murna sabo da ita Bata Haihu ba,ba a Dade ba Annatu ta yanka tinkiyarta tare da cajawa Yazed suna ta sa Masa Yazed,Haka Yazed ya taso cikin duka,zagi da tsangwama wajen Malam sabo da Aljanu sun bada suna Anna ta canja masa.

Bayan Shekaru Bakwai Hajiya ma ta samu ciki,murna Kamar tayi hauka itama tana samun ciki Malam ya tsaneta,bayan ta Haihu Nan ma Aljanu Suka ce a sa Mata Masatura,Itama Hajiya ganin an canjawa Yazed shine ta canja zuwa Farida,Malam ya dinga Bala'i yace sai ya koresu da kyar aka bashi Hakuri,Bayan wasu Shekaru Anna ta sake Haifo Manal,ranar Suna rikici ya hauke tsakanin Malam da Anna, aka sawa Manal Waqia da Umarnin Aljanu,Yazed da Kansa ya canja Mata suna Manal,Lokacin sai da Malam ya Kori Yazed daga gidansa ya koma kwana a masallaci,sai da ya kwashe watanni kafin Malam ya dawo da shi,duk wani aikin walaha Malam to Yazed yake sakawa har Yazed ya taso sosai tsakaninsa da Malam sai Harara,Kudin Makaranta ma Anna ke siyar da dabbobinta tana biya masa.

Lokacin Aljanu Suka hanashi Saduwa da matansa na sunna sai dai matan banza kullum baida Aiki sai Zina da Mata iri iri,gashi duk irin asirin da aka ce yayi ba ruwansa aikatawa zaiyi,ya raba aure ba adadi,ya haukatar da mutane,yayi Abu munana iri iri Wanda kisa ne Kawai Bai taba kashewa ba,Hajiya gajiya tayi ta fara masifa akan baya Bata hakkinta har an kwashe shekara Biyu,ganin Haka sai ya koma amfani da Yatsansa Wai Haka zai biya musu bukata,Kowacce ranar kwananta to da yatsa zaiyi amfani,Annatu ta rasa Gane inda yasa gaba Ganin irin wulakancin da yake wa matansa

Ganin Haka Hajiya ta tashi tsaye tace ai shima mutum ne Dole tsafi zai ci shi direct ta tafi gidan Malam Dan Haru Wanda taji Mata suna labarin iya aikinsa,tana zuwa Tace so take a juyo da Hankalin Malam gareta ya dinga Mata abinda take so,Ai Kuwa Aiki yayi Malam sai yanda Hajiya tayi da shi,ita Yana biya mata bukata Amma Banda Annatu da ta Zama aikinta gyaran gida da girki ta koma Yar aiki a gidan sun hade Mata Kai da Hajiya,Ana Haka Hajiya ita taci gaba da Haihuwa ita Kuwa Annatu shuru Sabo da baya ma Saduwa da ita,Katsam Watarana aka Kama Malam da yarinya karama Yar Shekara goma zai Mata fyade Allah yasa wasu maza a cikin Almajiransa suka Tona masa asiri sai da ya zauna a gidan yari na wata takwas,Bayan ya fito ya Dora daga inda ya tsaya ba abinda ya fasa,tunda Manal ta taso gwanin sha'awa kyakyawa da ita Fara kwal Hajiya ta tsaneta,Watarana Annatu ta shiga makwafta kafin ta dawo Hajiya ta durawa Manal Fiya fiya a kunne,Anna ta Iske Yarta ta sankame da gudu ta kaita asibiti yarinya tana Suma,Malam Kuma yace kwandala bazai biya ba,tunda Anna ta samu Manal ta warke ta hada tarkacenta da Manal ta gudu kauyensu,Malam sai takardarta ta saki ya aika Mata,Yazed yayi kuka ya gode Allah.

Daga Nan Kuma Hajiya ta koma Kan Yazed,Yana Namiji amma har girki shi yakeyi a gidan,ga shara da sauran ayyuka,Idan yayi ma Bai huta ba Haka Malam zai bishi da zagi da duka,Itama Hajiya tana yi masa mugunta kala kala a Haka Yazed ya taso har ya girma,duk da Haka Kuma Yana Dan fita ayyuka iri iri idan ya samu kudi ya biya kudin makaranta ko Annatu ta siyar da dabbobinta tana turo Masa kudin a Haka har ya Kai matakin Degree Lokacin Hajiya tana da Yara biyar hakan Kuma Malam Aljanu Suka hanashi Haihuwa tunda ya bawa Hajiya wani ruwan Rubutu ta Tasha Bata sake samun ciki ba har yau,duk Halayen Malam Dana Yan Uwansa babu Wanda Bai Sani ba,ba a yabonsu ko kadan.

Katsam Allah yajarabce shi da wata cuta wacce an rasa kanta,Kafafunsa basa Aiki,Haka wuyansa ya karkace gefe ga hannu ma ba sosai yake Aiki ba komai sai an Masa,magani ba Wanda basuyi ba,test anyi iri iri ance lafiya komai nasa,gaba Daya cutar Saida ta cinye arzikin da Malam ya Tara kaf Haka ta cinye na yan Uwansa,ga Harkar malitar tasu ta tsaya an daina yayinsu maganinsu ya daina Aiki kaf,gaba Daya sai Suka daina ta Dole,ga Talauci Yana Kara riskarsu Yan gonakin ma da suka rage Gomnati ta kwace,Ganin Bala'in yayi yawa Malam da Yan Uwansa Suka Fara Dana sani,kullum cikin nadama suke,Yazed Kuma ya gaji sabo da lalura akwai tausayi,Malam Salahu yace yazo da Malam Kaninsa a gwada Yi Masa karatun Qur'ani na sati biyu ko za a dace Suka tafi da Malam Kauye za masa maganin.

Ci Gaban labari

Fuzail da fara'a ya furta Ina kika Shiga Haka? me ya samu wayar? Manal tana wani murmushi Jin muryar Sahibinta harda lankwashe Murya Wanda Bata San ma tayi hakan ba ta furta Wayar ce jiya ta dauke duf nayi nayi taki kunnuwa na rasa dalili,yanzu wannan layin na waye? Fuzail ya tambaya ta furta Na me Shago ne,Kishi ne ya Kama Fuzail me ya hada ki da me Shago har da wani karbar wayarsa? to ba Kai Zan Kira ba shine hadina da shi kawai,Ana yin Sallar Magriba Zaki ganni a Kofar gidanku,Manal ta matsa gefe tana kasa da Murya cike da Jin Dadi tace kayi min kwalliya Shadda zaka saka min,Fuzail yasan an bashi Aiki sabo da saka shaddarsa baifi sau hudu ba a duniya,to Kawai yace,Tace Anjima Yaya Yazed zasu da dawo da Malam idan kazo sai ku gaisa,Fuzail yace Allah ya kaimu,me Zan siyo Miki? Ba komai gwara ka dinga Tara kudin Nan sai munyi aure ka siya Mana kayan abinci shinkafa buhu Guda nasan ma Sai mun shekara Bamu cinye ba,Dariya ta bawa Fuzail ita Bata da Aiki sai zancen abinci.

Kannen Fuzail ne Suka shigo part dinsa su Hudu,Yan Mata biyu Na'ima da Fatima sai Maza biyu Yan matasa Hassan da Hussain,Duk sun Sha gayu suna zuba kamshi sanye da wasu arnayen yadika masu tsada,matan Kuwa wasu lace ne a jikinsu masu tsada,Fuzail Yana waya da Manal suna Kallonsa sai Dariya yake Yi,suka dinga mamaki su Basu San ma ya iya Dariya ba, Kallonsa suke Yi Kawai kamar sun samu Tv,Har ya Gama sannan Na'ima Tace Yayan Brazil wannan tayi sa'a ko wace Wai a Ina kuka hadu ne ko a London kuka hadu? Fuzail yace no a Nan take,Wow Yar waye Haka nasan ma Yar gidan wani kusan ce a kasar Nan ya sunanta? Fuzail ya fadada murmushinsa duk akan zai ambaci sunan Budurwarsa ya Furta Manall harda wani Jan L din,Fatima ta koma kusa da shi Tace Nice name yaushe zaka hada mu da ita ta Zama kawar mu? Fuzail yace me tsada ce sai an kusa biki Zan hada ku,wannan Kalar ba irin Taku ce ba ta manyan Yara ce,Huuuu Na'ima ta Furta Allah na matsu Naga irin Haduwar ta nasan ma muguwar Yar gayu ce,Fatima Tace me Ilmi ma Kuwa Allah yasa muma a London Muka Yi karatu mun Iya irin turanci nasu, Fuzail shi yasan me ya sani Kawai Hmmm yace,Hassan Yace Watarana zamu rakaka zance tun yanzu ya kamata na Zama Dan Gaban goshinta,Hussain yace nine me rike Mata jaka Yayan Brazil,Fuzail ya wani harde yana karkada kafafu Yana hango Kansa Manal ta Zama matarsa ma yace Wanne Dan Gaban goshinta zaka Zama Ni Kuma ta kaini Ina? A keya za a ajiyeni Ni ko a gadon Baya? Fuzail yace ji min yara so kuke ku kwace ta ku kuna a gabanta Ni ta maida ni Bayanta kenan, Su Na'ima Suka dinga dariya su dama suna son Hira da Fuzail zasu ci Dariya.

Yau Farida da Rana ta shirya zuwa gidan su Ruma zata karbo kwancen kayan sawa,ta sauka a Napep kenan zata Dan shiga ta layin su Ruma a kafa sai ga Arnayen Motocin Fuzail sun Kai hudu ko wacce tana sheki da walwali masu tsadar gaske,sai binsu ake da kallo,Katsam Farida taga Number Fuzail ai sai ta hau dagawa Motocin Hannu suna wucewa tana daga musu Hannu tana washe baki tana Mijina...Mijina,Fuzail Kansa na kasa a mota gashi ta Sha tint Bai ma ga wata Farida na daga Hannu ba,Yau Kuma a cikin motar Fadawa masu kula da prince Tanko Yana ciki shine ya kula da Farida a gefen Titi tana daga musu Hannu,Dake Motocin a hankali suke Tafiya da sauri ya sauke Glass kasa tare da leko da Kansa ta window yace da karfi Faridaaaaaaaa.......na gani na gode daga Hannun ya Isa Haka Kar damatsanki su kumbura,Ganin Tanko ne da sauri ta sauke Hannunta tare da Jan Tsaki kafin ta tafi ma tuni Motocin sunyi nisa Amma duk da Haka Farida da Murna a ranta ta Shiga gidan su Ruma Baki Kamar gonar auduka.

Manal shirin tarbar Masoyi akeyi da wuri ta wuce gidan su Shukrah Kamar yanda Suka tsara ,Shukrah tace tazo su yiwa Saurayin nata Samosa da Springrolls, Shukrah sabo da kirkin Manal da kudinta ta siyo kayan hadin komai,Itama Iyayen Shukrah da danginta zuwan Manal biyu kacal amma ta Shiga ransu,Maman Shukrah harda ita ta tayasu aka Yi da yawa yaji Hadi,Maman Shukrah tace idan Bai ci ba ki zuba Masa a Leda ya tafi da shi,Manal wacce ta koyi yanda ake abin itama Tace to,a gidan tayi wankanta sannan ta maida kayan jikinta, Haka su Shukrah Suka ebi nasu Suma Manal ta taho gida da abinta harda siyo lemo Cock da ruwa Faro.

Tana zuwa ta ebarwa su Hajiya Nasu sannan ta ajiyewa Yaya Yazed da Malam sabo da sunce suna Hanya Suma,ganin Magriba ta kusa Manal tayi sallar Magriba yanzu ta iya Sallah babu gargada ta koyi abubuwa da yawa na Boko Dana addini ba laifi sannan ta Dan goge an fara samun canji zuwan Shukrah ya jawo.

Cikin kayan da Shukrah ta bata ta dauki atamfa wata Brown and Black Yar dubu Uku da dari biyar ce Amma sabuwa duk wannan Shirin Ameer ne aka ce size ne ya yiwa Shukrah kadan shine ta barwa Manal,Dinkin Riga da skert ne,Shukrah Bata San Manal ma a Haka ake rainata Amma a jikinta tana da kauri kayan da kyar suka shige ta musamman wajen Kirjinta da Hips dinta ta cika su fam kadan suke jira jip ya Balle Kuma duk kayan kala Uku atamfofi sai lace Daya Haka dinkin yake Kai Daya,ta zuba kyau,cikin kayan kwalliyar nata da Shukrah ta Dan Bata ragowar nata ta shafa powder tare da zizara tozali kadan yanda Shukrah ta koya mata,Sai Maroon jambaki ta Dan shafa sama sama shike Nan ta hakura gudun kar ta Bata fuskarta,Dan Ragowar Body spray dinta ta Ajiye a gefe tare da dakko mayafin da Shukrah ta bata Guda Daya Baki da takalmi me Dan tudu Baki shima duk sababbi ne Amma aka rainawa Manal hankali Wai wani a kwance suke,Ita Kuma ganin kayan Yan Birni fes sai ta yarda.

Ameer ne ya sa Fuzail a gaba Yana ta dariya an Kira tela ya Gama auna size din Fuzail zai Masa dinkunan Shadda da yadika,Fuzail ya zabo colors da yake so kala bakwai,Yace Masu Araha nake so,Yadin ya zabi gaba Daya Ishurunka Maraya Shaddar Kuma me mugun Araha Suma Ana gani anga na talakan Dan gayu,Ameer ya dinga cewa Talakan Dan gayu,cikin shaddojin masu Araha tela ya dinka Kala Daya wata dark Arsh shima dinkin aka Yi shi wani na takakawan samari dai Amma yayi kyau musamman anyi shi dai dai jikinsa cif cif,tela ya kawo kala dayan Guess House yace sauran sai jibi Zan Gama dinkawa na kawo,Ai Kuwa tela ya washe ya samu kudi a wajen Fuzail da yawa,Babu Wanda yasan me su Fuzail suke kullawa da Ameer, Ameer yace ka taso muje na saka a Taxi wannan gyaran naka ya Isa Haka kayi kyau,karka fesa turare sai Dan kadan zaka goga,turaren ma marar kamshin kirki ya shafa kadan,aka Dora sabuwar Hular gashi Amma wannan gashin Bai Kai na farko yawa ba Haka gemu da sajen ma kadan aka kara sai yasa Face mask Kalar Shaddar tasa,Kyan da dinkin ya Masa ya Isa sai dai me Araha ne, Takalminsa yasa normal Black Slifas yanda ba Wanda zaice Yana da kwandala,Bakar ledarsa ya dauka da sakon Manal a ciki,Ameer ne yayi Driving nasa zuwa Gefen kwalta ya tare Masa Taxi sabo da shi baya son Napep Bai iya hawansa ba sai Dole.

Lokacin Farida ta fito da Kaya Niki niki a Hannunta tana gefen hanya gashi Ana wahalar mota ga dare Yana yi tana ta faman jiran Napep ko Taxi,Fuzail ya hangota a duniya baida wacce ya tsana irin Farida,tunawa yayi Yar Uwar Manal ce ko ya auri Manal sai ta dinga zuwa wajenta zumunci sai yace da Me Taxi ya tsaya ya dauke ta.

Farida Bata lura ba tana ganin Taxi Tace da sauran masu jiran mota ku taho mu shiga waccen ai Kuwa aka ruga da gudu,Farida ta Fada mota abinta Kawai kayan nata ta Dora a saman cinyar Fuzail yaji uban nauyi,Murya ya canja yace Malama kin Dora min Kaya,Farida da bala'i ta kalle shi sai taga Farooq ne,wani tsanarsa taji tare da Jan mugun Tsaki sai da kowa ya kalleta,ko a jikinta tace ka tarewa mutane waje a Ina kake so na Dora kayan Nan motar Haya ce idan kayi zuciya ka siyi taka,Tunda baka da motar ai Dole kayi Hakuri da halin daka tsinci kanka Malam da Allah Miko min Daya Ledar Nan, aka Miko Mata ta sake jibga Ledar a Cinyar Farooq,Ransa ya baci ya kusa loosing Control Kawai ya danne da kyar,Driver da Kansa yace Amma ke Baki da tarbiyya shi yace a tsaya a dauke ki Ana wahalar mota amma sai ki Masa Haka a mutane banza dakikiya dalla fitar min a mota na fasa daukanki.

Farida ta sake Jan Tsaki tace yo da ace nasan shine ma yace a dakko Ni ai bazan shiga motar ba,wannan banzar motar ma an fada maka Nan gaba wannan zata gagereni ne?kazo Nan da wata Daya nayi maka alkawari Ni Zan siya maka Motocin da Suka Fi wannan tsada na baka irinsu goma kaci gaba da haya a ciki kana kawo min balance,Driver ya Mata up and Down yace a hakan? Amma kike faman yawo a kasa da motar haya ke dalla fita Mahaukaciya gaja dake,Uwarka ce gaja ta furta tana fita a motar tana sani ta sa Hannu ta hankada Kan Prince Fuzail ba zato ji kake Kummmm....a jikin glass din Window, badan sumarsa ba da yau sai gefen goshinsa yayi kulu Allah yasa tudun gashin ya Dan tare kadan ya bige,Wajen ya Sosa tare da jinjina kai,Farida ta fice tare da banko Kofar da karfi,Driver ya fito Wandonsa 3qtr Yana sabulowa gaba Daya Rabin duwawunsa a waje yake tsabar tashanci shi ko Boxers baya sawa Haka yake barin Rabin Duwawunsa a waje,Matakan tsaro Indai Suka gani sai sun Masa nasiha Amma yaki ji,Haka ya fito tare da tsayawa a Gaban Farida yasa hannu a hantsar Wandonsa ya tattaro gaba Daya harda Sandar girman tasa yayi sama da su ya samu Farida ya kwada Mata Mari yafi biyar sai da aka rike shi da kyar amma har yasa kafa ya fatalar da ita gefe zai taka Mata ciki aka rirrike shi,Fuzail ya gyara kwancinyarsa a mota Yana kallo Yana Jin Dadi.
A ransa yace Inama yarinyar Nan tasan waye Ni na samu nasa a kaita a garkame shegiya a prison na gidan sarauta kullum ta dinga kula da dokunan gidan Sarki gaba dayansu duk yawansu wallahi har wanka sai ta dinga musu tana brushing musu jiki.

Driver ne ya shigo motar ya bar Farida a gefen kwalta tana tsala ihu wasu da Basu San me ya faru ba suna ta Bata hakuri aka sa ta a mota,a ranta tace wallahi akan Manal Zan Rama zaka gani yau Indai can zakaje wallahi Nima yau sai na Bata maka Rai shege da shaddarsa Yar Dubu biyar talakan banza.
Driver Kuwa passengers suka cika a motar aka matse Fuzail Dan sarki Guda a lungu yana manne da Jikin Kofar mota numfashinsa Kamar zai dauke ya Saba idan a turai ne duk inda zaka je a taxi to Kai kadai za a dauka komai nisa,a Nan dinma Farida ce ta jawo masa wajen Kiran sauran mutane suzo ga mota.

Ga goslow kafin azo ma ya Gama jigata a mota Shaddar tasa duk ta yamutse,Ana zuwa ya mikawa driver 1k zai bashi canji yace barshi Kawai,Driver ya dinga godiya ya wuce,da bakar ledarsa ya karaso Kofar gidan su Manal wacce lokacin ta Gama shirinta tsaf,Falaqi Yana waje ya Gane Farooq da gudu ya shiga gidansu Yana kwalawa Manal Kira ga Wannan mutumin Nan da kika taimakawa me gashi da yawa,Manal a fili Tace baiyi Aski ba kenan,Mayafinta ta yafa tare da lekowa ta hango shi Kuwa a gefe yayi wata tsaiwa ta manyan Yara a tsaye an harde kafa,Manal ita dai wankan Nan ya Gama tafiya da Imaninta Allah sarki Bata Raina ba ai ita gani tayi ma ya Gama kure karshen wanka a duniya,sai da ta Kare Masa kallo sannan ta fito gaba Daya tana takawa inda yake da kyar take tafiya sabo da Bata Saba da sa Kaya damammu ba,bayan Haka ma sun so suyi Mata kadan,Fuzail sai kallonta yake yanda ta zuba kyau Kamar a sace ta a fece,Shi Bai ma San ta Kai Haka ba sai yau,har kunya taji yanda yake Kare Mata kallo a ranta taji Dadi tasan ta Gama haduwa tayi kyau tunda ta Zama abar kallo a Wajensa da duk Wanda ya kalleta.

Tana zuwa gabansa yace Sannu da zuwa Kareena Kapoor Yaya su Salman Khan suna lafiya dai ko? Dariya Manal ta dinga Yi tana boye Fuska Tace wannan ai tsokana ce.
Daga soron gidan nasu ta shimfida musu Tabarma ya zauna shi dai Yana kallo ta
Showing 42001 words to 45000 words out of 153479 words