maza wani ji sukeyi da Fuzail,Haka matan sarki Basu dorawa kansu bakin ciki ba yanzu,a baya ma kishi ne ya sasu takurawa Maman Fuzail,yanzu Kuwa sarki Bai Aurenta ma tun Fuzail Yana yaro me zai dame su Kuma duniya ta canja kullum Kara wayewa akeyi shi yasa Suka canja halayensu Suma Fuzail Kamar su Suka haife shi Haka suke ji da shi.
Me martaba Sarki Usman Ali Dan Lamido Iyalansa ya tara Kamar yanda Watarana ya Saba idan za ayi muhimmiyar magana Hajiya Babba me Suna Balkisu ita ta fara shigowa katon palon Wanda kuyanginta ke take Mata baya Tasha wata Shadda dark blue Yar gaske Kaya na Alfarma tana kamshi da uban Izza wacce kudi da mulki ya ratsasu,Yaranta Yan Mata Wanda duk sun wuce 23yrs Saima tana auren wani Dan Sarkin kano,Naja'atu tana auren Dan Sarkin Adamawa,sai Yan yaranta Yan auta twins Yan 8yrs sune Suka shigo Suma Dukkansu sun Sha gayu cikin English Gown masu tsada amma na mutunci sabo da sarauta ba wasa ba,Magajin Sarki uban gayya Fardan Kyakyawa da shi wankan Tarwada shima zai Kai 39yrs yana da Mata har biyu da yaransa biyar Mata biyu maza Uku, ya shigo cikin wasu Kaya na sarauta sosai yasha rawani ba karamin kyau yayi ba Dake shima hakimi ne Kuma Yana da sarauta Zata kai kala Uku a Kansa,Yana Zama cikin Izza sai ga Salman shima Matashin saurayi Wanda zai Kai 36yrs Yana da Mace Daya da Yara biyu shima Hakimi ne sannan da wasu sarautar cike da shigar sarauta,sarki ya kalle su shi kadai ne Kawai a kujera gaba Daya a kasa suke zama kowa yazo sai ya kwashi gaisuwa,Kuyangu da fadawa suna ta sintiri,tawagar Uwar gida kenan Hajiya Babba Wato Bilkisu.
Hajiya Luba wacce ake cewa Hajiya ta Bangon Yamma itace ta shigo gaba Daya da yaranta samari matasa kyawawa Yan gayu Dukkansu Suma suna da sarauta ta gaske Mahmood 30yrs Yana da mace Daya da yaronsa Daya,Ishaq 28yrs baida aure shi,Farooq 26yrs baida aure,Ammar 24yrs baida aure Dukkansu a London suke karatu Hutu suka zo,kusan basa hausa a gidan sai turanci kowa ke zubowa,gaba Daya Hajiya ta Yamma yaranta maza ne Kuma Bata Yara kanana.
Itama Zama sukayi ta Sha wani danyen yard tana sheki Haka yaranta ma,ba karya Luba akwai kyau Haka yaranta ma.
Mace ta Uku itace Hajiya Raheena Hajiya me Bangon gabas kenan Sarkin Hakuri da kawaici ita Kuma gaba Daya yaranta Mata ne Bata da Namiji ko Daya sannan gaba dayansu Yan Secondary school ne Na'ima, Fatima,Hanna,Rumaisa sune yaranta Suka shigo duk sun dauki wanka na Alfarma,mutum Daya aka zauna Ana jira Bai zo ba Fuzail kenan,sai da suka jira sannan wani kamshi na musamman ya daki hancin kowa sun San shine ba sai an fada ba sabo da shi din na daban ne,Sanye ya shigo cikin wasu arnayen kana Nan kaya,wasu farare Kal idan ka kalli Fuzail sai ka lalace a wajen kallon gayunsa ya Gama haduwa,shi Bai son Harkar mulkin sarautar Nan da akeyi takura ce,kowa a kasa ya zauna shi Kuwa Yana zuwa a gefen Sarki ya zauna kusa da shi a kujera Yana latsa wayarsa me tsada,Mai martaba ya hanashi turanci gashi Bai iya hausar ta gaske ba Bai Saba ba,ya rasa me zai ce,da lalatacciyar hausarsa yace Sanu(Sannu) Sarki murmushi ya saki yace Haka aka koya maka gaisuwa? Bai Gane Hausar sarki ba Sam zai ce what....tunawa yayi yace shi Kar ya sake ya Masa turanci,ya rasa me zai ce sai Kawai ya tuna ya musu Sallama tare da mikawa kowa hannnu har matan Suka gaisa a Haka,Fardan yayi Dariya yace to gashi an Hana muyi maka turanci sabo da ka koyi hausa sosai,Fuzail Bai San me akace ba ya dai Gane koyo da yaji ance da Kuma Hausa ya Gane akan yaren suke magana,Sai Kawai yayi Shuru,sarki ba ruwansa da hausa ya fara magana Bayan an Bude taro da Addua yace Fuzail cika Mana da Addua,Fuzail yace Cika? Meaning? Du'a Sarki ya sake magana,Okay ya furta ya fara zazzago Addua sosai yanda sunna ta koyar,hakan ya birge sarki,Bayan Haka yace You Fuzail,da sauri Fuzail ya kalli sarki yaji ance You Fuzail yasan da shi ake,Sarki yaci gaba da magana da hausa a kanka na Tara mutane,a shekarunka sannan a mu al'ada ta sarauta ya kamata ace yanzu ka ajiye iyali,ya kamata ka fito da matar aure kafin kannenka su taso su nake so Nan gaba na Aurar Mata da maza,yanzu burina kayi aure shine zaka Zama cikakken mutum me daraja,sabo da Haka mun yanke hukunci da shawarar matana da Mahaifiyarka dake Brazil tare da yawun Yan uwanka gasu Nan gobe ka shirya Mata kyakyawa Yaran sarauta da Yaran masu Hannu da shuni zasu zo zasu ci abinci a gidan Nan tare da Kai cikinsu zaka zabi Daya wacce tayi maka ka aura.
Har sarki ya Gama bayaninsa Fuzail Bai San me akace ba,Fardan murmushi yayi tare da Furta Me martaba Bai Gane kalamanka ba,ka bani dama na fada Masa da turanci yanda zai fahimta Inshaallah a hankali zai iya Hausar ba tare da mun takura shi ba,Sarki ya furta na baka dama Fardan,Fardan cikin yaren turanci ya fassarawa Fuzail.
Sai lokacin Fuzail yace Okay,shi har ga Allah yaji wasu abin da sarki ya Furta fes a kunnensa yana sani ya nuna Bai Gane ba, irin matan zabi basa ransa,yafi so yaga yarinya da Kansa yaji Yana Sonta sannan wacce zata so shi tsakaninta da Allah badan kudinsa ko kyan sa ba,Amma bazai iya yiwa Sarki musu ba a ransa ya tabbatar babu wacce zata Masa ma cikinsu Amma yace suzo ya gani idan wata tayi cikinsu shike nan,Sarki baiyi zaton zai Amince ba yanda baya tsoron kowa baya kunya ba abinda ma ya hadashi da wani kunya ko tsoron fadar duk abinda yaga Dama,saukinta ma Don sarki ya takura shi sai ya dinga yin hausa Bai iya ba Kuma sai yayi Shuru kawai da Haka Sarki ya samo lagonsa sabo da yanda ya Raina kowa da sarauta ba ruwansa komai yawan mutane abinda yaga Dama zai fada.
Ya Riga kowa tashi ya fice ba tare da ya kalli kowa ba ya fita,sarki yasan shi Daya zaice zai fita zaga gari ai Securities ya bawa Umarni Kar a sake a barshi ya fita shi daya ko yaje da guards ko ya hakura,shi kuma akan ya fita da wani gwara ya hakura sai ya koma hadadden part dinsa Kawai ya kwanta Yana tunanin shi wa zai aura,kullum sai yayi Addua akan irin matar da yake so ya aura Amma har yanzu Bai samu ba,gashi sarki ya takura Masa,shi kasar ma Sam baijin dadin Zama kamar a prison Haka yake jinsa.
Washe gari Kuwa 5pm Mata zankada zankada Yan gayu na karshe Yaran sarauta da Yaran masu kudi Suka dinga sauka a jirgi,har da Yaran kwarori da jinin larabawa farare kwal kwal, ko wacce da securities dinta tana zuba Uban yanga da Iyayin masifa,dama sunga pics dinsa duk an nuna musu da Amincewar Iyayensu,wani Palo aka ware musu Wanda komai fari ne kal,Yan Mata su goma ne Suka zo kowacce na yiwa Yar uwarta kallon hadarin kaza,Ko wacce tana nuna na fiki kudi da gata.
A Haka Prince Fuzail ya shigo sanye cikin wasu fararen kayan again na Alfarma wani danyen yard ne an Masa wani dinki Kalar namu na Nan Fadin irin kyan da yayi Bata Baki ne ma,Kallo Suka bishi da shi gaba Daya sai da suka Raina kansu ganin irin haduwarsa da kyawunsa a fili,Hajiya Babba ce ta shigo da kuyanginta JakadiyaTace your Dinner is ready sabo da lokacin da Fuzail ya fito dare ma yayi sun Sha jira, babu wacce ya kalla cikinsu Haka Suka Mike a gabansa kowacce tana rangwada da karairaya Dan a birge shi,Wata ciki tana bankaro kirji ta fara Gabatar da kanta dama an gargade su Banda turanci,Tace Sunana Neena Yar Gomnan Adamawa state,Nayi karatu a Uk sannan Ni class mate din Kanwar Barak Obama ce,Sai da ta jawo Fuzail ya kalleta sabo da karyar data surfo sauran sai da suka Yi Mata dariya,ita Kuwa ta Bata Rai tare da ci gaba da cin abincinta tana yanga.
Daya ciki itama harda wani Dan Matsawa kusa da Fuzail Yana shakar Kamshinta tana lumshe Ido tana wani lashe lips ta furta Laila nake Yar Vice president,Nayi Degree da Masters Dina a Qatar Ina Aiki a NNPC I love you Or Sorry kasan na Saba da turanci Ina sonka Baby itama aka tabe Mata Baki.
Haka kowacce ta shiga Gabatar da kanta suna shiryo karya iri iri,ta karshe tana tashi Tace Sunana Sumayya Alhaji Dan Paris Sumy kenan,duk Fadin kasar Nan an San Alhaji Dan Faris har Exam na taba zanawa da Sunusi Lamido Sunusi,Fuzail yace Oh Really? Tace sosai ai Queen Elizabeth ma Muna mutunci sosai da ita Ina Kai Mata Ziyara har gida,Fuzail yayi Murmushi yace Zaki rakani nayi gaisuwa Nan gaba ai murna ta Kama Budurwa Sumy tunaninta ma ta cinye zabe.
Bata san babu wacce ta masa ba,Baki ma ya tabe su gaba Daya serving nasu akayi shi Kuwa da Kansa ya zubawa Kansa abinda yake so,suka dinga mamaki,ko kulasu baiyi ba yaci gaba da cin Abincinsa suna ta faman kallonsa ko wacce tana Buri ace ya zabe ta,Yana gamawa ya Mike ya bar part din gaba Daya zuwa sashen me martaba.
Sarki Yana ta murna yasan ma a cikinsu Dole ya zabi daya, Fuzail ya shigo Sarki da murna yace you can speak English today,Fuzail da hausarsa ya fara kokarin magana Dole fa shi sai ya koya yace Babu,Sarki yace ban Gane babu ba? Zancen kurame yayiwa sarki Wai ba wacce tayi,ran sarki ya baci yace duk kyawunsu? Fuzail yace Yeah Babu, sarki masifa ya shiga Yi masa,Fuzail shima yace ya daina turancin a Haka zaina magana,ai Kuwa da zancen kurame ya nunawa sarki Kirjinsa yace One of them is too big,da zancen kurame ya gwadawa sarki idan suna bacci Boobs dinta zai dameshi,Sarki ya rufe Baki da sauri sabo da kunya ta Gama kamashi,da sauri ya canja zancen yace sai wace tayi Kuma shima ya Masa da Maganar kurame,Fuzail yace daya...no shape, she is like 1, Sarki yasan Kawai bayaso ne shine zai Masa tsari yace cikinsu babu wacce tayi? Ya tambaya da turanci,Fuzail ya furta capital YEAH,shima da turanci yace a bashi lokaci zai samo da Kansa,Sarki Bai matsa Masa ba,ya yiwa matan kyauta Suka koma gidan Iyayensu gwiwa ba kwari.
A Haka Matan sarki da Yan Uwan Fuzail sai tallan mata suke kawowa Fuzail amma Sam Bai zaba ba yace duk Basu Yi ba,har an gaji an kyale shi,Yau Sarki ya matsa Masa sai yaje ya zauna a fada yaga yanda ake mulki,kayan sarauta aka sashi ya saka Dole yaje,Yana zuwa ya Iske masu busa Algaita suna ta busawa sarki sabo da Dole ne kullum sai anyi ta a Gaban sarki da safe,ai Kuwa Fuzail yaji kida yaki karewa gashi Yana tausayawa masu Algaita yanda suke kunburo kumatunsu,tun Yana kallo Yana danne zuciyarsa har ya kasa ya daka musu Tsawa tare da mikewa tsaye Yana masifa a Fadar yace Wai sai Kun cire kumatunku? Nawa za a baku please ku bari Nan,ba ruwansa ya kunyata Sarki a Gaban manyan masu sarauta,Ba shiri Me matarba yace yaje inda zai je ba sai ya zauna ya ga wani yanda ake mulki ba.
Kuma shi Fuzail ba ruwansa da wasu Fadawa Bayi da kuyangi duk Fadawan Nan maza Hannu yake mika musu suna gaisawa,matan Kuma Hannu yake daga musu,an Masa fada yace shi bazai iya ba Ana gaisar da shi Yana share mutane sannan musulunci yace ayi musabiha da Sallama Dole aka barshi Nan ma.
Akwai abokinsa Guda Daya Dan gidan Kanin Mai martaba Kuma wazirin sarki Ameer,Ameer Dan Waziri ne tare Kuma sukayi University da Fuzail sabo da Haka a Nan Baida Abokin da ya wuce Ameer,Shima Ameer Yana da sarauta,shi Kuwa Fuzail yace Bai so shi Business man ne ko a can Yana da Company shi Karan Kansa me kudi ne Bai dogara da kudin Iyayensa ba,akwai shi da son Neman na kansa tun Yana yaro Hajiya Ayusha Umminsa ta dorashi a Harkar Business dinta har ya girma Kuma ta bashi jari me yawan gaske Haka Sarki ya Kara Masa shine yake Harkoki da dama na Business masu kawo kudi,Yana da shares a wani katafaren Mall Dake Korea Republic,sannan Yana da shares a wani Company na kera motoci,Haka Yana shares a hukumar kwallon kafa ta wani team dake Brazil,ko ta Ina kudi shigo Masa sukeyi dama sai da kudi ake Neman kudi,sai kaga Kamar baya neman kudi Kuma a Haka millionaire ne na gaske duk yafi Yaran Sarki kudi sosai sabo da a waje akwai Harkoki na samun kudi idan kana da jari.
Ameer ne zaune a palon Fuzail,Cikin Harshen turanci Fuzail yace Ina son Inga rayuwar talakawa,tunda na taso rayuwa kala daya nayi ta masu kudi,ban San Daya bangaren talakawa me suke ciki ba,Ina so Naga irin rayuwarsu,Ameer yace ya kamata Kuwa amma Kai Mene damuwarka Allah ya baka kudi Ina ruwanka da su,idan taimako zakayi kayi Kawai amma ta ya zaka ga wani rayuwarsu.
Na fa tambayi Me martaba zanyi tafiya nace Masa Zan je yawon Bude Ido a Nan Nigeria Zan Shiga kauyuka zanyi Kamar 1 to 2 weeks sannan yace indai ba tare da Kai zamu tafi ba bazai barni ba,Amma Indai dakai zanje ya Amince ko gobe zamu iya tafiya.
Dariya Ameer ya dinga Yi yace Shikenan Prince ban Isa na kasa bin umarninka ba yaushe zamu tafi? Fuzail yace gobe amma fa kasan baza muje a Haka ba,ka samo Mana kayan talakawa mu saka sannan Ni gaskiya sai na canja ma fuskata Zan saka hular gashi ta maza me uban yawa sannan na Kara da gemun karya kaga idan mun Shiga mutane babu me ganewa su waye ko ya kace? sannan Suma talakawan baza su gujemu ba tunda munyi iri Daya da su cewar Ameer tafawa Suka yi suna ta shirye shiryensu.
Washe gari da zasu Yi tafiyar cikin shigarsu ta Alfarma sukayi Sallama da kowa Suka fita,suna barin gidan Sarki Wani Guess House Suka shiga me kyau anan Ameer ya saka wani dogon wando jean Wanda yaronsa ya tura layin Yan gwanjo ya siyo musu kayan aka wanke su tas,Ameer Dogon wando ya saka jean black duk ya Dan kode da ka gani kasan na talaka ne,t-shirt dinsa wata Grey me karamin Hannu shi Bai rufe Fuskarsa ba.
Fuzail Kuwa Wandonsa blue jean ne 3qutr da t-shirt me dogon Hannu wata me zanen layi layi red and Black,Wani hular gashi me uban yawa na maza ya saka a Kansa sai kace a Kansa aka halicceta,babu Wanda zai Gane sawa yayi yayi wani kyau abinka da me kyau,Gemu dogo ya Kara a kasan nasa da saje duk Fuskarsa ta Kara Rufewa da gashi duk Wanda yasan Fuzail to ba shakka bazai taba Gane shi ba duk da yayi kyau,skin dinsa ce Kawai ta nuna Hutu,suna kallon kansu a mudubi suna ta dariya,Ameer wankan Tarwada ne shi,Bai Kai Fuzail tsayi ba amma shima ba baya ba ya hadu.
Fitowa sukayi Suka jawo wani tsohon machine da Ameer ya siyo a wajen wani bakaniken machine,Dariya ce ta kamasu Suka dinga yiwa kansu Dariya Musamman Fuzail Bai taba Dariya ba irin ta yau ba Ameer har mamakinsa yakeyi yanda yake nishadi,Ameer ne zai tuka machine din Fuzail ya hau bayansa Yana dariya ya daki kafadar Ameer yace let's go man.
Ameer Yaja machine cike da kwarewa,Fuzail Cikin turancinsa yace a fara zuwa unguwannin Talakawa sai mu shiga kauyuka baza mu koma gida ba har Jigawa state sai munje,Ameer yaci gaba da tafiya Yana bin unguwannin Talakawa na garin suna kallo wani abin ya Basu tsusayi wani ya Basu Dariya da sha'awa,Wani abin ya Basu haushi,Har Yamma suna yawo gaba Daya yunwa ta kamasu,lokacin Kuma Farida taci Uwar kwalliya cikin wani lace dinta Dan dubu goma fari tas ta tafi gidan Sarki yau ta rantse sai taga masoyinta Fuzail.
Tana tafiya a layinsu tana yanga,Manal Kuwa tana gida yau ma tayi Awara da yawa gashi ba Wanda yazo ya Siya har Yamma tayi ganin zata sake tafka asara sai Kawai tayi wanka ta Sanya doguwar rigar atamfarta Leda wata maroon and milk tayi kyau dake me kyau ce Manal fara tas ga kyan sura ko Bata Yi kwalliya ba kyau takeyi,gashi Yazed da Malam Basa Nan ya tafi kauyen su Malam za ayiwa Malam maganin Hausa ko za a dace sai sun kwashe sati biyu kafin su dawo.
Dole ta dauki katon botikinta na Awara ta fito da Niyyar ta zaga ko zata samu masu siye,tana tafiya a layinsu Kamar zata Yi kuka ba mutane ko mutum Daya a layin Kamar ba kowa a layin nasu Haka take tafiya ita daya.
Farida Kuwa juyowa tayi ta hango Manal da bokitin Awara ta dinga dariya ko kallon hanya Bata Yi tana faman yiwa Manal Dariya,Kawai Su Fuzail Suka yanko kwana sai ganin mace sukayi a gabansu,Fuzail ya saki Kara,Ameer ya firgita garin zai kaucewa Farida Kawai ya daki jikin katanga da machine din Suka Fadi gaba daya,Farida tsorata Kawai tasa ta Fadi a kasa Amma ba abinda ya sameta ta Mike da sauri tana Tsaki tana goge jikinta tsayawa tayi akan Su Fuzail Wanda basa ma Hayyacinsu Amma ta dinga zunduma musu ashar ta uwa ta uba,tana shegu matsiyata talakawan banza,Kun jawo min yanzu sai na koma gida na canja kaya sannan zanje ganin masoyi na.
Allah ya Isa tsinanannu talakawa matsiyatan banza Yan Iska Shegu,Juyawa tayi zata koma gida ta kalli Ameer Ido cikin Ido Tace sai kunci Uwarku yayan mayu ta tafi abinta,Fuzail Yana numfashi sama sama yace kaga wannan Bata taimakemu ba sai fada takeyi,Kamar naji zagi take
Showing 18001 words to 21000 words out of 153479 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52