciya. Sai kawai ta ji hannun Abdool cikin nata yana ƙoƙarin luma yatsunsa cikin nata, matse mata hannu yayi gam kamar za a ƙwace masa ita, be wayancin Asim sosai ba kasancewar gani ɗaya yayi masa lokacin da zai bata kyautar gida, gashi kuma yana nesa da su balle ya iya tantancewa, sam be kawo zuciyarsa Asim zai so gurin ba, a tunaninsa wani ɗan shaye-shaye ne a cikin ƴaƴan manya maybe wani abokinsa ko ƴan'uwansa suka gayyato shi.

Hawayen da ya tsinkaya a idon Namra ne yasa shi zira hannunshi ya kama nata, domin idan akwai abunda ya tsana a duniya a yanzu zubar hawayenta ne.

A tsanake aka yi komai cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka gabatar da walimar kowa sai yabawa yake, babu ƙaryar kuɗi kuma komawa ya samu takeaway, abinci kuma sai wanda ranka ke so zaka je ka ɗiba.

Nasiha mai ratsa jiki da kunnuwa Mai martaba yayi ma duka ma'aurantan guda biyu, sannan kuma yayi jawabin godiya. Bayan anci an sha sai wani babban malami ya miƙe tsaye yayi addu'a akan ma'auratan da kuma Mai Martaba gaba ɗaya.

Sai a lokacin da za a tashi sannan Abdool ya sake hannun Namra suka miƙe tsaye a tare ana musu busa da kirari a lokaci ɗaya.
A tare suke aje ƙafa, su ɗauka a lokaci ɗaya har suka kai bakin ƙofar faɗar. Anan sojojin da aka jera a gurin suka fara tasu busar suna sare masa barori na watsar jar fulawa wasu kuma na fesa turare. Mai Video Camera na gaba yana ɗauka, ɗayan kuma yana a baya yana nashi ɗaukar, masu ɗaukar hoto kuma suna aikinsu.
Bayan Ango da Amarya sun wuce ƙannen Abdool mata suka jera ɓangaren dama kowa da sari ja, mazan kuma suna ɓangaren hagu da farar shadda, haka suka jero suka biyo hanya gwanin ban sha'awa suna wucewa. Mai Martaba ne na uku bayan sun wuce, masu busar suka biyo shi suna masa busa dogarai na tare shi dama da hagu har ya wuce.

A harabar Masarautar suka tsaya suna hoto tare da ƴan'uwa, Mai Martaba kuma suka isoshi faɗarshi aka ɗauke su hoto.
Ɗakin Hajiya Shafa aka Mayardar da Namra, yayinda Abdool kuma ya nufi ɓangarensa da ke cikin gidan.

A lokacin ne Meesha ta cirewa Namra Alkyabar da ke jikinta ta miƙa mata abinci domin ita da Abdool basu ci abinci ba a gurin walimar.

“Bana jin yunwa”

Hankalinta gaba ɗaya yana gurin Asim, ta kasa gano dalilin daya kawo shi gurin.

“Dan Allah je ki kira min Maryam”

Amal ta aje wayar da ke hannunta ta miƙe tsaye da sauri.

“Adda Namra bari na kira ta”

Meesha ta taɓe baki.

“Ƴan ƙwaran suna nan kenan”

Bata ɗauki lokaci ba sai gata ta dawo tare da Maryam ɗin. A nan Meesha ta miƙe tsaye ta kama hannun Amal suka fice saboda ta san komai yana buƙatar sirri.

“Anty Namra ga ni”

“Maryam kin ga wanda ya tada rigima ɗazu?”

“Eh amman ban ga ko waye ba”

“Asim ne fa”

“Asim?”

Ya amsa da ƙarfi.

“Miya kawo shi a nan? Ko ganin ƙwan ya zo zuciyarsa ta kasa ɗauka shi ne ya tada rigima, yaso ya ɓata bikin ne Allah be bashi dama ba”

“Tsoro nake ji Maryam idan ba wani abun ya zo yi ba, idan ba haka ba to me zai kawo shi nan?”

“Ya zo yaga abunda za a yi ne, babu wani abunda zai yi rigima ce kuma ya samu dai-dai shi”

Maryam bata gama rufe baki ba wata mai kama da Abdool ta shigo ɗakin cike da ladabi ta ce

“Adda Namra Mai martaba na son ganinki yanzu”

Gabanta ne ya yankeya faɗi, cikin rawar muryar tace

“Maryam ɗauko min mayafina”

Maryan taƙe tsaye ta ɗauko mata farin mayafin da dake saman gado ba tare da ta kawo ma kanta komai ba.
Sai da ta yafa mayafin sannan ta miƙe tsaye yarinyar ta kama hannunta suka fice.

Ɓangaren Mai Martaba Yarinyar ta nufa wato turakarsa, wani ɗan ƙaramin falon Mai Martaba yarinya ta kaita, cike da ladabi Namra ta shiga kanta a ƙasa, sai dai hakan be hanata ango Abdool dake gaban Mai Martaba kamar mai neman gafara ba.
Ita ƙasa ta zauna, sai Yarinyar ta juya ta fice tare da rufo ƙofar.

Sun daɗe a haka, baka jin sautin komai a ɗakin sai sanyin ac dake tsara jikinsu. Zuwa can Mai Martaba ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman ɗaya ya soma magana a tsanake.

“Namra kin san Asim?”

“Allah ya taimaki mai martaba, tsohon mijina ne”

“Taya zamu iya tabbatar da ya sake ki?”

“Ya sake ni a shakarar da ta gabata, kuma iyayena sun san da hakan”

“Akwai takardar saki a hannunki?”

“Be bani ba, da baki yayi furucin Mai Martaba, Allah shine shaidata”

“Mutumen da ya ɗauki hankalin mitane a ɗazun tsohon mijinki ne, kuma yana da'awar be sake ki ba har ma akwai akwai ɗa a tsakanin ku...”

Da sauri Namra ta ɗago kai ta kalli Mai martaba for the first time, idonta har ya kawo ƙwalla, kai ta girgiza.

“Ƙarya yake yi Mai Martaba, Wallahi ya sake ni”

Sai hawaye suka fara mata zuba. Kan Abdool na ƙasa saboda Mai Martaba be bashi damar magana ba.

“Babana!”

Mai Martaba ya kira sunanshi. Sai.ya ɗago da idonshi da suka rine suka canja kala saboda ɓacin rai ya ce

“Wallahi ya sake ta Mai Martaba”

“Kana da takardar sakin ne?”

“A'a amman nasan ba zata min ƙarya ba, kuma na san babban mutum kamar Manjo ba zai yarda ƴarsa ta yi aure kan aure ba”

Mai Martaba ya ɗauki wayarsa ya kira wata number.

“A shigo da shi”

Yana faɗar hakan ya sauke wayar. Ko minti uku ba a ƙara ba, sai ga Asim an shigo da shi yana tsingilta, gaba ɗaya kammaninsa sauya jini sai zuba yake a kansa.
Dogarawa suka durƙusar da shi gaban Mai Martaba.

“Me aka masa haka?”

“Allah ya taimake ka dukan da sojoji suka masa ɗazun ne”

Kai kawai ya ɗaga musu suka juya suka fice. Mai Martaba ya kalli Asim da kyau ya ce.

“Wannan ita ce matarka?”

Sai kawai ya fashe da kuka ya girgiza kai.

“A'a ba ita bace ƙarya na ke”

“Karka ji tsoro kar dukan da aka maka ya tsoratar da kai, na maka alƙawari babu wanda zai sake sa maka hannu, faɗa min gaskiya wannan itace matarka?”

Mai Martaba ya faɗa a natse. Da idonsa ɗaya ya kalli Namra saboda ɗayan ya kumbure, sai kuma ya maida dubansa gurin Abdool, sai a yanzu ya iya tantance Abdool.saboda ɗazun be san ko waye ba.

“Itace ranka ya daɗe. Namra ina ɗa na? Da cikina ta gudu, kuma sanadin wannan mutumen ta gudu, saboda yana tare da ita har yayi mata kyautar gida sanadin hakan na daketa sai ta gudu ta bar gidan, gidan yana nan a unguwar nasarawa”

Kai kawai Namra take girgizawa hawaye na mata zuba. Abdool kuma zuciyarsa ta yi mugun kawowa sai dai babu yadda zai yi tun da a gaban Mai Martaba suke, kuma duk wani unƙuri da zai yi zai ƙara ɗaure kansa ne kawai. Can ciki ya jiyo muryar Mai Martaba na jefo masa tambaya.

“Ka taɓa mata kyautar gida kuma tana da aure?”

Sai da ya taushe fushin da ke zuciyarsa sannan ya iya furta.

“Na taɓa Mai Martaba, amman ba da wata niyar na yi ba, a lokacin basa da kuɗin biyan hayar ne kuma Ummi ta basu lokacin tashi, saboda gidan Amal ne wanda gobara ta ƙone, a lokacin za ayi gyaransa ne”


Mai Martaba yayi shiru yana nazari a zuciyarsa, yasan ɗansa ba zai masa ƙarya ba, kuma baya daga cikin ƴaƴanan mazinata balle har ya zarge shi, kuma yasan lokacin da ya kawo masa labarin Namra, sai dai ɗan yau ba a shaidunsa, kuma zai iyayuwa ita Namra ɗin ta yaudari ɗansa.

“A wani guri kake zaune?”

Mai Martaba ya tambayi Asim a take ya amsa masa ya faɗa masa.

“Tashi ka yi tafiyarka”

Har ya miƙe tsaye sai kuma ya ce

“Mai Martaba kar naje gida wani abun ya same ni”

“Babu abunda zai same ka, indai ni na haifi Abdallah ko hararka ba zai sake yi ba”

Da tsinginta ya fice. Sannan Mai Martaba ya kalli Namra ya ce.

“Za a maidaki gurin Ummi ba zaki tare a yau ba, zan yi magana da mahaifinki”

Cikin wani irin nauyin jiki da zuciya Namra ta miƙe tsaye jiri na ɗibarta, aiko tana kaiwa bakin ƙofa ta sai tayi baya-baya ta faɗi ƙasa sumamamiya.
A take Abdool ya manta da agaban Mai Martaba yake, a guje ya ƙarasa inda take yasa hannunshi ya ɗauke yana kiran sunanta amman ina ta riga tayi nisa.
A firgice ya fita da ita a falon kamar wanda ya tallaɓo jaririya. Mamaki da aljab ya hana kowa magana sai kallon ikon Allah suke, Abdool ya talloɓo Namra sai gudu yake ya nufi parking space da ita. Sojojinshi na hango halin da yake da sauri suka buɗe mota ɗayan ya shiga a driver seat yayi ma motar key, Abdool na isa ya saka Namra gidan baya, sannan shi ma ya shiga.
Wasu sojojin suka shiga wata motar suka rufa masa baya.

@360 suka isa asibiti kai tsaye aka wuce da ita emergency, likitoci suka shiga bata taimakon gaggauwa.
Yana gurin zaune ya dafe kai wasu ƴan gidansu suka iso, cikin har da Hajiya Shafa.
Bayan kamar mintuna talatin likitocin suka fito, ɗaya daga cikinsu ne ya tsaya yana yi ma Hajiya bayani wai a barta ta samu bachi sun mata allura saboda akwai gajiya sosai a tare da ita.

Abdool na zaune a gurin har su Hajiya Shafa suka shiga suka fito, tare da sisters na shi.

“Babangida (Sunan da take kiransa da shi kenan kasancewar sunan mahaifin Mai Martaba ne aka sakaasa) Mu zamu tafi tun da abun da sauƙi, kuma likita yace ana buƙatar ta huta, Hajiya kilishi zata tsaya nan ta kwana, kuma ka faɗawa sojojinka kar su bar kowa ya shigo, ga kuma dogarawa nan Mai Martaba ya iko maka in case of...”

Kai kawai ya iya ɗaga mata, sai sisters ɗinsa da waɗanda suka zo tare suka masa Allah ya sauwaƙe.

Sai da suka fice sannan ya miƙe tsaye yana faɗawa sojan da ke kusa da shi cewar kar ya bar kowa ya shigo gurin, yana rufe baki sai ga Asiya Sister shi ta dawo da gudu ta miƙawa sojanshi carpet da hijab.

“Wai ance a bawa Gwaggo”

Da kanshi ya karɓi sallayar da Hijab ɗin ya nufi ɗakin. Wani abun burgewa sai da sojan ya sare masa sannan ya miƙa nasa.

Yana tura ƙofar ɗakin ya hango Namra kwance gefen gadon an ɗaura mata drip. Hajiya Kilishi kuma na zaune saman kujera sai amsa waya take. Tana ganinshi ta miƙe tsaye ta fice, ƙarasawa yayi ya aje carpet ɗin ya zauna saman gadon ya kai hannunshi ya shafa fuskarta. A hankali ya sauke ajiyar zuciya sai ya sauka ya zagaya ta bayanta ya hau saman hagon ya rumgumeta ya luma yatsunsa cikin nata, sai hawaye suka gangaro daga idonshi suka sauka saman ƙananan kitson da ke kanta.
Jin wayarsa na ringing yasa ya fiddota daga aljihun wandonshi ya kashe ta gaba ɗaya, ya lumshe ido yana ƙara janta jikinsa.

A wani ɗakin Hajiya Kilishi ta kwana, domin be sauka daga kan gadon ba sai da aka kira sallah asuba. Sannan ya sauka saman gadon ya shiga banɗakin dake room ɗin yayi alwala ya fito shi da sojojinsa suka nufi masallaci yayinda aka bar dogarawa suna cigaba da gadinta.

Bayan ya fita ne Hajiya Kilishi ya dawo ɗakin ta yi sallah asuba, bayan ta gama ya hau amsa wayar da ake mata dan tambayar jikin Namra. Sai ga Abdool ya dawo ɗakin a dole ta miƙe tana amsa gaisuwarsa ta fice daga ɗakin.
Wannan karon saman kujera ya zauna ya matsa can kusa da fuskarta ya ɗora tashi saman gado ya kwantar, sai hancinshi ya riƙa gogar nata, numfashinsu na taraiyya da juna.

A hankali ta buɗe ido karaf cikin nashi, bakinta da ke saitin nashi yayi ma kiss sannan ya tashi zaune daidai yana riƙa hannunta, sai itama ta tashi tana cigaba da kallonshi idonta sun yi wani fari.
Har cikin jininshi yake jin tsanyin dake cikin hannunta, zuciyarsa cike da tausayinta.

“Sannu”

Ya faɗa yana kai hannu ya shafa gefen fuskarta.

“Sallah”

Ta ce a kasale. Miƙewa yayi tsaye ya shiga bathroom ɗin ɗakin ya ɗauko ƙaramin bokin da ke ciki ya fito sai ya buɗe ƙofar ɗakin yayi magana da boys ɗinsa da suke gurin, sannan ya dawo ya zauna a kusa da ita.

“Za a kawo ruwa yanzu, muje ki yi fitsari”

Ƙoƙarin saukowa ta riƙa yi sai kawai ya ɗauke ta ya nufi bathroom ɗin da ita.
Ƙoƙarin ɗaga mata saket ɗin ya riƙa yi sai ta riƙe, ya kalleta.

“Baki da ƙarfi Abnam”

“Zan iya”

Baya son musa mata, sai kawai ya fito yaja mata ƙofar. Da dafe dafen bango ta yi fitsarin ta fito, sai ya sake ɗaukarta ya maida saman gadon.

“Allah ya baki lafiya”

Ya faɗa yana kwantarda kanta saman kafaɗarshi. Cikin ƙanƙanen lokaci aka buga ƙofar ɗakin sai ya ɗagarda kanta shi kuma ya tashi ya buɗe ya karɓo robar da carton ɗin ruwan faro, sai da ya buɗe ruwan sannan ya zauna kusa da ita ya kama hannayenta ya wanke mata su sau uku, sai ya zuba ruwa a hannunshi ya kai mata a baki ta kurkure bakinta ta zuba cikin robar sai yasa yatsansa ya wanke mata haƙora, sai ya sake zuba ruwan a hannunshi ya kai mata a baki ta kkurkura har sau biyu sannan ya shaƙa mata hanci sai kuma ya riƙa mata hancin ta face, ya wanke mata fuskarta sannan ya wanke hannayenta zuwa murafiƙai, ya shafa mata kai ya ƙwaƙwala mata kunnuwa sai ya saukar da robar ƙasa ƙasa ya kama ƙafafunta ya tsattsafe ya wanke su tas, sannan ya ɗauke robar ya kai bathroom ya fita ya karɓo mata carpet da hijab.
Sai da ya shinfiɗa mata carpet ɗin sannan ya saka mata hijabin, ya sauƙo da ita saman gadon ya tsayar, ganin jikinta rawa yasa ya zaunar da ita, ya tattara hankalinsa ya miƙa mata yana kallon yadda take sallah a zaune cike da tausayawa. Tana ƙarewa ya dawo kusa da ita ya zauna, sai ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi tana hawaye. Hannayensa biyu yasa ya ɗago fuskarta ya kai bakinshi daidai hawayenta yayi mata kiss.

“Babu wanda ya isa ya shiga tsakanin mu Inshallah”

Ya faɗa kamar mai raɗa, sai kawai ta fashe da kuka shi kuma ya rumgumeta a ƙirjinsa, ya lumshe ido yana sauraren sautin kukanta dake tashi a hankali.



RASHIDA FINAL POINT OF VIEW (POV).

Ita ce ta biyu wacce ta miƙe tsaye ta yi jawabin bayan shugabar ƙungiyarsu ta gama, kasancewar yanzu ita ce mataimakiyar shugaba, a duk inda za a je da ita ake zuwa cikin da wajen garin kaduna, har South west, south south suke zuwa gurin wayarda kan al'umma akan a daina ƙyamar masu ɗauke da cutar hiv, suna kuma wayarda kai akan masu cutar su daina takura kansu da ganin kamar mutuwarsu tana kusa da
Showing 258001 words to 261000 words out of 280121 words