ya fice ba tare daya faɗa mata abunda yayi niya ba.
Da sauri Asmee ta ƙaraso kusa da ita ta dafa ta.

“Ke lafiya Hilal yake kuwa? Wai jiya bayan na bar nan asibitin na ji mummunan labari da gaske ne kuwa?”

Kwantowa tayi kikin Asmee tana kuka

“Da gaske ne Asmee ya sake ni”

“Me kika masa?”

“Ban masa komai ba haka kawai ya sake ni”

“Hmmm sherin kishiya ne, ai kinsan yadda mijinki yake son ki ba zai sake ki haka nan kawai ba, wani asiri ne aka masa”

“Ba zai mai da ni ba, shikenan ƙarshen aurena da shi”

“Wallahi ƙarya ne, ƙarya ne wallahi Allah ya sa kiji sauƙi da wuri, kin ga malamin nan da na kai ki gurinsa? Wallahi ki koma yayi miki aiki a gigice Hilal zai maida ke”

“Zan koma yayi min aiki, amman bana Hilal ya mayarda ni ba, sai dai na wani abun daban, na riga na yafe Hilal har a bada”

“Kar kice haka Allah dai ya baki lafiya”

Ƙara fashewa tayi da kuka ta ƙamƙame Asmee tana jin wani irin zugi da zuciyarta ke mata.


AMIRA POV.

Daga ita sai tawul ta fito daga banɗaki, ta zo ta zauna gaban mirrow tana taje kanta. Sai da ta gama ta shafa mai tayi kwalliya sannan ta kalli Guy son dake kwance saman gado yana kallonta tace

“Amman kasan matar nan ta raina mana hankali? Sai da tasa muka bincika ko waye likitan sannan zata ce mana wani ta fasa”

“Manta da ita kawai, akwai wani aiki da zamu je yi Abuja jibi, akwai wanda ya kira ni kuma na san zamu samu kuɗi da yawa”

Ta baro inda take zaune, ta nufo inda yake tana wara ido

“Da gaske?”

“Na taɓa miki ƙarya?”

“No I'm just asking, you know how a like Abuja”

“Yeah shiyasa zan je da ke ai”

Rumgume shi tayi cike da jindaɗi, shi kuma ya shiga shafa jikinta.


NAMRA POV.

Cikin wani irin kuka ta isa gida. Yau duk wani tsoro da take na gidan be ziyarce ba, dan baƙinciki dake tare da ita tafi tsoro, yadda ta ga dare haka taga dare, sai ta tashi tayi sallah, tayi addu'ah samun mafita da sauƙi a zuciyarta. Tana gurin bata tashi ba har aka kira sallah asuba, kasa cin komai tayi da safe, ji take kamar ta kashe kanta ta huta, kalaman Asim sun tsaya mata a rai, sai yanzu ta fara gasgata kalaman Anty Amarya, ayau Asim ya nuna mata ko waye shi, ya buɗe mata sirrin dake ransa, sannan ya zarge ta da abunda wani be taɓa mata ba.
A tau ta tabbatar da tayi zaɓen tumun dare, sai a yanzu tana ganin laifin zuciyarta.

“Miyasa kika bar ni na kamu da son wanda ba dan Allah yake so na ba? Dan me baki bar ni na so waninsa ba? Duka yaushe muka yi aure da shi amman yau ya sauya min ya nuna min abunda ban taɓa mafarki ba? Yanzu ya zanyi da rai na? Na bar karatuna saboda shi na zo garin da ban san kowa ba saboda shi amman duk ban masa ba?”

Ita ƙaɗai take magana da kanta, tana wani irin kuka mai taba zuciya. Bata ji a yau zata iya kwana a katsina, dan a yau bata buƙatar kowa a kusa da ita sai yan'uwanta, da mahaifiyarta, tasan ko hira kawai tayi da su zai rage mata damuwa, sama da zaman kaɗaici da take yanzu.
Tashi tayi ta matsa kusa da inda ta aje ƴan komatsanta.
Jakarta ta buɗe taga kuɗin da yayi mata saura, sai ta shiga BQ ɗin ta ɗauko Sarƙa da wayarta ta saka a jakarta ta sauya hijabinta ta jawo BQ ɗin ta fito tana kuka.

Sai da ta tari Napep ta shiga sannan wani tunanin ya zo mata. Idan ta koma gida da wane ido zata kalli Anty Amarya? Me zata cewa Abbah? Masu jiran su yi musu dariya tasan zasu yi. Har ya kai ta tasha bata samawa kanta wata mafita ba, sai dai hakan be hana ta shiga motar sokoto ba, tun da bata da wani gurin zuwa sai can.


ABDOOL POV.

Yana zaune ƙasan Carpet yana cin abinci, Ummi dake zaune saman kujera ta tsare sa da ido tana kallon ɗan nata cike da tausayawa.
Sai da ya gama cin abincin sannan ya kalleta yana murmushi.

“Ummi wannan kallo ai sai ki tsorata ni, gani zanje Abuja gobe ai sai kisa nayi tunanin ko mutuwa zan yi”

Ɗan murmushi tayi ta kawar da kai.

“Kawai ina tausayin ka ne, jiya da zafin jiki ka kwana saboda tunanin nan yarinyar how i wish ina da wani abu da zan yi akai”

“Karki damu, ni ai haka jiki na yake, mutane suna cewa ba komai bane dan kaji mutum da zafin jiki”

“Ba irin naka zafin ba, wacan ɗan ɗumi ake nufi kuma shi ma a mace ne ba namiji ba”

Dariya yayi ya tashi tare da plate ɗin

“Ummi kenan, ni fa bana da wata damuwa yanzu sai ta Mai Martaba”

“Zan yi magana da shi ai na faɗa maka, kawai kai dai ka samu natsuwa kuma ka kwantar da hankalin ka”

“I will try inshallah”

“Ni Allah yasa ma Abujar nan da zaka je ka haɗu da wata wanda zaka so fiye da wannan ma”

“Ai gurin aiki zamuje ba gurin hutawa ba, idan kuma kina son na ɗauko miki soja shikenan, sai na auro soja”

Wani tsaki taja ta ɗauke kai ta mayar gurin tv. Shi kuma yayi dariya ya shige kitchen.


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*


*© Khadeeja Candy*

*PAGE - 42*

NOT EDITED ⚠

Da yamma lis Namra ta sauka babbar tashar sokoto, sai da kowa ya gama fita motar kasancewar ita ce a can baya sannan ta fito jiki a sanyaye, tana kalle-kalle kamar mai tunanin inda zata je.

A hankali ta cira ƙafarta da tayi mata nauyi saboda zaman mota ta fara takawa, ta doshi ƙofar fita tashar gabanta sai faɗuwa yake kamar zai fito, wani abu ta ji ya zo ya tsaya mata a zuciya, yana ƙoƙarin danne mata numfashi.

Ta daɗe a tsaye bakin ti-ti sannan ta tari Napep ta shiga, sai da ya fara tafiya da ita suka yi nisa sannan ta ɗan karkato ya tambayeta inda za a kai ta ganin bata ce masa komai ba tun da ta shiga Napep ɗin.

“Hajiya ina za mu?”

Shiru tayi kamar mai tunani, ta ɗauki tsowon lokaci bata amsa shi ba, har sai da ya ƙara tambayarta.

“Clapperto....road, gurin....gawon nama”

“Dari biyu zaki biya Hajiya”

“Ok..ay.. Allah Kai... Mu lafiya”

“Amin”

Ya kai hannu ya kunna waƙar Umar M Shariff ta duniya makaranta. Sauraren waƙar take tana hawaye, hankalinta da tunaninta gaba ɗaya ya tattara ya koma gidan su da take tunkara yanzu. Abunda zata faɗa musu take ta saƙawa amman har ta saka samun mafita.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta furta a hankali lokacin da Mai Napep ɗin ya kunna kai cikin unguwar. Jin tayi kamar tace ya juya da ita, sai dai idan ya juya da ita ɗin ina zata ce ya kai ta?

“Ya isa...”

Ya faɗa a lokacin daya kawo bakin ƙofar gidan su. Sai da ta share hawayen idonta sannan ta ciro kuɗinsa ta miƙa amsa, sannan ta fita jikinta har rawa yake irin na tsoro da rashin gaskiya yana tare da ita.

Sai da Mai Napep ɗin ya wuce, sannan ta doshi ƙofar gidansu, cikin wani irin mugun faɗuwar gaba. Har ta kai hannu zata tura ƙofar gate ɗin sai kuma ta tsaya tana jan numfashi.
Tafi kowa sanin waye mahaifinta, ta kuma san halinsa ba zata manta furucin da yayi mata ba, bata san iya furucin da zai ƙara mata ba.
Babu wacce ta faɗo mata a rai, sai Gwaggo Kulu, ƙanwar Abbah, mahaifiyar Anty Yasmin.
Tasan ƙanwar Abbah ce amman Abbah yana jin maganar ta sosai kuma tasan yadda Gwaggo Kulu take son ta cikin ƴaƴan Abbah.

Juyawa tayi da saurin ta nufi farƙon unguwar dan ta can ne zata fi saurin samun abun hawa. Sai da ta kusa ƙarasawa babban ti-ti sai ta ga Motar Maryam ta kunno kai cikin unguwar. Da sauri Namra ta kawar da fuskarta dan kar Maryam ta ganta, ashe tayi a banza dan baya-baya Maryam tayi da mota ta fara leƙen fuskarta, hakan be gamsarda ita ba har sai da ta faka motar gefe ta fito ta fara bin Namra da ƙafa tana kiran sunan ta.

“Anty Namra ke ce?”

Juyowa Namra tayi ta kalleta idonta da hawaye ta ɗaga mata kai.

Wani irin tsalle Maryam ta daka ta rumgumeta tana ihu.

“Wallahi ban ɗauka ke bace nayi zaton wata ce mai kama da ke, Anty Namra ina za ki?”

“Gidan Gwaggo Kulu zan je”

Ta faɗa cikin kuka tana rumgume da ƙafaɗar Maryam. Maryam ta ɗago ta kalleta

“Miyasa ba gida kika zo ba?”

“Amman nasan Abbah ba zai bari na zauna ba, korata zai yi”

Maryam ta dafa kafaɗunta.

“Fushi kika yi?”

Tayi shiru bata amsa ta ba, hakan ya tabbatar ma Maryam amsar tambayar.

“Wani abun Asim yayi miki ne? Karki ɓoye komai Anty Namra ki faɗi abunda yayi miki, dan ba zai yiyu ya taɓa mana ƴar'uwa ba mu ƙyale shi”

“Be min komai ba, ni dai kawai na gaji da zaman can ne”

“To ki zo muje gida”

“A'a ni ba zan je ba, Abbah zai kore ni kuma Anty ba zata ji daɗi ba”

“To ya zaki yi? Kina da inda ya fi miki gidan uban ki ne? Ko yanka namanki zai yi yayi gunduwa-gunduwa da shi dole ne ki shiga tun da baki da inda ya fi miki nan”

“Ni dai ba zan je ba, gidan Gwaggo Kulu zan je”

“To muje na kai ki”

Maryam ta faɗa tana nuna mata motarta. Kamar ba zata shiga ba, sai kuma ta nufi motar ta buɗe ta shiga. Sannan Maryam ta shiga driver seat ta tashi motar, ribas tayi ta juya ta inda ta fito, sai da suka hau babban ti-ti sannan Maryam ta kalleta tana takaicin halinta tace

“Wani lokacin Anty Namra kina ban haushi da mamaki wallahi, kina abu kamar ba kece yayata ba, abunda kike yi ko Aisha da take ƙaramar mu ba zatayi ba. Kin san abunda yake cutar da ke? Tsoro da gudun zuciya, da ganin ke ba zaki iya ba, sune suke cutar da ke.

A duk kuma lokacin da kike ganin ke ba zaki iya ba, to ba zaki taɓa iyawa ba har a bada, lokacin da zaki hankalto kice zaki yi a lokacin ba ki da time, shiyasa yan karon magana suka ce if you say yes to others make sure you didn't say no to yourself, saboda zaki cutar da kan ki ne kawai, ba zaki taɓa burge kowa ba a duniyar duk abunda za kiyi wani sai yace kin masa ba dai-dai, ya kamata ace kin canja haka nan accept responsibility for your life, ya kamata ki san it is you who will get you where you want to go, no one else, duk wanda kika gani yana kusa da ke wallahi da zaki waiwaya wata rana zaki ga duk babu so, sai mai miki so na haƙiƙa, wasu duk dariyar fuska ne bda xaki san abunda yake zuciyarsa da ba zaki sake kallonsa ba.

A maimakon ki ƙara hankali da tunani amman kullum sai wata iri kike zama, kamar wanda ake cirewa ƙwaƙwalwa ana zubarwa, tsoron nan da yake ran ki dan Allah ki cire shi Namra, you have to your fears, kuma ya kamata ace kisan cewa kema kina da right and freedom...”

Tun da Maryam ta soma maganar in banda kuka babu abunda Namra take, ta san gaskiya ƴar'uwarta ke faɗa mata, tabbas akwai tsoro a a tare da ita, tsoron abunda mutane za su ce, tsoron ɓacin rai, tsoron ganin ita ba zata iya ba, da kuma gudun zuciyar wanda duk take tare shi. A rayuwar Namra bata iya so ba, irin son nan take yi na sadaukar da komai nata saboda wanda take so ko kuma ta yarda da shi. Indai Namra ta aminta da kai to kai je ka kwanta kawai kayi kwana, ita zata maka komai idonta ya kan makance ga duk wanda take so, bata ji bata gani.

“Mtsssssss”

Maryam taja tsaki.

“Aikin kenan sai kuka, da anyi miki abu kuka dai kuka, da kuka zai miki magani ai da tuni yayi miki, haka kika zo kika sakarwa yarinyar Amira jiki ta yi ta cin amanarki, Allah kaɗai yasan dalilin guduwarta daga gida, amman kullum uwarta ke take cewa ke ce sanadi”

Unguwar Bafarawa estates Maryam ta kai Namra, gidan Gwaggo Kulu.
A bakin gate ɗin gidan tayi farkin ta kalli Namra

“Yanzu idan kin shiga sai kice mata me?”

“Zan ce nan na fara sauka ne”

“Toh nidai ba zan shiga ciki ba, kuma idan na koma gida zan faɗawa Anty duk yadda muka yi da ita zan dawo na faɗa miki”

“Amman dan Allah karki faɗawa Abbah”

“Tau ina gaida Gwaggo”

Namra ta fita motar cikin yanayin damuwa ta shiga gidan Gwaggo. Sai da ta shige sannan Maryam ta juya da motarta tana mamakin lamarin Namra.

Cikin sanyin jiki Namra ta shiga harabar gida,har ta ƙasa falon tana jin tsoro kamar wanda za'ayi ma wani abu.

“Assalamu alaikum”

Cikin sanyin muryar tayi sallamar Yasmin da Gwaggo Kulu suka amsa mata. Tun da ta shigo cikin falon Yasmin take mata wani irin kallo kamar bata gane ta ba. Kallon gulma take mata ganin yadda tayi baƙi sosai, daman can ba fara bace amman baƙin na yanzu ya ninka sosai, ga wata rama da tayi kamar wanda ta kwanta ciwo.
Ita kuma duk taji wani yanayi na daban, musamman ganin Yasmin da tayi a gidan. Bata zace zata rarar da ita ba.


AMIRA POV.

Duk wani farinciki da Amira take yi na zuwa abuja, a yanzu na zama labari, tun jiya da Guy son ya labarta mata dalilinsa na zuwa abuja da
Sam bata son aikin da Guy son yake wani lokacin ƙara kidnapped da saffara ƙwayoyi da yake da aikin kisan kai, sai dai ta san bata isa ta hana shi wannan aikin ba, dan be haɗa aikinsa da komai ba, bata wani daɗe da shi sosai ba, amman ya sake da ita ya shigar da ita jikinsa ya nuna mata so da yarda sai dai be yarda ta hana shi aikinsa ba.

“Wa zaku je yin attacking?”

Ta tambaya tana saka kayanta a jaka.

“Wani soja ne, amman ba a Abuja za muyi attaching nasa ba, daga nan sai za mu bisa za a bamu address nasa sai idan ya koma gida za mu ƙaddamar masa”

“Kashe shi zaku yi?”

“Haka ake son mu yi”

“Waya sa ku?”

“Wata mata ce amman bata son a gane ita ce, shiyasa take son mu bishi daga nan abuja ta yadda za'ayi zaton ko abokan aikinsa ne, yanzu haka ance mana yana cikin garin abuja”

“Amman Guy miyasa kake son kashe rai?”

“Saboda ban ɗauki rai a bakin komai ba, kema wata rana zaki aikata”

“Bana fatan aikata kisan kai har a bada”

Zuwa yayi ya dafata yana murmushi.

“Karki damu idan har kin kashe mutum kin lasa jininsa babu abunda zai same ki, ki shirya muje kar mu yi latti”

Cikin sanyin jiki ta rufe akwatin. Bata san wanda zasu kashe ba amman tana jin rashin kyautawa a lamarin.
Zama tayi saman gadon kamar mai jimami har sai da ya shigo ya ɗauki akwatin nata sannan ta tashi ta fita cikin sanyin jiki.


ABDOOL POV.
Jirgin safe ya bi ko da biyu na rana tayi har ya gama meeting ɗin da zasu yi, ya koma masaukinsa.
Kwantawa yayi ya ɗan runtsa na mintuna sannan ya tashi ya shiga yayi wanka, ya ɗauro alwala sannan ya fito, ƙananan kaya ya saka yayi sallah la'asar sannan ya ɗauki wayarsa ya kunna, text ɗin Ummi ya gani, hakan ya sashi jindaɗi tare da murmushi, sai ya danna numberta ya aika mata kira. A harabar gidan yana waya da Ummi, sai shafa kansa yake yana mai jin shauƙin son mahaifiyarsa cikin ransa.

“Alright Ummi i will, Thank you love you lot”

Ya kashe wayar fuskarsa da murmushi, yana kallon wata kurciya dake sha'aninta a harabar gidan nasa.

Ido ya tsura mata sosai yana son tantance abunda ya gani rataye a wuyanta. Ɗan matsawa yayi a hankali yana kallon layar dake wuyan nata, sai ya shiga ƙoƙarin kamata, be yi nasara ba ta yi firrrrr ta tashi sama, ta haye saman ginar gidan.

Tsaye yayi yana kallonta. Sai ya ƙwalama yaransa kira.

“Hey Boys”

“Sir”

Duk suka sheƙo da gudu, sai dai kamin su ƙaraso har ta ƙara fira ta bar gurin.



1869k words. Sorry for the short chapter 🙏🙏🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*


*© Khadeeja Candy*

*PAGE - 43*

NOT EDITED ⚠

Cikin rashin kuzari Namra ta zauna saman kujera tana kallon ƙasa kamar mai jin kunya.

“Namra...”

Ta ɗan ɗago kaɗan ta kalli Yasmin data kira sunanta, sai kuma ta kalli Gwaggo Kulu dakr tambayarta saukar yaushe.

“Yanzu na zo”

“Ya hanya ina mijin na ki?”

“Yana lafiya”

Kallon Namra Yasmin take zuciyarta na raya mata ba haka kawai Namra ta zo gidan ba, idan ma wani abun ne ai gidansu zata sauƙa. Murmushi tayi ta tashi ta nufi Namra ta riƙa hannunta.

“Tashi muje ciki kin wani zo nan kin zauna kamar baƙuwa”

Kallon Yasmin Namra tayi, murmushin data gani a fuskarta ne ya bata kwarin guiwar tashi ta bita. Ɗayan ɗakin Gwaggo Yasmin ta shiga da ita, daman can ɗakin ta fi zama a duk lokacin data zo gidan.

Yasmin ta buɗe bathroom ta duba ruwan dake ciki, sannan ta fito tana miƙawa Namra tawul.

“Shiga ki yi wanka, sai na kawo miki abinci”

Idonta a ƙasa take miƙawa Namra tawul ɗin irin bata son kallonta tana jin nauyin Namra sosai.
Hannu Namra tasa ta karɓa, sai Yasmin ta fice, ita kuma ta kwaɓe tufafinta ta ɗaura tawul ɗin ta shiga wanka, ko da ta fito Yasmin ta aje mata gown ɗin atamfa da abinci.

Ɗaukar rigar tayi ta saka, daman tayi alwala tun a toilet ɗin, sai kawai ta saka hijabinta, tayi sallah. Bata ci abincin ba dan bata jin cin komai, lemum kawai ta sha, sai ta ɗauki carbi tana tasbihi.

“Assalamu Alaikum”

Yasmin ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, murya ƙasa-ƙasa Namra ta amsa mata, sai ta zauna kusa da ita tana wasa da hannayenta.

“Kin abincin dai ko?”

“A'a bana jin yunwa”

Kallon fuskar Namra tayi da kyau-kyau, tana ƙoƙarin karantar danuwarta

“Namra, kiyi haƙuri na ji ance mijin ki
Showing 93001 words to 96000 words out of 280121 words