ta saka cif sukai Ma Husy da yake kusan Jikinsu iri d'aya ne Suhaima tayiwa Husy kwalliya Hassy tace "wow my twin sis kinyi kyau"


Murmushi tayi "thnks Sis"


Hassy tace " Oya zomi Selfie🤳🏻 nan Hansai ta tsaya Hassy ta saita Ipon dinta ta daukesu sunyi balain kyau sai kamar su ta fito Rad'au.
Direct ta dora su kan Instrgram tana she's my twin sis.

Sai Dariya suke Arfif ya shugo yace wow "kunyi kyau Amma ya Suhaima Ai Husy tafi Hassy kyau ko?"

Hassy tace Lallema Lil Bro nidin?"

"No Hassy ai gaskiyane kefa bakki da Wushirya" Gwalo yayi mata.

Hassy tace komai NO Mr No kawai"

Yace "Naji tadai fiki kyau"

"Ai sekayi tayi"

Suhaima tace "zancen Gaskiya husy tafi ki kyau."

Hassy tace "Wayyo koma dai me zakuje Tweeny Dina ce munfi kusa kano da
Jigawa."

Ita dai Husy Dariya kawai take yi sai kallonsu take. Nan duk suka fita sukayi Breakfast Dady ya kalli Husy yace ya kika kwana My Lovly douter?"

Tace "Alhamdlh Dady" Mum ta kamo ta zo nan my Twin" nan Husy ta agida ta.

Hassy tace "shikenan ta k'wacen fada" dariya Arif yasa dama Dan adawar tane yace "sede ki hkr."

Dady yace "haba keda ita ai duk d'aya ne nan suka gama suka d'au Damarar tafiya Mama ta Rungume Husy "Allah yayi maki Albarka" ta bata wani Leda nan suka tafi.

Direct Gidan Kakan nin su suka tafi nan ma Sai ganin Husy ake yar dangi kakarta kuwa harda kuka tamkar ta Maidata ciki sai wajen 12 suka dau Hanyar Birnin
Tarayyya,hansai ta kunshe kai tana kukan tuno su Malam da Inna Jummai.

Muje Zuwa Dai

By
Queen Meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.



.
[4:33pm, 28/02/2017] 👑Meemi💋: . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣41❣


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


*Wan Nan page din naku ne Aneesa rimi (Anee) Swt Anty Maijidda & Fatyma Nagode da kaunar Da kuke ma book nawa Oneluv❤*




********

Tafiya akace yankin azaba hakan su Husy suka yi tayi har suka je Abuja direct Osokoro sukayi ainihin Gidan su Wani Babban Gida suka dosa Hon sukai Maigadi ya wangale gate Nan Motocin suka shiga da gudu mai bawa Fulawowi Ruwa ya bud'e Musu "Barka da dawowa Oga" Dady yace "yawwa."

Su Hassy ma duk suka fito Husy tasbihi tayi Azuciyarta domin ganin Gidan tamkar ya fad'o kansu saboda Girma da kyau tamkar da kwali akayishi,duk haduwar Gidan su Sady sai taga yazama Mara kyau akan wan nan ,Lalle kafi wani wani yafika.

"Twinny tawo mana!" sai Lokacin ta dawo da kanta kansu Arif yace "idi kaga Husainar Hassy" zaro Ido yayi "haba ikon Allah ko itace wadda ta bace ko?"

Arif yace "yeah"

Nan Maigadi ma ya tawo yace "ikon Allah gashi kuma kamar su d'aya" nan suka yiwa Mum da Dady barka suka koma.

D'uruwa sukayi cikin Gidan Husy ta kuma sandarewa domin falon ma kamar ba a Nigeria ba, Matatta kalar bene 2 ne a falon Wanda kowanne da Decoration din sa Dady da Mum sukai d'aya su Suhaima kuma sukayi d'ayan Husy ta bisu a baya suka hau, nan taga d'akuna Ajere Guda Hudu a gefen kowane d'aki Flower ce Masu kyau Jikin bangon kuma wasa Frames ne masu kyau, can gefe kuma Dan karamar Dining table ne me kyau Black me kujeru 3 nan Arif ya shige nasa D'akin, haka Suhaima Har ta shiga ta fito.

"Sis Husy Bari na nuna miki d'akin ki don tun jiya Dady yayi waya aka shirya Miki shi."

Nan suka shiga bud'e baki tayi don duk haduwar d'akunan su Sady wan nan ya zarce nasu (sawun giwa ya zarje na Rak'umi ) wani gado ne Purple madai-daici da Cover da Mudubi Fentin d'akin ma purple ga Decoration masu kyau. Nan Hassy tace "nikam tare da Husy zamuna kwana ki dawo dakina kawai."


Husy tace "Nima dai Nafison mu kwana mu 2"


Suhaima tace ai gadon daya ne can sai de akoma da komai naki can." Mum ce ta lek'o My husy d'akin yayi maki ko a canja?"


Tace "Aa Mum yayi" Hassy tace "Mum so Muke akomar da komai nata d'akina na munfi son mu biyu."

Tace "Okey ba damuwa tunda dama d'akin nada Girma zai cinye."

D'akin Suhaima suka shiga Mum ta kira masu had'a Funiture waya yace nan da awa d'aya zai zo.


Husy sai kallon D'akin Suhaima take ko ina Hoton Suhaiman ne Lik'e a bango Gaban Mirrow kwa kayan Makeup ne turmus nan duk suka zube a gadon ta Suna hira.

Wajen kamar k'arfe 6 ya zo su 2 kamar injina suka Fidda kayan dakin zuwa dakin Hassy suka jera yayi kyau na Hassy Pink nata Purple 7 suka gama suka tafi.

Nan suka koma dakin Hassy tace "wow yanzu ma yafi kyau" husy kam Godia take ga Allah kan Niemar da yayi mata, nan sukayi Sallah tare da wanka Hassy ta bude wardrobe d'in Husy gefe abaya ne da Pakistan sai Atamph da shaadda su Materials wanda ba d'inkakku ba, ga takalma da Jaka nan duk suka fito da Jakunkunan da takalmin suka kai su Mazauni .

Hassy tace "Twieeny yanzu Gobe sai muje akai din.kunanki" husy tace "ok sis.

Arif ya shigo "food is Ready."

Garam ya koma.

Dariya suka saka dukan su suka fita, Suhaima ma ta fito "hi sisters."
Sukace "ya gajiyar tafiya sis?"
Tafe "fine"

Itama tayi wankanta nan suka jera suka sauka k'asa.

K'amshin Girki ne ya doshi hancinsu sai lokacin Husy ta kalle Falon tas iya had'uwa ya had'u tv 2 ce aciki sai Aiki suke ga wani Gabjejen hoto na Art work Dady ne da Mum sai Suhamina Hassy da Arif akasa sunyi bala'in kyau me Art d'in ya iya. Murmushi Husy tayi suna Lura da ita Dady yace "Lovely Douter kema za 'a yi maki za'a dauke wan nan Ayi sabo wanda hardake."

Dariya tayi tace "Ngd Dady" Suna tacin abincin su har suka gama Dady yayi Gyaran Murya "Godia ta tabbata ga Allah Wanda ya k'addara Rabuwar da gudan Jinin mu gashi kuma ta dawo to ku zama Tsintsiya Mad'aurin ku d'aya ku zama Masu san Junanku da Girmama Juna kai Arif Banda raini ku kuma ku soshi Banda Wulakanta Mutane."

Mum tace "ai yaran nawa sai san barka Musammn Husyna."

Dady yace "Husaina ya batun karatu kinyi Secondry ne?"

Tace "eh Dady nayi acab Anan Abuja na karasa."
Au kinyi Zaman Abujan nan?"
"Eh Dady nayi Aiki Gidan Antyn Maman kano"
Nan yace Rabia Matar Alhaji tanko?"

Yace "eh."
yace "ikon Allah."

Mum tace "Allah Sarki 'yata Husaina, d'an bamu Labarin Rayuwar ki."

Husy ta sunkwi dakai kamar zatayi kuka nan ta fara basu Labarin tun bud'e idonta a Mangalu har yau.

Kuka Suhaima da Hassy keyi na tausayawa Rayuwr Husy idanuwan Mum yayi tana matsar hawaye hakan idanuwan Dady ma yayi ja.

Hassy tace sis Duk da *RABUWA CE SANADIN* shiga Hali wannan dalilin ne yasa duk kika shiga wancen wahalar, da ace kina tare damu dabaki shiga haka ba."

Dady yace "Hassana karki d'auka Rabuwa damu ne yasa haka! to Daga Allah ne shiya tsara hakan don Gwada imanin mu da ita Husaina Dana wanda suka riketan, koda tana gaban mu ma hakan sai ta iya faruwa, wani abun shine Sanadin wani dama ita Rayuwa yau bak'i gobe fari,kin gane?"

Tace "eh Dady"

Suhaima tace "Nikam wan Nan Gwamma ke ban haushi wlh Muguwa ai gashi nan taga k'arshen Mugunta,kuma hakan ma bataga komai ba."

Arif yace "ni kuma su Sumy da Sady ke ban haushi Mugwaye don tayi aiki Gidan su."

Hassy tace "hmm Tweeny da tuni fa kina da Aure da Muntari."

Husy batace komai ba sai sunkwi dakai tayi jin gabanta ya Fadi

Suhaima tace "Aikuwa Su Sady sai na Raina musu hankali."

Arif yace "Amma wan nan Lawandin Mugu ne Allah ya kareki, wai Shi wan nan bad Mudi din shine harda wani wulak'antaki wai yafi k'arfin ki,Arif yace kece Ma ai kika fi k'arfin sa." Arif ya sunkuyar dakai cike da Haushi.

Hassy tace "nikam wlh duk nafi tsanar Gwamma."

Suhaima tace "Baba da Inna kuwa Muna k'aunar su sun so Jininmu."

Dady ne yace "ya isa hakan komai yawuce kud'au komai k'addara kuma duk wani Mugu k'arshen sa baya kyau."

Mum tace "hakane Ku manta da komai" ta kalli Husy "sannu Husaina Allah yayi maki Albarka da dukkan ku" suka ce "Amin."

Dady yace "yanzu kan karatun Husaina zan samar mata."
Mum tace saura fa 3 Month mu koma London!ko Anan zatayi?"

Dady yace "Aa" acan d'in nake nufi" tace "maddala."

Sai wajen 10 kowa ya koma side din sa,da tunanin Labarin Hansai (Husy)



*Washegari*

Suka mike Sukayi wanka Husy ta sauka kasa ta shiga kitchen Mum ce tsaye tana yiwa Dady Farfesu nan Husy ta gaisheta ta hau taya ta don karasa breakfast.

Mum tace "Husy Kin ganni nan banida masu dafa Abinci nike Yima Dady."

Husy tace "Yawwa Mum ki kawo ina mana"
Mum tace "haba ai Dalilin daya sa ban d'au yan Aiki Masu Girki ba kenan Saboda su Suhaima su koya, kinga mu ba Mazauna bane shiisa ma ban d'auka ba sai Mai goge-goge kawai kullum tare da Suhaima Da hSsy Muke Hada breakfast."

Husy tace "Mum Tunda Gani Yanzu kawai koba zamanki muna yi kawai."

Mum tace "Yayi kyau douter."

Suhaima ce da Hassy suna suka shiga Suna kirchen din Nan suka saka hannu sunayi suka gama aka kai Dining sukaje suna breakfast.

Wajen 10 suka mike kowacce suka sake wanka suka fesa Makeup,Mum sai kallinsu take Musammn Husy tana godewa Allah.

Falon Dady duk sukaje Arif Na danna computer Suhaima tace zasu Kai dinkin Husy kuma zasuyi Mata shopin .

Nan yace Suhaima ta tuka bai san tukin Motar Hassy saboda tana da Tsoro,sai nan da 1 yr kin dada k'warewa"

Dariya Arif Yasa "Dady wallahi koni na fita iyawa"

Harara ta kaimai "Oho dai Mr No kawai."

Dady yace Hussaina ma Zan kawo Motar ta Sai afara koya mata"

Kudi ya zaro ya basu yace "kuje ku taya Husaina shopin" jin Hakan Arif Ma ya Bisu Nan Suka Lodu a Benz din Suhaima ta kwashe su Gwanin sha'awa,Kyawawa dasu.


Haka sukaje Shoprite suka jido Mata kaya san Ransu suka biya ta gun tailor dinsu Suka jidemai kaya kan Suna san yayi masu express ya gaya masu kudi suka bada deposit,suka biya suka sha icecream san nan suka koma Gida agajiye wajen 1.


Kowanenn su yayi sallah sai bacci Husy kuwa Sabuwar Wayarta ta Kurawa Ido wayar data ke ganin ta hanun su Sady Ashe itama da Raban ta riketa.Murmushi tayi har Wushiryar ta ta fito ta kwanta kan Luntsuman Gadon ta,nan ta kira Inna dama ta bata wayarta sanda zasu tawo.

Daga can ta dauka nan Husy ta fasa kuka "inna Jummai"
Tace "Allah sarki munyi kewarki Husaina"
Tace "ina baba?"
Jummai tace "ya fita?" tace "Dan Jummai fa"
Tace "yana Allo kullum sayya yi kewarki"sun dade suna Waya san nan ta kashe.

Gadon Hassy ta kalla taga sai kwasar bacci take nan itama Batasan sanda ya d'auketa ba cike da farin ciki.



By
Queen Meemi👑
Queenmeemi.WordPress.com.


.
[11:00pm, 01/03/2017] 👑Meemi💋: . . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣42❣


_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman Family's_


*Ban manta kuba wan nan page naku ne@ Maryam Oumiey,Juwairiyya, Ummen Yusra & Aysha Maman Umayma❤*


*********


Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta wurin Hussy domin Rayuwa take cikin 'yan uwanta cike da 'yanci da walwala Uwa uba soyayya gaya ake nuna Mata sosai. ko tari tayi sai suce meye sis, ko meye Douter wan nan sakewar yasa Husy ta fito ta kara kyau fatar ta tayi kyau hatta gashin ta yasan ta samu canji shima ya dada kyau haka ta sake tsakanin su ta ware dasu komai nasu iri daya ita da Hassy abin sha'awa.

Ganin tana son computer Dady ya d'auko wani ya koya mata nan ya sai mata laptop kirar Apple Already dama su suhaima nada ita ga dalleliyar Motar ta mekyau Red cikin 2 weeks ta iya Rayuwa kenan.


Yau Dady ya sanar ma Mum gobe zasu d'aga Landon don Hutun su Arif ya k'are shida Hassy, dake Yniversty acan dama ita Suhaima ta gama.

Nan suka hau shiri wajen 1 sai ga driver Anty nan yazo zo kuga Murna gun Husy Rungume Anty tayi tareda yaranta.

Anty tace "lalle Hansai!" Husy tace Anty "ai wan nan Old name ne"dariya Anty tasa tace "wlh naji dadi Husy tace wlh Anty nayi missn naku tace ai dole.

Nan Hassy ma tazo suka gaisa dasu Arif suhaima ce bata nan ta tafi saloon.

Hassy tace "Yawwa Anty karki gayawa su Sadyn nan Husy yar uwarki ce ki barsu kawai zami basu Suprise" tace to ba Masala hakan sukayi ta hira har Dady ya dawo suka gaisa sai dare Anty ta koma gida.


*Washegari*

Da Asuba kowa ya gama shirin sa k'arfe 9 duk sun gama komai shi duk sun kulle Gidan Sukai sallama da Maigadi Suka d'uru A Family Motor Driver yaja suka tafi 10 sunje Abuja International Airport Dady ya Juya baiwa Idi sak'o kan ya je Bunkure ya kaiwa Malam.

Husy taso ace taje sunyi Sallama da Su baba da Inna Amma ganin ba time ta kyale nan jirgi ya d'aga dasu Sararin Samaniya.


*Gidan Alhaji Tanko*

Sumy ce tsaye kan Sady A Runfar wajen aje motoci kuka take sosai sumy tace "haba sis yanzu kan Shi Handsome d'in kike kuka ai wan nan abun kunya ne."

"Sumy kina ganin Na buga mai waya yayi man Wulakanci wai baison mace Mara kamun kai,Wai nadena kiransa."

Tsaki Sumy tayi "ai sekiyi tayi dama D'an nacinki ne yazo faruq yanzu Dana fito nan Maigadi je gayan na can waje a waje."

"Bazani ba Cuz I hate him"

Zubaida ce ta shigo da Mota Adaide Lokacin Tayi faka tafito rik'e da Baby boy a hannunta Dan 3month data haifa.
Gano su tayi yasa ta je wajen ta
Showing 111001 words to 114000 words out of 155648 words