ne itama taje gida sun Sha farfesu Amma tana kallo Ahmad ya dauke Dan mugunta.
Tunda Siyama ta Shiga shi ya fito ya tsaya a waje,Aamna Tace ka shigo Mana yace a'a Machine Dina nake jira tafiya zanyi,Siyama ta kalla tace ina zuwa kawata ta fito Wajensa suka tsaya,tana ta Kallonsa a ranta tana ayyana irin kyansa,Shi kuwa ganin tana kallonsa harda Kara gyarawa Kamar za a dauke shi hoto,idan ta kalla ta kalla sai ya sake canja style din tsaiwarsa Haka yake ta Mata ya tafi da hankalinta sai daga baya ta lura da abinda Ahmad ke Yi Yana ta canja style din tsaiwa,Dariya ce ta Kama Aamna ta danne kadan tayi Murmushi Kansa ya shafa tare da mazewa kamar ba shine yayi ba,Hannunsa Aamna ta rike ya Janye hannunsa da sauri,Aamna tace lafiya? Kitsonsa ya Sosa yace ba komai Kawai Ni ba a taba min jiki kin sani ko kin manta ne?
Baki Aamna ta tabe Tace daga an Dan rike maka Hannu sai kace Dan gwal? Yace ai nafi gwal Ni,Harararsa tayi a ranta tace Dan ma na Dan nuna Masa caring shi illarsa Bai San arziki ba,Ganin ta harareshi yace Jaraba tare da miko Hannun yace ungo cinye shi ki huta,Bige Hannun tayi tana Dariya Tace bana so,Suna Haka Yaron ya dawo da Machine din Ahmad ya karba tare da bawa Yaron dubu biyu,ya dinga Murna yana godiya,Ina Handbag dinki? Ahmad ya tambayi Aamna.
Tana ciki yace dakko min ita,me zakayi da ita Fuska ya Bata yace ki dakko Mana Ni ba Mudubi ko powder dinki Zan gani ba nasan ku ba Uwar komai a jaka sai Kuna boyeta,Dakkowa tayi tare da Mika Masa yace Bude abarki ki rufe idonki Kuma,Aamna ta zuge jaka ta rufe ido,ganin Haka Siyama ta leko tana kallo Ahmad ya zaro kudi masu yawa Yan dubu dubu ya zubawa Aamna a jaka yace to Bude,Bude Idonta tayi taga kudi dama Bata da kudi tayi broke Bata da ko sisi gashi tana son siyen abinda ba a rasa ba na bukatar rayuwa,taji Dadi sabo da ya Bata lokacin da take bukata Tace Na gode Allah ya Kara budi Amma sunyi yawa kamar,Kansa ya dauke yace na tafi Mummyta ta aikeni tun dazu wani waje zanje na Mata Abu,Aamna Tace Kai dai kana son Mummy kullum Mummy,ai Mummy ta daban ce,Mummy na tafi Mummyn kowa cewar Ahmad,Aamna Tace Nima tawa tafi ta kowa,Murmushi yayi yace kin nemi Number Abbanki kuwa? Aamna Tace me Zan Masa tunda ya manta da ya auri Uwata ya Kuma haife Ni idan na karba me Zan Masa?
You are not Serious Haka aka ce Miki Iyaye suna laifi?Shuru Aamna tayi Watarana tana mamakin Hankalin su Ahmad,gasu dai suna tafka abin tsiya sai Suna Abu Kuma na basira da hankali, a fili tace Suma Yan Uwan nasa Dana je Sokoto nace su bani number dinsa Suka ce wallahi wurin shekara Uku kenan duk sun kasa Samunsa sai dai suna Kiran Yan Uwa na can kasar sunce yana Nan lafiya Kawai dai yanzu yayi retire a aiki Bai da aikin Yi ga Yara da Mata sun Masa yawa wahala ta kamashi,Ahmad ya girgiza Kai yace tab nasan yanzu ya sake kanjamewa Allah Sarki Abbinki,Aamna Dariya ya Bata ta bigeshi a kafada kadan Tace Wai Mene Haka ka dameshi Akan ramarsa, Murmushi yayi yace Bai yuwa ya rasa waya sai kace a Nigeria ai can ba a wannan talaucin, Ni Zan nemo Miki number dinsa,Aamna Tace Okay thanks, Machine dinsa yayiwa key tare da tafiya abinsa.
Siyama tana zaune ta kumbura tayi fam kamar ta fashe tace ke dai Aamna kinyi asara,wallahi Baki da hankali to wannan abinda yake nuna Miki ba so bane,Kar ma ki yaudari kanki Ahmad bazai taba shiryuwa ba ko jiya naje wajen Jibson a club Suka kwana suna shaye shaye suna rawa,Aamna Tace karya kikeyi Siyama wallahi Ahmad baya rawa,Yana Jin kida Yana bin Waka Amma in Banda ya Dan kada Kansa ba abinda ya taba Yi na rawa,Da kike cewa bazai shiryu ba kece Allah,Ina ruwana da Club dinsa,Siyama Tace Iyye to Bari kiji idan Baki sani ba Neman Mata suka koma Yi yanzu,kije ki tambaya Ahmad lallabaki yakeyi ki saki jiki da shi ya samu biyan bukata,Aamna Tace karfa ki manta Mijina ne,ko ma me yayi Hakkinsa ne ko ciki ya min akwai me zagina a duniya? Wai me yasa kika tsani Ahmad Haka ne Siyama? Siyama Tace sabo da Ina sonki kawata Ina kaunarki bana so ki fada wani Hali,Aamna tayi shuru....Tace to yanzu me kike so nayi? Karki bashi dama Kawai Kuma karki yarda da shi karki Bari Zuciyarki ta fada sonsa cutarki zaiyi,ki kiyaye Aamna bana so na ganki cikin wani Hali,plan suka hada Miki,Ahmad tun Yana yaro kangararre ne a Haka ya girma a tunaninki dare daya zai shiryu sabo da ke? Kiyi tunani fa,wanne duka da wulakanci ne Baki Sha ba a Wajensa? Ai Ni nake tsokanarsa Aamna ko a lokacin Ni ke shiga harkarsa da ban kulashi ba babu abinda zai min,Siyama tayi Dariya Tace kina Abu kamar yarinya 25yrs Sam Baki da wayo Baki da hankali Ni Naga wani Tsoronsa kike ji ma kina wani biye Masa,Dan giya irin wannan Dan kwaya abin kyama cikin Al'umma mutanen da Basu San darajar kansu ba bare ta wani Nan fa Siyama ta dage ta dinga zuga Aamna tana fada Mata karya,har ta Gama sannan Aamna Tace Ni fa bazan iya wulakanta shi ba,Kuma bazan iya masa komai da zai Bata Masa Rai ba,Kawai dai nasan bazan Bari na fada sonsa ba,ko cewa yayi Yana so na Zan Amince Amma badan so ba Zan Amince Dan nayi kokari na canja shi ya dawo mutum Kamar kowa ya daina wannan shaye shayen shine Kawai abinda Zan iya Dan na taimaki Iyayensa,Siyama tace ya dai fiye Miki Ina Baki shawara karki fada sonsa.
Bayan wasu satikai Ahmad Haka yake ta wahala da zuciyarsa ya kasa fadawa Aamna idan yaje da Niyyar fada sai ya kasa babu irin plan din da Basu hada ba da su Mashkoor Amma idan Ahmad yaje Gaban Aamna sai ya kasa furtawa,Yau Suna zaune da Mashkoor suna shaye shayensu Mashkoor yace yau shine Plan na karshe King idan baka iya fada Mata ba wallahi gidan Nan Zan Bari kaje ka karata,Ahmad ya daki Center table yace yau Dole ne na fada ma Dole babu fashi mene plan na gaba?wayarsa ce tayi Kara Yana dubawa yaga Bash ne abokinsu dagawa yayi yace ya akayi ne guy? King ku fito Umman Jibson ce ta rasu a asibiti ciwon Sugar dinta ne ya tashi Ana kaita Hospital ta fece wallahi,Ba ko Salati Ahmad yace yanzu Ummati ta ware itama? Yace kwarai kuwa Kun manta yau Kuma ake Sadakar Arba'in din Baban Tawaga da ya Dier shima ya kamata ku fito fa Jibson Yana wani Hali, Mashkoor ya kashe waya tare da kallon Mashkoor tashi mu tafi Ummati ta arce itama shikenan mijinta yayi asarar matarsa Allah sarki Shan maganin Mata ya Kare Abbin Jibson Kuma karya ta Kare Dadi ya kare Masa ya Gama Shan rabonsa, Mashkoor yace Kai tsohuwar Nan ai ta godewa Allah ai su Kam sunci duniyarsu me zasu ce da Allah mu ware kawai.
Machine suka figa Suka tafi Ahmad ya kalli Musa yace Kai Musa ka taho ta'aziyyar Ummatin Jibson kaga ku na kirki ne wala'allan adduarku tafi Shiga,Dariya abin ya Bawa Musa ya danne ya nuna jimaminsa yace gani Nan kuwa Bari na kulle gida,Ahmad yace biki ya same mu sabo da yanzu mutuwa ta koma biki Yan iskan mutane su taru ayi ta kwasar girki, Mashkoor yace Ana kaita kabari muje a agazawa su Jibson da tallafin kayan abinci kasan babansu ba harka Yana Shan wahala,Haka ne fa Guy cewar Ahmad,ai kafin kace me Yan shaye shaye ta ko Ina abokan su Jibson suna ta sauka wasu a mota wasu a machina, da su aka yiwa Ummatin Jibson Sallah aka kaita,Tabarmar su daban a Kofar gida sunyi jungum jungum Ana zaman makoki,Jibson ya dunkule waje daya a tsakiyarsu tare da sunkuyar da Kai kasa Yana Dan Hawaye motsi kadan sai Yace Uhmmmmm........Uhmmmm.....su Kuma abokan suna Sorry...sorry....Guy,Baban Jibson Yana kusa dasu Yana jinsu da mutanensa shima Ana karbar gaisuwa,duk Wanda yazo yiwa Jibson gaisuwa yace Ashe Ummati ta rasu? Jibson sai yace da Uwata ta mutu gwara Ubana ya mutu wallahi,Kowa yazo sai Jibson ya fada Masa da Uwata ta mutu gwara Ubana ya mutu Abbin Jibson Yana ji Yana ta Jan kwafa,wasu kuwa dariyarsu Kawai suke dannewa.
Tawaga ne yazo ya kotse machine tare da bulbule mutanen wajen da hayaki ya sakko wajen su Ahmad ya Bude hannaye da sauri Yana takowa Yana an Kuma...an Kuma Yan Uwa an Kuma jama'a...suka ce cikin jimami an Kuma Guyu......ciki yazo ya zauna yace Yau akayi Sadakar Arba'in ta Abbana Ni fa yanzu gaba daya na koma Wani shege....shegeee ne Ni Kawai bani da uba...kaf mutanen wajen babu Wanda Bai Basu Dariya ba Amma wasu Haka suka danne sabo da wajen Mutuwa ne,wani Wanda ake cewa Gayu yace ai Nima Ina cikin Shegun mu mun Zama 'yayan shege to ba uba ai Kawai ka Zama Dan shege....wani Ana kiransa Jagu Dan wiwi a cikinsu yace wannan abin idan na tuna ba karamin kuka yake sani ba ya fashe da kuka shima Yana cewa Nima Ina cikin 'yayan Shegu,Wai su Kawai idan baka da uba ya mutu to ka koma Dan Shege,idan Kuma Uwa ce to ka Zama cikakken Maraya komai girmanka.
Ahmad ya dafa Jibson yace ai gwara na Zama Shege akan na Zama Maraya Jibson,Mummy ta Mutu ai Kawai ku kaini kabari da Raina Nima ku binne,Mashkoor yace mu Kuma mu zauna da wa idan mun binneka shike Nan muma Bamu da kai? Ai bazai yuwu ayi biyu babu ko daya ba,Ana ta kallonsu Dariya ta cika mutane Amma an kasa Yi sabo da mutuwa kowa sai ya bar wajen yake Dariya,Wani Dan Majalisa yazo Ta'aziyya,Baban Jibson ya Kira shi yace ga babban Dana can,Jibson ya karaso wajen,Dan Majalisa yace Sannu da Hakuri Allah yaji kanta yaro kayi Rashi,Jibson yace Babban Rashi yau na tabbata Maraya Dan Allah ku bani mukami a Gomnati na shugaban Marayu na Nigeria da Uwata ta mutu wallahi gwara Ubana ya wuce sau dubu dubu,Danmajalisa shima abin Dariya ya bashi gashi da yanda suke Maganar abin Dariya ta Yan maye.
Kudi ya zaro dubu Ashirin ya mikawa Jibson yace gashi ko ruwa a siyawa Mutane Jibson yace Allah kiyaye na karbi bakin kudi,wannan bakin kudi ne tunda baka bani ba sai da Uwata ta mutu zaka bani wanne amfani zasu min,Baban Jibson ya daka Masa Tsawa Amma Jibson yace wallahi bazan karba ba,da karfi ya daga Murya Dan wulakanci sai da aka ga Uwata ta mutu Za'a taimakeni duk an wani cika Mana Kofar gida Ana cinye Mana Dan abincin Daya rage Mana,Dame zamu ji da cinye abinci ko da jimamin,kowa Yana ci Yana wani jimami,Mata Yan Uwa suna kuka suna ta girki Ana Dora tunkunya Ana saukewa wallahi baza mu lamunci wannan ba,Ahmad ya mike shima yace a barmu da abinda ya dame mu na rashin Ummati mun gaji tun safe muke bi layi layi na mutane Muna rabon ruwan Sha da Abinci,Tawaga yace aikin banza Muma Haka Dan kudin Sadakar da aka Tara Mana da abincinmu cikin sati Daya aka cinye shi tas ga tarin Yara an mutu an bar min,Baba ya dinga aure aure ya Tara Yara Ashe duk Haihuwar da akeyi Ni ake haifawa ban sani ba, wallahi da nasan hakane da kaina Zan dauki matan Baba na kaisu asibiti Dan ubansu duk a daure bakin Haifarsu,yanzu ga Yara can sunfi ashirin Ni kadai ne Babba Kuma ba Wani Abu ya mutu ya Bari ba gona ce Kawai a Kauye Guda biyu.
Ina Shiga gida Yara suna zare Ido Yan kanana turagutsa ba Wanda zai iya aikin karfi to wallahi a Nan ma tunda Ummati ta rasu Baba baza ka Kara aure ba wallahi ko wace zata aure ka sai mun farke Mata ciki,Ahmad yace bazai yuwu Iyaye ku dinga aure aure Kuna mutuwa Kuna bar Mana masifa ba,ga yanda kasa take ciki yanzu a mutu a bar maka Yara Kai kanka da kyar kake iya rike cikinka, daga yau mun Zama masu yaki da Aure auren Iyayenmu maza,duk tsohon Daya matsu zai Kara aure to ya Nemo juya wacce Bata Haihuwa ko Kuma aje a cire Mata mahaifa.
Jibson yace Iya Ummati Abbi ya aura Amma Haihuwar ta Sha Uku Haba jama'a sai kace macen Zomo, Guda Daya ne ya rasu Sha biyu suna Nan cas da me zanji gasu duk mata,ko wacce na shiga Yaya kudin makaranta,Yaya kudin kitso,Ya..ya..ya...masu auren ma yau Fa'iza mijinta ya hanata abinci ta dawo gida an auno Mata shinkafa ta tafi da ita,gobe Safiya mijinta ya mareta ta kawo Kara,jibi Zakiyya mijinta ya korota to a gaskiya bazai yuwu ba,daga yau kunci abincin karshe gobe ko koko ba me Fitowa da shi wallahi.
Mutane suna ji Ana ta kallo wasu suna zanzarewa Baba shima yasan Yaran sunyi gaskiya tsoro yake ji Kar a cinye Dan abincin nasu su fada wani Hali Amma sun tozarta shi ya zaiyi dole ya kyalesu tunda su suke siyo komai abokan,Ahmad kadai mota guda ya sauke musu ta kayan abinci da safe,Haka duk abokan kowa iya karfinsa sun kawo tallafi daban daban,Kuma ko ba mutuwa sune suke taimakonsu basa kukan rashi.
Ranar da akayi Sadakar Uku suka Kori kowa Suka ce Sunna sak ba zaman makoki ya Kare,Ranar Bash ya tafi gida ya Iske Mamansa tana Aiki yace Mama Yaran naki Mu bakwai kika Haifa Dan Allah Mama karki sake Haihuwa Haka,Mama ta kalle shi tayi murmushi Tace baka da kunya Bashir Ni kake gayawa Haka? Wato ka Sha ta maka yawa zaka zo ka min hauka ko? Bash yace Mama Naga darasi Yaran Nan Ni fa kuke haifawa kina ganin Yayana ba lafiyayye bane yanzu nine kamar Babba gashi Mama da kuruciyarki,Dake ita Maman Bash sai ka rantse ba ita ta haife su ba,Allah ya Bata kyan jiki karamin jiki gareta sai ka rantse Yayarsu ko kanwarsu,Bash yace Mama gobe Monday ki shirya zamu je asibiti ki duba abokina,Mama Tace Allah ya kaimu Bashir.
Washe gari da Sassafe Bash ya dauki Mama zuwa Asibiti,wajen Likita Mama taga sun shiga,Bash yace Likita gata na kawo maka ita akan Maganar da mukayi,yace matarka ce ko me? Kawai Bashir yace Matata ce, Maman Bash Dake akwai saukin Hali ba ruwanta yaranta Kamar abokanta tana kallo Bash yace a Mata Allurar Family planning Haihuwar ta Isa Haka,Likita yayiwa Mama tambayoyin da Suka Dace itama dama ta gaji da Haihuwar,Test aka Mata Bata da ciki Nan Likita yayiwa Maman Bash Allurar wata biyu,yace idan time ya cika ku dawo Karku tsallake,Bash yace an gama,ya figi Mamansa a Machine suka dawo gida,Kuma Mama Bata fadawa mijinta ba sabo da Bash yace karki fada Masa kin San Baba Dan gargajiya ne sai dai yaga Shuru kin daina Haihuwa,daga yau Haihuwa ta Kare a gidan Nan sun Isa Haka, Mama tana ta dariyar su Bash.
Bayan Mutuwa ta lafa anyi Sadakar Bakwai Aamna yau kwana bakwai Bata ga Ahmad ba,duk ta Shiga damuwa ta Kira wayarsa Bata shiga,Bata San mutuwa aka musu ba,Shi kuwa Ahmad da dare Bayan sun Gama shaye shayensu da safe 7am ya koma gida, Mummy ya Kira a waya, yace Mummy Ina cikin wani Hali,danki ya fada soyayya jiya jiya na gano cewar Soyayya na fada,Farin ciki ya Kama Mummy Tace wannan wacce me sa'ar ce? Bata kawo Aamna bace tunda yace wata ce tasan da Aamna ce zai ce Aamna ce,ta so ace Aamna ce,Mummy Tace to itama tasan kana sonta ko me? Ahmad yace Mummy kwarjini take min na kasa fada Mata,zuciyata idan na ganta bugawa takeyi,Mummy Tace karka damu Son ka cire tsoro Kai fa Namiji ne ko wace kaje Ni na baka dama ka fada Mata duk irin son da kake mata,Ni Mummy Umarni na baka ka furta Mata karka ji tsoro,ta dinga zuga Ahmad tana dorashi a Kan hanya,suna Gama Wayar yaji wani kwarin gwiwar da Bai taba ji, yace Mummy ce ta bani Umarni,wannan Umarnin Mummy ne naje na fada Mata.
Ai zumbur Ahmad ya mike sanye da 3qutr blue da Riga Armless wata white and sky,ba Wani shiri ko wani wanka da canja Kaya na Kamala,lokacin zuciyarsa ta Gama tunzura, Kansa Kuma ba Wani saiti tunda jiya an cake da yawa,7am da sassaffe ya tsaya a Kofar gidan su Aamna ya Shiga dukan gidan Baji ba gani kamar zai balla musu gate,gaba dayansu a tsorace Suka yo waje Baba,Mama , Aamna tare da Siyama sabo da ranar Siyama a gidan su Aamna ta kwana,Baba Ne ya bude kofa,ko kulashi Ahmad Baiyi ba ya fada gidan a fusace da Masifa hankali a tashe Yana Bala'i ya tsaya a Gaban Aamna Dake tsaye sanye da kayan bacci ya nunata da yatsa da karfi a gigice ba nutsuwa Yana haki yace
Kin hanani sukuni...tun Sanda na ganki Bayan kin bar gidana kina shago...zu..zuciyata...ta kasa sukuni...Dora Hannu yayi aka ya sake nuna ta da yatsa da sauri da sauri yake magana ba kakkautawa Yana zaga compound din gidan Yana Wallahi na rantse.....ko idona na rufe bana bacci fuskarki nake gani kina min gizo....kullum idan na ganki zuciyata bugawa takeyi...Ina Jin tsoronki......ko yaushe bani da sukuni....burina kullum na ganki....ko naji muryarki.....bana...Bana Iya motsi sai da tunaninki......komai nakeyi kece a Raina....kece.... kike min gizo....sunanki idan aka ambata sai zuciyata ta buga.....Haka nake tsallakowa gidanku cikin dare in labe inyi ta kallonki.....Rannan ma Dan karku kamani nayi muku basaja na sace muku startime da Radio....Baba ya kurma Ihu tare da nuna Ahmad yace Kaine??......Ahmad Bai kulashi
Showing 51001 words to 54000 words out of 142807 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18 Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48