da Ido na shike nan ya kusa warkewa sannan ya juyo.

Manal ta zuba Masa Ido kamar me yace lafiya? Tace tsaya a Haka inyi ta kallonka ka hadu inji Yan Birni Suka ce ka haduwa,Dariya yayi ta sake cewa bature yace Handsome,kaji haukar Bature Hand fa Hannu kenan to some din ta mene chab hauka,Sanda Yaya Ya fara koya min turanci tunda Muka zo kalmar Nan na tsani turanci gaba Daya sai da na daina kula Yayana nayi gaba ta tawon kwana Uku da Yaya na akan Handsome din Nan,sai gashi ashe tana da Rana Kaine ma kalmar Handsome din gaba Daya Kai bature ya kalla ya kirkiro Handsome,Fuzail Yana ta kyalkyala dariyar da Bai ma taba yin irinta ba,Kuma sai Dadi yake ji Manal tana ta yabonsa shi Kam yau ya Gama Jin dadinsa duk yabon da ake Masa Bai taba murna ba sai akan na Manal.

Manal ce ta dauki wayarsa tare da Kara haske Fuskarsa ta karewa hancinsa kallo Nan take ta furta Chab Surayya sunan wata,Dariya ta kwacewa Fuzail sosai yace Hanci na Surayya ne?Manal tana Dariya tace Sorry karka ce na Raina ka,kasan Allah muje kayi Aski gobe sai kafi Haka kyau,Dan Allah kayi Aski gashin yayi yawa kalli tudun gashi ga gemu dogo da kasumba Haka ai Dole su rage maka kyau Amma daga hancinka bakinka zuwa idonka an San Handsome ne Kai kawai kallonka ne ba ayi,Fuzail ji yake kamar ya tashi sama Sabo da farin ciki.

A hankali yace gashi Ni talaka ne Amma na tambayeki? Manal Tace Ina jinka,yace Zaki iya aurena a Haka idan na samo Mana ko gidan haya ne Zan fara sana'a ko dako ne a kasuwa Ina ciyar dake da sauke duk hakkinki na matata dai dai talauci na kafin Allah ya Buda min? Idan na samu kudi Zan saki a makaranta kuma kema ki Zama Yar Birni yanda kike da kyau nasan sai an kalleki Nan gaba,Manal sabo da Murna ta rufe Ido tare da dauke wuta tayi duf,yace ko bakya so na? Manal ta girgiza kai,shi Bai San wata kunya ba,yace talk yanda Zan gane,Manal a kunyace tace Allah sai Naja Aji Haka Kawai na Fadi gaskiya da wuri,Shuru yayi Yana dariya a ransa,sai da tayi minti Uku sannan Wai har ta Gama Jan ajin ta furta Ina sonka Nima sannan Ni ba kudinka Zan aura ba Kai Zan aura ba ruwana da talaucinka,Kuma Inshaallah baza kayi dako a kasuwa ba,Idan Yaya ya dawo wallahi Zan fada Masa Dole sai ya min aure idan ka samo Mana gidan haya ka dinga siyo Mana Dan waken mu gongoni biyu Ina Yi Mana faten wake,Allah na tuba Ni Dana Saba rayuwa ma a daji rugar Fulani ko a daji ne Zan bika mu zauna Matukar kana cikin dajin Zan zauna tare da Kai iya wuya Rai da ajali.

Kuma ai sai mu dinga wata sana'r a gidanmu kaga sai mu dinga samun kudin da zamu rufawa kanmu asiri,muna samu wata sana'ar sai kaga Sanadiyarta Allah ya rufa Mana asiri mu haifi Yarmu Shafa'atu,Fuzail yace Shafa'atu? Yana dariya yace no ba a Kan 'yata ba ,Manal ita a Dole Yar gayu tace Kai Shafah za Ana ce mata,Fuzail yace no...no....

kallon Manal Kawai yakeyi da mamaki matan yanzu taji wannan talaucin Amma tace zata aure shi Haka tana ganin yanda ko Naira dari baya iya Fitowa da ita itace ma ke dawainiya da shi Amma ta yarda,a ransa yace irin matar Dana ke so ce with Good heart,matar rufin asiri matar da zata so ka ta zauna tare da kai a cikin ko wanne yanayi na rayuwa ba wacce zata so ka Dan kudi ko Dan wani sura naka ba.

Manal kunya ta dameta Yana ta kallonta ta Mike zata koma shimfidarta ta kwanta da sauri ya sa Hannunsa me Matukar taushi ya rike Hannunta yace kwanciya zakiyi? Manal tana boye Fuska ta daga Kai Wai ae yace Good Night tare da sakar Mata hannu.

Dukkansu kwanciya sukayi kowa yayi Shuru Yana Jin wani farin ciki marar misaltuwa a ransa,Ga wani shauki Yana fisgarsu,a hankali Yana daga kwance ya Dan matso jikinsa,Manal ma da wayo tayi step Daya daga kwance zuwa inda yake,Ya sake matsowa a hankali,itama ta matso again suna Haka har suka zo gaf da juna,ga wani shaukin juna Yana fisgarsu,tunawa yayi da sauri ya matsa can baya tare da Furta Devil Shaitan,Manal ta matsa itama da sauri tare da cewa marar mutunci zai sa na a sukurkutani kafin biki a tsotse min madarata Dan ance idan aka kebe mutum biyu na Uku Shedan ne shine yazo to mun Gane,Yana jinta Bai San ma nufinta ba Wai da Shedan take ya koma inda yake a Haka bacci ya kwashe su kowa can nesa gefe.

Washe gari Farooq yayi Sallah da Azkhar dinsa sannan yayi wanka tare da canja Kaya cikin na gwanjonsa,Manal Kuwa Dama Bata Sallah wanka tayi ta canja wata Yar jemammiyar Atamfarta koriya wacce Farida ce ta Bata kwancenta,zata bayar a makota Manal ta dinga rokonta da kyar ta bar Mata rigar Dake dinkin birni ne sai tayi kyau a ciki.
Farooq Bai San ma ta Bude gidan ta fita ba, Manal Shago taje ta siya Indomie biyu da kwai danye hudu,sai ruwa Pure water na Hamsim,ta siya musu Omo da Sabulun wanki,ta dafa musu Indomie harda kwai kowanne Guda biyu dafaffe a gidan Baba me kayan Miya tayi girkin da kanta ta zubo a flask,Lokacin Fuzail Yana ta Neman Manal har ya bude kofa ya fito hankalinsa a tashe sai ya hangota da Kaya Niki niki,farin ciki da tausayinta ya kamashi yanda take dawainiya da shi,da sauri ya karasa tare da karbo wasu kayan na Hannunta ya rage Mata nauyi Yana cewa baza ki fada min ba na taimaka Miki sai ki tafi ban sani ba kin San hankalina ya tashi.

Murmushi Manal tayi tace ka yarda Dani ba inda Zan tafi na barka Suka Shiga gidan nasu tana cewa Kamar yau ko gobe naji Likita yace za a sallami Dan uwanka,Fuzail Wanda ta sani da Farooq yace sai jibi ma naji Likita yace,Allah ya kaimu karka damu Inshaallah zai warke,Farooq yace Yeah,Abincin ta zuba Masa a plate wannan Indomie ya santa Yana ci sosai Kuma ta Masa Dadi cikin kwanciyar hankali yaci ya koshi abinsa ya Sha ruwa,sai da suka Gama ta wanke komai ta mayar gidan Baba,sai yaga ta dawo da wani botiki,kayansu da Suka cire ta eba zata wanke,karbe wankin yayi yace Ina Nan kiyi wanki kawo na wanke,Bata Yi musu ba Tace to wanke kawo naje na Kai maka wayarka wajen caji,Wayar ya Bata ta tafi ta Kai wajen me cajin kusa da su,kafin ta dawo ma ya wanke kayan Dake ba Dirty,lokacin data shigo Yana daurayewa ta kwasa ta samu Kan wasu katako a tsakar Gidan ta Shanya musu kayan sannan ta dakko wata tsohuwar bra dinta wacce ta Gama tattalewa zata wanke da kanta sai babboyewa takeyi sabo da Kar ya gani Amma ya gani ma.

Ya fisge Bra din ya Shiga kallo Yana ta dariya yace wannan trash ne fa,ya duba Size Amma tsabar Jin jiki size din ya goge babu, tambayar Manal yayi yace Kuma wannan Yana Kama chest naki? Manal ta Harare shi ban sani ba ta ce,da Kansa ya wanke ta fes Yana ta dariya Wai mutum ke sa wannan lalatacciyar abar,pink ce ya wanke ta Kuwa fes ta kwace ta Shanya a barta Hannayensa da yayi wanki yake kallo shi Bai taba yin wanki da Kansa ba gaba Daya Dan wankin da yayi Yatsunsa sun farfashe suna Jini,Manal ta zaro Ido tace baka wanki ne muga hannunka ta fisgo hannayensa tana kallo,Idonta ya ciko da kwalla Tace me yasa baka fada min ba baka wanki kalli hannunka muje asibiti,duk ta rude.

Hannayensa ya kwace Yana cewa wani ciwo ne Dani shi yasa Idan nayi wanki suke Haka ai dama tun Ina yaro Haka sukeyi zasu warke in two days,Manal tace ka tabbata? Yace ae tace to,tayata yayi Suka gyara gidan fes harda wanke toilet Kal abinsu.
Da Rana Kuwa Jullof din taliya ta karbo musu a gidan Baba,Da dare Kuma Waina ce da Miya,tare Suka karbo wayarsa daga wajen chaji ta cika full.

A saman shimfidar zanin ya kwanta Yana latsa wayarsa,Manal ta shigo dakin Tace Farooq Kunna Mana kallo kafin na tafi gida yau a gida Zan kwana Kar a kala min wani sabon sharrin,baida film din hausa sai American film,Yace American film ne Dani,Manal ta Bata Rai Tace Ni hausa nake so Gaskiya yaren da Zan Gane,Bari na duba ko Ameer ya tura wani,a Haka ya Mata wayo Nan take yayi Mata Download ing hausa Film latest sababbi kala Uku ko wanne complt 1&2.

Yace kinyi sa'a ga wasu Ashe Ameer ya bari,Manal ta washe baki,ya dakko flask ya jingina Wayar a jiki Suka zauna kamar tv Haka Suka sa waya a gaba suna kallon hausa Film.

Yana satar kallon Manal yanda gaba Daya kamar ta shige cikin Wayar Yana ta dariya a ransa,Manal tace wallahi Ina son waccen efto din Ni ko a kauyenmu film Indai bana sa bane bana bin su Khaltum zuwa kallo,a duniya Yana birgeni Ina sonsa wallahi ya hadu,ga iya soyayya ga tsara Yan mata ga iya rawa,Nan take Farooq ya hade uban Rai Idonsa ya canja,Ransa yayi masifar baci sai da Manal ta tsorata ta ja baya daga kusa da shi,karfin Hali yayi yace waye shi? Manal da tsoro ta nuna Masa Adam A Zango tace gashi sunansa Adamu Usher,Farooq yace wow then ba a wayata za a kalle shi ba,sai kije Wajensa tunda sonsa kike Yi,wayarsa ya dauke tare da kashe kallon yace dama ba so na kike Yi ba? Manal tace baka da Hausa Farooq ba irin so na aure ba so na film nake nufi ba,okay karki sake cewa kina son wani da Namiji a gaba na Kawai kice kina son Film dinsa,to naji Zan kiyaye kayi Hakuri kunna min,Yace bani kunnawa sai kince kina so na,Manal taji kunya ta Shiga yarfe Hannu tana boye Fuska,Kallonta Kawai yakeyi tana birge shi kunyar Nan tata tana birge shi a duniya,Manal tace Ina sonka sai ta kife kanta a cikin cinyoyinta,gyara zamansa yayi sosai Yana ta Jin Dadi yace I love you too,Manal tana ta Jin dadi kunya tasa ta fice da gudu ta bar gidan gaba Daya zuwa gidansu.

Haka suka ci gaba da Zama tare Amma suna kiyaye duk wani Abu Wanda Shedan zai shiga ciki suna tunatar da kansu,Farooq ya fara koyawa Manal turanci sannan Yana Kara gogewa da hausa sabo ita Bata Jin turanci Dole sai Hausar yake Mata ta karfi hakan yasa kullum Jin hausarsa da iyawarsa karuwa sukeyi,irin Hausar Yan Fulani duk ya koya wajen Manal,Manal ma tana ta koyon turanci a Wajensa Yan kana Nan kalmomi Wanda ya sansu da hausa su yake koya Mata,komai ta fada ko ya furta sai ya koya Mata da turanci,hakan yasa Suka wani mugun shakuwa da juna ka rantse gida Daya Suka taso,Komai tare sukeyi Yana ta Dan Wayar da Kan Manal,hakan yasa ta siyo littafi tunda ta fara primary ta dinga koyon Rubutu da karatu,Fuzail ya dinga koya mata a nutse yanda zata gane.

Yau sati Guda kenan da Haduwar Manal da Fuzail Wanda ta sani da Farooq,sun shaku matuka Kamar kullum yauma da yamma suna zaune ya rike Hannunta Wanda take rike da biro Yana koya Mata rubutu,Haka ake rike biro,Hannunsa Daya hade da nata yasa taji wani Yama-Yama a cikin jininta wani Abu na Mata yawo har kwakwalwarta,shima wani Shock yake ji a jininsa duk Sanda fatarsa ta Gogi fatar Manal,tsoron Allah yasa ya janye hannunsa da sauri,Suna Haka Ameer ya Kira Fuzail yace an sallame shi.

Manal ta Mike zumbur tace muje mu taho da shi Alhmdllh dama bana son kebewarmu mu kadai sabo da shedan,Fuzail yace Me too ya rike Hannunta Suka fito,suna Fitowa ta Zame hannunta Tace ba kyau fa,Yayi Murmushi yace sai yaushe zai koma da kyau? Manal ta kalle shi tace idan ka biya Sadaki Mana an daura Aure,Murmushi ya saki tare da cewa Talaushi akwe babu dadi,Dariya tayi taji Hausar sai a slow itama Suka shiga Napep zuwa Hospital Suka taho da Ameer.

Ameer da kayansa shima na gwanjo mamakin shakuwar Manal da Fuzail yakeyi,Fuzail da yake baida fara'a baya Shiga safgar kowa,ba irin matan da basu kawo kansu gare shi ba Amma ko kallo Basu ishe shi ba sai Manal,a Napep Yana kallonsu sai kus kus sukeyi suna dariya Kuma yasa Manal a gefensa shi Yana gefen Ameer sabo da kar Ameer ya taba jikinta.

Ameer mamaki yakeyi yanda yaga gidan da Manal ta Nemo suka zauna,suna cikin gidan Manal ta tafi karbo musu abinci,Ameer ya samu dama Bata Nan yace Prince wallahi Mai martaba Yana ta kirana akan lallai mu dawo gida sati ya cika,Fuzail yace Ina sane ai zamu tafi,Kuma dazu naji Kamar kana cewa you love her is tht true? Fuzail yayi kayataccen murmushi yace Yeah I do really love her, Ina so Aurenta verysoon,Ameer yace ta cancanta gaskiya Amma Kuma Umminka fa kasan warning dinta fa sannan gidan sarauta za a maka Dariya ba lallai su Amince ba,Fuzail yace wallahi Dole kowa ya yarda ko na bar kasar Nan Zan iya Aurenta a boye ma so is better for them su Amince ma shine samun lafiya,Ameer yace nafi Jin Umminka Fuzail, please Ameer bana son zancen Nan Na fada maka babu Wanda zai hanani abinda nake so Ina komawa Zan sanarwa sarki,Shuru Ameer yayi Yana hango irin rigimar da za a kwasa,shi Kuwa Fuzail sauri yayi ya Kira Umminsa suka gaisa,ya Kira Mai martaba yace gobe zai dawo,sarki yaji Dadi sosai da baya karya dokarsa.

Suna ta Hira Kasa kasa Manal ta dawo Riki Riki da Abinci Shuru sukayi sai Sannu da Fuzail yace mata,ta Ajiye a daki ta dawo tsakar gida inda Suka zauna suna hira,Fuzail Yana ta latsa waya baya saurarar Hirar Manal da Ameer,ba zato yaji an kwace wayar,Manal ya gani tana cewa sai naga mene a wayar,ai da sauri ya bita zai kwace ta zille da gudu,Bai so taga sirrinsa shi yasa ya dage sai ya kwace wayarsa,tsakar Gidan Suka shiga zagawa suna Dariya,ganin Haka Ameer ya saita wayarsa ya shiga Daukansu video,suna ta guje guje daga Nan ya cafke Manal ta cikwikwiye shi sosai tana jikinsa Ameer Yana ta dauka,sai da ya kwace wayarsa sannan yace Yi Mana pics Ameer,Manal ba ko gyarawa ta dinga yin tsaiwa iri iri sai ta matsa nesa da shi sosai sai tayi style a dauka Kawai haukar tsaiwarta takeyi ta Kauye,Ameer Dariya Kamar ta kashe shi.

Yace gyara Manal ki koma kusa da shi,Manal tana komawa ta sunkuya tayi ruku'u sosai Tace da Fuzail nayi Salona Farooq dafa ni,Farooq dai shima Dariya yake Yi ya daura kirjinsa da Fuskarsa a gadon Bayanta Suka kalli Ameer ai Kuwa ya dinga dauka kyas kyas,ta Mike tsaye ta Mika hannaye sama tayi Handsup shima Fuzail yayi Haka tare da manna jikinsa a Bayanta aka dauka Nan ma,Hannayenta ya rike suna kallon juna aka dauka,a gabansa ta tsaya tare da tale kafafu ta daura Yatsanta a karshen gemunsa Wai style tayi ai Kuwa Ameer Yana ta kyas kyas Yana uban Dariya sai da Fuzail ya Harare shi sannan ya rage dariyar.

Manal ta tsaya a gabansa tare da rike Kugu Tace Ameer dauke mu Ina Yi Masa masifa da bala'i,Ameer yace to an Gama har Video zanyi ya fara dauka,sannan yace Zan fara Video ki fara Masa Masifar kinji?

To Manal ta furta tare da rike Kugu ta zarowa Fuzail Ido tare da Furta sunan wata Yayata kenan Farida sai ta fara yiwa Fuzail Fari farrr.....farrrrrrr tana jujjuya ido tana yin tafi ya kasa rike dariyarsa,Manal Dan taji sunan Namiji Man da turanci Tace Hey Mans tana nuna su duka su biyun Tace Ba Singular nake nufi ba Plural Ameer yana ta uban dariya Kuma Bai fasa daukan Video din ba,yace nasan wallahi Farooq ne ya koya miki,Manal tayi Dariya tare da Furta Confirmed past tense nake nufi Kai Ameer, Suka sake shekewa da dariya Fuzail yace Haka Ana ce plural na Man? tunani tayi can sai ta kwaikwayi Muryar Fuzail yanda yake irin na turawa Oh My Gosh Men,Ameer Yana dariya yace kina da Basira Manal Kin Iya yanda yake magana wlh.

Fuzail Cikin Farin ciki ya Riko Manal Yana dariya yace ci gaba da Masifar Yana dauka fa,Manal taci gaba Wai masifa take yiwa Fuzail Tace Your Nose is like Biro like pencil,Ameer yace Iyyee Yana dauka,kasan me? Kai wani market ne wlh,wani ShopRite da Kai,Ameer wata Mahaukaciyar Dariya yake ta yi,Manal tace Finished Wasa ya watse an gama, tana shigo kaima Ameer ya shiga ya dinga haukar tsaiwa shima Yana biyewa Manal Yana ta musu Selfie sai da Suka gaji sannan ta zubawa Ameer Jullof din shinkafa da nama Guda Daya tal,Tasu da Farooq Kuma a flask din itama Mama Daya tal.

Tunda Manal ta samowa su Fuzail gidan Zama Farida kullum sai taje gidan Sarki taji ko masoyinta ya dawo daga tafiya Amma sai ace Bai dawo ba,Yau ma tana zuwa Tanko ya washe Baki,Farida tace Tanko Babban Bafade Ina labari? Tanko ya washe Baki tare da furta sai mun kebe akwai labari na kirki.

Farin ciki ya Kama Farida Tace Muje,Tanko ya jata inda Suka Saba kebewa Tanko ya furta fara Yi min Service da garanbawul Ina bukatar ayi min Juye,notika na sunyi tsatsa ya kamata a goge min su,Farida ranta Bai so ba ta zumburo Masa Baki tare da tsayawa kerere,Tanko ya shafa Hannunta yace wow Fatarki santsi wanne Mai kike
Showing 30001 words to 33000 words out of 153479 words