kala biyar masu tsadar masifa,Mamaki takeyi a Ina ya samu kudin,Haka Shukrah ta zabar Mata Lace fari and Golden,wurin make Suka je aka tsara Amarya,ciwonta ya kusa warkewa dama,dauri aka tsara Mata da Golden Head sannan Suka dawo gida,Farida ma sunyi dinkuna sosai duk sunsha gayu Amma Bata da sukuni sabo da bakin cikin Manal data ga Angon ya kawo mata Kaya masu tsada,Shukrah Tace Saura Lefe bayan daurin aure za a kawo shi, musamman takalma da jakankuna da mayafai kyau da tsadarsu ya Isa,ga Kuma yau Fuzail din nata shima ance zai angwance.
Suna zaune Speaker din Farida na tashi su Masatura sun kunna da kawayensu sai rawa suke Tika,Su Falaqi da abokansa Suka shigo da gudu gida suna cewa Wallahi an daura Sadaki million Daya da mota sabuwa,Manal ta dinga dariya tare da furta mahaukata ku wuce a wanke muku rigunanku Kun lalata su da Miya,Sa'iha ce itama da kwalliyarta ta gaske ba karya sunyi kyau Tace wallahi sarakuna ne a wajen na rantse Aunty Manal,Sadaki Million Daya da mota,Hajiya kirji ta dafe tace bana son karya,wallahi Allah da gaske cewar Alhaqatu data shigo har wajen Muka je,Muka ji Ana sanarwa an daura auren Manal Rabiu da Fuzail,Farida Tace Fuuu me? Fuzail, Farooq ake cewa Yan Mata Manal ta Furta.
Taron daurin aurem Ana ta yiwa Fuzail Murna,Duk Yan Uwan Fuzail tuni sun watse sai Hassan da Hussain da Ameer tare da wasu abokan Ameer na jiki su Biyar da su aka tafi gidan Amarya.
Fuzail ya kalli Ameer yace to yanzu duk abinda za ayi sai ayi,Dariya sukayi,Ameer yace yau fa Dole a nunawa Su Farida zahiri,Sured cewar Fuzail,Motoci na gagara sunfi goma Sha biyar harda jiniya Securities sojoji da Dogarai a saman dawakai Kamar ana hawan sarki suna take musu baya,Jin Jiniya motoci suna ta tsayawa a Kofar gidan ai Farida da Hajiya sun Riga kowa fitowa Sannan auran Yan biki har Shukrah a Amarya Wanda sun Sha gayu,Dogarai suke faman Kirari suna Wasa Fuzail ana Masa Algaita ka rantse shine Sarkin,Manal, Hajiya,Farida,Shukrah da sauran mutane makwafta Yan Uwa da abokan arziki duk suna wajen an cika makil Ana kallon kudi,Fuzail aka Budewa murfin motar da yake ciki rantsatsiya,Wata Sanda Fara tas kwagirin kudi Wato Sandar girma kenan ita ya fara zurowa waje sannan kafafunsa masu dauke da takalmin sarauta na ubansu,Fitowa yayi Kamar daga inji aka fito da shi,yasha uban kyau,Binsa akayi da kallo yuuuuuuu,Ameer Yana Fitowa Manal ta Bude Baki ta Zama gunki,Farida Kuwa Hannunta na rawa ta duba hotunan Fuzail da suke Wayarta ta tabbatar shine ai Hajiya ce ta fara rike katanga Gam sabo da Kar ta Fadi,ita Kuma Farida ta kankame Hajiya Hawaye ya fara zariya a Idonta,Manal ita taga ya Mata Kama da Farooq Amma Bata Gane shi ba,Gabanta ya tako da Gadara Yana Izza yace afwan My wife,Sunana Prince Fuzail Usman Manu Lamido,Bako Wanda yazo gidanku kuka sanshi da Farooq Kuma angonki a yanzu,Karki damu duk abinda nayi banyi Dan wata manufa ba sai don Alkhairi da so da kauna,Manal tayi mutuwar tsaye Hassan da Hussain Sai gulma sukeyi Auntynsu me kyau ce,Jan Hannun Manal yayi Kawai Suka tsaya a gefe ta kasa magana,shi Kuwa Ameer ya musu pics kala kala har su Hussain tare da Amarya Bata magana sai yanda akayi da ita.
Suna gamawa suka shiga motocinsu zasu tafi kenan Farida ta sulale kasa Sumammiya su Kuwa Suka ja motoci suka Kara gaba Basu San dalilin sumanta ba,Hajiya ta rude tana a Miko ruwa,Shukrah itama ba bakin magana Haka taja Manal ciki,Anna Dariya tayi Kawai tayi tana murna,Yazed da Malam ko a jikinsu Abin ya Bawa Manal mamaki,Manal tana yin magana Tace ai Kuwa bazan so wannan ba Ni waccen Farooq Dina nake so wallahi kuka ta saki tana wallahi baza a kaini gidansa ba,sai Kuma ta tuna wani Abu ta goge hawayenta Suka Yi ciki.
Farida Kuwa Ruwa Hajiya ta sheka Mata ta farfado ta Gama Zaucewa Kawai cewa takeyi a Haka Rami a binne ni....a Haka min Ramin Kurege nace Hajiya,wayyo wallahi shine Farooq din Manal ce Kuma ta Zama matarsa....Zumbur ta Mike tsaye sai ta sake komawa dabar tayi zaman Yan bori tare da Bata Rai tace ai Kuwa an tsokalo bala'i Manal baza ta samu Jin Dadi ba Matukar Ina numfashi,Hajiya ihu ta saki lokacin da ta sake tunowa tabbas Fuzail ne Farooq Kuma Basu da bakin Magana a Wajensa ai sai ta sake Rungume katanga Kam kam.
Amarya kuwa tana Shiga cikin gidan ba kida ba komai ta fara Rawar yarabawa tayi kasa tare da dukawa tana ballako kirji har kasa ta Kai sannan ta Mike tayi rawar Galala son ranta yanda Manal ke walwala kafafu ba'a magana,Shukrah Tace kwaso Shoki,Wani wawan Shoki ta kwaso Kamar ta kamfato ruwa a kwano ta wani watsa a gefen inda su Hajiya da Farida suke,Shukrah Tace Kara na biyu, Manal ta sake Ebowa da Hannu Daya ta yafawa su Hajiya a kansu,Na Uku Kuma ta kwaso Shoki da Hannu biyu ta watsa a saman kanta sannan ta shige cikin bedroom dinta,wani tunanin tayi sai ta koma kururuwar kuka ta tuge kwalliyar...
Anna tana zuwa tsinke Manal da Mari tayi tace Yi Mana Shuru Yar Iska marar mutunci duk makiyan Nan bakya gani shine Zaki ce baza a kaiki ba,Yanzu fa kika Gama rawa na zaci ma murna kikeyi to ki bar gidan na gani,Ki kiyayeni wallahi wanne Farooq kina ganin zahiri wannan baifi Farooq kyau ba Mahaukaciya an Miki bayani bakya ganewa duk mutum Daya ne,yanzu da ya Fadi gaskiya da wuri da tuni wannan sun shiga sun fita sun lalata abin,Anna shine fa Wanda Farida ke mafarki,mafarkin banza ke take yiwa Bata Gane ba yanzu Allah ya fassara mafarkin ta gani Kuma Basu da bakin magana tunda ita tayiwa kanta,ta Isa ta kalli Fuzail tace tana sonsa ai Bata Isa ba, Idan Baki sani ba kaf Dangin Fuzail Basu San aurenki da shi,ko Uwarsa Bata sani ba sai yau tana Nan wala'allah ma ta tsine masa yau.
Manal fa Bata yarda ba duk Nasiha da fadan da aka Mata Bata yarda ba,Malam ya kirata tare da Yazed Suka Bata labarin komai Banda na Shukrah sabo da su kansu Fuzail Bai fada musu sun San Shukrah ba,Shukrah ma Bata San Fuzail ba Ammar da Ameer ta sani,Duk da Haka Manal ita Bata yarda ba sun Mata karya sun Raina Mata hankali ai baza ta taba yarda da su ba a duniya,duk abinda akayi dama karya sukeyi Kai gaskiya sun zalunce ta,ita Kuma ba Fuzail take so ba Farooq dinta take so,wannan auren babu so a cikinsa kawai cewar Manal,Tace wallahi Malam auren Nan ya koma auren Dole ya tashi daga na soyayya.
Fuzail sai da Suka je wani wajen cin abinci me tsadar gaske a Nan Suka Yi Walima bayan sunci sun Sha anyi Addua da pics Suka nufi gida, Yana zuwa gida akace yaje Maimartaba Yana jiransa a part dinsa,Yana shiga dammmmm gabansa ya Fadi ganin Umminsa har tazo tare da wasu tsala tsalan Yan Mata guda daya Budurwar Balarabiya a gefenta biyu Kuma da gani kasan Hausawa ne Amma fa Hutu da Naira ya ratsa su Yan Mata na kirki manya masu ji da kansu.
Ummi fuskar Nan tata ba Rahma babu walwala ko digo,tun kafin ya karasa ciki ta watsa Masa harara,Baki ya Bude da Niyyar Gaida ta da sauri ta daga Masa Hannu Tace dakata.
My family my pride
Fadeelah Khan
Maman Dr Khalifa
Zara u
Hauwerh ZD
Maryermdra
Bilkisurabiuado5
Aminat s Abdullahi
Zainab
Zakiyya Bello
Niimatu Musa Mashi
Lilmama
Maryam T Baliya
Sadiya Muhannad Bala
Fatima
Maman Dr
Kallon Ummin tasa yake yi Yana kallon sarki Wato sabo da Sarki baya son auren Manal shi yasa ya hada Kai da Ummi,Magana ta fara ma Fuzail da turanci yanda zai fi ganewa,Haka muka Yi da Kai? Shuru yayi Mata,Tace ka bani mamaki yanda Mukayi dai Ni zaka yiwa Iskanci? Nasan kana sani kayi Haka ba Wani so,Kawai ka rainani,Mahaifinka ya fada min komai da irin matar daka dakko mana,To Bari na fada maka kaji da kunnenka Wallahi baza a haifar min jika ta tsatson wannan yarinyar ba,bazan yarda ba,kaga matan Nan gasu Nan na tabbata sun Fi Manal sau dubu cikinsu ka zaba Daya a aura maka ita idan ma duka kake so zasu aure ka ba matsala.
Akan Yarinyar Nan na dawo gidan Nan da Zama da kanta zata fice ba duka ba zagi,ko an kawo ta baza ka Shiga sashenta ba Itama baza tazo naka ba bare a haifar min jaraba,Maimartaba Yana ji shima murna yayi da hukuncin Ummin,Muna so kayi aure Amma ba irin wannan auren ba,Ummi Masifa da bala'i Kawai takeyi,ciki ka zabi matar da ta Dace da Kai,Ummi Masifa da bala'i take Yi ba ji ba gani kamar zata Ari baki,Dawowa ma tayi Tace Indai aka kawo wannan Amaryar taka gidan Nan sai an daura maka Aure da Khadija ta nuna wannan balarabiyar da Hannunta Wanda Ummi dasu tazo duk Yaran Kawayenta ne Yaran manya Fuzail ganin za a takura Masa sai Kawai ya sulale kasa yayi suman karya,Kansa akayi gaba Daya har Sarki Ana yayyafa Masa ruwa Amma yaki farfadowa sai da Umminsa ta fashe da kuka zata rasa danta Guda Daya tilo,Sarki da masifa ya kalleta yace Taya Zaki ce Za'a daura Masa aure da wasu,tunda kince baza a kawo Manal Nan ba ki barshi Haka Mana,Ummi tana jijjiga Fuzail tana kuka Tace Wasa nake bazan maka auren Dole ba Kuma Amaryar taka zata tare Nan da sati biyu,Sai lokacin Fuzail ya farfado Yana tari kwal kwal,Ummi sai murna takeyi danta bai mutu ba.
Yana tashi ransa a bace ya fice ya barsu,Maimartaba yace da tsohuwar matarsa Ayusha ki sassauta fa kin takura da yawa,ganin Fuzail ya warke Tace wallahi baza ta yuwu ba Ina gidan Nan ko an kawo Yarinyar Nan baza ta haifar min jika ba, sabo da an Raina min hankali wani ne yasha wahalar rainar min yaro in haifi Dana wata tazo Tace zata min iko da shi,Sarki baiyi magana ba sabo da baiga laifinta ba shima,Ummi Tace har gidansu zanje na ci musu mutunci daga ita har iyayen nata sai na musu abinda baza su manta Dani ba a rayuwa ba.
Matan Sarki Kuwa zancen ma basa Yi sabo da Yarinyar Bata Yi musu ba,su a masarauta da Yaran masu kudi Wanda Suka shahara kusan auren Hadi ake musu tsakaninsu masu sarauta da manyan masu kudi,su Basu San ma ta Ina Fuzail ya hadu da Talaka ba har sukayi soyayya,Na'ima da su Fatima Gulmar sukeyi a gidan Taya ma Fuzail ya hadu da ita oho sabo da su Basu ga hanyar da zata hada talaka da Mai kudi ba,Tsabar munafunci har sun samu labarin ai Fuzail ne ma ya Gina musu gida shine yake tallafa musu abinka da Dangin Miji sai suka Kara Jin haushin abin.
Bangaren Fuzail Yana fita wajen Ameer ya wuce yace Ameer kayi sauri ka sanarwa su Yazed suyi Hakuri sai Nan da sati Daya ko biyu za a zo daukan Amarya,Ameer yace sabo da me? Labarin Ummi Ya bashi kaf,Ameer yace tab Aiki babba lallai Kar a kawo Manal yanzu,to yanzu Hotel za a kaita ko me? Fuzail yace Taya Zan ajiye matata a Hotel ai babu Security so kake wani abin tsautsayi ya sameta,Yazed da Malam Basu da matsala nasan zasu yarda ka fada musu a gidansu zata zauna kafin sati biyu,Ameer yace itama fa Manal Fushi takeyi da mu is better a barta kafin ta huce,yanzu Kawai a samu School me tsada a kaita a Bata Driver shike Nan kaga ta fara karatu zata rage damuwa..
Haka Kuwa akayi Ameer ya lallaba su Malam da kyar Suka yarda,Yazed yace Kun San da Haka kuka Bari aka Daura aure so kuke a Mana dariya,Ameer yace ayi Hakuri na Dan lokaci ne,Shike Nan tunda zai Sata a school ba damuwa Naga ita kanta Amaryar Fushi takeyi an Mata karya Kuma Banga laifinta ba,Dama Bata da laifi Dole tayi fushi cewar Ameer, bayan Haka Yazed Anna ya sanarwa yanda ake ciki,Tace dama Manal kuka take Yi ita baza a kaita ba shike Nan Allah ya gyara kaddara ce ba yanda za ayi,Manal tana Jin an fasa kaita sai murna,tuni ta daina Fushi ma yayin da Farida da Hajiya hankalinsu ya kwanta sai murna sukeyi.
Farida Fitowa tayi tana Dariya tana kallon Manal Tace Amarya ta Ango yaushe za a shiga gidan Sarkin ne? Manal tayi banza da ita,Shukrah ce ta bada amsa Tace ai an Riga anyi me wuyar sabo da ta Riga da ta jefa ta Kuma Cafke,karki manta Amaryar Fuzail take har gobe,Farida ta juya idanuwanta tace sai mu gani a kasa idan an isa a kaita dakin mijinta mu gani,ke Shukrah kyaleta cewar Annatu,Hajiya Baki ta tabe tare da zuwa ta fisge Plate dinta a Hannun wata yarinya Yar Uwar su Manal da Suka zo biki,daki suka shige da Farida,Hajiya ta kalli Farida wacce ke Shirin Fara kuka tace karki Yi kuka akan me zakiyi kuka ai wallahi Indai muna Raye ko to
Yarinyar Bata Isa ta zauna lafiya a gidan miji ba tunda Bai aureki ba Itama Bata Isa ba,Yanzu tuggu zamu koma kullawa kafin Nan Gaba idan abin yaki mu koma wajen Malam Dan Haru Haru,Yanzu tunda a gidan Sarki Dangin Fuzail Basu San Manal a Fuska ba kece Zaki koma Acting Akan kece Manal,kafin ta tare kici mutuncin har Uwarsa a matsayin kece Manal,Kinga Dole su bashi Umarni ya saketa,nasan Dole wasu a ciki zasu Zo gidan Nan tunda naji ance Kafin a kaita za a kawo lefe Ke dai Kawai mu Zama cikin shiri.Zuwa dare Annatu da danginta maza da Mata fada Suka yiwa Manal da Nasiha sosai,washe gari da Sassafe Suka tattara nasu ya nasu Suka koma kauye sabo da Hajiya ta hanasu sakewa.
Shukrah Zama tayi tare da Amaryar Suka gyara inda su Annatu Basu karasa gyarawa ba a gidan ko Ina na gidan tsaf da Yamma itama Shukrah Tace Amarya sai munyi waya,kinji na fada Miki Dan Allah kibi komai a hankali Banda wulakanta Ango ki nutsu,a dage da Addua cewar Shukrah,Yamma likis Manal ta zunduma Hijab dinta tace muje na rakaki Titi,Rufa min asiri ai yanzu kin Zama matar aure sai da izinin Ango Zaki fita.
Manal Tace karki dameni Ni yanzu ba Wani sonsa nake Yi ba ya Gama sire min Yan karya sun min karya muje,Manal ta sa Kai Suka fita,suna fita taga galleliyar bakar Mota a Kofar gidansu,Hassan da Hussain ta gani Wani Dogari ya Bude musu mota sun fito suna ta washe Mata baki,Manal tagansu Basu fi 17yrs ba da Alama daga makaranta suke domin sanye suke da Uniform dinsu hadaddu,A tsaye Suka rusuna Aunty Ina yini? Manal tace lafiya Alhmdllh ta ganesu anzo da su jiya bayan daura Aure,Hassan Yace kannen Yayan Brazil ne Muka ce Bari mu biyo mu kwashi gaisuwa wajen Aunty,Manal tayi murmushi Tace na gode,Hussain yace Aunty Yar fillo ce gaskiya wannan Maganar Taki ,Dariya sukayi Manal Tace Bari na raka kawata na dawo,tafiya zamuyi daga school Muka yo nan kawar Taki tazo mu sauketa a gida,Shukrah Tace na gode kuje kawai,Tsoro take ji haka kawai,Su Kuwa Suka tafi,Farida tana labe a soro tana kallo,ranta ya baci,Manal tana shigowa gida Farida ta Mata wata wawar Hankada ta hankadata gaba Wanda Saura kadan ta fadi.
Manal Takaici ya kamata Tace Allah ya Isa wallahi ban yafe miki ba,Farida ta dura Mata ashar,Hakurin Manal ya Kare ta dauki Farida tare da makata da kasa,Farida ta hau kuka tana Kiran Hajiya,Ni na sa ki wulakantasu akan ya aureni Zaki gallabeni ,ai dama na fada Miki Dan Adam daraja gareshi baka San waye wani ba,ko ba me kudi bane shima Yana da baiwar da Allah ya Masa.
Bayan Kwana Uku da daura Aure Manal bata Kira Fuzail ba shima Fuzail Bai kirata ba sabo da Yana so ta Dan huce ne,Manal ma Bata neme shi ba Amma kullum tunanin Farooq dinta takeyi ta damu da shi kullum,yau tana zaune tana cin shinkafa da miyar data dafa sai ga Yazed da uban tarin Kaya a Leda a gabanta ya ajiye tare da furta gashi Nan kayan School dinki ne inji mijinki ki shirya gobe Zaki fara zuwa school 7:30am Driver zai zo ya kaiki ya dawo da ke,Allah ya kaimu cewar Manal Amma Ni Yaya Ina tsoron wulakancin Yan Birni azo a kaini makarantar masu kudi yanda bana Jin turancin Nan Yar Kauye Dani su dinga min wulakanci.
Ai sai ki tsaya kina saurarar mutanen Birni da Yan karya,Ana birge Dan Adam a rayuwa?idan kace Dan Adam zaka biyewa to baza ka tsinana komai ba a rayuwa,Sannan Ina laifi ma yanzu kin iya Dan rubutu da karanta wasu abubuwan,Kuma ai kullum Zan dinga koya Miki a gida ga Shukrah ma Haka ga su Sa'iha Baki da matsala,kayan ta Bude taga Uniform farar Riga da farin Hijab sai wandon Dark blue,sunyi kyau har kala biyar,takalma kala biyar,Haka school bags ma masu tsadar gaske na Yan gayu kala biyar sai littafa da duk wasu kayan karatu,Manal ta washe Baki tana murna tare da cewa Allah ya Kara arziki,Kayan ta hau gwadawa ta gansu dai dai ita sai ta koma wata Yar gayu da ita..Yazed yace sai ki Kira shi ki Masa godiya to Kawai tace amma a ranta Tace wlh Bai Isa na kirashi ba bare na Masa wata text.
Da dare Alarm ta saita sabo da Kar ta makara,tanayin Sallar Asuba wanka tayi da brush ta shirya cikin uniform dinta masu kyau ba karamin kyau yayi ba,takalmanta dark Blue
Showing 54001 words to 57000 words out of 153479 words

Masu Sharhi Ina miko godiya.
AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭
IS DEDICATED TO
DUNIYA TA AAMNA FANS GP.
41-45
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19 Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52