haka ya fara koya Mata da amincewar mlm, ba haka gwamma taso ba, don yamma k'arfe 4 yake zuwa asoron gidan su hansan,yana da k'wak'walwa sosai haka ya Farai Mata harda na bokon, kullum Kuma sayya zo da kayan k'walam ya bata .Daga baya ma sai sahura tazo shima ya had'asu yana koyawa,haka dai rayuwar hansai ta kasance yau fari gobe baki,cikin wata safiyar laraba gwamma ta haihu ta samu mace tunda ta haihu bayan anyi suna yarinya taci suna khadija suna kiranta dije, sai ya za mana duk wani Aiki hansai akeyi wanda ma yafi k'arfin ta ga yawan dukanta da mudi keyi yayi tai Mata wasan banza sai de inta ganshi ta gudu d'akin jummai.


*BAYAN SHEKARA HUDU*


wani busa Ke tashi a tsakanin duwatsun dake wajen hansai Ke busa Shi tana murmushi taci irin kwalliyar su ta k'auye Masha Allah hansai ta K'ara girma kyanta ya dad'a fitowa duk da ban tab'a suffanta muku ita ba .
hansai 'yar farar yarinya ita ba irin gau d'in nan bace, ita Kuma ba za a kirata bak'a ba tsaka -tsaki ce'yar lawai-lawai bata da kib'a sosai sai de Allah ya horema ta kuturi(hips tun ma bata K'ara girma ba Ke nan ,shiisa jummai take bata hijab tasa domin tasan tana da baiwar da daukacin Mata Ke so,Kuma hakan shine ya kamace ta duk da yaran k'auyen kamar ta wasu basa yawo da mayafi.
Sam hansai in ka ganta bazaka ce zatayi k'arfi ba komai a sanyaye ta keyi, siriryar fuskarta wadda Allah ya wadata ta da Dan dogon hanci siriri da bakinta madaidaici sai gashin Ido da suke gazar -gazar dogwaye tamkar tasa eye lashes ,idan ka kalli jikinta duk gashi ne ajiki sai de bata dayawan gashi kai tana da de na fakin Amma gaban goshin ta cike yake da gashi a kwance luf-luf hansai Ke nan😉
Muntari dake saman bishiya yana murmushi Shi kad'ai ya d'ago da idon sa, "Anya hansai duk k'auyen nan A kwai me kyanki kuwa"? dariya tayi "haba dai ka dad'a bincika yace to ni dai masoyiya ta tafi kyau,tun bayan shekara d'aya kenan suka fara soyayya shida hansai wanda kowa ya sani agarin, kullum nan ne wajen hirar su cigaba tayi da busa usur d'in .D'an dogo wa tayi ta kalli saman bishiyar lokacin muntari ya juya, kallon Muntari tayi azuciyar ta tana sonsa, domin ya taimaketa arayuwa, ya Sanar da ita ilmi da yawa ya taimake ta sosai, magana yayi firgigit ta dawo Daga duniyar data tafi tare da jin kunya da gudu tayi hanyar gida .......




*By Queen meemi*
[12:02am, 15/01/2017] ‪+234 903 281 0350‬: . . .
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣6❣
*JAN 2017*

*®NWA*


*Queenmeemi.WordPress.com*


*_Sadaukarwa ce ga Basheer Usaman family's_*


*ABUJA*

A fafare Zuby ta shigo da motar ta ta faka a tafkeken filin gidan su.
Ruby dake bayan motar ta fito a zafafe suna hararar juna kowacce d'auke da jaka sukai ainihin cikin gidan wanda Ke d'auke ta kafcecen falo, wanda Ke d'auke da K'ofar shiga part guda hud'u falon dake tsakiya wanda yake a circle ga manya manyan kujeru na leda masu D'an karan kyau, d'aukacin falon an kewaye Shi da labulaye masu kyau, ga wani site dake yamma da falon an k'awata gun tafkekeiyar plasma ce awajen tana ta aiki,ga wani kuku na k'alk'ale tile d'in falon.


Shigar su Zuby da Zuby kowacce tayi part nasu .Ko wacce ka shiga part d'in nasu wani falo ne shima again d'auke da kujeru lintsuma- lintsuma ga decoration me kyau a falon, sai plasma tv da dining area da kitchen San nan jerin d'akuna guda uku,kowanne part haka yake duk gidan,d'akin mama. Tashiga ( hajiya khadija) tana zaune bakin tamkeken gadon ta, wanda ya malaye Babban d'akin ta zauna kusa da ita ,Mama tace "zuby har kun dawo"? "eh wallahi Mama gashi yunwa nakeji, sai de Kuma raina a b'ace yake" tayi tsaki ,"wallahi Mama wataran saina fasa bakin Ruby" Mama tace "haba Ke Bakya rabo da fad'a, Ruby ai kin San bada fad'a, dama Sumy kika ce ne da saina yarda".


"Mama wai akan driving yarinyar nan zata min rashin kunya, dan taga itace babba,Allah ni banso dady ya had'ani mota da ita ba" ,dai-dai lokacin Sady ta shigo tana rawa mama tace "har abada dai Sady bakya rabo da shirme" sady tace "mama wallahi wak'ar ce da dad'i ,nan ta kalli Zuby tace "ya zuby mai naji kina cewa ne? inde zan cen mota ne wallahi mu had'u muje ga dady Kowa a sai mai dai -dai, ta yaya za ace kamar mu Kowa sai ace su biyu ne a mota d'aya. jiya fa haka sai da Sumy ta lalato motar ta, bayan na hau tace ni na lalata har sai da umma tayi min fad'a"

Zubi tayi tsaki "gaiskiya Ya Ruma ta huta ita kad'ai da motar ta" ,mama tace "to sai kuyi hakr, ai ruma dai yayar kuce dole abata girmanta". D'an fita zuby tayi ta tafi Babban falo ta zauna tana kallo Rabia ce ta fito Daga nata falon itama ta zauna, Zuby tace "Anty Rabia ina gajia" batai mamakin jin yadda Rabia ta gaisheta ba tamkar ba matar baban su ba, "lafiya tace" ,da dai- dai da d'ai-d'ai Matan gidan da 'ya'yan suka fito sukai birjik a falon, gidan Alhaji tanko kenan. .

Alhaji tanko Babban Dan siyaya ne, da yayi shura yana zaune a garin Abuja,yana zauna A maitama yana da kud'i na fitar hankali ,yana d'auke da muk'amin minister na kudi ,yanzu hakan yana da matan aure guda uku Hajia khadija itace matar sa ta farko ,tana da 'ya'ya da Shi Rumasa'u (Ruma) itace babba sai Zubaida (zuby) San nan Sadiya(sady). Wan nan sune na b'angaren ta San
Showing 9001 words to 12000 words out of 155648 words