kalli meya sameki Sady?"

Sumy ta gaya Mata ta kalle ta "lalle Sady kina son kiyi Saki na dafe great man irin Faruq ga kyau meye aibun Faruq Kodan kinga Dady na cewa sai masu Naira."

"Hmmm wlh wani Auren me kudin wahala ne azamanin nan ki Auri me sonki da yawa Shi yafi domin wani Namjin wallahi komai kudin babanka sayya taka ka,Naga ishara akaina."

Sady tace "Nifa sis bana sonsa, haba ya k'yaleni kofa Mota baida ita meyaci meya bani,gashi bai iya dressn ba."

ta kalli Sumy ke yanzu bagashi da Nazy kike luv kuma ba kinsan baban sa me Naira ne,ba wlh bazan taso a wadata ba Kuma nakoma talauci"

Zuby tace "Dalla shut up ur Mouth ,ke naki Baban ba mai kudi bane ba, haba wlh Nikam na dawo daga rakiyar wai sai me Naira wallahi ka samu mai sanka shine."

Akwai sirri da ban tab'a gayawa kowa ba wlh kun ganni nan kunsan dai Auren so mukai da Fawwz ko, ina balain sonsa to sai da Mukayi Auren na tabbatar nafi sonsa domin da Gangan yake mini abu yasan son danake mai da wuri zan huce, wataran se mi 3 days muna fushi dole ni zan bashi hkr yana basar dani,himm wlh ina baki shawara ki Auri Wanda ya fi sonki domin Faruq Masoyi ne kusan fa shekara kenan kina mai wulakanci!"

Sumy da Jikinta yayi sanyi tace Zuby "Nikam na kad'e."

Zuby tace "akan me?"

"Maganar da kika fad'a mana don alal hak'ik'a Madam nasha wahala gun nazi dole na canja salo tumma ba ai auren ba."

Zuby tace "atoh ki zauna kina hauka akansa."

Sumy tace Wlallahi Sady ki rabu da wani Handsome karki ki 2 -0

Tashi tayi a Fukace ta fita Zuby tace Allah ya kyauta "iska na wahalar dame kayan kara." nan suka mike sukayi cikin gida.


*LONDON*

Sun sauka a katafaren Gidan su ma can bayan sun huta yan Nigeria Mazauna Landon sukazo Sunaima Ambassador nasu barka da dawo wa.

Husy tasha kallo bata tab'a zaton zata bar Nigeria ba Lalle ikon Allah yau gata A landon.
Nan ma Husy da Hassy daki daya suke kowa ya kwanta baccinsa na gajiya.


*Washegari*

Bayan sunyi breakfast Arif ya tafi Makarantar su inda yake SS1 Hassy ma ta shirya Driver ya kaita Cumpus na su.

Haka Suhaima ta shirya zata shiga School karb'o wasu Ducument nata Harta fito Mum tace ta tsaya Husy ta rakata saboda kar abarta ita daya Agurguje ta shirya suka fita.

Dady ma ya fita Office sai Mum kad'ai agidan ta kishingida Bacci.

Acan kuwa Suhaima kuwa Cumpus dinsu tayi don ba School Nasu d'aya da Hassy ba ,turawa keta wucwa Wanda suka Santa suna Hi Suhaima Har sukaje office Husy ta tsaya abakim Bishiyaa sai k'ikkifta ido take.
wani siririn Saurayi ne yazo ya tsaya gabanta "Hi Baby".

Ko kallonsa batayi ba,wani abokinsa shima yazo wucewa ya d'aga murya "Bobby come here!"
What Wrong frnd?
"See beauty" ya nuna mai Husy nan ya matsa kusa da ita Jikinta sai rawa yake neman kai hannu Jikinta suke Suhaima ta k'araso ta harare su.

Dariya suke suka bar wajen Husy tace "sukuma haka suke dama ance fararen nan 'yan iska ne!"
Suhaima tace "no koda ba Musulmai bane Amma ko ina akwai na gari dama wad'an nan basu da kirki kin san me sis duk abinda kika ga Namji yayiwa mace ita ta bada dama suma sun sani kuma su Al adarsu ba wani abu bane su rike mace don haka inkin fara zuwa School karki sakarwa kowa fuska tunda Al adunmu da nasu ba daya ba."

Husy tace "Gaskiya ne inasha Allah zan kiyaye."

Bayan ta gama komai taja su suka tafi gida suna komawa suka shiga taya Mum Aikin Girki.

Suna zaune Husy tace "nikam ya inason layi zan kira Nigeria" nan Suhaima ta bud'e wata Jakarta tace "ga wani Empty" ta karb'a tayi Godia don so take ta kira su Baba.

"Ya Suhaima Nikam ban san yayan namu ba" kashe ido daya Suhaima tayi tace "lol bari na bashi ku gaisa."

Nan ta kira domin acan Nigeria kusan dare ne nan ya d'auka tace "my safwan ga Twin din Hassy zaku gaisa"
yayi mamaki tace mai "ai ta dawo" karba husy tayi.

"Yaa Safwan ina maka barka da dare" yace lafy k'anwata, Inaga sai na biyoku Landon ganin ki" tace "Aa ahakan ma yayi basai kazo ba"
Suhaima takarb'i wayar tace "ko na bugo maka ta Imo ka ganta?"
yace "eh."
Nan ta buga mai ta Imo Lokacin yana zaune kan kujera yana Shan tea Husy tace "ya Suhaima nima zai ganni kamar yanda nake ganin sa?"
Dariya tasa "kai husy yan zuma Ai yana ganin ki"

karbar wayar tayi Suhaima tasa dariya.

Dak'yar ta bud'e har da Dan sunkwi dakai ta gaidashi yace "Lahhhhh kaiii zankadaziyya ashe k'anwar tamu ta kudi ce."
Dariya tasa haka sukai ta hira yana kallonta tana kallonsa nan tabawa Suhaima Suka cigaba.

Bayan ta gama Husy tace "ya Suhaima Allah yasani kunya" tace "haka yakema Hassy ma D'an shaftane."

Husy tai Dariya Wushiryar nan ta fito tace "Amma kundace."
Suhaima tace Tnks sis, Wai kuma fa so yake asaka Rana."

Husy tace "ai gwanda Musha Biki Dan kallonta Suhaima tayi "lalle sis Kema A ce."

Sai 5pm Hassy ta dawo agajiye.

*Washegari.*

Dady Bayan sun gama break Dady yace Monday husy zata fara zuwa cumpus din su Hassy" tsalle sukayi itada Hassyn cike da murna .


*4:30*

Kowacce tasha Makeup Husy da Hassy sun saka wata Riga da siket ,Rigar Red ce haka Siket din black sai suka dora Top black,sun nad'e kansu da Red d'in Gyale sunyi kyau sosai Manyan takalma suka tsikara.Dak'yar Hussy ke takawa saboda tsinin sa tunda ba sabawa tayi ba sai da Hassy ta koya mata.

Nan Suhaima tasa wata bak'ar Abaya Anyi shape din ta tad'an bazo da gashinta gaba ta na nada Mayafin abayar Akanta gashin yadan fito ,tasa no Respect Glass ta kwashe su suka fita zaga Gari.


Sunje Super Market suka D'an siyo abun Motsa baki end suka je gurin shak'atawa suka Shimfid'a Carpet sai Selfie suke suna Dan ciye- ciye da drink.

*BAYAN WATA DAYA*

Hassy ce ke Zaune a 'yar Runfar Gidan su ta shak'atawa sai Murmushi take ita kad'ai Husy ta d'ago d'aukeda Fruit Salad A cup ta zauna tana sha tana kallon Pictures a instr .d'agowa tayi ta kalli Hassy .

" Tweeny" ta dago "Naam sis."
Tace "ya naga sai Murmushi kike ke d'aya."

Tace "kin san me sis? wallahi ba abinda yakai so dadi Musammn in ka samu wadda ke sanka kake sansa."

Hussy tace "tabbas" Hassy ta matso Dan gaba tace "bantab'a gaya miki inada Saurayi bako? to ina dashi .

Husy ta tasa dariya "ya Sunansa?" tace sunan Yasir"
tace "kai yanzu yana Nigeria ne? tace" Nop a Cumpus namu yake Last yr yayi Graduation yanzu one yr kenan da fara Soyayyarmu farkon shigana School."

Husy tace "Wayyo Amma nayi maki Murna, ki tayani da Addua Allah ya had'amu da Muntari na domin yazama heartbeat dina,Allah yasa ya rike Amanata duk da rabamu akayi tayiwu yayi aurema.

Share Hawaye tayi Hassy ta taso ta Rungumeta ta baya.
tace "ai insha Allahu zaku had'u Ameen"

Haka rayuwa take gudana ga wad'annan Family' kowa nasan Dan uwansa fans in kunga Hansai to sai kun tsaya kun sake kallonta tamkar wadda akaiwa wankan inji ta kile ta sake wayewa ga kwalliya su Hassy duk sun koya mata tun sanda ta fara shiga school.........


*fans Caji yayi tsiyar ya kare banzo inda nake san tsayawa ba Amma dai ku biyo ni.*


By
Queen meemi
Queenmeemi.worldpress.com.



.
[10:29am, 05/03/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣43❣ *FEB,2017*


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


_*Wan nan Page naku ne dukkan 'yan NAGARTA WRITERS ASSOCIASION onluv❤*_




*********

Bayan wata Uku da fara zuwan Husy School Aka saka Ranar Suhaima Nanda 3 Month Lokacin su Husy sunyi hutu Alokacin zasu tafi Nigerian don gudanar wa Murna gun su Hassy ba Magana Sai shiri suke abinda Hankali kwance.


Husy da Hassy ke zaune a Garden na School suna karatu Wayar Hassy tayi K'ara ta d'aga Ganin Sunan Yasir yasa ta d'aga da wuri "haba kazo Landon ne."

"Ok sai kazo."

Juyowa tayi ta kalli Husy "kinsan me? Husy ta dago "Aa" tace "to Yasir yazo tun jiya Yanzu zai zo ya ganni kinga dama kina son ganin sa."

Husy tace "ai kuwa domin hirar sa Harta isheni Hassy tace yau kwa zaki Ganshi wallahi Mundace."

Bayan kamar 1 hour Kiran sa ya K'ara shigowa "Yawwa kazo?" yace "eh"

Nan tayi mai kwatance da suna Garden, direct yasan wajen dama ya tawo Hassy harda d'an Goga Powder Shigowa yayi Garden d'in daga can ta gano Shi ta tashi tana Murmushi.

Yana Jingine kusa da Wata bishiya sumar nan tasha k'yalli yasa tshrt black da farin wando sai agogo fari da shoe black wani d'igon sonsa ne ya motsa Mata sallama tayi ya juyo suka yiwa juna Murmushi yace "I Mssd u dear na" tace "me too."

"Oh ina Tweeny namu ne inason mugaisa" ya tambaya, tace "woo ai itama kai take son gani tare muke tana can zaune."

Anutsue suka jero Husy kanta na sunkuye tana karatu ,har sukazo inda take hassy tace "Tweeny ga yasir."

Dago kai tayi Eyes nasu suka had'u a razane ta kafa mai ido shima sakin baki yayi yana kallonta kallon Hassy tace "dama shine yasir din?" Hassy tace "eh kun san juna ne?" Husy tace "no"

Da kyar ya bude baki yace "Amma kunyi kama" kirjinsa ne yaji yana bugawa sabili da jin wani irin Abu tabbas yasan Hansai din sa ce Mamaki ne ya isheshi taya haka ta faru bayan Malam yace Aure za amata, Jiiyayi kamar ya cire kansa saboda zafi da yayi .

Husy kuwa Hawaye ke neman zubowa tayi saurin tare su, ba yabo ba fallasa ta gaidashi, tace "Tweeny bari na tafi Ana jirana zami Lucture in kun gama kimin waya sai na fito mu tafi."

Binta yayi da ido cike da Razana akan face nasa.

Bayan class taje ta tsaya sai kuka take harda d'ora hannu aka tana kuka "wayyo ashe Tweeny Muktar ne saurayin nata" can Wata zuciyar tace Mata kefa wan nan sunan sa yasir nan taji hankalinta ya kwanta kanta har ciwo ya fara ta fito ta ta shiga class.

Sai wajen 3 ta fito Lokacin Hassy na jiranta suka tafi.

***********

Yau kwana 2 kenan sa had'uwar su ya kasa Sukuni domin tabbas yasan Hansai ce yana Mamakin meya kawota Landon kuma yaji Hassy na cemata sis dinta to dama Hansai ba yar can bace duk wan nan tambayoyin ya rasa amsarsu.

Duka gwiwowinsa yayi ya dau phone dinsa yana tunanin wazai kira a Nigeria,k'anin sa ne ya fad'o mai da yake shima yana Secondary yanzu yasan yana da waya kuma yana Aiki.

Nan ya buga mai yace "wai ni na tambayeka? ya Labarin Hansai ta Gidan Malm tsohuwar budurwata da aka fasa auren mu ? Tana ina ne wai?"

Daga can Musa yace "ai yaya kwanakin baya naji Labarin anga iyayenta har Sun tafi da ita abuja ashe ba yar gidan bace" Dam! gaban Muntari ya fadi.

Yace "ok ba matsala" kwanciya yayi a kan gadon sa ,yana dafe kirji kansa duk ya daure

Husy kuwa kwana biyu duk tayi suk'uk'u zuciyar ta takasa sukuni zuciyar ta na gaya Mata shine domin tabbas ko da cikin duhu zata nuna Shi duk da yayi D'an kiba da tsawo Amma kuma taga sunan sa yasir .

Tana zaune tana Latsa waya cike da k'unar rai Hassy tashigo "Tweny na" ta zauna "yanzu muka gama waya da yasir baijin dadi gaban husy ne ya fadi tace "eyya Allah sarki" "wallah hussy duk na damu Domin Soyayyr dana kewa Yasir daban ce domin shima yana sona sosai saboda yasha gayan wai ina kama da wata first lov dinsa shiisaa yake balain sona.

Husy tai dariyar takaici domin wan nan Maganar ta sa ta dad'a tabbatarwa shin Amma kuma dole taji daga bakinsa tace "haba Tweeny yanzu bakya kishin saboda kamar ku daya da wata yake sonki?"

Hassy tace kai Tweeny to meye ai dama badole sai ya dade da itaba."

Suhaima kam duk ta zama busy sai shirin yanda zata gudanar da bikin ta take suna zaune kan kujeru dake kewaye a falon Mum na kallon wani film .

Husy ta shigo da Gudu ta fad'a kan Mum tana kuka hankalin Mum ya tashi tace "meya faru?" kuka take na fitar hankali tace "wai ke meye? tace Mama su baba nake missn Dariya Mum tayi kai Husy shagwab'a.

Tace "karki damu ai saura wata biyu bikin yayarku kinga Idan muka rankaya can sai ki je bayan gama biki."

Husy ta kwanta jikinta tana maida zuciya domin son Mukhtar ne ke dawainiya da ita ga kuma yanda Hassy ke san sa tabbsa tasan da matsala.

Suhaima ce ta shigo da Album "mum kinga irin kayan nan nakeso" Mum tace "kai suhaima ba kunya agabana" sunkwi dakai tayi "yi hkr mum" .

Dariya tayi bakmi ai gwanda ki zabi irin kayan da kikeso" ,Arif ya shigo yana neman Hassy Mum tace tana bedroom bacci.

*BAYAN SATI D'AYA*

Husy ce zaune a Garden din da ta Saba karatu domin yau Hassy bata da lucture Ganin Mutum tayi agabanta ta d'ago.
Muktar ne ya zauna daya kujerar kauda kai tayi .

Yace Hansai ashe zanganki a Rayuwa?
Kallonsa tayi kawai sai ya koma Mata Muntari k'auye kuka tasa harda shashsheka sai datai mai isarta.
Muktar yace kiyi hkr idon sa shima yayi jan "abubuwa Sun faru.Muktar tayaya kasan ja suna? kuma yaushe har ka manta dani ka fara soyayya ni ina ta Dakon son ka!"

"Am so sorry Husaina"

Bayan Rabuwar mu kinsan dai kano na koma gidan kanin Hajiya to anan na zauna nafara sana'a sosai daya yana legs yace zai mani cuku cuku don cigaba da karatu"

"Dalilin Sanja suna na kuma shine:
Hatsari ya faru dani da Dan Alhaji mai suna yasir Lokacin zamu wani gwaji da za ai mana duk credentials D'ina da nasa na tare to nawa yana hannu na nasa na jaka, Munyi hatsari sai Allah yayi mai Rasuwa saboda motar ta kone ni kuma fad'owa nayi Asume waje.

To abinciken Motar ne sai aka gano takardunsa a jaka Allah yasa bata kone ba. komai nawa ya kone to wan nan dalilin ne yasa kikaga na canja suna Sabili da duk da komai nasa Alhaji yayi Mani cuku- cuku na samu Scholarship na tawo nan karatu shine nake amfani da sunan yasir anan."

To karshen shekarar da zan gama ne muka had'u da Hassy ita lokacin Zata shugo ,nayi Mamakin ganinta irin kamar da kuke da ita komai naku iri d'aya yananyi dukka sai de abinda dai bambancin kadan ita yar Birni ke k'auye."

"Soyayyr da nake miki ce ta darsu naji ina son ta.

Ban kulataba har saida na koma hutu Nigeria Naje Bunkure har gun Malam naje na tamaye ki yace ai an kaiki aiki kuma ma Aure za'amiki da jin hakan nasan Malam be manta abinda akai maki ba,haka nai jinyar Rashin ki na hkr"

"Wan nan Dalilin ne yasa na hkr ,Amma Still kina Raina domin True Love Never end.
Ganin kamar kun yasa nace inason Hassyy saboda ganin ta nake tamkar ke."

Kiyi hkr Amma wlh kece Araina domin ance kama da wane ba wanen back.kuma ganin ki yanzu yasa Soyayyrki ta dada ninka da naji bazan iya ba."

Kuka Husy keyi sosai domin tasan tabbas bai da Lefi kallonsa tayi cike da k'auna tace "kayi hkr Tweeny blood Dina ce abinda take so ina son sa don haka na barka da ita kucigaba."

Domin bazanso abinda zai shiga tsakanin mu ba Muktar yau na tabbatr Rabuwarmu itace Sanadin Abubuwa da dama ni gashi na samu iyaye na ta hakan ma na samu ilimi.

Juyowa yayi burinmu ya cika husy saura Daya domin bazan iya rabuwa dake ba"
Ya zakayi da Tweeny to kasan hakan bazata sabuba?
kansa ne yaji ya d'au zafi ji yayi bashida mafuta.
Sallama yayi mata
Showing 114001 words to 117000 words out of 155648 words