ya tashi yayi ya tafi.

Tace "OMG! Matsala tabbas ta tunkaro ni,domin tasan yanda Hassy ta mato kan Muktar.



By

Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.

.
[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣44❣ *FEB,2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_



*NWA*


*Nagode Waheeda da kulawa Allah yabar zumunci👍*

***********

Tunda abun ya faru Husy ta shiga neman yanda zata Manta Muntari sai de hakan ya faskara daurewa kawai takeyi.

B'angaren Muktar kuwa har wani Dan rama yakeyi saboda rad'ad'in da zuciyarsa ke ciki domin koda Hassy ta buga mai waya bai dauka aganin sa yanzu ya zama dole ya yakice ta.
Ammawata zuciyar na tunatar dashi inyayi hakan kamar zata ha yaudarar ta yayi.


Yauma d suke zaune suna hira ad'akin su Hassy tace kin san me sis? na rasa mai yasa yanzu Muktar yake shareni"
Hussy taji gabanta ya fad'i tace 'kiyi hkr tayiwu ko yana Busy Hassy tace Allah dai yasa."


Tunani hussy ta hauyi tabbas dole na San yanda zan don bazan so sis taji ba nan tad'au wani layi ta saka ta awayarta ta d'au Number din sa a wayar Hassy Direct tayi mai text Msg kamar haka:

_"Muktar ka manta dani saboda hakan Allah ya kaddaro akanmu balalle sai mun zauna inuwa daya ba wato aure, kadaina wulak'nta sis Dina plss ,kuma karka bari tasan mun tab'a soyayya karka nuna mata kaine muntari na idan ma ta sani to sai kun aure ,ka kyaleni kawai dama ba komai Mutum keso ya samu ba ,Matar Mutum kabarinsa wani baya Auren matar wani Bye"_

Yana gaban Computer yana wani project sak'on ya shiga nan ya d'auka ya karanta ji yayi kansa na bugawa ya daki Bench na gaban sa .

"Tabbbas kece farin cikina bazan iya babu keba Amma zan d'au shawarar ki na daina kin d'aukan wayar Hassy Amma ki sani ke tawace"Shi kad'ai yake Maganar kamar da wani.

Ita kuwa tana gama tura.Msg din ta cire Layin ta Maida nata,da Gudu Hassy ta shiga "Tweeny!"
zo kika wani d'anyan Material da Dady ya sai mana" nan ta nuna Mata "wow Amma sunyi kyau",Suhaima da Arif suka shiga nan suka baje kowa yana fad'ar irin Bikin da za a gudanar.

*Bayan 2 weeks*

Su Hassy Exams suka fara tukuru haka Hussy ma ta bangaren Hassy kuwa hankalinta yad'an kwanta ganin Mukhtar na kiranta yanzu,damma ya koma Nigeria domin fara shiga office Aikin daya nema ya samu.


Yau suka Gama Exams dukkansu cike da samun nasara,nan fa suka fara shirin tafiya inda suke ta siyo lates kaya Wanda zasu ci biki dasu, Ranar Asabar itace ranar da suka d'aga kasarmu ta Gado wato Nigeria.

Sun sauka Abuja da misalin 6 na yamma Mota 2 ke jiran isowar su suka kwashe su suka je gida Agajiye duk suka zube don Gajiya.

**********

Yau saura Sati biyu Bikin Suhaima, dinki kawai suke kaiwa Ana musu tsaddadu abinka da yaran manya.

Ganin da sauran sati hakan yasa Hassy ta damu zata Bunkure .
Dady shida Mum na zaune a falonsa suna hira ta shiga ta gaidasu Ta zauna Dady yace "Douter da Magana abakin ki" tace Dady ina son zuwa Bunkure ne?" Mum tayi dariya "ai tun a Landon harda su kuka zata" yace "ki shirya gobe Idi ya kai ku keda Arif."

Hassy kuma zata taya Suhaima rabon kati ,kema sati d'aya zakuyi ku dawo saboda Biki."

Dad'i ne ya kamata nan ta sanar da Arif yace ba Matsala Amma Shi ba sosai yake son zuwa k'auye ba harara ta kaimai ,"dole kaje yaro."

*Wshegari*

Hussy ita da Arif Idi driver ya tafiwkaisu da tsaraba Jingim musalin k'arfe 5 suna Bunkure.


Tun shigar su garin sai kalle kalle take ganjn wani gun ya canja sai 5:30 suka k'arasa Mangalu,tsayiwar su ak'ofar Gidan Husy tace Baba idi ka manta Gidan ne? yace "Aa nan ne ai" Mamaki k'arara afuskarta ganin yanda gidan ya koma Ginin bulo yaci fenti.

Abdallah ne zai shiga gida tace Dan jummai Juyowa yayi shikam bai gane ta ba Arif ma ya fito suka shiga gidan.

Nan ma taga yasha gyara dakuna Shima harda tile an canja tsarinsa, Jummai ta fito itama har dan kiba tayi "wa nake gani kamar husaina?"
Tace "nice inna" zama tayi tace "naga gida ya canja?"

Inna tace "kedai bari Dadynki ne da wan nan Aiki wlh ai sede godia domin Malam ma yana cikin gari kantin kayan Masarufi yake siyar wa."
Husy saboda dad'i harda kuka.

Inna ta kalli Arif "Dan lukuti ba magana kayi shiru" Murmushi yayi ya gaida ta.nan ta bud'e ciki da rumfa ne da malam nan aka budewa Arif Rumfar ya shiga.

Tsaraba husy ta fito da ita duk ta warewa kowa nasa "gana Baba wai yana ina?" Jummai tace "ai Malam sai 7 zaki gansa."

Gidan aka shigo aguje Dije ce ke rusar kuka tace ku taimaka Mama zata mutu."

Sam bata gane Hansai ba ganin kamar an canja ta inna tace "to Husaina Dan jeki ni kinga ba damar fita tunda Malam baya nan." bin Dije tayi tana tafiya Anutse Suka shiga Gidan, d'akin Gwamma sai tashi yake k'afar da aka Guntule ke ciwo Sai kuka take ga iya agefe suka shiga.

Jin k'amshin turaren Husy yasa suka d'ago dafe k'irji Gwamma tayi "wa nake gani kamar Hansai!"

Tace "nice"
kuka Gwamma ta fara "don Allah kiyi hkr kan abubuwan Danai miki, nasan na zalunceki gashi nan ina Girba yau wata biyu kenan k'afata ke ciwo har Ruwa take futar wa, ga bak'in cikin Mudi se yayi wata baya lek'oni, Ga Dije ko Samari Sun Dena zuwa gunta kowa bai sonta, saboda rashin tarbiya da fada da Maza,don Allah ki yafeni domin naga izina ba irin gorin Aure da ban maki ba, gashi na ga ishara ga 'yata domin ita akwai Wanda ma ya kusa yi mata Fyad'e irin Mazan da takewa rashin kunya koda bai Matan ba ya Cuceta dalilin da yasa kenan ba mai zuwa Gunta kowa cewa yake ta gama lalacewa. Malam yace bashi ba ita, Nasan nice sila domin ni na b'ata taribyar su, dama ance kak'i naka Duniya taso shi Hakan ka soshi Duniya ta kishi."

Iya tace "ke yimana shiru duk wanda yaja ruwa ai shi kan doka."
Hussy tace "ba komi na yafe" Gwamma tace "yanzu kece kika dawo haka! tamkar Balarabiya.Ashe! ke yar Manya ce."

Hussy tace "yanzu insha Allahu Gobe za a kaiki Asibiti."

Dije kuwa bin Hussy tayi ta Rakata ta dawo tana murnaa.

Husy shigarta kuwa Malam har ya dawo nan yayi Murna sosai da ganin su Arif na gefe yana Latsa waya, haka sukayita hira har ta mai zancen Gwamma yace Shi ba ruwan sa da Gwamma ,Husy tace Baba kaban izini na taimaka Mata" kallonta yayi yana cewa dama 'yar sace ta cikinsa,Amma ahakan ma yana Alfahri da ita matsayin 'ya yace "ba komai 'yata ai Rama Alkhairi ga Macuci."

*Washegari.*

Wajen goma aka taro taxi aka tafi kai Gwamma Asibitin ciikin Garin kano wani k'anin iya ne ya kai ta.kudi Hussy ta ciro a Accnt nata aka kai ta akace sai am Mata aiki a k'afar inda hali ma asaka Mata k'afar Roba.

Da yake duk wata Dady na zuba masu Hussy kowa dubu d'ari a Acccnt yasa Hussy ta bud'e bakin Accnt nata akai wa Gwamma Aiki aka sa Mata k'afar roba.

Tun daga nan Dije taji tana k'aunar Husy sai hkr take bata kan abubuwan data yi mata tace bakomi, ta bata shawarar zuwa islamiyya Harta bokon ma.


Jummai da Malam sai San barka suke da ita Sam bata duba sharrin da Muguntar da Gwamma tayi Mata ba, gashi ta rama tayi Mata Alkhairi.


(Shiiisa akeso ka rik'e Mutum tsakani da Allah Musamm irin Matan dake rike D'an kishiya suna Musguna mai kod'an ruko, 'ya'yansu sune 'ya'ya to bakasan wa zaka Mora ba ba Lalle ka mori d'an cikin ka ba ,sai dai ka Mori na wasu, shiisa akeso ka Maida D'an wani na naka, Domin Masu iya magana nacewa D'A NA KOWA NE Allah yasa agane)



*Ina busy ne fans ga Wan nan ba yawa.*


By

Queen meemi
Queenmeemi.WordPress.com.




.
[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣45❣ *FEB,2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


_*Wan Nan page din naki ne Surayya ngd da kaunarki agareni ngd sosai nima ina kaunarki ngd da support❤*_


*********


Yau suka shiga sati a Mangalu nan suka had'a inasu inasu sukayi Abuja.

Tunda suka koma basa zama kullum suna kai d'inki da rabon kati kuwa duk Sun gama inda sukaje aka fara Gyaran Jiki ,ba Amarya ba hatta Husy da Hassy an musu Amma kwana biyu Sun fito kamar taurari Amarya kuwa kullum na kunshe Ana Gyara ta .

Wasu frnd nata su 2 suka zo suna tayata don su yauta Mata,Mum kuwa wasu k'annenta su 2 daga Adamawa sukazo sauran Dangi duk sai ran laraba zasu zo ,Ga Anty Rabia ita kullum tana gidan don gudarwa abubuwan tunda su basu da yawa.

Gidan su Ango ma ba abarsu abaya ba, shiri suke sosai Dady ma shiri yake su Masu mutane komai atsare ake ma'aikata ne aka d'auko duk wani Prepartion su ke gudanar wa .

Hassy kwa koyaushe suna mak'ale a waya da Muktar kullum Maganar sa d'aya abasa Husy su gaisa shima yayi Alk'awarin zuwa.


******

Yau data kama Ranar Alhamis aka fara Gudanar da Kamu da Walima wajen k'arfe hudu da rabi aka kwashe su zo kuga kyanda Amarya tayi.
Tayi shigar Golden Colour abinka da me kyau sai ita da kayan suka haska Juna ga k'wararriyar me Makeup ta tsantara Mata .Ango ma shigar Light golden shadda yayi.

Su hussy kuwa shigar wani Black nd Red Less sukayi sunyi buba da zani Sun dora zanin kan Rigar Sun balain kyau Me Makeup ta matso masu kyan su ,haka Arif ma yayi shigar sa black nd Red shadda combination yayi kyau shida yaran kanen Mum nan aka kwashe su.

Fati Niger ce ta wak'e su ko ina sai san barka Musammmn su hussy duk inda suka Gifta sai an kallesu.


Haka aka gudanar aka watse.

*Washegari*

Ranar Jumaa shine aka gunar da Mothers Event Manyan mata kuwa in banda kece less ,less da Manyan atampopi da Tsaddun Materials ba abinda suke, wan nan na Wace wacccan kowacce ka kalla zabba ne fal ahannun ta matan Ministoci Sanators nd others duk sune gun, wuyan nan yasha english fasion ,Indian, etc duk sunci Gwara Gwarai duk k'awayen Mum ne da 'yan uwanta.

Lokacin da Amarya ta shigo kallo ya koma kanta domin ta had'u ta hade ga Twinss agefen ta sunyi shigar Ash colour kamar ka sace ka gudu haka, Arif ma yasa Ash colour na shadda da wasu bayan su Frnda din suhaima ne Dana hassy suka rako su.

Husy sai kashe selfie suke da Hassy Musammn da frnds na Suhaima don Sun basu sha'awa.

Mum ke kiran Husy tazo fita Sai idonta ya gano mata Mama da Umma Matan Alhaji tanko suma ita suke kallo Musamm ganin Twins ne .

Umma tace "kai Yarinyar nan tamakar mai Aikin Anty Suna kama dande wannan tafi haske ne da wayewa.Mama tace wlh tun dazu nake kallonta cikin sani.

Murmuahi Husy tayi ta zata wuce ta sunkuya ta gaaida su ta wuce don shigo da bak'i.

Arif kuwa tsakiyar fili ya shiga sai Rawar shoki suke shida frnds nasa nan kallo ya koma kansa sai sakar Musu Lik'i ake Amarya ma ta fito tana mai Liki don ya Birgeta ga Hassy na d'aukansa video, sai da Mum tazo ta fidda shi.

Haka akayi akai ciye-ciye akasha aka watse.



*****
*Washegari*

Ranar Asabar kuma aka gudanar da Dinner kwalliyar yau da akayi masu dukkansu sunyi kyau Amarya tasa Blue Dark tayi balain kyau Gwan din kamar ka dauke saboda tsaruwa an adon Ash ajiki sai walwali take .

Shi kuma Ango yayi shigar Light blue shima yayi kyau.

Su Hassy kuwa shigar wani Materls sukayi Light pink sukayi duka an musu adon Dark pink hakan head nasu ma, Arif shima yasa Ligh Pic D'anyar shadda anyi mai dede Shi sunyi balain kyau Musammmn husy.

Frnds din Amarya kuma Sun shigar ankon su mai kyau Material Brown sukayi abokan ango kuma sukayi Brown shadda wow sunyi kyau .

K'arfe 7 Manyan motoci suka kwashe su aka kaisu hole da za a gudanar.

Husy ce ke Driving sai Hassy a gaba sai Arif a baya da wasu 'ya'yan yar Anty maza su 2 .

Shigar su Filin hole din Motoci ne Birjik fitilu sai walwali suke ,Big gals ne da had'addun Maza keta shiga,Husy ta tsaida Motar .

Hassy tace "ke kalli can ga wad'ancan 'yan Matan pls ba sune su Sady ba?"

Hussy tace "eh sune" hassy tace wlh nasan Motar nan taki ta tafi dasu kin san fa Motarki tafi tawa kyau ,jibi tasu irin Tsohuwar ta ya Suhaima ce data canja."

Husy tace "hmm Tweeny kede ki yishiru ki k'yalesu" Hassy tace "to ai ba Magana zan masu ba kawai ina son kima canja tafiya nasan zasu gane ki." Dariya husy tayi kawai

Arif yayi tsaki "ni ku bud'en plss!" Hassy tace "anki kaji kid'a ka rikice."

Atare suka fita Hassy na yatsina Husy kam kawai fitowa tayi suka jera.


Sady ta kallli Sumy "ke dama Hassna twnss ne? Sumy tace "ke dalla bakya ganewa wai bama ki ga kamar da suke da Hansai ba?"
Sady tace "haka kuma fa."

Hassy Sun gifta su tace "Hi" Sady tace "yaran fa Sun Birgeni wai ni,Kinga motar su irinta fa nace Dady ya saimun wai tayi tsada, Sumy duk had'uwar ka kana ganin ka kashe kala in kazo gun biki sai kaji d'ar."

"Babies din nan na kill me wallahi sun balain kyau",Sumy tace "agidan su fa ake Bikin."
Allah ko ba agidan su ba,nasan Sun kai mak'ura
Ni bama wan nan ba dama twnss ne ?"
Ke ni kije ki tambayesu kindamen zo Mishiga ai Anty tazo sai mu tambaye ta."

Nan
Showing 117001 words to 120000 words out of 155648 words