⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣58❣

*March 2017*

_Sadaukarwa ce Ga Basheer Usman family's_



*********
Bayan kwana biyu duk abu ya dagule domin Shuriem ko husy ta buga bai d'auka itama sai ta share Amma zucciyar su na manne basa daina tunanin juna,tana cikin bacci k'arar shigar msg ya shigo ta dauka ta duba Shuriem ne ke shaida mata anjima zai shigo, bai ji mai zatace ba ya kashe Amma ya matsu yaji voice nata.
5:00 Shuriem ya cinno hancin motar sa cikin gate din ,ganin wani saurayi yayi a d'an nesa da gate din gidan ya basar da sauri saurayin yazo yana k'ok'arin yi mai magana ganin hakan ya tsaya yace "wa kake nema ne?" Yace "nazo wurin husaina ne" "meye alak'arku juyawa yayi "gal frnd nawa ce" Shuriem yaji mamaki ya kamashi bai sake magana ba yabi k'aramin gate ya shiga inda suka Saba zama kamar mintuna sai ga tanan ta fito ya k'ura Mata ido santa da kishi ya kuma kamashi kanta ak'asa ta zauna saboda kunya da k'yar take magana yace "husy nasan bake bace Amma xuciyana ta kasa hkr wlh wani kishi nake" dagowa tai ta kalle Shi "am so sarry dea" yace "nasan wan nan joblesss yarinyar ce Amma karki damu ina sane da ita duk ta gama shirmenta zan maganin ta" nan da nan suka manta batun suka hau hirar su maidadi.


********

Hayaniya suka ji Maigadi da wani nan. husy ta daga kai ganin kamar kokawa yasa ta kira mai gadi ya tawo tace "meye? yace "yar Dady ai wani ne yazo wajenki wai ni kuma ba aban list da Shi ba" Dan shiru tayi tace "ka koreshi saboda ban San shi ba",Shuriem yace "no barshi yazo don tun d'azu na ganshi sa gudu mai gadi yayi ya koma yace ya shiga gyara riga yayi ya shiga farfajiyat gate din ganosu da yayi yasa yadan murmusa ya fito da wata wayar sa ya kira wayar husy nan ta fara ring @ten times yana kira tana kashewa don bata daukan no daba ta sani ba,Shuriem ne ya kalleta "finest ki daga mana" nan ta d'aga "waye? yace "juyo ki ganni ina kallonki" jikinta na rawa ta juya tare da kashe wayar Shuriem ya jingina da kujera baice k'ala ba, ganin hakan saurayin ya k'araso yace "Aa sweat heart tun a school nake kiranki kin share haba kodan kinyi sabo shine zaki watsar dani" husy ta mike tsaye "niii! Ta ina na sanka,pls kace ban sanka ba plsss ka fitar mana agida." murmushi yayi "husaina kenan! ba kyau yaudara don kin samu wancan had'ad'den to nima ai ba baya ba ,duk tsiya dai munyi luv sosai don haka ga pictures da muka d'auka duk da kince bakyaso dan gulma nan ya fito dasu ya watsa a kan table ya kalleta beauty sai minyi waya" ya juya ya tafi. Hannu tasa aka wlh ni bansan Shi ba sharri ne d'aya bayan d'aya yake kallon hoton kala -kala wasu rungume da shi wasu suna kallon juna Shuriem kuma Afusace ya mik'e ya watsa Mata pics d'in zatai magana ya dakatar da ita "bana son any word da zata fito daga bakinki, saboda komai na gani da ido na" juyawa yayi ya fita ransa adagule.



*********

Da gudu ta shige gida ta haye bene tana kuka lokacin hassy na aiki kan laptop ta fad'a gadon tana kuka hassy tace "meye?" nan ta nuna Mata hotunan San nan ta kwashe duk yanda akai ta gaya Mata hussy ta fara huci "lalle sady kinyi kuskure."dafa husy tayi tace kiyi hkr gobe zan San yanda zanyi don rana tayi yau."k'aramin zazzabi ne ya rufe husy wan nan kenan.

*Washegari*
@12am
Hassy ta mik'e tsaye tace "zo muje sis nasan inda zan kai atabbatar min da hakan" husy cewa tayi ba zata ba nan hassy ta cewa mum zata karb'o books nata take ta zari motar ta wani had'ad'den studio taje tana shiga suka gaisa da wanda ke bakin wajen nan ta zauna ta tambayeshi yanda ake had'a picture idan a rabe suke misali mace da namiji da yake sun saba dama dashi nan ya bar aikin ya d'auko wata computer yana nuna mata sample har da zata nuna mai pic d'in sai kuma ta fasa don bata so aga face na 'yar uwarta. Hotuna ne birjik na Mata da Maza sunyi kyau a gabanta yayi editin ya cire kan wani ya sa akan wani saurayin sai kace shine haka ya nuna mata kallonta yayi "kin gane yanzu" tace "eh" nan ta d'an zauna sai tace "nikam ban Naga pics din Naga style masu kyau" mika Mata laptop d'in yayi ta dinga gani zaro ido tayi ganin saurayin da aka had'a pics nasu da Husy kuma ga budurwar agefe wadda aka cire kanta aka sawa Husy hannunsa cikin rigarta wani wawan nishi ta saka tayi murmushi Alhmdlh nuna ma salihu tayi tace ya tura Mata pic d'in a waya hakan kuwa take ya tura maata ta bashi 1k ta tafi tana murna.

********

Da gudu ta shiga d'akinsu husy na zaune tana aikin dube duben waya sai lek'a groups take tana dubawa Allah yasa kartaga hotunan nan domin tasan Halin Sady zata iya watsawa hamdala tayi ta kashe data k'ululin bak'in ciki ne ya kamata don tunda jiya Shuriem yazo da abinda ya faru ta kasa sukuni ta rasa wane mataki zata d'auka jitake kamar tace ta fasa auren Shuriem din ,kuma da mamakin inda saurayin ya santa da fata tayi ta dago kai "tun dazu naga kina tunani ai kisani komai yazo end na samo bakin zaren" ta zaro wayarta ta lalaubo Gellary "kalli nan" da sauri ta karba tace "ke kuwa ya akai kika gano? hasy tace "haba yanda take da ilimi haka muma" zuwa tayi akai editin aka cire kan wan nan ladyn aka saka naki ai duk ya nuna ke bakya ce anyi wani abu ba" "Amma Allah ya isa wlh ban yafewa Sady ba." nan ta fashe da kuka "gashi Shuriem yana fushi tun abun fa ya faru jiya ai wallahi sai Allah ya sakamin,ni bansan taya ma akai saurayin jiya harda no dina ya kira fa." Hassy tace kede yanzu kawai musan yanda za'ai na nunawa Shuriem ya tabbar da Gaskiya, bayan hakan zamu gano waye wlh bazamu yardaba,kuma dole ta hakura sa Shureim" husy tace "kyaleshi tunda har ya yarda , ni na hkr na barmata Shi bazan iya jidalin nan ba" Hassy tace "kiyi hkr kin san fa makirci dole yaji ba dadi .Amma batun wai ki bar mata Shi bata tasoba saide in shine yace ya fasa" nan ta mike "bari naje nai wanka don na dauko rana duk da a mota nake amma ina dan jin zafi,tsunduma kogin tunani husy tayi wanda bata san bacci ya kwasheta ba tare da mafarkin abin sonta.


By
Queen Meemi.👑
.
. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣59❣
*March 2017*


_*Sadaukarwa ce ga Basheer Usman Family's*_


*********

Washegari kuwa wajen 10 sai ga Sady a office d'in Shuriem yana zaune yayi shigar shadda hartin da wando farare k'al -k'al ya turo hularsa gaba yana ta Rubuce -Rubuce tura k'ofar tayi ta shiga tana karai raya sai kace tarwad'a kujera taja ta zauna bai d'ago ido ba, tadade a zaune san nan tace "Shuriem kaga abinda nake fad'a ko? kaso mai sonka don hussy ba sonka take ba, domin da idona a sch nake ganin ta da wan nan saurayin" nan ta zaro pic ta aje agabansa. "saurayinta ne sosai kowa ya sani don haka ni Sady ni ce mai sonka kayi tunani idan kayi Accept you can call me" da sauri ta mik'e har taje k'ofa yace "wait" nan ta tsaya yace "zoki d'auke haukanki kuma ki saurari Punishment dina san nan nace maki bana yinki, plss ki je gun masu sonki su aureki maana! Domin duk wani makircinki sai de ki gama amma mutu karaba nida fines kingane"
Murmushi tayi ta fita Amma ak'asan ranta kamar ta kwanta k'asa tayi birgima haka taje gida. Sumy na had'a wasu kayanta ta Sady ta zube a gado "sumy nayi-nayi ba irin abinda banba handsome ya kasa ganewa ya nace wa waccen fool gal d'in dame tafini? dame Allah ya rageni? harda zai na min hakan"nan ta fashe da kuka Sumy ta tab'e baki "ai dama duk Wanda yasai Rariya yasan zata zubda ruwa kuma duk abinda kayi za'aima, karki manta irin wulak'ancin da ki kaiwa faruq wlh nasan ko rabin sa Shuriem bai maki ba, nadai gaya miki kiyi karatun ta nutsu kin dace kinada farinjini ma don Naga wani kamal na sonki yana zuwa shima kina wulakanta shi to kiyi ahankali tun kan dare yayi maki."Tsaki Sady tasa ta tashi tace "naji kuma ban d'auka ba" "jiki magayi ai" cewar sumy.


********

Husy kam da safe data tashi sukayi break suka tafi School itada Hassy domin lucture safe ce dasu. Kamar k'arfe 11 Hassy na zaune a Captaria tana try Number d'in Shureim 3 missd call san nan ya d'auka suka gaisa tace "don Allah kazo Cumpus namu akwai wani Abu da zan gaya maka da zaka san gaskiya plss." "Okey hassy zan zo after 2" nan ta kashe ta tafi Lucture.
@2:00 Shuriem ya shiga school din ya faka bakin Bishiya ya kira Hassy dama ta dad'e da fitowa ta fito tazo inda yake ta gaida shi san nan tace "Shuriem hak'ika duk abinda ya faru wlh sharrin Sady ne, domin da bakinta ta gaya mana duk plan ne donta sameka haka saurayin da yazo jiya shima plan ne plss ka gane. bari kaga" nan ta d'auko Pic ta nuna mai ya karb'a yaga asalin pics d,in yace "to na jiya fa? tace shima duk had'inta ne, kaga kenan baruwan husy bai kamata ka d'ora laifi akanta ba" jikinsa yayi sanyi."Hassy ina son sisi naki ne shiisa nake jin kishinta, wlh duk da nasan ba gaskiya bane Amma na samu hujja insha Allahu zan maganin ita Sady." nan tace "yawwa Shuriem." Dai de lokacin Hsusy ta tawo sanye da dogon hijab bata kalli inda yake ba shikam idansa na kanta wani Birgeshi tayi wani d'an Murmushi ya saki ta kauda kai tayi gaba ta shiga motar su .Hassy tayi mai sallama suka tafi ya dade a tsaye yana Murmushi ya shiga Motar sa ya d'auki hanyar fita.
Hasyy dake kwarara gudu a Mota ta kalli Husy tace "yanzu komi Normal, kiyi hkr nasan zai taushi zuciyarki, itakam Sady daga wan nan ta daina domin zami maganin ta".husy tayi murmushi "nifa kaina yau ciwo yake" Hassy tace "ba wani ganin na k'arfen ne ya birkita lissafinki" .Dariya suka saka 3:00 suka shiga gida.



**********

Shuriem kuwa adai-de layin da zai shiga gidan su yaga saurayin nan da yayi pretending as saurayin Hussy nan ya sha gabanshi Saurayin ya fito zaiyi bala'i yaga Shuriem nan ya sandare don ya ganeshi, a nutse Shuriem ya tako ya tsaya yace "wato han baka kud'i ake ka kashe aure ,ko ka b'ata da d'ad'diyar soyayya ko? to kayi na farko kayi na k'arshe" nan ya d'auko hotunan ya mik'a mai, "kaine ko zakace ba kai bane na asalin kuma kazo jiya" nan ya dabirce take Shuriem ya bugawa Police dake kusa domin ya damk'e hannunsa ya kasa kwacewa, ba'a dad'e ba sai gasu nan yace atafi dashi anjima zai zo....
Sai da Shuriem ya koma gida yaci abinci yayi wanka yadan matse barcinsa gajiyar sa duk tabi jiki san nan wajen karfe 5 :00 ya mik'e ya tafi police station zuwan sa Sauryain nan ya gaji ga yunwa nan ya zauna yayi wa DPO bayani kan abinda saurayin yayi don ai musu tsakani, yace ayimai hukunci nan suka tambayeshi dalili ya fad'a kan Sadyce ta saka Shi yayi aikin ta biyashi.ya d'ora da cewa suyi mai rai domin Shike dawainyar gidansu
Nan DPO yace "yi mana shiru kune masu d'aurewa karya lasisi" yace ya a kirawo ta nan saurayin yayi kiranta kan tazo ya samu wata idea, 6 dai -de motar ta ta k'arasa Station d'in tana shiga suka gaya Mata abinda ke faruwa nan hankalin ya tashi suka tambayeta sunanta ta gaya musu. DPO yace "wato ke 'yar gidan Alhaji tanko ce ko shine kike haka, lalle kuwa zan sanar mai" jikinta yayi sanyi Kudi ta zaro ta aje ma Wani kurtu sukace Aa Wanda ya kawo case Babba ne sai de tai hkr.Shuriem ya shigo wajen suka gaidashi ya zauna gefen da Sady take ya kalleta "yanzu sai kibi wani sarkin don husy ta miki nisa." DPO yazo yace "ya sunan yarinyar da sukaiwa haka ,nan ya fad'a Sunan ta dana babanta hankalin DPO ya tashi yace "wait itama 'yar manya ce ashe!" ya kalli Sady "dole mahaifinki yaji."nan ya dauko zai kira tace "plss kayi hkr karka fada" "dole na fada domin idan sukace basu yarda ba fa?"
Dady na zaune dawowar sa kenan wajen 7 DPO ya kirashi ya sanar mai cikin tashin hankali ya tashi yace "yanzu zai zo Umma ce dama a d'akin tace "meye?" yace "kinji Sadiya ce ta cangwalo wai suna hatsaniya da yar Ambassado,r komi ya kaita l yanzu Shi saurayin ita yarinyar wai ya kaisu station ita da saurayin da tasa yayi ma dayar sharri, wama ya bata izinin fita da dare?" nan tace subhanallah tashi yayi ya tafi driver din sa ya mika shi.


**********


Sady ido ya raina fata domin Abun kunya ne agareta .DPO ya umarci da Shuriem yace itama Husy tazo Ana nemanta. Shuriem yace basai tazo ba ga shaida duk agunsa. zuwa Dadyn sady duk aka gaya mai aka nuna mai abinda tayi agun ya wanka Mata mari ,yace "ni zaki kunyata da girmana! wato ki b'ata wa wata suna ko? akan son zuciya kuma 'yar Ambassador to ki sani afagen mulki ma yana sama dani donni yanzu bana cikin mulki don haka dole na baki Punishment" "Dady Kayi hkr" yace "yi min shiru" ya kalli Saurayin kai-kuma anyi Sahorami da za'a baka kudi kayi shirme" nan yace wa DPO itama asata a cell d'in kya k'ara hankalta .
Shuriem cike da girmamawa yace "ba za'ai haka ba, kawai de ta saka hannu nima na saka bani ba ita, kuma ba ita ba husaina domin tana yawan Cusguna mata don haka ai musu Tsakani." DPO ya kawo Paper ta cike tana kuka shima haka Shuriem ya cike shima. Saurayin kuma akai mai afuwa kan ya kuma sai yayi watanni acell nan duk suka tafi. Dady kuwa kamar ya cinye Sady fad'a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.
Saurayin kuwa da gudu ya fita yana mai dana sani domin sun wulakanta shi bai tana zuwa police ba kan wani lefi ba. Shuriem kuwa dad'ine ya kamashi domin yasan ya rabu da naci .

Muje zuwa.

By
Queen meemi👑



. ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜
Showing 141001 words to 144000 words out of 155648 words