Bikin hansai da Muntari yana ta k'aratowa ayanzu saura wata d'aya,nan gari ya d'auka saboda an Dad'e ba ai biki gidan maigari ba ga kuma Hansai da ake ganin ta dad'e.San nan gashi soyayyr su mai Asali wadda ta kaisu ga Shekara hud'u da rabi kenan shiisa kowa Ke zumud'in Bikin.

(Bari mu waiwayi Lawandi muga wane waina aka toya tun lokacin shigar sa gun 'yan Sanda).
Bayan da suka tafi dashi dama suna da case dashi sai direct suka kaishi cell saboda dama andad'e Ana neman sa, bisa dalilin satar da sukayi wa wani D'anfulani ,sai lefin nasa ya zama biyu gana satar yarinya gana kayan D'an fillo ,kawai sai aka sashi cell na wata uku ba beli .
To ayanzu wata ukun ya cika ya samu ya fito . Zuwan sa gun kaka lokacin tayi fishi dashi tace ya bar Mata gidan ya Koma gun Dangin Maman sa kaka sai kuka take hakan yasa ta d'akko wata Jikarta suke zama tare Shi kuma Lawandi ya had'a kayan sa ya cale Lagos neman kud'i ,acewar sa sai kaka ta neme Shi .
kaka tace "nikam nayi nan kayi can .Allah ya bada sa a can yayi tafiyar sa.

Al amuran Gwamma kuwa tayi ladaf din k'arya don har ciwon karya tayi domin ta jigata matuka. Malam na zaune tazo ta zauna sai matsalar k'walla take "Malam kayafeni na tuba bazan K'ara ba na jigata tamkar a Kurku ku nake ,ka taimake ni ba donni ba.
Malam ya kalleta "Ashe har kin horu" Gwamma tace "na horu Malam."
"To kije na janye. Amma idan sab'anin hakan ya kuma faruwa zanyi mai gabad'aya."
"Malam aina saduda".
Tashi yayi ya fita domin Shi kam yasan tuban muzuru Gwamma tayi.
Showing 48001 words to 51000 words out of 155648 words