na Yaro woooooo......cikin tsawar data razana ta yace Open the door,Ba shiri jiki na rawa ta zaro key ta Bude Masa ya fice a fusace tare da banko Kofar kamar zai ballata.

Ita kuwa murna da farin ciki ya kamata ta dauki dubu biyu ko wanka Bata Yi ba ta gyara Hijab dinta tayi waje,ko me Gadi Bata aika ba ta fice daga gidan,a Unguwar tana tafiya taga wani Resturant da sauri ta Shiga ciki tayi Order taje Away na Jullof rice with salat and chicken,ta siyo lemuka harda su Icecrewm Yogourt ta dawo gida ta baje abinta a Palo taci ta koshi tayi dam sannan taje tayi wanka tasa wani gajeren Wandonsa ta zabo fari ya Mata yawa Amma ta saka Haka,ta dauki t-shirt dinsa baka ta saka sun Mata yawa Amma abinka da me kyau sai tayi kyau,Haka ta gyara palon ta Karo karfin Ac tare da kunna kallo tana kallo ta wani can saman Hannun kujera baza ma ta zauna a kujerar ba ta tale kafafu tana Shan Iceream dinta tana ta Dariya a Haka ya shigo gidan ya sameta,Kallo ya bita da shi ganin kayansa a jikinta tana Shan Icecream,Wayar charger ya fisgo da sauri yace kayana are you Mad,Da gudu tayi cikin wani daki ya bita da kyar ta samu ta buya a toilet,yace Zaki fito ne,idan kin Isa kina ji ke kece ki fito,Tace kaima idan ka Isa ka shugo,baka kunya fada da mace,Namiji da Kai kaje kayi da maza Mana idan ka Isa a tumurmusa ka,Yace Zaki fito ne sai na Ballaki Kuma wannan kayan da kika sa wallahi sai dai a kone su ban Haka skin da ke Idiot ya juya tare da komawa palo.

Tunda Aamna tasan tayi laifi Bata sake Fitowa ya ganta ba sai washe gari ta fito sanye cikin wani Lace fari Riga da skert daf da ita tayi kyau sosai Sanda ta shigayi tana tafiya a hankali,a main Palo ta Iske shi yayi Order Breakfast ya hada tea lafiyayyen gaske ga chips and Egg da farfensun kaji Yana ci hankali kwance,Aamna ta hadiyi Yawu ta fito a hankali yaji motsinta Amma ko kallonta baiyi ba yaci gaba da cin abinsa,a gabansa ta durkusa Tace Ina kwana Yaya Ahmad,sai lokacin ya kalle ta kadan Yaja uban Tsaki,tace Nima yunwa nake ji,wata Uwar Harara ya aika mata,Dan Allah San min ko na fita na siyo? Dama jiya na fita na siyo Abinci na manta ban nemi Izninka ba ka yafe min,Cikin tsawa yace Ina ruwana da rayuwarki Ni da Zaki tafi ma bangon duniya Ina ruwana,wallahi bazan je bangon duniya ba salon idan tashin kiyama yazo yajuju da majuju su fara ta kaina,Kinga ki daina Shiga harka ta,na fada Miki kiyi rayuwarki Mummy ce ta kawo ki to duk wahalarki sai ki fada Mata,Yar wahala Kawai,Yar walagigi Kawai,Ai kuwa Ni gaskiya Raina ya biya da wannan Abincin naka ka fada min Inda ka siyo naje na siyo ai Ina da kudi sannan ko ka bani naka na ci,Tana Gama fadin haka ta janyo plate din chips din gabanta ta fara ci Tace Dadi,sai ta dauke plate din ta gudu daki ta sa key,Ahmad ya dura wata Ashirya yace yau ba abinda zai Hana ban karyaki a gidan nan,Sa'anki ne ni? Aamna Tace ae daga bedroom,Sai da ta cinye tas ta fito lokacin ya bar gidan ma,ta kalli kwanikan Daya Bata duk abincin ya rage Bai cinye ba duka,ta zauna gaba Daya ta cinye sannan ta hau gyara gidan tana mita mutum sai yawon jaraba kullum Yana waje.

Duk wani Aikinta sai da ta Gama sannan ta zaro Yar Wayarta Vivo ta Kira Mama suka gaisa da Baba,ta Kira Zuhra ma Suka Sha Hira,Siyama ta Kira karshe,Siyama Tace Amarya bakya laifi kin tafi kin barmu da Aiki a Resturant,Yaya Mutumin naki ko anyi abin ne? Aamna Tace Allah ya kiyaye na hada jiki da Dan giya,ke Siyama wallahi baya kaunar Mace,wannan ko tsirara Zaki zo gabansa baza ki birge shi ba,Dariya Siyama tayi,wallahi Aamna ga masifa kullum Fuskarsa ba Rahma Abu kadan Kuma sai masifa,wannan bazai shiryu ba,banga abinda za a Masa ya shiryu ba,to Ina ma yake Zama da har zai fahimci wani Abu mutumin da sai ya kwana a waje can ko sai cikin tsakiyar dare zai dawo,ga Dan Ido na Guda Daya a manne,Suna ta surutu har suka Gama ta fara karatun Qur'ani,Jin yanda aka banko kofa tasan Ahmad ne ko Sallama dama bayayi Yana shigowa yace ke koma dakinki kiyi karatunki ko ki koma masallaci ki tare,Ganin yanda ya shigo a buge sai ta tashi tsam tayi bedroom shi Kuma ya kwanta a saman kujera,Ya kunna tv ya kure volume karshe kida ya cika gidan a manyan speakers Yana sani yayi Kuma dole Aamna ta hakura da karatun Qur'anin sabo da yanda kida yake dauke Mata hankali,Fitowa ta sake yi,ai kuwa ya Mike a fusace yace ba nace ki daina matsowa inda nake ba ya dauki Remote ya jefe ta da shi da karfi ji kake kwas a goshinta,sosai taji zafi wajen ya kumbura yayi Mata kulu,Itama ta dauka ta jefa masa a bayansa,ta gudu ya bita cikin zafin nama Amma ta kulle Kofa Haka ya rabu da ita yace Zaki fito ne.

Sai bayan Sallar Isha Aamna ta fito sanye cikin doguwar Riga Yar kasar masar,me shape sosai wata silver,ba karya tayi kyau,Mayafinta tayi Rolling ta dauki kudi ta fito,yau ma tayi sa'a sai ta ganshi a kwance Yana cin green Apple,Aamna cike da tsoro ta karaso inda yake wani kamshi yake na musamman,a gabansa ta tsuguna Tace Sannu da hutawa zanje siyo Abinci,Baki ya tabe sai da ya dauki mintuna yace Ina ruwana,mikewa tayi ganin masifa yake ji kadan yake jira sai tayi tafiyarta kuwa,taje tayi take Away sharp sharp ta dawo,Lokacin Yana Zaune Yana kallon wani American film, Sakwara da miyar kifi, ruwa Eva da fruits salat,tana ci tana kallon Film, .

Wayarta ce ta hau Ringing tana dubawa taga Mama,da sauri ta daga,bayan sun gaisa Mama Tace Aamna ga fa kudin sadakinki Baki karba ba,Aamna Tace Ina sane da abina,suna Rai na,a ciki ki dauki dubu Goma kyauta,ki Bawa Baba dubu Talatin,Zuhra a Bata dubu bakwai,Siyama kawata a Bata dubu Uku Kinga dubu Hamsin ta Kare ko? Mama Tace Haka ne,to dubu Hamsin din a ciri dubu biyar a bayar Sadaka Allah ya Kai ladan kabarin mamata sumayya Allah ya Mata Rahma,a sake cire dubu biyar Abba na Daya gudu ya barni ayi Sadaka nayi tawasili da ita Allah ya shirye shi ya canja Hali,Mama tayi Dariya Tace ai duk kin rabar da kudin ba Haka akeyi ba,Zan dai cire na Bawa kowa abinda ya Dace sauran ai naki ne,Aamna Tace to koma dai mene abinda aka barmin a kaiwa Kawu Isma'il can kauye ya Siya wake da Alkama a ajiye idan sukayi tsada sai na siyar na samu riba,Nan fa Ahmad yace tab Riba kudin riba ai masifa ne, ka siyi Abu ka boye sai yayi tsada kazo ka siyarwa mutane,Wannan ba Business bane,Aamna Tace Kai baka ga laifinka ba barasa kwalaba Nawa kake dirkewa cikinka wlh kayi hankali Kar Hantarka ta tabu tam,Hannu yasa ya murde Mata kunne ta kwalla Kara,Mama ta waya taji Kara Tace lfy? Mama wani kwaro ne ya firgita Ni.

Can Baba ya fisge Wayar yace ke Aamna Dan Ubanki kiwa fa mijinki biyayya,duk abinda yace kiyi bana son sakarci,Kuma ko me Zaki shuka ki shuka gaskiya kiyi gaskiya ato sabo da mu dangwali arziki da kyau,Aamna Tace yo Baba ai Gaskiya Ni a jinjina take da ita aka haife ni,dankwalin Aamna ne ya zame layar ta Guda biyu Dake soke a kanta suka bayyana,Ahmad Yana gani ya girgiza Kai a zuciyarsa yace mashirkiya,Ita dai Aamna abincinta take ci tana Dan juyowa ta kalle shi kadan sabo da faratansa na Hannu Dana kafa Daya Tara sunyi tsayi Kamar Arne Amma da gani suna Shan gyara wani fes da su sai dai ba a Yankewa,Allah yasa kayi bacci sai na yanke wannan uban faratan Aamna ta furta a ranta.

Ganin tana ta Kallonsa Yaja Tsaki tare da mikewa ya dauki key din machine dinsa zai fita,Aamna Tace Ina zaka je da daren Nan Haka?Ni tsoro nake ji gaskiya,Kwafa Yaja a ransa ya furta Mummy ta Gama Dani,idan na Mata Illa tsinuwa ta hau kaina,juyowa yayi a fusace yace Allah ya taimakeki Ina son Nonon Mummy Dana yasha yabi lafiyar jikina Amma da kin Gane kurenki,Aamna ta kyalkyale da Dariya Tace au har yanzu Nonon Mummy Bai Gama bi maka jiki ba? Sanda aka haife Ni ko yaye Ni ba ayi ba aka samu cikin Saddeeq shi yasa ya cuce Ni na Sha gubar cikinsa,Aamna sake kecewa da dariya Tace ko shi yasa aka ce ka Dade a tsumbure baka girma ba Dan Mummy Tace har cutar koshokwo kayi Haka Kawai Aamna tayi karya Tace Mummy ce ta fada Mata,ai kuwa shi da saurin Fushi kwaya tana sashi saurin Fushi ai Kan Aamna ta rufe baki yace uwar Koshokwo nayi,Aamna ta Mike zata gudu Suka dinga zaga palon Nan sai ya kamata ya dake ta Itama ta guduwa,ta samu tayi waje Compound da gudu,fita yayi Yana huci ya hau lifan dinsa ya fice sannan Aamna ta dawo ciki abinta.

Bayan Sati biyu da Auren Aamna kullum fada sukeyi da Ahmad ba Wani mutunci, Mummy ce ta Kira Aamna Tace,bayan sun gaisa Aamna ta saki kuka Tace Mummy wallahi kullum sai munyi fada ya Duke Ni saurin duka ne da shi Kuma yaki siyo kayan abinci kullum sai dai naje na siyo ko na aiki me Gadi shima Haka Mummy, Dariya Mummy tayi Tace Kuma wallahi Ahmad ya Iya girki sosai a haka,kin San nice na sallami Peter me dafa Masa abinci, Aamna ki Kara Hakuri,bazan turo Miki kudin Abinci ba Yana da kudi,kece Zaki San yanda zakiyi Masa dole ya Baki kudi ki zuba abinci a store kin Gane,ae naji to ta furtawa Mummy,Bayan sun Gama Wayar Aamna ta zauna tayi tagumi tana saka Taya zata sa ya siyo Mata kayan abinci ko ya bada kudin ta siyo tunda kudin hannunta sun kusa karewa.

Bayan tayi Shirin bacci cikin wata Riga da wando farare masu laushi ta zuba kyau ciki,a Palo ta zauna tana jiransa ai kuwa taci sa'a yau Ana Sallar Isha ya shigo gidan Yana tafiya da kyar da yanda yake Gadara ya nuna yau baiyi shaye shaye da yawa ba,Sannu da zuwa Aamna ta Furta,ko kulata baiyi ba Direct sama ya haura ya fada toilet,wanka yayi ya fito tare da Gabatar da Sallar Isha ko Addua baiyi ba ya Mike ya saka wasu kayan bacci dark blue me digon fari Riga da wando,fresh milk ya sha sannan ya kwanta a Gadonsa Nan take bacci ya kwashe shi me nauyi,Aamna ta biyo shi dakinsa Wanda Bata shiga sai idan zata gyara,a hankali tayi knocking Shuru taji,tayi Sallama Shuru,sai ta bude Kofar a hankali saman bed ta hangoshi ya wani Yi dai dai Yana baccinsa,Aamna tayi murmushi Tace Allah sarki yayi bacci,a gefen bed din ta zauna a hankali gefen kafafunsa,Nan take ta tuna da taga faratansa ya Tara sun Sha gyara,Room dinta ta koma ta dauko razor blade sabuwa dal ta bare,a tsorace tayi shahada ta Dan rike Yatsansa kadan sannan ta fara yanke Masa farcensa daya Tara Yana gayu da abinsa,ta fara yanke su Daya bayan daya,gashi da nauyin bacci har ta Gama hannaye Bai ko motsa ba Kawai baccinsa yake Sha,ta dawo kafa ma ta yanke Masa tas ta gyara ta kwashe farcen data yanke ta zuba a trash da razo din duka,ganin Bai da Niyyar tashi ta hakura itama ta koma dakinta Bayan ta kashe Masa hasken wuta ta Dan rufa Masa blanket sabo da taji sanyin ac yayi yawa.

Itama komawa tayi dakinta ta kwanta abinta,sai 2am Wayarta ta tashe ta sakamakon saita Alarm da tayi, Mikewa tayi tare da Gabatar da Sallah Nafeela raka'a hudu tayi Adduointa sannan ta koma ta kwanta,sai Asuba ta sake tashi tayi raka'atanil fijr tare da Sallar Asuba ta zauna ta Gabatar da Azkhar sannan ta koma bacci,10am ta tashi ta hau gyaran gidan,Compound kuwa me Gadi ya Gama gyara ko Ina har Garden,Dakinsa ta shiga karshe taji karar ruwa alamar ya tashi Yana toilet,bedroom din ta hau gyarawa komai ya koma neat dama shi Sam Bai da kazanta akwai tsafta,ko Ina kamshi ne ke tashi,toilet ya Bude ya fito daure da towel a Kugunsa karami Kuma a hannunsa Yana goge wuyansa ga kitson kalabarsa Nan sabo an canja Masa sabo sai wani sheki yake Yi Bai jika gashinsa ba sabo da Attachment aka saka yellow, red and green,Aamna jikinsa ta kalla lukwi lukwi sumulmul,Fuskarsa a daure ko kulata baiyi ba ya tsaya a jikin Mirror Yana karewa Kansa kallo,Muryarsa taji yace Sexy Guy,gemunsa da Sajensa ya shafa yace Fresh Guy,Aamna ta zaro Ido taga Yana ta yabon Kansa Yana kallon Kansa a mudubi Yana shafa kitson kalabarsa,Toilet din ta shige ta gyara masa a ranta tana jinjinawa tunda take gyara Masa gida Bai taba nuna yaji Dadi ba ko abin ya birge shi ba,harkarsa Kawai yake Yi,Tana wanke toilet taji Muryarsa Yana Kiranta Bush girl.....Bush girl....tsoro taji Kar Taki zuwa ya Mata duka a banza Fitowa tayi da sauri Tace gani,Wani murmushi ya saki me tsada yace Good girl Ashe kin Gane sunanki,da Hargowa yace Ina wani perfume a Nan sabo? Murmushi Aamna tayi tace ai na dauke shi Ni zanyi amfani da shi sabo da Naga na Mata ne Kai Kuma Namiji ne,wani Ashar ya dura yace kin San tsadarsa kuwa? Yo ba gidan mijina bane,Kuma ma kayan Mijina ai Nawa ne ta karasa da shagwaba,Tsaki Yaja yace why are you always looking for my trouble? Idan na balla ki hmmm common dakko min kafin Raina ya baci,Aamna Tace Idan kana son na baka ka bani kudin Abinci ko ka siyo kayan abinci a gidan Nan yanda Zan na girki da kaina.

Wani Takaici ya kamashi ji yake kamar ya harbeta yace bana Baki kudin abincin ba uban me Zan Miki,Aamna Tace Ni ka bani Dan Allah yau naje kasuwa na shirya store da kitchen dina,kana min fuck up fa a gidana,kanta yayo Aamna ta fisge towel dinsa ya Fadi kasa ya dawo zigidir, da sauri ya dauki towel din ya daura kunya ta balain kamashi,Abu na farko a rayuwarsa da yake Jin kunya Bai so aga tsaraicinsa Amma wannan Yarinyar ta cuce shi,Aamna takawa tayi zata gudu ya cafko ta ya dakko belt din Wandonsa tana Ihu ya riketa Kam ya dinga tafkarta iya karfinsa,tana ta Ihu tana cewa banga komai naka ba,kayi Hakuri,bazan fadawa kowa,bazan cewa kowa ga Kalar abinka ba,ganin zai Mata Illa a banza Tace Tsinuwar Mummy a kanka,Yana huci Idonsa yayi jajir ya tsaya cak Yana haki,Ita kuwa Aamna da Dan Idonta Daya a manne ta Mike tana kuka Wiwi,ta koma toilet din ta karasa wanke Masa tana kuka ta fito zata fita kenan ya shirya cikin wasu kana Nan Kaya farare tas marasa nauyi wandon pencil irin na shakatawa a gida da Alama ba fita zaiyi ba yau,rafar kudi Yan dubu dubu ya jefo Mata yace gashi Nan ki Siyo Uwar kayan girki,last warning ba ruwana da ke,karki sake Shiga harkata,ke magana ma ban so ki min,Aamna Tace ai wallahi baka Isa ba Mijina Guda ai dole na maka magana,Kwafa Yaja yace to kuwa Zaki ci Ubanki wallahi.

Key din machine taga ya dauka Ashe fita zaiyi
Ba zato Aamna ta sa key din kofarsa ta kulle ta cire key din ta jefa a bra dinta Tace Yau ma baza ka fita Muna dakin Nan zamu yini sai dai yunwa ta kashe mu,lips dinsa ya tamke tare da rufe Idonsa kam tsabar bacin Rai,yace ban so Tsinuwar Iyaye ta shafe Ni,sannan gwara nayi komai Akan na taba Nonon mace Bude min kofa ko yanzu na karasa Miki idon Daya,Aamna ta tsaya sanye da Atamfa Riga da skert na lefe ne sun kamata sosai,Tace tunda aka auro Ni baka taba ko Dan Rungume Ni ba,Please yau kafin ka fita Ina bukatar warm Hug,just ordinary Hug,Nima yau Ina so na motsa jam'iyata,kina hauka ne? Meke damunki,Ni zanyi Hugging naki? wata Dariya yayi yace Ashe nine ma na ganki nace Ina so,kanki akwai motsi lallai,Aamna Tace to lallai zamu kwana a Nan,tsayawa Suka Yi a Gaban kofa har na tsawon minti biyar ba Wanda yayi magana,nisawa yayi tare da girgiza gashinsa yace open the door,Aamna tace Baby Hug me Mana ka fita abinka,tunani ya tafi idan ya duketa Mummy dinsa,idan yace zai kwace key sai dai ya zura hannunsa a Boobs dinta shi gaskiya Bai son taba Nonon Mata,Baya Yaja kadan yayi Dan tangadi sannan yace Okay ya runtse Idonsa sannan ya Bude hannayensa,Aamna tana murmushi taje ai kuwa ya cakumeta irin bai iya ba Kawai cakumarta yayi ita Kuma tana sani ta kankameshi ya fisge jikinsa da bala'i yace bazan tabaki ba din,kinyi kinji Dadi Bude min kofa,Tace yanzu kuwa ta dakko key ta Bude Masa ya fice a fusace,ya hau machine dinsa kenan sai ga Aamna ta fito da gudu tana wait wait...da masifa ya juyo sai yaga Ashe wayarsa ce ya manta,Tace ka manta wayarka Baby,fisge Wayar yayi tare da Mata wani kallon banza ya Bawa machine dinsa wuta ya fita,Aamna kuwa wanka tayi ta shirya tsaf ta Kira Siyama kawarta suka je kasuwa,duk kayan Abinci na more rayuwa sun siyo dai dai gwargwado,tare suka dawo a taxi Suka shirya kayan a Store tsaf,kitchen kuwa komai na amfani akwai dama,sabo da Haka Jullof rice sukayi da wake taji kayan lambu da nama,Zuhra ce itama tazo ganin Amarya suka zauna suka ci abinda suke so,sannan suka gyara wajen,Palo Suka dawo suna kallo,Zuhra Tace Kan bala'i gaskiya gidan Nan ya hadu ba karya,Siyama ta Mike a saman doguwar kujera Tace
Showing 21001 words to 24000 words out of 142807 words