mammakeki,Falaqi ta Harara tace zaka sani idan anyi hutu baza Azo gidana da Kai ba,Dariya yayi yace naji,Kayanta ta hada ba Wanda ta fadawa zata tafi tayi tafiyarta cikin fushi,tana zuwa motar ta Balle ta shiga tare da jefa Jakarta ta zauna tana hawaye,Fuzail yace tashi ki koma a kwana lafiya,Ba kunya Manal ta dauki Jakarta tana murmushi Tace na gode I love you ta juya zata tafi,a fili yace Kaiiiii Baki Bude,Juyowa tayi tare da shigowa cikin motar ta manna Masa kiss a kumatu Tace sai gobe ko jibi? Fuzail ya kalleta ransa a bace yace Baki San laifin da kika min ba? Laifi Kuma? Ni din? Baki ga Ina Fushi ba? Au Fushi kake Yi ? Dan Allah? ai ban sani ba wallahi Yi Hakuri ta dawo Tace me nayi? Au Baki San ma me kika Yi ba?

Au na tuna me yasa ka tafi dazu bayan Kuma Kai ka kirani ai Ni ya Dace ma nayi Fushi da Kai,kasa na fito Kuma kayi tafiyarka Allah ka bani haushi gaba Daya badan na Bawa zuciyata Hakuri ba yau bazan kulaka ba kwata kwata ai Ni baka kyauta min ba,sannan yanzu kazo na tafi gida gaskiya banji Dadi ba, ka nuna min iyakata,ka kunyata Ni a Gaban mutane kaga Kuwa yanda ake sha'awar mu Ana yabonka ka iya kiwo yanda na canja na Yi kiba nayi kyau,sai dai kaji ana ta cewa wannan Yaron Dan Albarka ne,ai Yaron Nan Yaron arziki ne,ai Manal ta Dace,ai koriyar shinkafa yake bata tana ci,ai ac ta sanyayata ai Baku ga yanda yake shagwabata ba,Yana ji da ita,Yana lilitata,Manal tana Jin Dadi,Manal ta Fuzail,Manal din Yarima,Yariman Manal,Ni Kuma Ina yanga Ana fasa min kai ai dole Haba tayi girgiza da kirji a motar Jin wani kida sabo Yana tashi,Tace Ni Kai zanwa Rawar tawa,Oya Fara liki,duk masifar Fuzail Daya kwaso sai ta hanashi magana ma ta sashi nishadi Nan take ya manta da fushinsa yabi Manal da kallo Yana dariya marar Sauti ganin tsakaninta da Allah Rawar takeyi a zaune Kuma kidan take bi,Yanda yake kallonta yasa taji kunya ta fada jiinsa tana Dariya,Yace yanzu dai yau baza ki koma ba? Manal Tace please ka barni kwana Daya Dan Allah duk Yan matan kwana zasuyi,ku dinga yawo ba Mayafi a layi ko? Kuna Hawa Napep Kuna zuwa yawo,Kuna kula mazan wasu Kuna musu surutu Kuna dariya,a Haka Zan barki? Kin tambayeni da Zaki hau Napep ki tafi unguwa? Manal tayi Mukus tace Ni din? Harara ya watsa mata tace to kayi Hakuri kaji ta fada Masa inda Suka je,Fitowa ba Mayafi Kuma na daina Inshaallah, Karki sake ban so na sake ganinki da Belloti a tsaye kinji na fada Miki Ni bana so wlh,Tsohon saurayinki ne fa,har yanzu nasan Yana sonki,Kuma zaina fakewa da gaisawar zumunci Yana kallonki Yana Jin Dadi,Baki Manal ta Bude tace Allah sarki Belloti yayi Aurensa Ina ruwana da shi,kinji ko har Allah sarki kike cewa ai kema wa ya sani ko har yau Yana ranki,Na shiga Uku manal ta daura hannu a Kai tace Sharri zaka min Kuma? Ke kika sani kuma,sabo da Annatu Zan barki ki kwana,Ki kunna wayarki Kuma ki samu room ke daya 2am Oral xxx zamuyi,Manal ta zaro Ido ni dai Allah a'a, Alright sai kizo mu tafi gida,No na yarda sai ka kira,ta yunkura zata fita a motar yace Zauna ai Hira zamuyi zance na Zo sai 10pm Zan tafi.

Manal Tace tunda ka barni na kwana ba damuwa,Ya fito daga motar itama ta fito ya daurata a saman bayan motar daram,Shima ya Dane gefenta ya zauna suna ta hirarsu ta masoya.
Farida da sauran Yan biki suna hango su,sai da aka Gama Dj Suka koma ciki bayan sunci abinci suka Yi wanka aka zauna Ana kwasar shafta da Rashin kunya iri iri, Walida tace wannan guy din fa na Kanwarki Farida Yayi wallahi gashi Yana Sonta da yawa,irin Mijin da nake so me kwarzabar jaraba,ya dinga nace min Yana Nuna min caring, idan anzo harkar bed Kuma ba sauki,Shukrah tace ai suna son juna,Farida Jin ba ita bace sai ta canja zancen da cewa idan Ina Kano sai yaushe zaku Zo to? Rumaisa tace Bayan Amarci yayi sauki,Farida Tace kin tuna min ma ta Mike tare da dakko zumarta da tarkacen magunguna tana Sha.

Sai 9:30 Tanko ya dawo,Ganin Fuzail Yana ta zuba Hirar love da matarsa sai ya koma gefe da Alawar madararsa a Leda da yawa Islaha ta bashi kyautarta,Sai bayan 11 sannan Fuzail yace zai tafi,kiss ya Mata a saman goshinta, Tanko da sauri yazo tare da mikawa Manal Ledar Alawar Madara,Manal ta duba ta dinga Murna Kamar taga Mama,Tace na gode Tanko wallahi kamar kasan ita nake nema,Fuzail yace sai kace me ciki,kudi ya Kara Mata kudin liki ya rakata ta shige gida sannan ya dawo Yana sane da Tanko,Tanko yazo ya Shiga mota ya jashi suka tafi, Fuzail Yana gidan baya yace wace wannan Yarinyar Kuma? Tanko yayi Murmushi ya bawa Fuzail labarin Islaha,Fuzail yace me yasa baka ce na rakaka zancen ba?yaushe zamu je? Tanko yace bazan je da Kai ba wlh Haka Kawai tana Dan ganin kyawuna ka jawo min ta daina gani Tace dama Kaine Saurayin nata,ba ruwana baza ka jawo min ba,sai dai na tafi da Sani tunda nasan nafi Sani Kyau,ai ba a tafiya da me kyau zance,Dariya Fuzail yayi yace shike Nan Allah ya tabbatar da Alkhairi,Tanko yace Ameen a sa Mana Albarka daga nesa.

Tunda aka fasa auren Tanko yasha jaje wajen abokan aikinsa.
Hajiya Kuwa a gidan ta kwana a dakinta tare da Yan uwanta Mata tunda bikin Yarta akeyi sai an Gama zata barwa Malam gidansa.
Washe Gari da wuri Belloti yace Amarya ta shirya zasu Kama Hanya,Duk iya kayanta na sawa da komai an shirya,Yana zuwa a bayan motar aka shirya komai aka rufe,Malam da Yan uwa sunyiwa Farida Nasiha daidai gwargwado,Har Hajiya an Mata fada yanda ya kamata sai kuka takeyi Haka aka sata a Bayan mota sabo da Belloti yace zai dauki Ubangidansa a gaba,shi kadai Yaja Amaryarsa Ana daga Mata Hannu Suka tafi,a Kofar gidan Yayan Uche yayi parking,Uche ya fito da kayansu shima aka sake lodawa a motar sai lokacin ya kula da mace,Bai San Belloti aure yayi ba,yace Me kanayi da Mata ga Wannan cikin mota? Belloti yace muje Zan maka bayani Oga,Uche ya Shiga karewa Farida kallo wacce ke lullube da mayafi tana shesheka,Shi dai Uche ba tare da yadda ba ya shiga mota Belloti Yaja Suka dauki Hanya.

Sai da suka danyi nisa Bayan sun hau babban Hanya Uche ya sake cewa cikin hausarsa da Bata fita we Ina Wana Mata za shi? Bana Gane ba,Beloti karka jawo nayi loosing Control baza kaji da kyawu ba ehem chike nan.
Farida kuka ya tsaya tana zare Ido,Matsiyaci Belloti sai da ya tabbatar sun shiga daji sosai sannan yace Amarya tace,aure aka Daura min,Uche yace I don't Understand you aure like how? Aure daka sani wallahi kaji karshen rantsuwar mu kenan,Uche yasan idan Belloti yace wallahi to da gaske yake, Hannu ya daura a ka Yana ihu yace ewoooo.....ewoooo.....tunda kayi ransuwar masallaci irin naku fa to fa nasan da gaske ne,Ke wannan yaro baka da ankali,ya Kuna aure Kamar wasan kanan kananan Yara? Yaushe ka fada soyayyar Belloti? Yaushe kasan Hali nasa? Aiki Nasa duk baka sani ba ka yarda just like that,yace Yana sonka ka Amince kace yes wannan yaro baka da ankali wooooo Hausa people wooooo,Farida ya sake juyowa ya kalla ta zazzaro ido,Uche ya sheke da dariya yace abeg no vex kaso mijinka wooo ba ruwana,bani Zana dau nauyinka ba Ina fada maka gaskiya ne baka Yi hankali ba,ko baka da Iyaye ne? A street ya ganka? Farida ta fashe da kuka Kawai,Uche ya Bude Baki yace I'm Sorry Baby sunanka Ummee? Belloti yace sunanta Farida,chaii da Ummee yayi Kama a hausa people,karka yarda da wani Farida kafi dacewa da Ummee,Uche idan ya kalli Farida sai ya kwashe da dariya yace zaka ci Ubanka yaro dakinku Daya tal a gidana.
Kidansu na church Wanda akayi da yaren Igbo Uche ya kunna,ya saki kidan ba Dadi Ana ta ambatar Jesus Ana gwalan gwalan din yare,Belloti duk ya iya wakokin sabo da Zama da su Uche sai bin wakar yake Yana tuki Yana shara uban wuta,Idan aka Ce Jesus sai ya daki sitiyari ma,Farida mamaki ya kamata,Sai ga Belloti ya zaro Wiwi ya kunna tare da furta Sorry Masta,Uche yace Miko min Daya Nima,Suka bulbule Farida da Hayakin Wiwi gashi sunki sauke ko glass,Farida dama ba kunya gareta ba Tace Dan Allah ku sauke glass kana uban shara gudu kana Jan wiwi ga Kun kulle ko Ina zaku sa min ciwon Kai ko tsoron mutuwa bakwa yi? Belloti yace kowa ya mutu kwanansa ne ya Kare Aljanna ta me Rabo ce Yana sheka dariya,Uche yace kai yarinya ka daina damuwa idan an mutu chike nan bacci akeyi me dadi a kabari ba Wanda zaiyi Disturbing naka, yana Kora wata Yar giya a karamar kwalba,Belloti yace ah Oga Ashe akwai ragowar Votka? Kwana Guda kenan ban Kora ba,ya motar kayan nan hope ba a Kama Mana ba? Uche yace Kaya suna Nan sunje tuni shi yasa na matsu mu koma akwai sabuwa an fitar da kwalaba karama Amma tafi ta Votka girma,Belloti yace Nice very very nice....akwai harka kace suka tafa,Farida taga ko kulata Basu Yi ba,Harkar gabansu Kawai sukeyi sauraronta ma basa Yi,Sai da aka Yi nisa Belloti ya juyo yace ke dama kina ciki ne? Ai na manta Dake wallahi,Farida ta harareshi tare da furta ta sama na tashi ai,karfa ka Raina min hankali wallahi nafika tijara,idan kanka Yana hayaki Ni wuta ke tashi a ciki,Uche Yana ji yace wuta na tashi a kanka zaka rasa gashi yarinya gashi wajen mace akwai Chau ,Tsaki Farida tayi Kawai,Belloti yace Zaki San kinwa uban gidana Tsaki Zan ga Tijarar da kika fini,wallahi kika min Iskanci a dajin Nan Zan tsaya na jefar dake,bana son Rashin kunya wlh ki kiyaye karki jawa kanki Baki Sanni ba bani da mutunci cikakken tantiri ne Ni,Bari muje gidan Zaki gani da idonki,ba wata Yar birni data Isa ta Raina min hankali yanzu,Aurenki nake Yi ki Lallabani ko ki Zama sakin Wawa kwananan Nan,Shuru Farida tayi Tace Amma kasan nayi maka Adalci ko zuwan farko na Amince na soka,da kika ga Baki da mafita ba ai dole ce tasa Kika aureni Amma da Wanda ya fini yazo ko kallona baza kiyi ba,wanne darene jemage Bai gani ba,wallahi duk abinda kikaga ya samu gafiya jelarta ce da ta Bari a waje,ki Lallabani mu zauna lafiya,bani da Burin zaluntarki ko Dan sabo da Manal,Darajar Manal zakici Amma idan kinyi Hakuri da abinda Zaki gani mun zauna lafiya,Ni soyayya nake bukata,idan Zaki min ba abinda bazan Miki ba,Bana Neman Mata shi yasa na aureki,Zaki ga abubuwa daban daban,idan kinji ki kinki gani mu zauna lafiya Idan kinki kince shishigi Zaki min Kuma jikinki zai fada Miki.
Idan Baki yarda ba idan munje sabon Hari ki Shiga cikin bariki ki tambaya waye Belloti,Sabo da Manal kadai Zan Dan dinga raga Miki.










Ina Matukar godiya masu sharhi.





AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭





DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP







81-85






Official





By
AsmaBaffa






Page naku ne

Bilyn Nas
Nafee
Leela
Tajra lollipop
Mom Aneesah
Maryam Adamu
Teema
Malakso
Fatima Bature Ali Mmn Muh
Amina Baba






Tafiya sukayi me Dan Nisa Belloti ya sake juyowa yace kina ciki ne?Farida tsoro ya kamata tace Dan Allah mu koma a dakko Yaya Yazed muje da shi yaga gidan,Belloti yayi Dariya yace kin fara tsorata kenan? Kin manta Sanda nace Zan dakko muku motar haya guda daya aje ko da kawayenki ne Hajiyanki tace ai tunda nace baza a Kai kayan jere ba komai na zuba a gidana ba damuwa,in Bari daga baya za a hada dangi suzo suga gidan daban tunda ba a shirya ba,ba uban Wanda nake Jin kunya a danginki tunda an rigada an daura magana ta kare,Malam Yana cewa zai hada dangi a Basu mota ke da Hajiya kuka zakalkale Kuna cewa da su Annatu Yan Kauye za a tattara a Kai Miki gida zasu lalata Miki gida,akan a kwashi Yan Kauye suje sai dai a tafi Dake ke Daya,Malam yace shi Kuma baza aje da kawaye ba sai dai danginsa idan Baku Amince ba kibi Ango ke Daya,kika biyo Ni,ai ban Miki dole ba,in Banda ke shashasha ce ance Miki aure Wasa ne? Dan kin San gidan Iyayena Ni kika sani? Kuma a kauyen nake? Ke Farida ban San Baki da hankali ba sai Dana aureki ke da Hajiyan Taki duk kwakwalwar tinkiya ce da ku,a Haka Kamar wayayya Ashe banza ce ai gwara Yan kauyen da ke,ke a jahilan ma kinfi jahili Jahilci wallahi har kina da bakin zagin Yan kauye? Uban me kuka Tara? Nawa ne da ku?

Tasan laifinsu ne ita da Hajiya sukace baza a Kai musu Yan Kauye ba, ba bakin Kare Kai sai Tace an kusa zuwa ne? Belloti yace sa takalminki...Farida taga anyi tafiya tafi ta 1hr, Uche Yana wakarsa Yana cewa sa min wakar Emenyi Wanda yayi a France Church,Belloti yace wayyo kalbina wakar tana min Dadi duk da ba addini na ba,Baki Farida ta tabe tare da kwanciya a Bayan kujera ta rufe Fuska da mayafi,Belloti yasa Hannu ya dage mayafin tare da cewa gashi Nan nayi Budar Kai tunda ita kike bukata a dakko dangi suyi miki, kin rufe Fuska kamar Munafuka,Farida Bata ce komai ba,Uche yace Amarya kayi Chau,ka kula da mijinka wooo Everytime Beer,Consumer ne ni a Kira giya cewar Belloti,Waka Suka canja ta Yan Naija suna bi da bakinsu sun cika motar da Hayaniya,Farida a ranta Tace komai akayi da jaki sai yaci Kara,dama mutumin Kauye Ina zai waye,Belloti yaji tsakinta yace kwantar da hankalinki Amarya munyi nisa a tafiyar Nan bazan gaji ba Muna zuwa akwai Fresh Cucumber, sabo da Ni kin San Cucumber aka min ba Banana ba,Banana ta Yara ce ai ni Belloti Rabajas,ga katuwar Katifa sai ki juya sau Uku Baki Fado ba ba irin ta dakinki ba, Juyawa Farida tayi ko kulashi Bata Yi ba.
Suka ci gaba da tafiya yunwa ta kwakwule Farida amma Suka ce su baza su tsaya ba giyarsu ta ishe su,Farida Tace Dan Allah karku kashe mu a mota kuna ta Shan Kayan Maye,just Ordinary Alcohol ce fa Cewar Uche,Belloti yace Kai rabu da ita cocaine Muka Sha Dan Uwarki.

Shuru Farida tayi taga abin nasu ba arziki,Sai lokacin Farida ta tuna da Innalillahi wa innailayhirrajun....ga yunwa ga gudu bana Wasa ba,ga Shan giya suna ta tafiya faaaaaaaaaaa Haka Farida ta bude Jakarta kazar maganinta na Mata da Walida ta saka Mata a Leda Tace Kar taci sai sunje gidan Belloti yunwa tasa ta dakko abarta ta Shiga yaga tana ci tana Shan Malitinar Dake jakar ta,Belloti yace kaza Haka ba bismillah? Farida ta dauke abarta daga saman cinyarta ma ta rike a Hannunta sai da ta cinye abarta tas har Kashin sannan ta jefar da Leda ta goge Hannunta yace Kara wuta ja muje kowa ya mutu kwanansa ne ya Kare cewar Farida ta cika timbinta,Basu je Kano ba sai dare suka isa sabon gari,Wani Dan gida ne me Dan kyau yasha tiles harda Gate gidan Uche kenan Nan Suka shiga,Farida ta danji sanyi a ranta ganin gidan ba laifi koma yane da sauki sauki,Gidan ga haske ko ina,Belloti Yana kulle mota yace shigo min da kayana,Shi da zai mata iso amma shi za a dakkowa kaya,Belloti yayi ciki abinsa Yana Mika,Farida ta dauki iya kayanta ta bi bayanta,Daki ne Kato yasha tiles da toilet a ciki sai Katifa da sauran tarkacen girkin Belloti da Dakin tsaf da shi sai Yar Kura ta alamar me dakin baya Nan,Ina kayan Nawa? Farida Tace suna waje a Compound Ni baiwarka ce,Mari Kawai taji Belloti ya kwasheta da shi,yace ki kula wlh ba a Gaya min ko wacce magana,Idan baza ki gaji da furuci anyhow ba to Zaki ga anyhow,If you do anyhow you go see anyhow wallahi,Ina tausaya Miki bakya gani,Tsawa ya Mata dakko min jaka,Farida tayi waje da gudu ta dakko ta kawo yace Fara shara da mopping bana son kanzanta yanzu Zan fita kafin na dawo Naga ko Ina tsaf.
Farida Hawaye ya zubo Mata na tausayin kanta Tace wallahi gwara Tanko na,na rantse da Allah bazan yafe maka ba,Belloti yace Bari na dawo mu Sha Amarci yayi waje.

Manal Kuwa Ana tafiya da Farida bayan mutane sun watse,Hajiya ma tafiyarta tayi gidan yayanta,Su Annatu ne suka zauna zasu gyara gida zuwa gobe su tafi sun fasa kwana ukun da Suka ambata sabo da irin wulakancin da Hajiya ta musu akan Kai Farida daga Malam yace aje dasu suga inda Farida zata zauna, Manal kuwa Jin jikinta ba Dadi kullum canji take ji sai ta tafi wajen me chemist Salisu Tace Test zaka min na ciki,Salisu yace Bari na turaki wani lab akwai kawata tana da private kije su miki a can,Idan ya wuce Unguwar nan ba inda zanje kasan Ina da aure,Salisu yace ga wajen can Yana facing chemist Dina,Okay Manal ta Furta tare da tafiya wajen,Kudi ta biya tare da Mika musu takardar da Salisu ya bata,Gwajin da ya kamata ayi Mata suka Mata ya tabbatar tana da cikin wata biyu,Result suka Bata,Manal ta koma wajen Salisu tana murna Tace Alhmdllh na tsallake shiga layin juya,Salisu yace na tayaki murna,Manal da Murna ta dawo gidan Malam,Aka ga tana ta murna,Hajiya Sharifa Ce suke Dan Wasa sai Manal ta fada Mata a sirri tace karki fadawa kowa ciki ne Dani wata biyu,Hajiya Sharifa ta rangada Guda kowa yaji Ana tambaya Mene? Tace ance Kar na fada Annatu ce zata Yi miji,Shike Nan zancen ya watsu kowa da abinda zai fada ana murna,Annatu tana jinsu itama taji dadi,Manal guduwa tayi ta
Showing 105001 words to 108000 words out of 153479 words