ɗa na, ko be faɗa miki yayi raped ɗa na ba? Idan be faɗa miki ba to yau ki sani, kuma dalilin zuwa na a nan saboda ina son na karɓi takardata ne, idan kuma be shirya sakina ba ni na shirƴa kai shi kotu”

Yasmin na maganar hawaye na zuba a idonta, hannu Umma tasa ta rufe baki tana kallon Uzair, furucin da Yasmin ta yi a yanzu yayi nauyi, sai dai ta fahimci gaskiya Yasmin ta faɗa tun da ya kasa ƙaryatata har ma ya sadda kansa ƙasa yana hawaye.
Yasmin ta kalleshi tana share hawayenta

“Ka daina yaudarar kanka da sunan wani yayi maka asiri, mugun abunda kake aikatawa ne ya kama ka, kuma Allah ya yanke maka wahala komai ya zo maka da sauƙi, da ace kana da lafiyarka wallahi da ko wace jarida sai ta buga hoto na da naka, dan sai na bawa duniya mamaki da kai mijina kuma uban ƴaƴana kotu, kuma ko yanzu ka taki sa'ah ne mahaifiyata ta hana ni, amman idan har shiga kotu kake so ka yi ƙoƙarin yin jayayya da ni akan aurena...!”

Juyawa ta yi ta fice tana kuka. Ajiyar Zuciya Umma ta sauke cikin muryar kuka ta ce

“Abun naka har ya ɓace Uzairu, wannan ba halina ba ne kuma ba halin Baban ka ba ne, ban san inda ka ɗauko wannan rayuwarba, yanzu a ce har ɗan cikin ka zaka aikatawa wannan abu? Ko a masu yi ƙoƙarin kare iyalinsu suke kada su faɗa wannan halaka balle kuma har su saka su da kansu, abun da naki ji a redio yau a gidana zai faru? Na yi tunanin ko zafi ciwo ne yasa ka faɗar haka a baya ashe dai da gaske ne, Uzairu baka kyautawa kan ka ba”

Ta rufe fuska tana kuka. Shi kan hawaye yake sai a yanzu yake ayyana zancen Allah na cewar cikin matan ku maƙiyanku, a cikin ƴaƴanku akwai maƙiyanku, ji yake kamar ma shi aka saukarwa ayar dan tsanar da Yasmin ke nuna masa ta yi yawa.

Wasa-wasa abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa magani yake amman babu sauƙi, haka ya kwashe wata shida a asibitin sannan aka sallamoshi ya dawo gida gurin Umma. Daman tun a asibiti aka siya masa keken guragu yana tura kansa a ciki duk lokacin da wani abun uzuri ya same shi ko kuma yayi sha'awar fita waje.

Ranar da Yasmin ta samu labarin ya dawo gida, ta samu Mahaifiyarta a falo akan maganar shigar da shi kotu tun da har yanzi ya kasa aiko mata da takardarta.

“Wai ke Yasmin wace irin zuciya ce da ke haka? Ke bakya ganin tausayinsa ne? Ki duba halin da yaron nan yake ciki wannan kawai be isa ya saka ki barshi da Allah ba, ai da Allah ya tashi kama shi sai ya kama shi ta wannan hanyar da babu wanda ya isa yai masa magani sai shi, ko ba komai fa Uzair ɗan'uwanki ne Yasmin ya kamata ki riƙa tausayinsa, sannan uban ƴaƴanki ne, ko ƙin ki ko kin so kin riga kin haihu da shi, nan gaba kina tunanin yaransa zasu ji daɗi idan suka samu labarin abunda kika yi ma Ubansu?”

Fashewa ta yi da kuka

“Idan na fita wani lokacin har nuna ni ake, na rikice gaba ɗaya yanzu ko gurin aiki ba komai nake ganewa ba, so nake ya sake ni ko na samu sukuni na natsu”

“Damuwace kika sawa ranki, bayan kuma be kamata ya dame ki, tun da ba ke kika ƙaddarawa kanki wannan rayuwar ba, focus on your journey ki cire komai a rankiz ina nan ina miki addu'a da sannu komai zai wuce”

Tashi tayi ta shige ɗaki tana kuka.


NAMRA POV.

Satin Hajiya Barau biyu ta Abbah ya dawo da ita saboda haƙuri da ake bata da kuma ganin idon ƴaƴanta, ita kanta yanzu ta saduda dan satan bata kyauta ba, duk abunda take tana yi ne dan kishin Anty Amarya tana ganin kamar Abbah yafi sonta da ita.
Ga kuma ƴaƴanta da suka sata gaba suka nuna mata rashin jindaɗinsu, ko ba komai dai ya ga ishara a zmfitowar da ƴarta tayi wato Zinatu, yanzu ba Namra ba ce kawai take zawarci a gidan har da ƴarta da uwar miji ta hanawa zama.

***
Anty Amarya na kallonta ta yi murmushi.

“Wannan shaddar duk tsadarta Lamido zaki bawa?”

Ta gyaɗa kai tana murmushi.

“Lallai ana jin Lamido nan, kar fa ya karɓe min faɗar ɗa”

Dariya ta yi wannan yaron tana shafa shaddar.

“Anty kina jin ɗan nan na ki”

“Ai bana da kamar sa ne Namra, kema kuma idan ba kin yi butulci ba baki da kamarsa, abubuwan da kike masa basa min daɗi, yaron nan yana son ki wallahi, kin san yafi ƙarfin wulaƙanci idan ba ke ba babu wacce ta isa ta wulaƙanta namiji kamar Abdallah”

“Ba wulaƙanci ba ne Anty, ni rayuwarsa ce bana so, ya cika zafin kishi, kuma bana jindaɗin abunda yake ma Lamido”

“Ai naji mahaifinki yana zancen sama masa aiki dan yace ya kusa barin driving ɗin ki”

“Saboda me?”

“Nima be faɗa min ba”

Ta faɗa fuskarta da Murmushi. Namra ta baro gurin da take zaune ta zauna kusa da Anty.

“Dan Allah Anty ki faɗa min”

“To aure zai miki”

“Anty Aure yanzu? Ni gaskiya ban shirya ba, halin mazan zamanin nan duk yaushe na fita daga wannan rayuwar kuma za a ce na sake wani”

“Toh sai ki tashi ki faɗawa Mahaifinki ai yana part ɗinsa”

Ta yi saurin rufe baki tana dariya, sai ta tashi ta ɗauki shaddar ta fice. Murmushi Anty Amarya ta yi tana unƙurin tashi ta nufi part ɗin Abbah.

Yau weekend ce daman babu aiki kuma babu wani taro ko wani abun da zai fitar da Abbah, dan haka yana part ɗinsa yana hutawa. Da sallama ta shiga, ya amsa mata yana kallon labaran bbc. Plate ɗin dake kusa da shi da ɗauke ta aje ƙasa ta zauna bakinta ƙumshe da murmushi.

“Yanzu na ke shirin kiranki”

“To Allah yasa samu ne”

“Samu ne kan, ɗana nake nemawa auren ƴarki idan kun aminci”

“Ai Abdool ɗana ne ba ɗan ka ba, ni ya kamata na nema masa aure”

Dariya Abbah yayi yace

“Amman miya hana ya biyo ta gefen ki? Ko dai ƴarki bata son sa ne? Bana son na sake mata wani zaɓin ne wanda ba shi ranta yake so ba, kar a sake samun matsala”

“Ba wata matsala, yanzu haka maganar da na gama da ita kenan”

“Toh Allah ya shige mana gaba, amman zan so jin ta bakin Namra”

“Ai gaka gata, waya isa ya shiga tsakanin uba da ƴa?”

Anty Amarya ta faɗa tana dariya.


*** *** ***

Kai ya girgiza mata alamar ba zai karɓa ba.

“Ba dan ki bani abu na zo gidanku ba”

“Ni ma na sani shiyasa na siya maka wannan shaddar, da wata manufa na yi ba”

“Na sani na gode?”

“Ba zaka karɓa ba kenan?”

“Gaskiya bana so”

Miƙewa ta yi tsaye ciki da jin haushin ƙin karɓar da yayi ta baro garden ɗin. Ko da ta shigo falo wayarta dake kan kujera tana ringing cikin sauri ta kai hannu ta ɗauka, Abdool ne rubuce a screen ɗin wayar. Tsayawa tayi kallon wayar sannan ta danna picking ta kara a kunne.

“Abnam gani kan hanya?”

“Ba zaka daina yi min zuwan ba zata ba ko?”

“Zan daina daga ranar da kika zama mallakina”

“Allah ya kawo ka lafiya”

“Amin Sweet Abnam thank you”

Shi kanshi baya son zuwan ba zata da yake mata, sai dai yana yin hakan ne dan ya riski Lamido gani yake kamar ya tare masa komai ƙara dai ya riƙa masa ba zata yadda zai riƙa fahimtar alaƙar dake tsakaninsu.

Kitchen ta shiga ta sarrafa masa abu mai sauƙi sannan ta haɗa masa fruit salad dan ta fahimci yana son sa sosai. Sai kuma ta shiga ta yi wanka ta saka abaya da jan mayafi. Tana jin lokacin da mota ta shigo harabar gidan kuma zuciyarta ta ayyana mata shi ne, amman saboda ƙarfin hali ta ƙi ta fita ta tarbe shi, har sai da ya buga ƙofar falon.

Turare ta ɗauka ta feshe jikinta sannan ta fito falo taje ta buɗe masa ƙofar, jinginawa yayi yana kallonta fuskarsa sa annuri, sai dai hakan be ma murmushinsa damar fitowa ba.
Yadda ƴake kallonta ta yi zaton zai ce mata tayi kyaune kamar yadda ya saba sai kawai taji ya ce.

“Ina Anty?”

“Tana ciki, ka shigo mana”

“No ba sai na shigo ba, ai baki bukatar ganina”

“Nace maka? Abdool miyasa kake irin wannan maganar ne? Sai kace wata maƙiyiyarka kace bana son ganinka”

Ya wara ido.

“Wasa nake miki fa, ai nasan ni kika yi wa wannan kwaliyar”

Sai kuma ta ji kunya.

“Zaka shigo ko part ɗin Abbah zaka je”

“Cikin wata tara kin zama wata babbar mace”

Ya salam. Ta juya ya bar masa jikin ƙofar, sai kawai yayi murmushi ya shigo. Daman gidan ba baƙonsa bane sai dai duk lokacin da zai zo Abbah ne kawai yake sanin shigowarsa garin. Kasa sakewa Namra ta yi haka take duk lokacin da ya shigo part ɗin shi kuma sai ya bi ya tsare ta da ido duk wani motsi nata yana idonsa.

Fruit salad ta fara kawo masa da ruwa sai kuma pineapple juice da ta haɗa masa. Gabanta sai faɗuwa yake kar Anty ta tararda su, tana jin kunyar Anty ta ganta da Abdool sosai.

“Gaskiya na yi sa'a, Matata ga iya abinci ga iya kwalliya ga haƙuri da kawaici”

Ƙasa ta yi da kanta tana murmushi, this is not the first time da yake yaba girkinta a duk lokacin da ta girka masa wani abu.

Kamar munafuka haka take satar kallonsa, yana mata kyau yau fiye da ko yaushe, ga wani ƙyalli da fuskarsa take.

Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dukan su suka kalli wayar, ita sam ta ma manta da wayarta tana saman kujera dan tun da tayi waya da shi ta aje ta a gurin. Hannu ya kai ya ɗauka.

“Waye Dr Faruk?”

“Likita na ne”

Ido ya sakar mata kamar be yarda da maganarta ba, kuma yaƙi ta bata wayar sai ringing take.

“Me zai sa ya kira ki yanzu? Baki da lafiya ne?”

Kasa amsa mashi ta yi. A take yanyinsa ya canja sai kawai ya miƙe tsaye ya aje mata wayar ya fice, zuciyarsa na masa mugun zafi.


AMIRA POV.

Kullum cikin ɗaki ta wuni duk tabi ta takura kanta, akan abunda ta san har a bada ba zai taɓa zama nata ba, babu yadda Ammy bata yi akan ta riƙa fita tana shan iska amman ina, har ta gaji yanzu ta saka mata ido sai kuma addu'ah da take mata.

Cikin rashin ƙwarin jiki ta fito ta daga ɗakinta ta haɗawa kanta tea, bayan ta haɗa tea ta zauna a falo, saboda ta samu falon babu kowa a ciki sai tv dake ta aikinsa.

Ƙofar falon aka turo aka shigo, mai gadinsu ne, hannunshi riƙe da wasiƙa, sai da kai ƙasa sannan ya miƙa mata takardar.

“Gashi inji wasu mutane suka ce a baki”

“Su waye?”

“Wlh nima ban sani ba, cikin mota suke kuma sun tafi”

Hannu ta kai ta karɓa, shi kuma ya tashi ya fice, sai da ya fita sannan ta warware takardar ta fara karantawa...


ASIM POV.

Yanzu tsawon wata tara kenan ana abu ɗaya, a duk lokacin da ya gina gida da sunan Mardiya sai gidan ya ƙone, idan ya kama haya ma abu ɗaya ne, tun lokacin da aka ɗaura auren ta gagara tarewa sai dai su kwana a hotel ko kuma gidan abokai, dan ko lokacin da aka ɗaura auren hotel ya kama mata, baya jin zafi cire kuɗi ya gina mata gida ko ya zuba mata dukiya amman ta kasa mararta saboda yawan gobara da take. Ita kanta yanzu abun yana damunta sosai, musamman da ta samu labarin Asim yana neman auren ƴar masu kuɗi, tasan babu namijin da zai juri zama da ita tana gora dole ko wanene ya nemin ƙarin aure, ga mafarkin wutar da take har yanzu bata daina ba, lallai haƙoƙan mutane da yasa yana kanta, domim ba Namra ce kawai ta taɓa cuta ba, mutane da tayi ma cuta suna da yawa ga satar da tayi ta yi, ga kuma yawan banza data ɗaukarwa kanta. Shi kansa Asim sai yanzi ƴake gane yayi zaɓen tumun dare, dan duk ƙyalƙyalin da yake hangowa sai ya tarar na ɗan maciji ne, be same ta a budurwa ba, kuma daman be aureta dan Allah ba, auren sha'awa yayi mata daga lokacin da ya kai ga jikinta sai duk da fita ranshi daman yanzu ba maxe ba burgeshi take ba, wannan ma da zai aureta dan kawai kariyar kai ne, kuma yana son ganin shi wutar take bi ko Mardiya.

Babu irin neman taimakon da ba ayi ba akan wannan matsalar, wani gurin ace aiki ne aka mata wasu kuma su ce iska ne yake mata, tana zuba kuɗi da yawa dan ganin ko za a dace amman babu wani sauƙi sai abunda ya cigaba.

A unguwa kuma sai gulma ake mata kowa da irin abunda yake faɗa, waɗanda suka san halinta suce amanace ciki har da masu cewa ai taci amanar Namra tun da ta aure mata miji....
[7/22, 10:00 PM] Khadeeja Candy♥: *87*

NAMRA POV.

Shiru-shiru bata ga Abdool ya dawo ba, hakan ya tabbatar mata da fushi yayi. Miƙewa tayi tsaye ta fita sai ta hangoshi jikin motarsa yana kallon ƙofar falon. Ƙarasa tayi cikin wani taku mai jan hankali da ƙasaita, ta rumgume hannayenta tana kallonshi.

“Ina da matsalar mahaifa ne Abdallah, ciki baya iya tsayawa tun ina gidan Asim, wannan matsalar ce tasa Dr Faruk ke kula da lafiyata”

Uffan be ce mata ba, sai kawai ya kawardar fuskarsa yana kallon part ɗin Abbah.

“Abdallah...”

“Abnam...”

Ya kira sunanta kamar yadda ta kira nashi, still be kalleta ba.

“Baka yarda da ni ba ko?”

“Babu rashin yarda a tsakani na da ke, sai dai zai fi idan muka bar maganar nan”

Murmushi tayi ta juya koma ciki. Haka ya tsaya a gurin har sai da yaji ya samu sassauci a zuciyarsa sannan ya nufi part ɗin Abbah. A falo ya samu Abbah daman yasan da zuwansa sun samu awa ɗaya suna tattauna akan rayuwa da abubuwan duniya sam ba zaka ce Abdallah ne yake neman auren ƴar Abbah ba, sam ba zaka ce surukinsa ba ne.


*ONE MONTHS LATER...*

Har yanzu jikinsa na nan a yadda yake, Umma yanzu na hausa take nema masa wai ko Allah zaisa a dace.
Bayan ya gama shan magani ya turo kekensa ya fito harabar gidan. Wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ya ciro ya kira Tahir.

“Bros ya ne, ya jikin naka ne?”

“Alhamdullah, ya aiki?”

“Mun gode Allah”

“Tahir tun ranar baka sake ce mun komai, ko baka kai mata ba ne?”

“Wallahi na kai mata, sai dai ban ji wata magana daga gareta ba, Uzair ina son na.baka shawara akan rayuwa, ka yi haƙuri ka rumgumi ƙaddara, wannan abun da ka gani na ishi kowa ishara ni kaina wannan ciwon naka yasa na zubar da duk wata muguwar da nake da ita, ba kai kaɗai ba, yawancin duk mai aikata irin wannan matsalar ce take faɗa musu, ka duba lamarinka Uzair ba haɗarin mota ka yi ba, ba kuma faɗowa kayi daga wani guri ba, haka kawai rana tsaka ance ka kamu da irin wannan ciwon, ita kanta Amira yanzu ta kanta take balle ka zargeta da aikata maka wani mummunan abu”

Tun da Tahir ya fara masa maganar jikinsa yayi sanyi, be san lokacin da hawaye suka zubo masa ba, lallai maso rai wawa, haƙiƙa yanzu Tahir ya lurar da shi abunda be kasa ganewa.

“Na gode”

Shine kawai abunda ya faɗa ya katse kiran. Hawaye na cigaba da masa zuba, tabbas wannan kawai ya isheshi ishara, a yanzu idan ba Mahaifiyarsa babu kowa a tare da shi, zai barwa ɗansa mumman tahirin da ba zai taɓa goguwa ba har a bada.

Kekenshi ya tura ya koma cikin falon, ƙanensa na zaune sai sha'aninsu suke ko kula da shi basu yi haka ya tura kansa ya shiga ɗakin da aka ware masa ya zamo kamar nasa. Farar takadarda da ya gani a saman gadonshi ya kai hannu ya ɗauka.

Sammaci ne daga kotun high court, ganin sunan Yasmin yasa shi murmushin da ya fi kuka ciwo, sannan ya sake tura kekena ya fito falon yana tambayar wanda ya kai masa wasiƙar.

“Ɗazu ne kana shan magani aka kawo, na shiga ban ganka ba shine na aje saman gadonka”

Ƙaramar ƙanwarsa ta faɗa. Sai kawai ya kaɗa keken ya nufi ɗakin Umma.



***

Hankalin Mai Martaba ya kwanta yanzu, har ma da na Ummi. Ganin an tsayarda magana, ranar da Mai Martaba ya aika aka yi maganar aure har da sadaka sai da yayi. Sai dai tun daga lokacin magana ta riƙa zuwa tana dawowa akan Abdallah zai auri bazawara, abun mamaki ne mutun kamar Abdallah ace zai auri bazawara kuma ɗan Sarkin Ƙatsina, wanda hakan sam be yi ma Mai Martaba daɗi ba, sai dai ya kan zuciyarsa nesa domin kawai ya farantawa ɗansa, domin yasan Annabi ma ya auri bazawara kuma yana sauranyinsa.

Ita kanta Ummi tana shan magana akan aure wasu su ce kar ta barshi wasu kuma su ce kamata yayi ya haɗa biyu. Sai dai duk wannan maganganun da ake be taɓa zuwa kunnen Abdool ba, ko da wasa ƴan'uwa da abokai basu taɓa masa wannan maganar ba, saboda sun san waye Abdool idan yana yin abu yana yi ne no matter what, ao faɗa mishi irin wannan maganar zai sa ya ɓata da kai ne kawai, ko kuma kai ma ya faɗa maka marar daɗi, sai dai abokai sun ka zolayeshi cikin wasa. Babu abunda yayi masa daɗi kamar auren da Abbah be yarda aka saka nesa ba, shi kansa da ansaka auren nesa zai roƙa a rage ne, domin ya matsu ya ɗauke Namra daga gidan. Ta ɓamgare ɗaya me yake jin zai iya zame masa matsala karatunta da take yanzu.



NAMRA POV...

Babu inda zance baikon Namra be kai ba cikin garin Sokoto da kewaye, a social media kan ba zaka iya lissafawa ba, babu abunda zai baka mamaki kamar ace bazawara ce aka yi ma wannan kayan, kuma duk da sunan an gani ana so abunda aka san budurwa ake yiwa. Kayan ƙwalah da maƙulashe ba
Showing 246001 words to 249000 words out of 280121 words