nan Hajiya Karima itace matar sa ta biyu, itama tana da 'ya'ya da Shi Rubayya(ruby) itace babba awajen ta sai sumayya (sumy) itace Ke binta wan nan sune iya 'ya 'yanta, sai Amaryar sa daya auro shekara 5 kenan tana da 'ya'ya da Shi khalili shine babba sai Mubarak, duk a gidan Ruma ce babba mai shekara 25, sai Ruby mai 23 San nan Zuby mai 22 sai sumy da sady sa'annine suna 20 sumy ta bawa sady wata biyu,sai khalil Dan 4 yrs San nan mubarak Dan 2 'yan gata ne sosai suna jin d'ad'in su San ransu ga gadara



*MANGALU*
Shigar Hansai gida yasa gwamma ta kwad'o mata murfn kwano a k'afa take ta dafe gun tana kuka gwamma tace "wallahi Hansai zamusa k'afar wando d'aya dake, kin gansame agari ba mai aurenki, duk sa aninin ki an aurar ,hatta ita tsaharen ankaita d'akinta bara Amma Ke. Kina nan shekara goma sha hud'u god'ai god'ia dake duk ba sa aninnki sai wanda kika girma,kullum sai aukin sa hijab tamkar matar liman,Ke ga malam ya tsaya miki wai sekin gama makarantar gaba da furamare ake cewa kome, to ayi Dai mu gani duk ran da aka fara saka ki A wak'a ai maji,ni b'acen da gani kar na ballaki ki,na k'arashe k'afar, je ki min wanki",tana d'ingishi ta tafi jummai ta fito lokacin itama Allah ya bata ciki ta kusa haihuwa tace "haba yaya hansai fa tana k'ok'ari miji Kuma ai lokaci ne Kuma ai D,an gidan mai gari ne Ke Santa, kin ga kuwa ai lokaci muke jira" gwamma tace "ayi Dai mu gani ba" dije ce ta shigo 'yar shekara hud'u gwamma ta kamo ta tace 'yar lele ina kika je ?tace "rafi kamo kifi" ,da sauri ta rufe bakin ta jin muryar malam dake k'ok'arin ya shigo ,tace "Ke yi shiru kin san malam baya so yi maza shige d'aki.

Hansai da kafar ta keta jini wajen da gwamma ta wulla Mata murfi,Daga gefe sai kuka take ga wunya dake d'ibar ta tace "mama gwamma zan d'auraye k'afata jini" tace "Dan k'aniyar ki sai da kikaga malam zaki ce haka to bazaki wanke ba gulmammiya kawai" jummai dake kusa da ita tace hansai zo na d'auraye miki sai kici abincin," da gudu gwamma ta taso "Ke karki tab'a ta domin Salam munafinci",Malam dake shigowa yace "Aa meye haka nan kukayi cirko -cirko.




*by Queen meemi*
[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . . . .





⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣7❣


*®NWA*


*Queenmeemi.WordPress.com*

*_sadaukarwa ce ga Basheer usman family's_*

_happy birthday *MIEMIE BEE 👄*Wish u more years ahead ,GOD bless u🎉_
****
Sun tsaya cirko-cirko Malam ya k'araso yana tambaya da sauri gwamma tace "Aa magana muke kawai" hansai da kanta na sunkuye gwamma na harar ta MLM yace "Ke Kuma meye kike d'ingishi"? jummai tace "ai bigewa tayi" yanki ya d'auko ya bata ta d'aure gun yace ta koma gefe ta tafi tana d'ingishi,gwamma haushi tamkar ya kasheta ga wankin da bata k'arasa ba kenan, domin tasan malam bazai K'ara fita ba tun daya shigo, haka ta duk'ufa tana K'ara sawa.

Washegari da jummai ta fita asibitin cikin gari Malam ya fita gona sai hansai da gwamma kawai ganin,hansai da uniform gwamma tace "Ke bazafa ki je ba, kizo ki d'eban ruwa"hansai tace baba gwamma yunwa nake ji" "baza ki ciba ki fita kawai wallahi" haka ta aje jakar buhun dake hannun ta,ta d'au botikin ta fita sai sauri take har taje rafin, ba kowa agun sai wasu mitsi-mitsin yara acan gefe suna wanki d'iban ruwan tayi ta d'ago kenan ta ci karo da lawandi k'irjinta ya bada dam! tayi gefe, bin ta yayi yace "Ke hansai"! taki tsayawa sai sauri take fit! taji ya ja hijab d'inta nan ta tsaya yace "Ke hansai don baki da rabo ina maki magana Amma bakiji don ina sonki kikemin wulak'anci.

tace "kayi hkr inada masoyi" yace k'arya kike da kina da Shi bazaki zauna Ke kad'ai a gari ba duk kamar Ke an aurar sai kace mai bak'in jini, koda yake wa zai auri yar tsintuwa" da sauri ta juyo "kadaina jifana da munanan kalamai saboda da iyayena dariya".yasa dariya "tafi can ki farka tun dare bai miki ba" ,don ma zam taimakeki duk kyan nan naki ace ba mashinshini" tace "wallahi karya ne da iyayena malam da inna dariya yayi "kinsan dai ni abokin mudi ne, don haka ya gayan Kuma nasan bazai miki k'arya ba"

fuu ta juya ya zata tafi ya cafko ta nan tahau ihu yace "bari na kwashi rabona tunda kince baki sona" k'ok'arin cire Mata hijab yake ta k'walla ihu dama kowa yasan lawandi a k'auyen bashi da mutunci shammatar ta yayi ya fisge hijab d'in ,kuka take sosai "kayi hk'r na tuba" jinjina kai yayi ya turza k'afafuwan sa a k'asa "gaki da kyan jiki Amma kullum arufe" hannun sa ya kai jikinta yaji an mauje hannun, Muntari ne Ke huci ya nuna lawandi "ka shiga taitayinka iskancin ka bai tsaya ba har akan budurwata, to wallahi duk k'auyen nan za'a jimu Kanmu" mazga ya kaiwa lawandi take shima ya rama suka nan suka hau naushe -naushe da gudu hansai ta juya ta yi hanyar gida tana kuka


shigarta gidan ta tarar da jummai na tsintar shinkafa,lokacin bata Dad'e da dawo wa ba sai ta shige d'akin jummai tana kuka, cike da jimami jummai tajata tace "meya faru hansai"? nan ta fad'a Mata abinda lawandi yace da ita ,hankalin jummai ya tashi ta tuno lokacin da Malam Ke shaida Mata karta bari hansai ta San basu ne suka haifeta ba to waya gayama lawandi nan tayi ta lallashin hansai tace zata gayawa Malam .


Makarantar daba taje ba kenan ,gwamma ta shiga d'akin jummai tana masifa "bafa zan d'au asara ba dole a biyani botiki na" ,hansai tace "kiyi hk'r tsautsayi ne yasa ya fad'i ,fizgo ta tayi ta fito da ita waje ta hau jibga hansai na ihu jummai ta janye ta tana haki "wallahi karki Kuma dukanta gwamma don Kinga Banda lafiya shiiisa kwanan nan kike dukan ta" ,gwamma tace "jummai dani kike zancen wallahi sai kun gane kalata ta kwanan" nan tayi k'wafa ta fita. jummai ta kamo hansai suka shiga d'aki tana bata hkr.


Muntari da Lawandi kuwa sai da suka ji jiki San nan suka rabu lawandi yace saiya ga bayan Muntari inde akan hansai ne. Hatsaniya sosai sukayi har wajen mai gari ina waje d'aya ya Tara su lawandi da muntari na agaban maigari yace "kaga kai D'ana ne Muntari, kai Kuma lawandi kai Nike jagorantar ka meya had'a ku"? .


Lawandi ya furzar da huci yace "yarinyar dana keso wai ita yake so" maigari yace "wake nan"? Lawandi yace "Hansai ta gidan Malam". Maigari yace "ayyo na gane" nan ya juya gun Muntari yace "haba Muntari na san ka da hankali ya da fada akan yarinya"? Muntari yace "baba wallahi tin hansai na shekara goma muke tare, atambayi Malam ma da ita Hansai d'in.

nan maigari yace aje akirawo malam , yana gona akaje kiran sa ya tawo suka gaisa a soron gidan maigari d'in, yagan su nan maigari yace "Malam ya maganar 'yar wajen ka hansai"? cikin lawandi da Muntari wake Sonta malam yace "Allah ya gafarta Malam ai Muntari na sani tun da dad'ewa".
"To kai kaji lawandi cewar maigari sai kayi hkr, karna K'ara jin wani tashin tashina anan" .Lawandi dake tsuke baki ya tashi ya fita yana mai k'wafar kota Halin k'ak'a sayya samu Hansai



*ABUJA GIDAN ALHAJI TANKO*
Sady ce da Sumy sukayi shawarar zuwa gun dady .yana wangamemen falon sa mai d'auke da kayan K'awa ,Anty Rabia taci uwar kwalliya tana gefe tana had'a mai tea zuby ta zauna daga gefe haka Sumy ma suka gaidashi " dady dama muna da complain akan mota wallahi yakamata ace kowa nashi dai-dai aka sai mai ,sady ta cafe "eh wallahi dady kullum baama jin Dad'i da sake wa ga frnds" har dariya suke mana A school" dariya dady yayi "har kun manta, Amma kafin na sai muku wan nan motoicin ai da kowa tasa
Showing 12001 words to 15000 words out of 155648 words