ta riƙa kunnensa ta ɗora goshinta saman nasa.

“Ai niban yarda zata gane kan ka ba, dan wata mace bata isa ta shigo gidana ta fini gane mijina ba, da dai Rashida ce da ita ba zan musa mata ba, saboda ta rigani saninka, ni kuma a yanzu na fi Amaryar ka sanin waye kai”

Murmushi yayi yana shafa bayanta da suka hannayensa biyu. Dauke kanta tayi daga nassa but stilll hannayenta na rike da kunnensa guda biyu.

“Wai ance ƙawar Rashida ce da gaske?”

Ya ɗaga mata kai yana wani lumshe idonsa da suka kaɗe.

“Uhnn amman ai ba ni nace ina son ta ba, Hajiya ce ta haɗa auren saboda ta yaba da tarbiyarta”

Ta yi murmushi kamar ba komai, alhalin na ciki na ciki.

“To Allah ya baku zama lafiya”

Sai ta saki kunnensa ta riƙa hannayensa dan tana jin yana ƙoƙarin wuce gona da iri, ta miƙe tsaye.

“Ina zaki?”

“Aiki zanje na ƙarasa”

Yayi saurin miƙa hannu ya riƙota.

“Haba karki zalince ni baiwar Allah”

“Ba wani zalinci, nima fa mai tsada ce kamar amarya, dan haka ni jiki zaka siya ba baki ba”

“Ai har kin fi amarya tsada, ke da ga wannan ciki, amman dai amin farashi mai sauƙi ta yadda zan iya biya”

“Ba yanzu zamu yi cininki ba, kai fa ango ne karka manta, nan da ƙarfe goma na dare sai yadda ka ga dama zaka yi da amaryarka”

“Bari wanka da kashi indan ganin hadari, ayi jiran abunda ba tabbas bayan ga ki ina gani”

Ta fisge hannunta ta nufi ƙofa.

“Ni kan nan gani na bari wannan wunin da daren ba nawa ba ne”

Ganin zata fice da gaske yasa shi wara ido, jikinsa a mace yace

“Wai da gaske kike yi? Ki taimaki bawon Allah, karki jefa rayuwarsa cikin haɗari”

“Au naka wasa ne kenan!”


Ta fice tana dariya kamar ba komai, sai dai can cikin zuciyarta ji take kamar an aza mata garwashin wuta a ciki, saboda kishi da baƙinciki. Tana ta ƙoƙarin yaƙar zuciyarta ne, dan bata son ta saka kanta cikin matsala saboda cikin dake jikinta, daman can lafiyar cikin be isheshi ba, idan kuma tace zata saka damuwa a ranta, to zata cutar da kanta ne kawai, tun dai aure an ɗaura, kuma tasan mijinta yana sonta, sai dai ɗan kishi da ba'a rasa ba.
Bayan fitarta, ta shiga bathroom ɗinsa yayi wanka, ya fito ya shirya cikin wata shaddar gizna mai kyau da sheƙi. Yana cikin saka agogon hannunsa Kalsoom ta shigo ɗakin ɗauke da plate ɗin abinci. Fried rice ce and pepper chicken sai ƙamshi take, kallo ɗaya yyi ma abincin ya ɗauke idonsa wai shi ala dole yana fushi da ita.

“Waya ce miki abincin zan ci? Ai ba yunwa na ke ji ba”

“Shikenan kuma ango sai yayi fushi ranar aurensa?”

“Waya ja nayi fushin? Sai ka taɓa abu a hanaka lasawa, ai wannan cin zalin ne”

Gwalo ta mishi taja ƙofar ta fice. Sai ta fashe da dariya.

“I love you”

Ya furta tana shirin zama ya ci abincin. Shi kansa be san yaji yunwa kamar haka ba sai yanzu, tass ya cinye abinci da da lemun kankana data haɗa masa mai lemun tsami ciki da sugar kaɗan, har ƙashin sai da ya taune ya tsotse ruwan, dan yaji daɗin abincin sosai, ga lemun da sanyi sai rmratsa ƙwaƙwalwarsa yake, bayan ya gama ya tashi yana hamdala. Tana shigowa ta saka masa ɗariya, har da riƙe ciki.

“Ni dai nasan mijin Amarya yana jin yunwa”

Shima dariyar kansa yake dan yasan yayi aiki.

“Ai ba ni na ci ba, aljanuna ne suka ci”

Matsawa yayi ya maita kiss a goshi.

“Amarya tace ta yafe miki daren nan na ta”

“Uhmmmm”

Ta wara ido.

“Wace sakaryar amaryace zata yarda ta yafe wannan daren mai tsada a rayuwar ko wacw ya mace, balle kuma da gwarzon namiji kamar ka”

Ya kalli kansa yana wani kaɗe shaddarsa.

“Allah? Ina jin daɗin yadda kike yaba ni”

“Ai ka haɗu ne Malam, dole a faɗa”

Ya riƙa fuskarta ransa fari ƙal da farinciki.

“I love you so so so very much”

Murmushi ta masa as respond, ya fice yana dariya. Sai ta ji tashin motarsa cire ɗankwalinta ta jefar, ta faɗa saman gadonsa ta fashe da kuka.


ASIM POV.

“Yes...!”

Ya bugi ganbun motarsa yana dariyar da har zuciyarsa ita ce.

“Kin biyani Mardiya, zan baki mamaki, kuma auren mu nan kusa nake sonsa ba sai nesa ba, dan haka daga yanzu ki shirya a ko yaushe zan iya zuwa gaishe da iyayenki, sannan na turo magabatana”

Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta 5ana dariya, sai tayi cikin gidansu da gudu kamar wata mai kunyar gaske.
Ya daɗe tsaye a gurin yana kallon ƙofar gidansu, sannan ya zaro wayarsa dake ringing ya kara a kunne.

“Na'am Hajiya kin dawo ne?”

Ban ji ma tace masa ba, sai kawai naga ya gyaɗa kai yana faɗin.

“Okay kina ina yanzu?”

Can kuma sai naga fuskarsa ta canja.

“Eh nasan gurin. Okay gani nan zuwa”


Ya sauke wayar kamar mai tunani. Can kuma ya ɗaga kafaɗunsa. Ya buɗe motarsa ya shiga.

Yana cikin driving ya kira ƙanen mahaifinsa dan jin yadda aka yi maganar gida.

“Eh yana da kyau sosai? Bedroom nawa ne a gidan? To ko dai mu bari sai an samu wani? Okay ba matsala”

Ya kashe wayar, sannan ya ƙara gudun motarsa, cikin ƴan mintuna ya isa unguwarsu Nably, a kusa da gidansu ya faka ya sake kiran Hajiya.

“Gani na ƙaraso unguwar, amman ban ganr gidan ba”

Daga ɗayan ɓangaren ta amsa masa.

“Baka ga wani green gate ba?”

“Na gani, Mai farin fenti”

“Eh to ka shigo ciki amman ka tsaya daga gate zan fito na kawo maka”

“Okay”

Ya tashi motarsa ya nufi gate ɗin gidan. Be ƙara gasgatarwa ba har sai da ya shiga harabar gidan, kusa da gate ya faka, yana ƙara kallon harabar gidan.

“Akwai bura'uba...”

Ya faɗa yana kallon Hajiya Sadiya wacce ta fito riƙe da ƙatuwar leda, sai faman sauri take kamar wacce ta yi sata.

“Ka saka min a wannan account ɗin”

Ya miƙa masa farar takarda tare da ledar dake hannunta. Cikin ladabi ya karɓa ya na faɗin

“Hajiya wannan ma gidanki ne?”

“Eh jeka dan Allah da sauri, bana son a tararda kai”

“Okay”

Ya koma cikin motar yana ta kallon gidan. He just can't believe gidan Hajiya ne, mi hakan yake nufi ita mahaifiyar Nably ce ko yar'uwarta.? Har ya bar gidan be samu amsar tambayarsa ba.


YASMEE POV.

Tana jin tsayawar motarsa ta tashi da sauri ta nufi kitchen, cox she dunno what to do, kuma tana jin kamar bata son ganinsa, duk da tana ƙoƙarin yaƙar zuciyarta dan sanin gaskiyar lamari. Hannayenta biyu tasa ta dafe fuskarta tana busar da iskar bakinta.

‘Ni fa lauya ce, ni nake fawa wasu magana, ni na saba bincike, dan me yau kuma zan rikice, i need to do this ko dan na cire kaina daga zargi’

A zuciyarta take wannan maganar, a fili kuma murmushi ne shimfiɗe a fuskarta ta juyo tana amsa kiran da yake mata.

“Yau wace rana baki je office ba ne?”

Yayi mata kiss.

“No naje yau cases biyu ne kawai da ni, ina gamawa na dawo, ya aikin naka?”

“Alhamdullah, ina da labari mai dadi, Abbah (Baban Namra) ya buɗa mana wani sabon kamfani a Abuja, kuma nasan niɓe zan kula da shi”

“Wow amman Abbah ya kyauta mana, Allah yasa hannu a ciki, ko shi yasa aka aiko maka da wasiƙa? Ɗazun an kawo wasiƙa a aje maka”

“Waya kawo”

“Wallahi ban sanshi ba, tana nan ɗakinka na aje maka”

Freezer ya buɗe ya ɗauki gorar ruwa ya nufi ƙofar fita yana tambayar abunda aka dafa. Da kallo Yasmin ta bishi bayan ta bashi amsa idonta cike da ƙwalla.

“Allah ka sani ina son mijina, Allah karka tabbatar da zargina akan sa”

Ta share hawayen da suka zubo mata. Tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo riƙe da wasiƙar hankalinsa tashe.

“Kin karanta wasiƙar nan Yasmin?”

“A'ah miya faru?”

Ba komai, ya juya ya fita da sauri. Sai da ta tabbatar ya shige ɗakinsa sannan ta rufa masa baya. A bathroom ɗin falo ta tsaya ta sakama ƙafafunta ruwa gudun kar yaji sawun takun ƙafarta. A bakin ƙofar ɗakinta ta kara kunnenta, sai dai bata ji alamar motsinsa a cikin ɗakin ba. A hankali ta tura ƙofar ɗakin daman be mata rufin ƙwarai ba, nan ma babu alamunsa har toilet ɗinsa taje ya leƙa bata ga kowa ba. Mamaki ne ya kamata ina yaje,da sauri ta juyo ta fito. Har zata shiga ɗakinta, sai kuma ta nufi gurin engine ɗin wankinta. Daga inda take tsaye ta hangosa yana waya, daga gani ba wayar aiziki bace yake, dan yadda yake jinjiga jikinsa yake safa da marya na ya nuna haka. Yana gama wayar ya juyo yana faɗin.

“Namra bata zame min matsala ba ke zaki zame min, babu wanda ya isa ya datsa min rayuwar jindaɗi wallahi”

Karaf idonsa cikin na Yasmin, dake tsaye gafen ƙofa.


THE GAME IS ABOUT TO START...😿
_____________________________________


I feel much better Alhamdulillah. Na gode sosai da addu'ah da kulawa, Allah ya bar zumunci. Jazakallahu khairan all 😘
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *74*

Ko parking ɗin kirkir bata yi ba a gidansu Teema ta fita Motarta, zuciyarta na bugun bugawa, taron mutanen da tara a gidan ya ƙara tabbatar mata da maganar Asmee da kuma Momi.

Teema na hangota ta tashi daga cikin mutanen da take ta nufi wani ɗakin wanda babu kowa a cikinsa.
Kai tsaye Rashida ta bita daman ta ga shigowarta, wasu daga cikin ƙawayen Teema har sun fara magana, dan wasun su sun san mijin Rashida ne zata aura, wasu kuma a yanzu suke samun labari, ganin yadda ta shigo cikin gidan a birkice.
Da wani irin ƙarfi Rashida ta banki ƙofar ɗakin da Teema take ta shiga hasale.
 
“Marar mutumci wacce bata gaji arziki ba, ni zaki yiwa ha'inci? Ki zagaya ta bayan idona ki ci dunduniyata”

Hannayenta biyu Teema ta kama ta riƙe tana hawaye.

“Dan Allah ki saurare ni, karki yanke min hukumci ba tare da kin saurare izuri na ba...”

Rashida ta fisge hannunsa tana mata wani kallo na uku saura kwata, kamin ta katsa mata tsawa kamar wata ƴarta.

“Babu wani daɗin baki da zaka min, macuciya wai tsabar rashin kunya ni zaki ciwa amana..”

“Ban ci amanarki ba Rashida ko kowa ya zarge ni ke be kamata ki mun haka ba, ni kaina ban san da wannan haɗin ba, dan be taɓa zuwa fira gurina ba sai da zai kawo min iv, su Hajiya ne suka haɗa komai”

Ta ƙarasa da kuka tana wani ƙara narkewa kamar gaske. Rashida ta watsa mata wani kallo.

“Ke kar nake kallon ki, kamar naira a hannun yaro, yadda kika yi boka haka na yi karki nemi raina min hankali, wallahi mafitarki ɗaya ki fasa auren nan ko kuma na ci uwarki”

Teema ta yi wani Shu'umin murmushi tana kawardar hawayen ƙarya dake fuskarta.

“Idan kuma ba ki ci uwata ba, ni sai na ci ubanki, da aka halitto Hilal an ce miki ke kaɗai zaki aure shi ne? Ke in ban da haukarki ma miye na kishi bayan ya sake ki da ya kama ki da wani ƙato ko kin ɗauka ba'asan abunda ya fitar da ke gidan Hilal ba? Kina ganin kamar ba san komai a rayuwarki ba ko? To malamin dana kai ki gunsa, shi ya faɗa min komai a kan ki”

Jikin Rashida yayi sanyi har tana sassauta murƴarta duk da tana cikin zafin rai ne.

“Yayi dai-dai kuma ina fatar ya duba miki ya faɗa miki igiyar aure ba zata taɓa shiga tsakanin ki da Mijina ba, dan Wallahi sai na rusa wannan auren ko ta yaya, dan babu yadda za'ayi yar iska irin ki ta tarbiyantar min da yara, sai na faɗawa Hilal irin matar da zai aura”

“Yar iska kamar uwarsu ko? Ai abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, kuma idan baki rusa auren nan ba, baki haihu ga uwarki da ubanki ba, ai Hilal ba mijin ki bane mijin Kalsoom ne da Angon Teema, ƴar baƙin asiri kinje kin yi ma kiahiya ya dawo kan ki kin kashe ɗan ki da hannunki, Ni ko nafi ƙarfin ki gaba ɗaya ke da danginki, kuma wallahi duk kika kuskura sake saka baki a maganar auren nan sai na faɗawa duniya dalilin mutuwar auren ki, da kuma dalilin mutiwar ɗan ki, ga kuma cutar da take tare da ke, dole har ƴaran ki su gujeki, ko kin ɗauka ba a san dalilin korarki da ubanki yayi ba?”

Gaba ɗaya jikin Rashida ya gama sanyi, zafafan kalaman da Teema tayi masa sun ƙatse mata duk wani hanzari da take da shi, har ta samu kanta da nauyin baki kasa furta mata komai, abun ka da mai sauri karaya nan da nan sai ta fara hawaye.

“Kin fi kowa sanin yadda na ke son mijina Teema, amman kika min zagon ƙasa har kika ja hankalinsa akan ki, waya sani ko asiri kika masa?”

Teema ta yi ƴar dariya.

“Wallahi ban masa magani ba, uwarsa cw da haɗa mu, kuma yaga yana so na, nima ina sonsa shikenan fa, amman ki kwantar da hankalinki zan ƙwatar miki ƴancin ki, kuma zan miki hanyar da zaki dawo gurin mijinki”

“Allah ya isa tsakanina da ke, kin ci amana ta kin min zagon ƙasa Teema wallahi ba zan taɓa yafe miki ba”

Tana kaiwa nan ta juya ta fice fuskarta da hawaye.
Wani banzan tsaki Teema taja.

“Aikin banza ai daman Allah ishenshe ne, kinji na roƙe ki ki yafe min ne, ni wallahi ko ubanki yayi min aurensa zan balle wani mijin ki ex-husband mtssssssss”

Rashida ya fito ɗakin idon kowa yana kanta, wasu na Teema rashin gaskiya wasu kuma suna ganin bata yi laifi ba, daman yanzu ko mijin ƙawarki ne aure shi za'ayi balle ita da har ta fita gidan miji. Bama kamar hawayen da suka gani a fuskarta. Ita kam ba ta nasu take ba, haka ta fito abunda yake ranta ya isheta, damuwarta tayi mata yawa.

Har ta shiga motarta ta fara driving bata da wani kuzari, hawayen da take kuma sun ƙi su tsaya mata. Wayarta da ke front seat ta yi ƙara alamar kira, kallo ɗaya ta yi ma wayar ta ɗauke kanta tana cigaba da rera kukan da bata san ranar tsayawar hawayenta ba, Alh Bashir ne, tasan shi ma ba zai wuce ya labarta mata Hilal zai auri ƙawarta ba, ita mamakinta ma ko Hilal ya manta Teema ƙawarta ce? Tsayawa tayi tunanin duk da tasan bata da ƙawaye barka tai hakan amman ba zai rasa sanin Teema ba, wata ƙila yayi mata haka ne dan ya rama abunda ta yi masa. Haka zuciyarta take nuna mata, cikin sauri ta ɗauki wayar ta faka gefen ti-ti, tana tunanin abunda zata faɗawa Hilal, da kiransa zata yi, sai kuma wata zuciyar ta bafa shawarar aika mata da saƙo. Sannan ta jefar da wayar ta cigaba da tuƙinta tana kuka har ta iso gida.
  Ga wayar sai ringing take, friends har da waƴanda suka daɗe basu kira ta ba, yau kiranta suke dan su ji ƙwan. Bata samu gurin faka motarta ba, saboda Motar Ummu Faisak da ke waje ta tare nata hanyar gareji, daman can gidan ba wani yarwantaccen gida ne ba, gida ne na zaman mutun ɗaya.

  Ba ta damu da share hawayen fuskarta ba ta shiga falon a haka. Ganin Momi da Ummu Faisak yasa ta ƙara narkewa ta fashe da kuka har da faɗuwa saman kujera. Nan take Ummu Faisak tasa kuka ganin yar'uwarta cikin damuwa. Momi kan tsawa ta katsa musu daga ita har Ummu Faisak ɗin.

“Miye abun kuka ga hukuncin Ubangiji? Ba ke kika jawa kan ki ba? Ai kin yi arziki da sai da kika fita gidan miji ita zata shiga, kuma ba ƴar'uwarki ce ta ci amanar ki ba! Ai ke kika fara yi ma kan ki zagon ƙasa da kan ki, kika taka mutumcin aurenki kika je kika bada kan ki ga wanda ba muharramin ki ba, ke wannan ma be isheki ishara ba? Cutar da take jikin ki bata isa ta nuna miki Allah ɗaya ne ba? Ai cin amanar miji Rashida ba ƙaramin haƙƙi ba ne, mijina yana can yana fafutar neman abunda zai kawo miki ke da ƴaƴansa, amman ke kina can kina cin amanarsa? Aiki hauka ne? Nasan 95% mahaifinki ne ya ja miki shi da ya tsaya kai da fata akan sai kin yi aiki, amman be ce kije can ki yi lalata ba, ai ba ke kaɗai ce mace ma'aikaciya ba, akwai da yawa waɗanda suke kare mutuncin mazan su da kuma na ƴaƴansu da na su da na iyayensu, ba ga ƴar'uwarki nan ba? Ummu Faisak aiki take, ita bata lalace ba saboda ta san mutuncin kanta, ki ba abun baƙin cikin ki ba ne ace wani namiji wanda ba mijin ki ba ya san surar jikin ki? Kin ɗauki rayuwar turawa kin sawa kan ki, baki da lokacin tarbiyantar da ƴaƴanki, tufafi ko sai waƴanda kika ga dama kike sakawa, nan aka auro miki Kalsoom na zo ina yaba shigar da take irin tarbiyar da ta samu a gidansu, kika ce min na fi son ta, da ke, kika ce  ina miki abu kamar ba ni na haife ki ba, a lokacin ruɗin duniya na ke guje miki amman idon ki ya rufe.

Dan baki da hankali zaki wanke ƙafafu kije gidansu Teema to ki ce mata me? Ki zauna ki yi wa kan ki karantun ta natsu, ki nemi yafiyar ubangijinki, kuma ki nemi yafiyar mijinki tun haƙƙinsa be cigaba da binki ba, dan duk abunda kika aikata da aurensa haƙƙinsa yana saman kan ki, kin yi sa'ah da Allah ya rufa miki asiri tun wuri, dan duk mai cin amanar mijinta sai taga ishara wallahi ko ba daɗe ko ba jima, kiyi taka tsantsan da duniya Rashida dan ta fara barinki tun kamin ke ki barta, karki yarda ki ci amanar wani, ƙara ke a ci amanar ki, balle kuma miji. Tashi muje”

Momi ta ƙarasa tare da kallon Ummu dake gefenta, kana ta miƙe tsaye idonta cike da ƙwallah, ranta kuma a ɓace ta fice, Ummu Faisak ta rufa mata baya tana cigaba da hawaye.

Hannu Rashida ta ɗora saman kai, tana kallon ɗakin kamar sabuwar mahaukaciya.

“Innalillahi Allah kasa mafarki na ke yi, Allah ka farkar da ni daga wannan mummunan bachi, Allah ka farkar da ni Allah, Allah ka tashe ni...”

Ta rushe da wani irin kuka tana dafe da kanta da take jin
Showing 201001 words to 204000 words out of 280121 words