ji tayi su Kande da Karime na Gulma ta zauna tace "kunga ku daina Gulmar su babu kyau barin ke Karime kin manta wuyar da kika sha ran na." Kande tace "hakane fa" nan sukayi shiru.

Hansai kuwa akwatin ta ta bud'e tasa hannun ta nan ta zaro wata Leda ta rasa ta meye Lokacin duk su Karime sun fita wanke -wanken dare jiki na rawa ta bud'e ledar kud'i ne a ninke a ciki sai farar takada da hoto ahankali ta juya Hoton Ganin fuskar Muntari tayi nan tasa Murumshi ta tuno Lokacin da zai tafi birni ya bata tsai ta k'urawa hoton Ido ta tuno Lokacin dayaje Birni ni ya d'auka da Sallah sai Kud'in data irga taga dubu biyu ne Hawaye ne suka subo Mata ta warware wasik'ar tun Lokacin da da k'anin sa ya kawo Mata, sai yau wajeen Shekara D'aya da wata biyar Allah ya nifeta da Bud'ewa nan ta bud'e ta fara karantawa kamar haka:

*By Queen meemi*👑
*Queenmeemi.WordPress.com*
[3:28pm, 31/01/2017] Miemee: ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣22❣
*JAN 2016*


*®NWA*


_Sadaukarwa ce ga Basher Usman Family's_


**********

Bud'e wasikar tayi tafara karantawa kamar haka:

_Hansai soyayyarki bazata taba Gushewa a Raina ba, kin zamo tamkar Jinin Jikina, wallahi Birnin da zani babu wata 'yar Birni da zata Rud'eni na manta dake,ina sonki Muyi hkr da Rabamu da akai domin Rabuwar tamu ta zamo Sanadin tafiya na Birni don Sanun Ilmi,San nan nasan ab'angaren ki ina ji A Jikina kema zaki samu Ilmin komai rintsi Ina tare dake.Karki manta dani ina Ji A Jikina ke tawa ce na d'au wan nan Alk'awarin ,San nan Hansai Masoyiyata ina so ki Jajirce kicigaba da neman Ilmi na Addinin Dana Bokon idan Allah ya sake had'amu dake zanyi Alfahari dake,duk wahalar da Gwamma ke baki ki jure da sannu zata Girbi abinda tayi,Hansai ina sonki sosai d'an digon Hawaye tagani adai-dai gun, nan tashafa gun bisssalam Hansai Allah ya sadamu da Alkairin sa I luv u & miss u so much._


Kuka mai tsuma Zuciya tayi tayi ta sa wasik'ar ahannunta ta duk'un-kune ta maida A kwati, kud'in kuma ta rik'e a Hannu. Iya ta shigo Aa "yata Hansai Meyasa kike kuka?".
Nan ta share Iya na tuno su Inna ne, tace Eyya sai hk'r kowa da yanda Rayuwar sa Allah ya tsara sai hk'r ai nan da watanni zaki gansu d'an Murmushi tayi tace Gaskiya ne .


Washegari Hansai taje ta kaiwa Anty kud'in tana zaune ta shiga tace "Yawwa Hansai Jeki min blandin kayan miya" da sauri taje tayi ta dawo ta zauna ta mik'awa Anty kud'in tace "Anty gashi ki aje min agunki tun agidane da aka ban na manta sai yau" tace "ba damuwa sai ki sayi kayan Makeup dasu ko?" Hansai tayi dariya Anty wane kwalliya?
"Tace haba Aidole kinayi gashi Allah yasa ked'in Kyakkyawa ce" tace to "Anty."
kamar ance ta fita taga Sumy zaune kan Kujera ga Kande da Karime duk a durk'ushe Sumy tace "kema zo nan!"
Asanyaye taje ta zauna Sumy ta fara Magana inaso ku sani daga yau babu wacce zata saka kayan Gida sai Uniform, kun gane nan ta zaro su guda Uku Riga da Wando Rigar iya gwiwa tace su zasuna sawa kullum ta kalli Hansai "banso ki maka Hijab kin gane Aiki kika zo Iyayi ba,ko me za kalla Jikin ki! atoh kuje ko wacce tasa ina nan kuzo."
Haka duk suka d'auka suka tafi Shigar su D'aki Hansai tace nikam kayan sun Birgeni Karime tace "tab! yanzu shikenan Mundena saka kayan mu!?
Kande tasa Dariya kide zauna Surutu Cas kayan sukayiwa Hansai kyau gashi sun D'an kamata daga kasa kamar ba ita ba,shape dinta ya fito daram tsakiyan cikin ta ya d'ame ga kirjinta har dan fitowa yayi, dogon wuyanta ya fito ya dace da beautiful face d'in, tsaki tayi "jifa yanda kayan nan sukayi mini? ni kam dama tabarni Nasa Hijab d'ina."
Karime tace "kai Hansai duk yafi miki kyau"Kande tace "eh wallahi" Karime tace "duk gayunsu wallahi kin fisu kyau" Kande tace "eh dande tana rufe Jiki ne."
Showing 81001 words to 84000 words out of 155648 words