zaka iya ƙigarsu ba, ga akwati goma da aka sako na tufafi har da zinari duk a cikin an gani ana so, kowa abunda yake faɗa to lefen me za'ayi?

Ba a gidan aka kawo kayan ba, daman haka Abbah yake duk lokacin da za a yanka ma ƴaƴansa sadaki ko a kai lefensu, gidan ƴaƴanshi yake turawa.

Ko da ake hidimar kai kayan Namra tana makaranta a lokacin duk da yake asabarce amman a ranar tana da darasin (lecture) da zata ɗauka a makaranta, bayan sun gama tayi sallama ta abokanta ta nufo gurin da tasan Lamido ya saba tsayawa ya jirata.
Ko da ta isa yana zaune cikin motar buɗewa kawai ta yi ta shiga ta zauna sai kawai taji ya ce

“Congratulations”

Tasan abunda yake nufi, yanayin muryarsa ya karantar da ita baya cikin daɗin rai.

“Na amince da auren Abdallah ne saboda mahaifina, kuma na san kai ma baka ƙi goya min baya ba wajen amincewa da hakan”

“Abdallah ya kasa ni, daman ya faɗa min zai kasa ni, ta tabba yanzu shi ne a zuciyarki ba kowa ba”

“Ya faɗa maka? Alfahari yayi, fariya yayi da zai kasa ka? Yaushe bakin ka ɗa nashi ya taɓa haɗuwa?”

Yayi ma motar key yana cigaba da magana a hankali.

“Bayan tafiyarki, abubuwa da tawa sun faru, ciki har da dalilin zuwa neman aurenki, da kuma neman zama direba a gidanku...”

Ta gyara zamanta a gidan bayan da take.

“Ban gane ba dan Allah ka ƙara min bayani, karka ɓoye min komai”

“Bayan kin bar Kaduna da kwana biyu, Yarima yasa aka ɗauko ni daga Kaduna aka kawo ni Katsina, mahaifata garin da ƙabarin ubana yake, kuma garin da nayi alƙawarin ba zan sake takawa ba.....”

Kamar wanda ya tuna abu sai kawai yayi shiru ya cigaba da driving ɗin da yake. Ita kuma gaba ɗaya natsuwarta ta bar jikinta hankalinta ya karkata kan labarin da Lamido ya fara bata...


IS BETTER THAN NONE... 😎 YI HAKURI DA SHORT CHAPTER 🙏
[7/23, 9:21 PM] Khadeeja Candy♥: *88*

“Ka tsayarda motar nan Lamido”

Ta faɗa a tsawace, umarninta yake bi tunda danta yake wannan aikin, a dole ya faka mota a gefen ti-ti, sai dai be juyo ya kelleta ba balle yace mata wani abu.

“Miyasa Abdallah ya sa aka kai Katsina? Miya ce maka? Miya faru bayan na baro Kaduna?”

“Faɗa miki abunda ya faru ba zai yi maganin komai ba”

“Wata ƙila zai yi wata ƙila kuma ba zai yi ba, amman faɗin shine mafi a'ala”

“Ni da Mahaifina asalin mu fulanin Katsina ne, mahaifiyata kuma ƴar asalin jihar kano ce, mahaifina ɗan kasuwa ne ya kan ɗauki kaya daga Katsina ya kai Kaduna idan ya siyar sai ya siyo na Kaduna ya kawo Katsina da hakan abun nasa ya girma, har ta kai ya kan ɗauka daga Katsina ya kai Nijar, a lokacin muna ƙanana, iya gata mahaifinmu ya nuna da kulawa mun taso cikin jindaɗi, arkizin mahaifinmu ya bunƙasa cikin ƙanƙanen lokaci, sai dai mahaifin mu be da amini irin Alhaji Mu'azu, ita kanta mahaifiya bata da ƙawa irin Hajiya Zuwaira, ba unguwar mu ɗaya ba, amman duk ranar weekend sai an kawo yaranta gidanmu su yi weekend,  bana da wayo sosai a lokacin, amman ina jin yadda Mahaifina yake faɗin idan har ya haɗa wannan kuɗin ya tura aka turo masa kaya zai samu kuɗi sosai, haka ya tattara komai na shi ya haɗa kai da Aminsa ya tura kudaɗensa masu yawa sosai. Shiru-shiru babu kaya babu labarinsu, har ta kai mun fara shiga wani hali na ha'ila i, Alhaji Mu'azu ne yake aiko mana da cefane wani lokacin kuma har da ɗinkuna da wasu abubuwan na more rayuwa, ashe duk wannan yana masa ne a cikin kuɗin da yake binsa, wata ranar Assabar mahaifina yake labarta masa kayansa suna nan zuwa, har an kamo hanyar nigeria da su ta jirgin ruwa, haka muka ɗauki tsawon wata ɗaya muna jiran isowar jirgin, sai kawai dirar ƴan sanda muka gani a gidanmu, wai ana zarginsa da safarar muyagun ƙwayoyi, haka suka tisa ƙeyarsa a gaba suka tafi da shi, sau ɗaya suka bar mu muka ganshi tun daga lokacin ba mu sake ganinsa ba, sai dai abokinsa ya zo ya faɗa mana cewar ana nan za a sako shi, amman shiru har Allah ya karɓi ransa. Bayan rasuwarsa Alhaji Mu'azu yake faɗa mana cewar babu dukiyar Mahaifinmu ko taro a hannunsa, sanadin haka muka bar garin Katsina ni da Mahaifiyata, sai muka koma garin Kaduna da zama wato mahaifarta, a gidan data gada gurin mahaifinta, tun daga lokacin garin Katsina ya fita daga raina duk da kasancewar a nan mahaifar ubana take, sai sai bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya sake waiwayar mu a cikinsu”

Namra ta share hawaye idonta cike da tausayawa ta ce

“Ba shi na tambayeka, abunda Abdallah yayi maka na tambaye ka”

“Abdallah yasa an ɗauko ni daga garin Kaduna aka kawo ni Katsina saboda kawai yana ɗan sarauta kuma ɗan mai kuɗi yafi ƙarfin ya bar garinsa ya zo kaduna saboda ni”

“Har yanzu baka faɗa min dalilin ɗaukoa da yasa aka yi ba”

Shiru be sake ce mata komai ba, hara aka kira sallah la'asar, tasan ba zai faɗa mata ko minene a yanzu ba. Zata sake magana wayarta ta yi ƙara number Abbah ta gani cikin sauri ta yi picking.

“Gamu nan kan hanya”

Shine kawai abunda ta faɗa ta sauke wayar. Shi kuma ya tashi motar suka hau ti-ti. Ta madubin gaban mota take kallon yadda hawaye suke zuba daga idon Lamido.

  Sai da suka kusa isa gida sannan ya ciro handkerchef ɗinsa ya share hawayensa. Yana faka motar ta buɗe ta fito sai shi ma ya buɗe ya fito ya miƙa mata keys ɗin motar.

“Aikina ya ƙare daga yau! Gobe zan kama hanyar garin mu”

“Ba a gurina ka karɓi keys ɗin motar ba, ba ni na ɗauke ka driving ba”

Tana bashi amsa ya gyara tsayuwar littafan da ke hannunta ta nufi hanyar falo.
Tana shiga Maryam da Wasu old friends ɗinta suka jo kanta suna mata murna da zolaya. A abubuwa biyu ta samu kanta, farincikin da akasinsa, ba data dalilin yin duka biyu ɗin, dan har ga Allah bata shirya aure a yanzu ba, sai dai babu yadda ta iya tun da Abbah ya nuna yana son ta yi, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta tuna halin da Lamido yake ciki sai ta ji Abdool ya fita a ranta. Cikin ƙarfin hali take musu dariya tana nuna musu farincikinta sannan ta wuce ɗakinta. Littafanta ta jefar saman gado ta shiga banɗaki ta yi alwala, ko da ta fito wayarta na ringing, wasu kawayenta ne na makaranta hakan yasa bata ɗauka ba, tasan ba zai wuce su taya ta murna ba, ko kuma su faɗa mata yadda zancen engaged ɗin ta ya cika social media. Har ta saka Hijab ɗinta sai wayar ta sake ringing wannan karon Abdool ne, tana son magana da shi sosai hakan yasa tayi picking tana aika masa sallama.

Ya amsa mata yana ƙarantar saƙon dake cikin muryarta na ranshin daɗin rai.

“Tell me i'm wrong, amman kamin ki yanke hukunci ya kamata kisan duk abunda aka yi Mai Martaba ne yayi ba ni ba”

A tunaninsa ko akan kayan ta ya tura ne wani abun be mata daɗi ba, sai kawai yaji ta ɗauko masa wata magana ta daban.

“Miyasa kasa aka ɗauko Lamido daga Kaduna ka kawo shi Katsina? Mi kace masa?”

Yannu ya kai yana shafa dogon hancinsa, tare da maimaita sunan Lamido a zuciyarsa.

“Be faɗa miki abunda Yarima Abdallah yayi masa ba? Be faɗa miki gaskiyar abunda ya faru ba?”

“Be faɗa min ba, amman ga dukan alamu abunda ka yi masa babba ne, domin har hawaye na gani a idonshi”

Ƙafarsa ya ɗora ɗaya saman ɗaya yana imaging fuskar Namra a wannan lokacin duk da kuwa bata kusa da shi.

“You're crying...”

Sai kawai ta katse kiran ta share hawayen idonta ta miƙe tsaye ta kabbatar sallah. Har ga Allah tana jin son Abdool a zuciyarta sai dai bata fatar ta yi amfani da wannan damar ta cutar da Lamido, dan tana jin rashin kyautawa a abunda ta yi masa, sai dai bata da zaɓi bayan na Allah daman can shi ta miƙawa lamurarranta, har gobe roƙon Allah take idan har babu alheri a aurenta da Abdool Allah ya musanya mata.

Haka ta kwashe kwana biyu, babu wata magana mai daɗi dake shiga tsakaninta da Abdool, saboda tana ganin kamar yana amfani da saurautarsa da kuma kuɗinsa ne wajen nuna mata ƙarfin iko ya ita da Lamido, ga kuma farin jikin daya samu a tsakanin iyayenta wanda hakan ya hanata ko da wasa ta cewa Anty wani abu ya shiga tsakaninta da Abdool ba.

Har yanzu Lamido ne yake kaita makaranta, bata tambaye shi yadda yayi da Abbah ba, shi kuma be ce mata komai ba. Sai dai ta kan tsargu da abu ɗaya a yanzu, ya kan tsura mata ido ta madubi mota ko kuma idan tana waje kamar madubinshi.
Ita kuma a yanzu bata magana da shi saboda ya ƙi ya faɗa mata.


ABDOOL POV.

Tun da ya karanci halin da Namra ta sashi, sai ya ke ganin kamar Lamido ne yake masa zagon ƙasa, daman shi zuciyarsa bata natsu da zaman lamido a gidan ba, a duk lokacin da ya tuna sai yaji kamar zuciyarsa zata rabe biyu, musamman da yasan shi yake kaita makaranta ya ɗauko ta, tabbas yayi sake da yaba har tsawon wata takwas tana keɓancewa da Lamido, aiko dole ta so shi fiye da shi.

Kamar an masa allurar ƙarfi haka ya zabura ya miƙe tsaye be damu da saka hula ba duk da shaddace a jikinsa ya fito ya nufo part ɗin Ummi.

Be same ta a falon ba, sai Amal ya samu tana ta faman solved Maths.

“Dude Ina Ummi?”

“Tana Garden lalle ake musu, Dude na taso mu yi wannan assignment ɗin?”

“No bari sai na dawo fita zan yi”

Ya juya ya fice. A garden ya sameta zaune saman carpet ta jera ƙafafunta ana zizira mata lalle irin wannan na zamani.

Tsaye yiyi ya jingina da icen guava yana wasa da keys ɗin hannunsa.

“Ummi na canja shawara, zanje na ga Mai Martaba”

“Shawarar me?”

“Nan da One Months nake son a yi auren nan?”

Da mamaki Ummi ta kalleshi.

“saboda me?”

“Kawai ni nafi son haka ne”

“To su ƙanenka da aka saka date ɗin aurenku a tare fa?”

“Su a barsu sai lokacin ni kan gaskiya i can't wait, zan samu Mai Martaba mu yi magana”

“Amman zai zama kun yi magana biyu Abdallah, da ka yi haƙuri har lokacin nan da wata biyar a ba wani abu ba ne”

“Haƙuri ba zan iya ba Ummi, kawai ki min addu'a”

“Toh Allah yasa alheri, amman nasan Mai Martaba ba zai amince ba”


“Zai amince ki daina ƙwanƙwanton mahaifina akai na”

Hannu ta ɗaga masa.

“Tafi kai da kan ka zaka dawo ka ba ni labari”

Murmushi yayi ya juya ya bar Garden ɗin tana ta saƙe-saƙe a ranshi har ya isa faɗar Mai Martaba.
Be same shi a gida ba, saboda wani taro da taje, haka ya zauna a gidan har aka yi sallah magariba, bayan ya fito daga masallaci ne Mar Martaba ya dawo, dan shima sai da ya tsaya a can suka yi sallah sannan ya kamo hanyar gida.

Mai Martaba na gaba Yarima Abdool na biye faɗawa sai zuba masa kirari suke har aka shiga fada. Kai tsaye Mai Martaba ya wuce turakarsa Abdool ya rufa masa baya yana masa bangajiya. A saman fafaffaɗa kuma ƙasaitacciyar kujera Mai Martaba ya zauna ya cire rawaninsa ya miƙawa Abdool. Bayan ya aje rawanin ya dawo kusa da ƙafafun Mai Martaba ya zauna yana mai natsar da kai kasa kamar yana gaban sukurinsa, ya kan yi hakan a duk lokacin da da yake neman wata alfarma a gurin mai Martaba saboda kawai Mai Martaba yaji tausayinsa ya amince.

“Buɗe baki ka yi magana, Babana ni mahaifinka ne idan ban maka uzuri ba waye zai maka?”

“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya, daman magana ce na zo da ita akan auren mu, sai dai ban san ta fuskar da zaka kalli abun ba”

Mai Martaba ya jingina da kujera yana cigaba da kallon ɗansa. Abdool ya cigaba ba tare da ya ɗago ya kalli Mai Martaba ba.

“Idan har ka amince min, ina son ka roƙa mahaifin Namra akan ya rage lokacin da ya saka na aurenmu saboda yayi tsawo...”

Sai da aka ɗauki tsawon ɗakika talatin da huɗu wata kalma bata fito daga bakin Mai Martaba, sannan ya nunfasa kana ya ce

“Ni kaina na yi tunanin hakan, saboda maganganun da suke ta zuwa suna dawowa, ba a son magana ta yi yawa akan aure, kuma idan har aka ja abu nesa wannan kan iya haifarda da wata matsala wace ba a tsammanin zata zo, sai dai ganin lokacin auren yayi dai-dai da lokacin auren ƴan'uwaka yasa ban ce komai a kai ba”

Abdool ya jidaɗin wannan maganar, daman yana neman da inda zai fake yayi hujja da shi akan maganar auren. Sai gashi Mai Martaba ya taɓo masa inda yake masa ƙai-ƙaiyi.

“Nima hakan na gani, kada sheɗan ya shiga ciki, ko kuma baki yayi mana yawa”

“Gaskiya ne, amman kai zuwa yaushe kake ganin ya dace a saka auren?”

“Allah ya taimake ka ina son ace nan da wata ɗaya”

Mai Martaba yayi masa wani kallo.

“Nan da Wata ɗaya sai kace wanda zai auri ƴar tsana? Wata ɗaya yayi mana kaɗan da shirya lamarin auren ka”

“Allah ya taimake ka duk yadda ka yanke dai'dai ne, amman be yi kaɗan ba, indai matsalar lefe ne ciki sati ɗaya za a iya haɗawa, kuma na san bama buƙatar komai daga gareta”

Ɗan Murmushin gefen baki Mai Martaba yayi, lallai ya tabbatar da ɗansa ya matsu, hakan ma yasa shi gane Abdool yama neman girma a yanzu, bayan kuma a da neman masa ake yana gudu.

“Za mu yi tunani akai, kar ya zama mun matsa musu, zan yi shawara da Umminka, nan kuma cikin gida zamu shawara”

Mai Martaba na gama faɗar hakan ya miƙe tsaye...



__________________________________

I think we should create a team for LAMIDO ko 🤔 i pity him bawan Allah 😢
[7/24, 9:38 PM] Khadeeja Candy♥: *89*

Yau day ta leƙa whatsapp domin ta kwana biyu bata hau ba, daman bata hawa sai idan tana da time saboda karatun da ta sawa gaba.

“Abbah na kiran ki”

Aysha ta faɗa tana tsare jikin ƙofar ɗakin Namra.

“Okay ga ni zuwa”

Ta kashe data ta sauka saman gado. Ko da t fito Zinatu na zaune falo ita da Anty Amarya suna cin ɗatun zogale (kwaɗo). Wara ido tayi ta sha mur

“Lallai Anty shi ne cika zauna da ƴarki kika ci ɗatu ni aka ƙyale ni”

“To idan ban ci da ƴata ba da wa zan ci? Kaji min yarinya”

Anty Amarya ta faɗa fuskarta da annuri tana murmushi. Zinatu tasa dariya.

“Na gan ki online fa kuma na miki magana kika share ni”

“Allah ban duba ba, hankalina yana can ina duba chat ɗin grp”

“Gashi ai sai ki zo ki ci”

“Abbah ya kira ni, aje min na dawo”

Ya aje wayarta saman kujera ta nufi part ɗin Abbah. Zaune ta same shi sanye da jallabiya, idonsa sanye da farin gilashi hannunsa da jaridar daily trust. Ƙasa ta zauna bayan ya amsa mata sallamar da tayi idonta kan Arewa24 da suke maimaita shirin Daɗin kowa.

Remote Abbah ya ɗauka ya kashe tv, ya aje jaridar da ke hannunshi sannan ya fuskanci Namra ya ce.

“Magana na ke son mu yi a tsakanin ni da ke, kuma bana son ki takura kan ki, na fi son ki faɗi ra'ayinki”

Ta ɗan kalleshi kaɗan.

“Abbah maganar me ce?”

“Akan date ɗin da aka saka ne na aurenki, Mai Martaba ya kira ni yace a rage musu ranar da aka saka ta yi musu tsawo, amman yace baya son a cilasta miki yafi son sai anji ta bakinki”

“Abbah ban da wani zaɓi sai naka, abunda duk zai fito daga bakinka shi xai fito baki na, kai da Mai Martaba duka iyayene a gurina, duk yadda kuka yanke yayi, idan ma a yanzu kuke son a ɗaura auren babu matsala ni dai a guna, sai idan gurin Abdool”

Abbah ya jidaɗin maganarta sosai, daman haka yake son ta kasance gareshi mai biyar dukan umarninsa da yarda da abunda ya zaɓa mata, babu ruwanshi da duba zamani ya canja a ƙyale yara su yi ra'ayin kansu, yafi son duk yadda ya zaɓa maka kawai ka bi.

“Na jidaɗi da wannan kalami na ki Namra, kuma tun da har kin amince zan faɗawa Mai Martaba kuma na san shi ma zai jidaɗin wannan maganar, daman shi yana son a saka me nan da wata ɗaya”

Dam! Gaban Namra ya yanke ya faɗi sai ɗai bata nuna komai a fuskartaba.

“Babu matsala a gurina Abbah, amman ya maganar Lamido?”

Abbah ya sauke ajiyar zuciya.

“Yadda kike so Namra ba zai yiyu ba, ba zan ɗauki mutun haka kawai na bashi MD, mutanen duniya a yanzu ba abun yarda ba ne, abunda Uxair yayi min kawai ya isa ya lurar da ni duniya, zan iya bashi aiki dai a ƙarƙashina, kuma daman ina da niyar gyara musu gidansu kuma na ƙullawa mahaifiyarsu jari, ko da be yi komai ba zan iya masa haka balle kuma ya taimake ki sun riƙa ki tsakani da Allah, na san yana son ki Namra kuma kema kin san da haka, sai dai hakan ba zai sa na ɗauke shi haka kawai na bashi mb ba”

“Amman Abbah idan ya fara aikin nan ka aminta da shi zaka iya bashi md, wallahi mutumen kirki ne”

Abbah yayi murmushi.

“Har yanzu akwai ƙurciya cikinki, ai ba a gane mutum mai amana a fuska sai a aiki, sai dai na yarda da abu ɗaya, duk yadda duniya ta lalace za a samu na ƙwarai, zan jarrabashi na gani”

“Na gode Abbah”

“Allah ya miki albarka”

“Amin Thank you”

Haka ta tashi jiki babu gwari ta fice. Tun daga lokacin aka fara shirye-shirye, a dukan ɓangarorin guda biyu. Kullum sai Abdool ya kirata safe, rana da dare domin jin muryarta da kuma son sanin ko akwai abunda take shiryawa, sai dai duk lokacin da ya tambaye cewa take bata shirin komai.

Hakan yasa ya baro Abuja a daren ranar ya sauka sokoto, dan kwata-kwata ya rasa gane kan matarshi (His wife to be). Haƙuri yayi har
Showing 249001 words to 252000 words out of 280121 words