asara,Dansu Yana raye suna da kudi abinsu kece a kasa Aamna ki Kama gabanki kinji na fada miki.

Aamna Tace Mummy fa ba Haka Mukayi da ita ba,Mummy din banza,wallahi ki farka daga mafarki Aamna ko sonsa kikeyi? Da sauri Aamna Tace Allah ya kiyaye min tir na so wannan mutumin,Siyama taji Dadi a ranta Tace to ki hada kayanki ki tafi gidanku na tabbata Baba bazai Bari ki dawo ba ki fitar da kanki daga wannan masifa,Aamna Tace gaskiya kika fada na gode Siyama ke me kauna tace Inshaallah yau a gidanmu Zan kwana Bari na hada kayana idan ya dawo da wuri Zan tafi yau idan Bai dawo ba gobe da sassafe Zan taho,Siyama Tace yafiye Miki Ni na tafi ta fice abinta,Duk Hirar da sukeyi Ahmad Yana jinsu ashe Daya fita da machine ta Kofar me Gadi ya shigo Dake Kofar me Gadi biyu ce akwai ta ciki akwai ta waje,Dama shi ya gaji da su so yake ta bar Masa gida ya samu Freedom ya gaji da shishingi da take masa,yafi so ta Kori kanta da kanta sabo da Mummy Kar taga laifinsa,farin ciki ya kamashi,sabo da tayi sauri ma ta bar Masa gida sai da 5pm tayi sai gashi ya dawo gidan da fara'a Yana ta rera wakar Bob merly Yana girgiza Kansa Yana lumshe Ido har Palo.





Sharhi Dan Allah

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵






36-40







FREE PAGE










DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.









NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.


ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39







Official









By
AsmaBaffa









Page naku ne

ZAHRAH
RAMALURV
JIDDAH
ZEEY SOORAJ
HAJIYA ABOU
SERLMAH
I LOVE MY SAIF







Aamna Tana kitchen kamshi na tashi ta fito tare da furta Sannu da zuwa,Annurin fuskarsa ne ya gushe ransa ya dugunzuma ganin Bata da alamar tafiya,Tsaki Yaja yayi waje abinsa Bai dawo ba sai 9pm zazzabi ya dawo da shi gida,tana kallo a Palo taga ya shigo Yana kankame jiki Yana Rawar sanyi da sauri ya fada saman doguwar kujera ya dunkule,Aamna Tace lafiya? Harara ya watsa Mata tare da furta duk bake kika jawo ba,bakin cikinki ya zuba min zazzabi,Aamna Tace au nice? da wacece idan ba ke ba Kawai kinzo kin tare min fili da Fadin gida,ba dama na samu Freedom na Wala Ni da gida na,Dariya tayi Tace to Yi hakuri,bazan hakura ba sai kin bar gidan Nan cewar Ahmad,Ni kwata kwata ba kaunarki nakeyi ba,Sam Baki min ba tsarin zubinki gaba Daya Bai min ba,Aamna Tace duk kyan Nan nawa? Wani kyau ne Dake an fada Miki kyau nake Nema idan kyau ne naje na kalli kaina Mana har Zaki fada min kyau? Dariya ta Kama Aamna yace ke Baki da kunya ko tsagera ko fitsararriya ko? Idan ba tsaurin Ido ba ki kalle Ni kice me? Ki tafi gidanku na gaji Dake Ni,Ina Nan daram wallahi baka Isa na bar gidan Nan ba.

Bargo ta Mike taje ta kawo tare da lulluba Masa Tace ko na shigo ciki na Dan jona maka heater? Wlh idan kika shigo bargon Nan yau Allah ne yasan irin dukan tsiyar da Zan miki,Dauko min magani a dakina paracetamol da ruwa,Aamna taje ta kawo Masa ya Mike ya karba ya Sha,Tace ko a Kira Likita ya maka Allura maybe Malaria ce,Ni ba a min Allura babu Wanda zai sokar min duwawu ko Hannu,Ina ma Likitanci na karanta ko Yar Hygiene din Nan da wallahi sai na tsira ma Allura cewar Aamna ta furta tare da daukan waya ta Kira likitan da Mummy ta hada ta da shi Wanda ke duba Ahmad,Bayan sun gaisa ta fada Masa,a daren yazo ya duba Ahmad ya rubuta magunguna yace malaria ce,Bayan ya tafi Aamna ta Aiki Musa ya siyo Magungunan.

Lokacin jikinsa yayi sauki ta hado Masa cous cous da miyar kwai ta kawo ya karba yaci ba laifi ta bashi Magungunan Tace sha,yace sai ki dura min ta karfi bazan Sha ba,Aamna Tace okay sabo da ba kwayar maye bace ko? Yace ae ai Wanda baya shaye shaye ya bar Dadi ya furta da slow, Zan fadawa Mummy Allah gwara ka karba ka Sha, ki fada Mata Mana tsoro nake ji ke Baki ga ba Wanda yake fada min naji bane?na gani Dan Allah ka Sha zaka daina zazzabin,Da kyar ya karba ya Sha yace gobe bazan Sha ba,ya tashi ya koma bedroom dinsa, kwana Uku Aamna tana fama da shi da kyar ta samu ya Gama shanye maganin Kuma ya warke fes.

Siyama ce ta kwada Sallama tare da shigowa,ta Iske su Mashkoor a palon lokacin Aamna tana bedroom tana bacci,ko nemanta Bata Yi ba ta zauna wajen Jibson ta kalle su Har Ahmad Wanda ke latsa waya,Ta kalli kayan mayen tace gaskiya Kuna birge Ni wallahi,Musamman idan na kalli giyar Nan Dake cikin dundumemiyar kwalaba,Ina so inga Ana daga Dunduma a duniya,Suka kwashe Dariya banda Ahmad,Jibson yace kaji fa sabo suna Wai Dunduma,Siyama taji Dadi Tace Ni ko Mijina naga Yana daga Dunduma bazan damu ba Zan koma Taya shi Sha ne, Mashkoor yace Baki da hankali mu kanmu so muke mu daina mun kasa Amma ke kina mace kina wani Eh yane Haba Yawa kike,Siyama taji haushi a ranta ganin Bata birge su ba sai ta tashi zata haura sama wajen Aamna Ahmad ya daga Mata Uwar Tsawa yace idan Baki bar gidan Nan ba wallahi na tashi ko ya Mike a zabure Yana cewa Upstairs din na Ubanki ne? Ko da kwandalar Ubanki aka gina gidan da har Zaki kallar min sirrin Dakuna,Shegiya da kanki Kamar butar Shayi, da gudu tayi hanya ta fice.

Jin Hayaniya Aamna ta tashi ta fito itama tana murje Ido Tace lafiya naji Hayaniya?Takalminsa ya cire a zuciye ya Wulla mata yace ai duk ke kika jawo Ina Zama na lafiya Yan Iska Kun dameni a gida wallahi ranar lahira sai Allah ya Kamaki da hakki na,sai Mala'iku sun jibge ki da almudun bakin karfe,Su Mashkoor cikin kwaya Suka ce Kuma ta saman kwakwalwarki zasu dirka miki kinzo kin Sa abokinmu a bacin Rai,Dariya ma Suka Bawa Aamna Tace Dani da ku zamuga Wanda za a jibga a lahira kuci gaba da Shan kwaya ku gani,Kana jinta fa King cewar Jibson,Ku kyaleta Bata da hankali ai.

Bayan wasu kwanaki Aamna Sam zaman gidan ya ishe ta shi yasa kullum sai ta fita siyo kayan Miya ko kifi ko nama etc Dan kawai ta Dan shakata,yau ma Shiryawa tayi ta tafi kasuwa zata siyo vegetables, Duk da Haka Siyama Bata hakura ba ta dawo gidan Aamna ta Iske Aamna ta tafi kasuwa,yau ba ma Jibson,Ahmad,Mashkoorsu Uku suna gidan suna kallon ball suna shaye shayensu,su Jibson sun turnuke palon da Hayakin Shisha da Wiwi,Ahmad kuwa Giya yake Sha a kwalabar Yana dagawa,Ganin Siyama ransa ya sake baci Amma baiyi magana ba,Jibson yace mayya an dawo ne? Mashkoor Yana tangadi yace Chaiii....Wai ko harda ke aka Daura Auren ne? Ko Mata biyu aka bashi Bamu Sani ba?to wallahi mu dai Iya Aamna muka ji ance an daura Aure mu ita Muka sheda an daura da ita cewar Mashkoor,Jibson ya kalli Siyama yace ke muna wajen fa har mandiri aka kada Ana Waka Ana Ahmad Angon Aamna Gam.. Gam... sannan kizo ki Raina Mana hankali.

Siyama tayi banza da su sai ga Aamna ta dawo Siyama ta Mike Tace balarabiya kin dawo? Da murna Aamna ta wani tuno Dan guntun larabcinta Tace Marhababiki ya Siyama ta wani Rungume Siyama har da Yi mata kiss a kumatu Wai ita Balarabiya,Siyama da munafunci Tace Aina tazhab? Wai ina taje, Azhab Ilal suk cewar Aamna wai da larabci taje kasuwa Wanda da kyar suke tuna Dan abinda suka tsinta wani ma ba daidai suke fada ba,kiyi Hakuri na Dade ban San kinzo ba,Siyama Tace Ma Fi mishkla,Mashkoor yace cab da Kun taimakawa kanku Kun daina Sam Baku iya Larabcin ba,bakinku ya dafe da miyar Kuka zaku Raina mana wayo Baku Iya komai ba,Jibson ya nuna Ahmad yace da kun San irin Larabcin da King keyi ai da Sai Kun Mari kanku da kanki sabo da haushin kanku zaku ji.

Aamna Tace Kai ku kiyayeni matar oganku ce Aunty ya kamata Kuna kirana bana Wasa da ku,Dariya sukayi Suka ce Aunty Balaraba daga yau,tun daga wannan Rana kaf abokan Ahmad sai dai sucewa Aamna Aunty Balaraba ita Kuma amsawa takeyi.
Washe gari da dare Aamna ta kawowa Ahmad Abinci ganin baici komai ba tun Rana,Ashe hakan data Yi shi haushinta yaji ya tsaneta ya gaji da takura Masa da take yi Kawai ya dauki abincin ya watsa Mata a jikinta stew din Allah yasa ba zafi ta Bata Mata riga,Taji Matukar haushi har ta fusata Tace barin gidan zata Yi ,da sauri ta dakko mayafinta,Yana ganin Haka sai murna ta kamashi,Aamna sai ta ganshi har murmushi yakeyi sai ta fasa tafiyar ta dawo gabansa Tace ranka ya Dade zanje na siyo Abu a shago tayi waje,ransa yayi bakikirin sabo da bacin rai tashi yayi ya tafi wajen Me Gadi Musa,Musa Yana Zaune a Bench Yana waya da matarsa Ahmad ya zauna a Bench din.

Musa cikin wayarsa yace da matarsa na Baki Ruhina gaba Daya,da sauri Ahmad ya kalli Musa yace baka da hankali idan ka Bata Ruhinka Kai Kuma ya zaka Yi da rayuwarka kenan ka bata Ruhin ka mutu kenan? Musa ya dagawa Ahmad Hannu Wai yayi shuru yaci gaba da cewa Ni gaba Daya na Baki duniyar Nan gaba daya ma Uwar gida na,Baki Ahmad ya bude da bala'i irin na Yan kwaya yace Kai...wai...to nufinka idan ka Bata Duniya mu da sauran mutane da muke ciki mu tafi Ina a Ina zamu zauna?ko sama ta Daya zamu koma,Musa ya kashe wayar yace a'a ikon Allah Oga Ni Matukar zata ji Dadi ku tafi sama ta goma Mana,Ahmad yace Kai Musa wallahi Indai zaka ci gaba da wannan furucin na soyayya wani ka Bata Duniya wallahi sai na koreka a aiki,akan me Dan wulakanci Muna zaman mu lafiya cikin duniya kace wani kayiwa wata banzar matarka kyautar ta,Baki Musa ya Bude sai Kuma ya tuna Ogan nasa Dan giya ne kwakwalwarsa da motsi Kuma Bai taba soyayya ba shi yasa.

Musa yayi Dariya yace Allah huci zuciyarka Oga ai duk kalaman soyayya ne ai duk abin karya ce,Kenan duk karya kake mata? Ahmad ya tambaya Musa yace ai Dan aji Dadi ne,yace kenan soyayyar da ake fada duk karya ce? Musa yace duk ita ake zugawa juna,Nima fa Oga cewa tayi ta bani zuciyarta,Baki Ahmad ya bude yace to yau duk sai kunci ubanku wallahi maza tashi ka dakko Cooler dole ta Ciro zuciyarta ta baka ka saka a Cooler,Musa Dariya ta Gama Kama shi,Yace zaka Yi Dariya da kyau yau sai naga ta inda zaka Ciro Ruhinka Dan Ubanka,Kai ba mala'ikan daukan Rai ba komai ba kace wani ka Bata ranka Dan Ubanka gashi kana motsi kana numfashi yau sai ka Bata ka mutu yanzun Nan,Musa ya sake kecewa da dariya shi Ahmad Bai San soyayya ba,yace tsuguna yau sai ka kinkimi duniya a kanka Baki Daya ka Kai mata har kauyenku sannan bayan ka Kai Mata mu Kuma kazo kasan inda zaka Kai mu,Musa yace kayi Hakuri Oga na fasa Bata wallahi bazan Bata ba na Kuma fasa karbar zuciyar Tata,Ahmad yace Yan iskan banza da ka Bata mu gani mana,Kun zauna Kuna biyewa Mata ya Mike ya fice daga gidan.

Aamna zaune take suna waya da Mummy,Mummy Tace Aamna me kike so a duniya ki fada min ko mene Zan Baki,Aamna Tace Mummy da gaske ko mene?Mummy Tace kwarai ai tunda kika iya jure Zama da Dana Ahmad a wannan halin ba abinda bazan Miki ba,Aamna Tace dama Ni burina idan na samu kudi naje Hotel na kama daki nayi kwana Uku Ina Shan ac,azo a gyara min room nayi order abinci naci nayi bacci,sannan Buri na na biyu idan samu kudi nayi wanka da ruwa Eva ko Swan,sannan naci abinci na wanke Hannu na da ruwan Roba,Dariya Mummy tayi Tace Anya kuwa Aamna kin Kai 25yrs ko kema kin fara Shan kwayar ne?Dariya Aamna tayi Tace Allah Mummy,to shike Nan ba yanzu ba ki Bari sai Nan gaba cewar Mummy sannan ta kashe wayar.

Da dare Ahmad zaune yake a bedroom dinsa Yana Danna System Aamna ta shiga dauke da tiren Abinci ta Ajiye Masa,Tsaki Yaja da masifa yace ce Miki akayi yunwa nake ji? Bazan ci ba ki dauke abinki tun kafin nayi fatali da shi,Wayarsa ce ta shiga Kara yaja tsaki sannan ya dauka yaga Humaira ce kanwarsa dagawa yayi,yace sis ya akayi ne Mene ne Zaki dameni? Yaya dama gobe zanzo na kawo maka Ziyara,Fuska ya Bata yace ke karki zo min Ni Kun dameni kije gidan Saddeeq Mana sai Dole waje na Zaki zo wannan Candy da kika Yi ai ta zame min masifa tunda damuna zakiyi Dan Allah ki fadawa Daddy ya saka ki a University da wuri Haba,Dariya Humaira tayi ta Shiga rokonsa Dan Allah Yaya so nake fa nazo na ganka please.....Shuru yayi mata,Tace Yaya Dan Allah zanzo kaji....ke mayya karki lashe ni ki tsotse min bargo yau she Zaki zo? Kwana biyu ko Uku Kuma Zaki Yi,Tace to Gobe Yaya da wuri zan bi flight sai kazo ka daukeni a Airport,Alright sai kinzo murna Humaira ke Yi harda godiya,Aamna tana jinsu ta dauke Abincin tayi gaba,me Gadi ta kaiwa gaba Daya.

Washe gari 2pm Humaira ta sauka,Aamna gani tayi ya Sha wanka cikin kananan Kaya wasu masu kyau ya fito ya hau wani machine dinsa Irin na Yan achaba Quilin ya tafi Airport,Humaira ta ganshi a machine ita Bata taba Hawa machine ba,ta Rungume shi tana murna ya janye jikinsa Yana dariya yace sis bana son wannan haukan kin girma ku Yan Lagos Baku da tarbiyya,Dariya tayi Tace Kai Yaya Kai fa yanzu muharramina nane fa,ku dai Kawai Kun dauki aladun turawa ya furta tare da rike Mata Hannu yace Oya hau mu tafi,ta kalli machine Tace Yaya kasan fa ban Iya hawa machine ba Kuma ai ya kamata ka aro mota ko ta abokai ce ka dauke Ni,Wanda Basu da motar kuma fa gasu Nan Ni ban Iya aro ba idan Zaki hau ki hau ko wallahi na tafi na barki iskancin banza Kawai ya fara bala'i,Humaira tayi Dariya Tace Kai Yaya ta ja kitson calabarsa tace da a Kano ne da tuni Yan Hisba sun Kamaka,Yace su ma Wanda suka Raina suke wa.

Daukanta yayi tare da daura ta a saman machine din,Jakarta Kuma ya daura a gabansa ya figi machine Kamar zai tashi sama Haka yake fyalla uban gudu da Humaira tana ta dariya ita Dariya yake Bata.
Aamna tana cin abinci a Dining suka shugo,Humaira ta taho da gudu zata tafi wajen Aamna Tace laaa Auntynmu...Auntynmu...da sauri Ahmad ya cafke ta yace ke wace Auntynki? Baza kije wajenta ba wajena kika zo ko wajenta? Humaira tayi Shuru yace muje sama,Murmushi Aamna tayi tace Barka da zuwa kanwata,Humaira ta dago Mata Hannu zanzo mu gaisa Aunty.....fisgar Hannunta Ahmad yayi Suka tafi sama Yana Hararar Aamna,Aamna Dariya tayi Kawai duk tayi laushi ta nutsu sabo da Duniya garata takeyi.

Hana Humaira Fitowa yayi sai da ya tabbatar ta shiga wanka sannan ya fita ya Mata take Away na abinci Wai baza taci na Aamna ba,Yana dawowa ya Iske Aamna da Humaira suna ta Hira suna dariya,Muzurai ya fara Yi ya karaso tare da fisgo hannun Humaira yace wa yace ki kula min kanwata ko kanwarki ce? Aamna tayi Masa shuru kawai, a palon Suka zauna Humaira gudun masifarsa yasa taci abincin nasa ta koshi,Humaira Tace Yaya yanzu a machine kake yawo?gaskiya Daddy Bai kyauta ba,Ke share wannan zancen Ni nafi Jin dadin ma machine Dina,Aamna ya kalla yace Baban wasu kuwa ko Tyre Bai da ita bare mota,Aamna Dariya Kawai tayi,Humaira tana ta Mata magana da Ido,itama Aamna tana maida Mata da Hannu da ido,Ahmad idonsu Kawai yake gani Yana motsi, tashi yayi Kawai ya fice abinsa,Nan Humaira Suka zauna da Aamna suna ta Hira abinsu.

Tunda Humaira tazo Aamna ta samu kawa har fita kasuwa sukeyi da yawo Ahmad ya kyalesu harkarsa yake yi,Haka shima Humaira ta takura Masa Wai sai ya kaita yawo a Machine,da ya fita da ita yawo yau suna ta zagawa duk Wanda ya kalli Humaira sai yayi Masa bala'i.
Wani guy ya ga Humaira kyakyawa ta birgeshi suna tsaye da Ahmad a jikin machine Yana ce Mata Sis na fada Miki kina saka Nikaf tunda ku Kuna kula da Addini Kawai ku rungumi Islama hannu biyu kina saka Hijab da Nikaf kin fa girma tam,I'm warning you Sis,Humaira tana ta dariya shima ya kalleta ya dinga dariya a jere a jere irin ta Yan Kwaya ba kakkautawa,Humaira Tace Yaya kaima kana ganin kyanka Mata sai kallonka sukeyi,Ke dalla rabu da su sun kalle Ni a banza ai duk wacce ta Soni to Allah ya jarabce ta sabo da ban Dace da a so ni ba sis,Humaira taji tausayinsa kwalla ta cika Mata Ido Tace Yaya Wai waye ya koya maka shaye shaye ne Wai? Handkerchief din Dake hannunsa ya zabga Mata a Fuska yace muje gida Yana Juyawa yaga saurayin Nan ya kafe Humaira da kallo,a fusace ya nufi wajen saurayin yace zaka lalata min kanwa Dan uwarka me kake kallonta kana ayyanawa a ranka? Kana Nan kana ta kallonta kana ayyana wani Abu ko ya Kai Hannu
Showing 33001 words to 36000 words out of 142807 words