⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣5❣



*®NWA*



*Queenmeemi.WordPress.com*

_*sadaukarwa ce ga Bashir usman family's*_


_sis Marwa Phart bb ,Anty maijidda ,Nazifa Ngd Ngd sosai da kaunar book nawa,San nan 'yan group Dina na QUEEN MEEMI FANS ina godia da kaunarku agareni sosai kuna nunan kauna nagode Nima ina sonku luv u_

*****
tana zauna tana kuka Muntari dake tawo wa Daga can ya ganota yazo kusa da ita yace "hansai meya sameki"? da sauri ta share hawayen daya zubo Mata Babu komi ta fad'a juyar Dakai yayi tabbas yasan da matsala can k'asan zuciyar sa yana tausayin hansai Ko acikin yara bata da kuzari ,"kina jina? kiyi hakr kinji yanzu ya makaranta?" ya tambayeta bata bashi amsa ba sai ma d'agowa da tayi ,yace "Ko bakya zuwa kema? kin zama su tsaharen?" da sauri tace "Aa ina zuwa ajina 4 a firamare Yawwa hansai ki dage Kinga Matan garin nan basu damu da zuwa ba, har mazan ma, ki dage kina zuwa ki zama gwania acikin su," tace "to" yace "San nan kullum kina zuwa gun sahura (kanwar sa) ina koya muku karatu," Dad'i ne ya kashe ta tace "to" mangwaron dake ledar hannun sa ,ya zaro ya bata ta amsa tana mai murmushi.

Muntari D'ane agurin mai garin ,garin mangalu a gidan su shine d'a na uku a ciki yayansa duk Mata ne sai maza kannen sa da Autar su mace,matashin saurayin k'auye ne D'an shekara goma sha takwas Allah yayo Shi da San karatu duk gidan su Shi kad'ai Ke zuwa, har ya kammala firamaren sa ,ya shiga secondary ta maza yana aji biyar ,duk k'auyen Ko acikin Samarin ya fisu ilmi ga kirki,tun ganin sa da hansai yake jin tausayin ta haka kawai ba don komi ba, hakan shine farkon alak'ar su da hansai.

Bayan kwana biyu a tsakani yau ma MLM ya fita gona gwamma ta aiketa rafi wajen k'arfe hud'u na yamma ta d'au botikin ta tafi ,da d'an nisa sosai haka taje zuwan ta rafin taga yara birjik.Daga gefe ta tsaya tana d'iban nata ruwan ,wata Daga cikin su tazo taja kan hansai "Ke waya baki izinin d'iba,? bayan Kinga ana fad'a" hansai tace "to ni meye ruwana daku" fitsararriyar yarinyar tace "to duk nan na Riga kowa zuwa Kuma ba wanda zai d'iba sai ni" ,hansai tace "tabdi" kande tace "hansai sahura fa yar gidan mai gari ce fa!".

hansai bata saurare su ba ta d'iba ta juya, jitai an jefar da botikin juyowarta, taga sahura na huci hansai zatayi magana sahura ta kamata da fad'a ,da yake sahura tafi hansai k'arfi ta jefar da ita a k'asa ,santsin k'asar gun taja ta tajita cikin rafi ,tinjim! kake ji k'arar fad'awar ta,Yaran gun duk suka saka ihu idanuwa sahura suka Rena fata,hansai kuwa sai ihu take duk tasha ruwa dai-dai lokacin Muntari ya taho yana zuwa yace "Ke sahura haryanzu aikenne? ga inna can na nemanki,"ganin suna kuka ya tambaya dije tace "sahura ce ta wulla hansai rafi" a kid'ime ya yi wajen ya ganta har ta daina motsi cikin ruwan ya shiga ya d'auko ta, ya fito da ita gefe yaran duk suka zagayeshi ya danna cikin hansai ruwa sai fitowa yake Amma duk da hakan bata farfad'o ba. haka ya d'auketa yaran suka bishi abaya duuuu.

malam dake zaune sai fad'a yake "bana ce adaina aiken hansai rafi ba,? haba gwamma mai sa bakyaji ?gwamma dake zaune ta had'e rai "haba mlm "wai duk yaran garin nan tafi su ne? da za'ace bazata ba",mlm yace "eh tafi su ,ace tun k'arfe hud'u har yanzu shida dai- dai Babu alamar ta" ,jummai tace "malam Nima hankalina bai bani lafiyaya ba" .

Sallama aka doka mlm ya amsa Muntari ya shigo da hansai a hannu jummai tace "la haula ,mai ya sameta Muntari ? yace "ai fad'a wai sukai a bakin rafin itada sahura, shine ta fad'a rafi" kuka jummai tasa ta k'ank'ame hansai, mlm yace "Muntari na gode sosai" bayan fitar sa ya dawo kan gwamma "Kinga ABINDA AKE GUDU (littafin batul mamman) ko, gashi kin gani dai Ko"! d'aki ya shinga ya fito da magani yasa a raunin hanun ta da k'afar nan yasa jummai ta D'an gasa jikin hansai ,haka dai sukayi ta treatment d'inta sai wajen k'arfe Tara ta farfad'o tana kuka yau a d'akin jummai ta kwana.

Washegari dak'yar ta taka, saboda yanda k'afarta Ke ciwo ,sai da aka gasata da ruwan zafi San nan ta samu sa'ida ,muntari ne ya shiga shida sahura da leda a hanun yayi ya jikin hansai, San nan ya umarci sahura data bawa hansai hak'r badon Taso ba, suka tafi.
yau 3 kwana kenan, kullum Muntari sayya zo duba hansai Kuma yazo ya jata da hira shak'uwa ce sosai ta shiga tsakanin su sosai bayan warkewar ta sai Muntari Ke zuwa yana biya Mata karatu irin su hadisi sira ,kawa'idi,alkurani,da tauhidi. (da yake da da yake D'an karami Dan shkear goma ankai Shi makarantar almajirai yayi shekara daya sai aka dawo dashi ya shiga boko Kuma daya dawon ya cigaba da d'aukan karatu gun malamin makarantar Allon su hansai).
Showing 6001 words to 9000 words out of 155648 words