ya share zufa duk sanyin da ake alokacin Amma gumi yake saboda zafin da gwamma ta had'a mai yace*_"rabuwa da Hansai ,tabbas zai iya zame min matsala,haka Sanadin Rabuwa da ita zai jefami a mawuyacin hali wallahi Ita nake k'auna _* gwamma tace "tab! anya kana da kai, lalle dole ne na Ke gidanku" .da sauri ta fice don jin da yayi kansa na juyawa. Ledar da ya shigo da ita ,ta d'auka ta duba taga soyayyan kifi, "hmm da wan nan cimar zan k'yale Hansai ta aure ka ,inaji ina gani Hansai ta auri d'an maigari ta shiga daula ,ai dole na tashi tsaye ,ai idan yasan wata bai san wata ba.Juyawa gidan tayi ta shiga d'akin ta suka ci ita da dije.

. haka Muntari yayi ta yawo baiga inda take ba ba inda baije ba, har wajen 9 na dare yana yawon nema harda k'walla don yanda yake jin Hansai a ransa.


****** Al amarin hansai kuwa, bayan da lawandi ya sace ta bai zame ko ina ba sai wani gida wanda ba kowa a ciki sai wata tsohuwa ,aje ta yayi a d'akin tsohuwar ya d'ago yace "kaka ga ajiyata nan" dafe kirji tayi!" kai D'an nan yau ma jafa'in ka jawo? har ka fara satar bil adama". Lawandi yace "kede kaka ba ruwanki ki sa Ido kawai" fit ya fice daga gidan.

Bayan fitar sa ,Hansai ta farfad'o ta hau kalle- kalle kuka ta kuma sawa, "na shiga uku wayyo baba, wayyo inna" ,tsohuwa tace "yarinya mai ya had'aki da lawandi"? Hanai ta kalleta "wallahi iya ,ya nace yana sona Alhalin an saka min rana da wani ,in dai zan fita sayya biyo ni, yau ma tsautsayi yasa naje jida ,shine ya d'auko ni don Allah kaka ki taimakan".
tsohuwa tace karki samu inaga Allahu gobe zan bud'e ki tafi,ina kike" ta tambaye ta ,Hansai tace a mangalu"tsohuwa tace "ai bamu da nisa ma" dadi taji tsohuwa tace ta tashi tayi Alwala haka tayi ta dawo ta zauna.Tai tsuru-tsuru tana jimami.
tsohuwa tace "ai lawandi kwai tak'adari wallahi tunb yana shekara goma nake fama, jika nane ni na haifi baban sa,babar sa tazo haihuwa ta mutu baban sa kuma ciwo yayi ya rasu, sai rikonsa ya dawo guna neman fada doke doke ba irin wanda bai ba daya fara girma ya tsiri dauke -dauke, har ya girma bai nutsu ba sai ma janyo fada wanda ya sha kwana gun masu kayan sarki('yan sanda) har yanzu sai adda'a domin kullum sayya yi wani abun rashin da'a,tun da nace ya samo Mata nai mai aure kowa nutsu ,shine ya satoki ko? kiyi hak'uri gobe- goben nan, zan saki a hanya ki Koma mangalu" Hansai tace "iya dama cikin gari ya kawo ni"? iya tace "ai nan cikin garin bunkure ne".kuka hansai tasa kaka na bata hak'uri.


*By Queen meemi*


.
[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣10❣
*JAN 2017*




*Queenmeemi.wordpress.com*


*dedicated this page to sis marwa &sis Ameener*


_jinjina gareku, *Anty maijdda* *Anty sis,Anty sadyjegal* *LubieD*, *Hapsert NM, Kursiyya* *yusha'u ,Aneesaty*, *respectable* *& Princess Amra*da sauran wanda ban fad'o ba duk kuna raina_


Washegari da sassafe sai ga lawandi nan tunda dama ba kwana yake a gidan ba ,kokon da kaka take sha ya d'auke ya d'ad'd'aka. Hansai kuwa rakub'ewa tayi a gefe ya kalleta .Hansai gani gaki sai yanda nayi dake zaki raina kanki keda ba gata gareki ba ,kaka tace" kai lawandi tsiyar ka da rashin da'arka ya kaini bango wallahi zan sab'a
Showing 21001 words to 24000 words out of 155648 words