cikin ɗaurin ɗankwali Anty Amarya ta shigo.
Ta jidaɗin ganin abincin da Hajiya Barau ta kawo ma Namra sosai, hakan ba ƙaranin faranta ranta yayi ba.

“Ai baki ma ci komai ba”

“Na riga na ƙoshi”

“Namra baki son cin abinci, wannan ma baki ci da yawa ba, gaskiya dole muje asibiti a duba lafiyarki, zan je na gyara sai kije ki gaida Abbah ki”

“Tau”

Ta amsa murya ƙasa-ƙasa tana jin kamar dai kar taje. Ɗankwalin ta aje ta ɗauki hijabin Anty ta saka ta nufi part ɗin Abbah tana wata tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.

da Sallama ta shiga sai ta tsaya can bakin ƙofa ta risina ƙasa ta gaishe shi, kanta na ƙasa tana mai jin kunyar haɗa ido da shi.

“Abbah ina kwana? An tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau”

Sai kuma ta rasa me zata sake ce masa.

“Mahaifiyarki ta faɗa miki sati ɗaya na yarda ki yi ko? Dan kin san na gargaɗe karki kuskura dako min gida da sunan fushi ko saki”

Idonta ya cika da hawaye, a take muryarta ta soma rawa.

“Abbah ba fushi na yi ba, na zo ganin gida ne”

“Ko minene dai na faɗa miki duk kika doso min gida da sunan saki, to sai dai mahaifiyarki ta tattara kayanta ku bar min gida, tun da kin zaɓi zama da shi sama da Mahaifin ki sai kije can ku ƙarata”

Da sauri ta ɗago kai ta kalli Abbah, sam bata yi tunanin abun nasa ya kai har haka ba.

“Inshallah haka ba zai faru ba Abbah, amman dan Allah ka yafe min kuma ka fahimce ni”

Da hannu ya yi mata alama da ta tashi ta bashi guri. Da sauri ta tashi ta fice tana kuka. Kamin ta ƙarasa part ɗin Anty Amarya ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta shiga.
Lokacin Anty Amarya ta fito daga wanka tana cikin shiryawa, falo Namra ta koma ta zauna sai da Anty Amarya ta gama shirinta ta ɗauko jakarta ta fito suka fita tare.
Driver Abbah ne ya kai su asibiti, sun yi sa'ar ganin likita dan tun kamin su isa Anty ta kaira likitan dake duba su ta faɗa masa, sai yayi ma wata likita magana dan shi be shigo asibitin ba a lokacin.

Mutum biyu aka duba kamin ita, sannan ta shiga tare da Amarya. Bata ɓoye komai ba da taji tayi ma likitar bayani, ita kuma sai ta rubuta mata text ɗin jini da na fitsari, sannan ta tura gurin hoto, dan akwai buƙatar su ga abunda yake ƙasan mararta da take ji yayi mata tsaye gefe ɗaya.

Basu bar Asibitin ba sai da suka je aka musu hoton, aka basu sai suka wuce gurin ɗibar jini aka ɗibi jininta sannan suka bata wani roba ta shiga banɗakin gurin tayi fitsari ta kawo musu, sai suka je sai gobe ta zo ta karɓi results, daga suka koma gurin likitar suka kai mata result ɗin.

“Subhanallahi”

Ta faɗa lokacin da ta kalli hotonnan guda uku da suke guri ɗaya, sannan ta kalli Namra ta ce

“Me kika sha na zubar da ciki?”

Ba Namra har Anty Amarya sai da gabanta ya faɗi.

“Ban sha komai ba”

“Kin yi ɓari amman ko?”

Ta ɗaga mata kai

“Eh na yi”

“Amman ba kije asibiti ba?”

“Na je sai dai ban tsaya ba, saboda lokacin mijina be da lafiya”

“Kin yi kuskure gaskiya, da kin tsaya an duba ki ai, yanzu kin ga rabin cikin yana cikin mahaifarki, hakan ya haddasa miki wannan ciwon da kike ji, mahaifarki ta saki sosai har wani ɓangare na jikin mahaifar ya buɗe ya hudu, jiki be yi saurin ɗauke miki ba lokacin da kika yi ɓarin? Ke duk baki lura ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Namra ta faɗa tana kallon Anty Amarya da tashin hankali ya bayyana a fuskarta.

“Yanzu likita me ye abun yi?”

“Za'ayi mata wankin mara ne, sai mu ɗorata akan magunguna, amman gaskiya akwai buƙatar tayi family planning na shekara biyu ko uku gudun karta ɗauki ciki har sai mahaifarta ta warki”

Kuka Namra ta saka tana dafe da cikin nata. Anty Amarya ta riƙa bata haƙuri, tana mamakin lamarin dan ita bata ma san lokacin da tayi ɓarin ba, kuma gani take kamar wani abu ta sha dan ta zubar da cikin.


KALSOOM POV.

Kwata-kwata yanzu bata gane lamarin Ezzah ta ɗauke ta kamar wata maƙiyiyarta, sam bata ma son zama falon idan Kalsoom na nan, abinci ma idan ba Doc ne yake gidan ba, sai ta ƙi ta koma can ɗaki ta keɓe kanta.

Bayan shi babu wata matsala da Kalsoom take fuskanta, ita kuma bata ɗauke ta matsala ba dan ba biye mata zata yi ba, zamanta da Doc lafiya ƙalau sai ƙarin so da ƙauna, ga ɗan cikinta tana raino gwanin sha'awa ɗan satin nan data samu har tayi fari sosai tayi ƙiba ta mulmule kamar ba ita ba, Doc har tsokanarta yake wai shi take tsotsewa ita tana ƙiba shi be gane ba.

Ita kuma ta san babu komai sai kwanciyar hankali da kuma kulawar mijinta da take samu a yanzu, ga Ulfah da Rafiq da suka zame mata tamkar ita ta haife su, dan ko maganar Mamansu basa yi, indai kaga wani baƙin hali to Ezzah da kicifin dan tafi kowa kishin uwarta yanzu.



500k words....


______________________________________________
Littafinan na kuɗi ne, idan kin san baki biya ba, karki karanta.
₦200 zaki turo ta wannan account ɗin 0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.

Sai ki turo da shaidar biyan kudin ta wannan number 08036126660

DON'T READ IF YOU DIDN'T PAY...!


*PAGE - 45*

NOT EDITED ⚠

Sai da Yamma lis Anty da Namra suka dawo gida, bayan sun yi mata wankin mara sai da suka bata 6 hours suka ga condition ɗin ta sannan suka barta ta dawo gida.

Jikinta ya mutu sosai, ga tunanin dake zuciyarta, tana jin gajiya a tare da ita amman tunanin dake cikin zuciyarta ya hana ta tayi bachi bayan sun dawo gida.
Tana jin kamar ta labartawa wani damuwarta, sai dai kuma bata san yadda za su kalli abun ba, ace kamar Asim ya juya mata baya, sannan tana ganin idan har ta faɗa Anty ba zata barta ta cigaba da zama da shi ba, Abbah kuma ba zai yarda ta zauna a gidan ba.

Haka ta kwana ciki damuwa da tunani har garin Allah ya waye, karin safe ma sai da Anty ta tirsasa sannan ta ci.
Tana cin abinci tana kukan zuci, kukan da bata san ranar tsayawar hawayenta ba, kuka maraici amman bana rashin uwa da uba ba, kuka take kukan butulci bayan hallaci kukan nadama da bata da gani.

“Anty Namra kuka kike?”

Hindatu ta tambaya tana dafata, yanayinta duk ya canja ganim ƴar'uwarta cikin damuwa.
Hannu tasa ta taɓa fuskarta dan tabbatar da hawayen ya fito, sai kawai ta share tana murmushi.

“Ban ma san ya fito ba, baki iya sallama ba ne idan kin shigo?”

“Na yi sallama baki dai ji ba ne, me kike ma kuka?”

“Ba komai, dan Allah karki faɗawa kowa kin ji?”

“Tau, ga waya Anty tace na kawo miki Asim.ya kira”

Wayar ta sakarwa ido, kamar mai tsoron karɓa, ji take kamar ba wani abun ƙwarai bane zai faɗa mata, what if yace ya sake ta?

“Anty...”

Hindatu ta kira sunanta ganin yadda ta tsurawa wayar ido tana nazarin zuci. Sai a sannan ta kai hannu ta karɓa, ita kuma ta tashi ta bar mata ɗakin.
Wayar na fara ringing gabanta ya faɗi, ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba wajen picking ɗin call ɗin.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikissalam Namra”

“Na'am”

“Kin je gida ba tare da kin sanar min ba, miyasa kika je? Kina son ki faɗa musu abunda ya faru ne? Na san ban kyauta miki ba, amman Wallahi sherin sheiɗan ne, ni kaina nasan ban kyauta miki ba, amman ina kishin ki ne Namra dan me zaki bar wani ya rako har cikin asibiti kin ganin hakan kyautawa?”

Hawaye ya fara bin fuskarsa.

“Kai yi min abunda wani be taɓa min ba, ko a mafarki ban za ci zaka aikata min ba, Asim ka yi taɓon da har na koma ga mahallacin na ba zai gogu ba, baka tambaye ni waye ba, baka bincike alaƙa ta da shi ba, sai kawai ka zarge ni, ka ɗaga hannunka ka mareni”

Ya fara mata kuka kamar gaske.

“Na san ban kyauta ba, kuma na cancanci ko wane irin hukumci, amman ki dubi girman Allah ki yafe min, dan Allah karki faɗawa kowa abun da ya faru tsakaninmu, Wallahi idan har ki ka bar zan iya shiga ko wane irin hali, haƙiƙa ni butulu ne kuma ajizi, Namra ki dubi girman ƙaunar dake tsakanin mu ki yafe min, ni har ganin nake kamar shiga tsakani ne”

“Ban faɗawa kowa ba, kuma ba zan faɗa ba, kuma na yafe maka”

“Na gode Allah yayi miki albarka, dan yaushe zaki dawo? Ko nasa Mama ta zo taje da ke?”

“Ba sai ta zo ba, zan dawo cikin satin nan”

“Yaushe?”

“Nan da kwana uku”

“Kwana uku yayi nisa Namra, da a'ce da hali sai ki dawo gobe ko jibi”

“Sai jibin dai”

“Na gode sosai Allah yayi miki albarka, duk suna lafiya ko?”

“Kowa ƙalau”

“Ina gaida kowa dan Allah”

“Za su ji”

“Na gode sai na ƙara kira”

Ta sauke wayar tana cigaba da hawaye.

“Na yafe maka, amman ba zan manta ba, zan zauna da kai saboda zama da kai ya zame min dole, son ka be amfana min komai ba Asim sai baƙinciki da damuwa”

Ta share hawayenta tana jin wani irin ƙuna da zuciyarta ke mata. Ɗan abincin da take ci sai ya fita ranta, ta tattara kayan abinci ta ɗauki tray ta nufi kitchen da shi, bayan ta aje ta dawo falonta zauna tana miƙawa Anty wayarta.

“Har kun gama”

“Eh wai tambaya yake yaushe zan dawo”

“Dika yaushe kika zo? Me kika ce masa”

“Nace masa sai Next week amman ya ce sai dai na dawo gobe, daker ya haƙura na kai jibi”

“Haba Anty Namra dika yaushe kika zo ma?”

Maryam ta faɗa. Anty tace

“Zan yi magana da shi ya bar ki kiyi ko wata ɗaya”

“A'a Anty kin san ba shida lafiya sosai ma, kuma bana son satin da Abbah ya bani ya cika ban koma ba”

Ɗaya bayan ɗaya Anty ta bisu da kallo, a tunaninta ko a cikinsu ne wani ya faɗa mata Abbah yace karta wuce sati ɗaya.
Maryam ce ta fara tsarguwa da kallon Anty ta yi magana.

“Wallahi ba ni na faɗa ba”

Aisha
“Ni ma dai”

Hindatu.
“Balle kuma ni”

“Waya faɗa? Ko muna da aljanu ne a gidan?”

Namra tayi murmushi, irin murmushin nan na ƙarfin hali ka danne baƙincikin ka.

“Ba suka faɗa ba, Abbah ne ya faɗa min da kan sa”

“Yaushe?”

“Jiya da naje gaishe shi, yau ma ya nanata min”

Anty tayi shiru bata sake cewa komai ba. Sai dai bata jidaɗin da Abbah ya faɗama Namra haka ba.

“Akwai abubuwan da kike buƙata ne? Dan a siya da wuri kar lokaci ya ƙure, ko kuma kuɗi zan baki kije can ki siya?”

“Kuɗin zai fi, dan ɗaukar kaya a nan ma ai aiki ne”

“Amman Namra ba zai yarda ku dawo nan ba?”

“Kwana ki ma yayi min maganar haka, amman nace ya haƙura har yaji sauƙi sosai sannan mu dawo”

“Gaskiya kam zama a nan zai fi, kim ga nan zai fi muku kuma kin ga nan ko ba komai kina kusa da mu”

Sallamar Doc Faruk ne yasa suka katse firar da suke suka amsa sallamar suna masa sannu da zuwa.
A kujerar da Namra take zaune ya zauna, kasancewar ta zaman mutum uku ce, sai ya soma gaiswa da Anty cikin far'ah, tun da shi ba baƙon gidan ba ne.
Maryam da Hindatu da Aisha sai duk suka tashi suka bashi guri, Anty ma tana gama gaisawa da shi, ta shige ɗakinta dan tasan abunda ya kawo shi, daman ita ta kira shi, ganin hakan kamar zai fi sauƙi tun da likitan gida ne.

“Daman akan maganar planning ne Anty tana tsoro kar ayi mai side effects, so ni abunda naƙe ganin ya fi shine ki yi na roba, saboda idan an saka mishi kin ga sai lokacin yayi sannan za'a cire, ba kamar allura bane da a za'a riƙa yi duk months, kuma kin ga shan ƙwayoyin zai iya ƙara miki matsala ma a mahaifa, za a iya tsuke miki bakin mahaifa”

“Amman robar idan an saka ba shi da wata illa ne?”

“Eh to kin san komai karɓa karɓa ne, amman gaskiya baya da matsaloli kamar sauran, kuma kin ga shi a duk lokacin da aka tashi cire miki za'a iya cirewa”

“Amman yanzu ina katsina da zama idan na saka ta nan za'a iya cire min a can?”

“Za'a iya cire miki mana, amman idan son samu ne inda aka saka miki a cire miki ita, saboda aikin wani ba shine aikin wani ba, kuma idan ma son samu ne likitan daya saka miki ita ya zama dik lokaci shine ya ke duba ki”

“Amman kana ganin ba zai haifar minnda matsala nan gaba ba?”

“Gaskiya bana jin zai haifar miki da matsala, indai ba abunda Allah ya kawo ba, sai dai kinsan komai yana da side effects sai dai wani ya fi wani”

“Okay, ba matsala when za'a saka?”

“Ko yaushe kika tashi, a hannun hagu ake sakawa kuma idan an saka miki ba zaki yi aikin da hannun ba tsawon 24h, amman za mu buƙaci sa hannun mijinki kamin mu saka miki”

“Mijina baya tare da ni yana Katsina, kuma idan da hali ina son a saka min gobe”

“Consider it done, zan yi replacement ɗin mijinki a gurin sa hannu ko da wannan zan yi alfahari”

Tayi kamar bata ji shi, sai ta tashi ta nufi ɗakin Anty tana faɗin

“Zan shiga ciki”

“Around nine za ku shigo”

Ya faɗa sannan shi ma.yasa kai ya fice.

“Mun yi magana da shi zai saka min roba ta hannu”

Ta faɗa tana ƙoƙarin zama kusa da Anty.

“Ta shekara nawa? Ita bata da matsala kamar sauran ko?”

“Eh haka ya ce, gobe da safe za mu shiga”

“Allah ya kai mu, ya baki lafiya”

“Amin”

Kwantawa tayi saman gado, Anty ta tashi ta fita.
Washen garin ranar da yace musu suka tafi aka saka mata, duk wani shirin a ranar Anty tayi mata shi, saboda komawar da zata yi gobe.
Hajiya Barau tayi mamakin komawarta da wuri haka, a take ta raya a zuciyarta ƙila Abbah ne yace be yarda ta daɗe masa a gida ba, ita tama yi mamakin da ya barta har ta zauna, goma na arziki ta haɗa mata, tun daga kan kayan sawa zuwa kuɗi da kayan mata.

Ranar da zata koma taje yi ma Abbah sallama, ranar ta sha kuka kamar ranar da za'a kaita ɗakinta, Anty ma tayi kuka sosai har hakan ya saka sauran ƴaƴan na ta kuka.
Direban gidan aka sa ya kaita har katsina dan Anty bata son ta shiga motar haya. Sai da ta biya gidan Gwaggo tayi mata sallama sannan suka kama hanyar katsina.


RASHIDA POV.

Washe garin ranar data dawo Malamin ya kira yana labarta mata bayanin da ƙasa ta bada akanta.

“Ba zaki taɓa komawa gidan Mijin ki ba, matuƙar wannan matar tana cikin gidan, sannan idan baki tashi tsaye ba, to har ƴaƴanki mijinki zai wulaƙanta su akan ta, kuma kin yi kuskuren ba mu suna, Ummu Kalsoom take ba Ummulkhairi ba”

“Na ɗauka ai duka ɗaya ne”

“Ba ɗaya bane, sannan mun ga wani baƙin hudu a tare da ke, kuma bayani ya nuna a halin yanzu tana sama da ke sai kin tashi tsaye”

“Malam wane irin baƙin abu ne wannan?”

Duk ta tsorta.

“Bayani be fito mana fili ba, amman lailai akwai baƙin abu yana biye da ke, kuma akwai abu a jikinki wanda kike ɓoyewa dangin ki”

“To Malam a taimaka ayi mana aiki, ta fita gidan kamin na cika idda kuma ayi min abunda zai jawo hankalin mijina gare ni”

“Dika za'ayi aikin ma nasa a aiwatar da shi yau”

“Amman ƙasa ta bada bayanin zan koma gidan Hilal?”

“Ƙasa ta bada bayani kan mijinki, matakin da muka ɗauka yanzu idan be yi ba, sai mu yi na biyu idan be yi ba, sai na uku wanda shi kam dole ne a samu nasara”

“Wane mataki ne?”

“Dika zaki jisu, amman na biyu da na uku abubuwa masu matuƙar wahala”

“To Malam na gode, amman dan Allah a taimaka a bincika min baƙin duhun nan”

“Zamu bincika”

Ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya tana dafa kai. Baƙin abun nan ya tsaya mata a rai, sai faman tunani take wane baƙin abu ne? Ko dai Ƙalsoom ce ko kuma ciwon da take ɓoyewa ne? Bata samu amsar tambayarta ba har ta gaji da tunanin ta tashi ta shirya ta nufi makarantar su Ezzah. A hanyarta ta tafiya ne Alh Bashi ya kirata wai yana nemanta kwana biyu yayi kewarta, tsaki taja ta faka gefe tana magana da shi.

“Hala baka san aurena ya mutu ba?”

»“Na sani mana, sai dai ban san dalilin mutuwar auren na ki ba”

“Kishiyata ce ta fi ƙarfina ta mallake min miji da ƴaƴa”

Daga can cikin wayar yayi dariya ya ce

“Ke yanzu kamar ki har wata mace ta isa ta fi ƙarfin ki, anya mijin ki ya san mace kowa?”

“Hmmm ƙaddarace ta gitta irin wace zata gitta ka saki Asmee nan gaba”

“A'a aure na da Asmee ai na zobe ne, idan kin ga na rabu da ita to na mutu, indai ina raye ba zan rabu da ita ba, idan kin ga na rabu da ita to na rabu da uwata ne”

‘Hmmm saboda ta maka mugun magani ba, ai wallahi tayi ma kan ta ƙiyamul laili’

Rashida ta faɗa a ranta, a fili kuma sai ta ce

“Kasan da ita kake zama da ni”

“Wannan ai daban, ni dai ki zo ina son ganin ki”

“Ko na zo babu abunda zan maka, dan ni period na ke”

“Na sani haba, ke dai ki zo ina neman ki, amman fa anjima idan mun tashi aiki”

“Na ji”

Ta kashe wayar, ta kunna motar ta hau titi.


ABDOOL POV.

Ko da sha ɗayan safe tayi Ummi da Jidda sun sauka garin Abuja. Kai tsaye ta wuce masaukin Abdool, a lokacin baya ma gidan yana gurin meeting, haka ta zauna a gidan har ya dawo sannan hankalinta ya kwanta ganin da gaske babu abunda ya same shi.

“Ummi na faɗa miki am fine amman kika ƙi yarda da ɗan ki”

“Yanzu ai na yarda, ina ita yarinyar ta ji sauƙi?”

“Eh ance min jiya ta farka, amman ban samu na je dubata ba, amman
Showing 105001 words to 108000 words out of 280121 words