uban rawa,tace Baby ka gama Iyawa ka huta....Ahmad yace ai na kware My world,tace basira ne da Kai.....a ransa Yana ta dariya,kukan dadin ma ta rasa wanne zata yi lokacin Daya fara Mata Wasa da Yatsansa a down......tayi wani shidewa tare da furta na samu Kalar da nake so.....ganin ta birkice yasan ba matsala,cikin rada yace My world na yi? Yesss....yess....ta Furta cikin Kalar muryar da yake mugun so idan tayi magana,Kuma sai ta Gama kaiwa karshe take yin irinta,sabo da haka a nutse yake Manta Uwa dinsa,tana Jin dadi kuwa,shi Kuwa yanzu ya karbe aikin zubar da surutun kalamansa barkatai.
Sun Dan dade kafin Suka samu gamsuwa kusan a tare.

Sai da suka gama nutsuwa Aamna sai murmushi takeyi ita kadai ta manta ma King Yana kallonta tana ta murna ita kadai tana Jin wani nishadi tana tuna abinda sukayi yanzu dama su dawwama a Haka,Ahmad shima bangarensa haka ji yake kamar ya hadiye Aamna,dariyar ta mene My World? Kunya tasa ta dukunkune a cikin blanket tana Dariya,yace na Iya ko.....Yana kokarin janye blanket din tana dunkulewa tare da dukunkunewa a ciki,Haka su Aamna Suka kasance suna darje Amarci har na kwana Uku.

lokacin Kuma Brown yaje wurin Humaira wacce suke tare da Mummy a gidan Amma sun Sha soyayyarsu, Mummy tace Brown ya Kai Humaira wurin Aamna zata Mata yini kafin jibi su tafi Lagos,a ranar Kuma Tawaga ya dakko Yar China taci gayu cikin sabon lace dinta Daya dinka Mata wani Brown and sea blue tayi kyau Riga da skert,takalminta me Dan tudu da mayafinta da jaka gaba Daya Brown Yar China tasan darajar wanka,a motar da Daddy ya Siya musu tasa baka ya zaba a ita ya dauki Yar China,gidansu da Suka tare Wanda yake a matsayin na Ahmad a da shi ya fara kaita ta gaisar da Mamasa da Yan Uwa,Dama komai tsakaninsa da abokansa ya bawa Yar China labari,Haka Nafeesat da Sameera duk sun San komai Suma irin alakarsu da abokai,Yar China anga gida me kyau tace Daddy ya kyauta Allah saka Masa da Alkhairi gashi gidan surukaina me kyau na masu kudi,da yanzu sai dai a kaini dan kangon gida,Dariya Tawaga yayi duk da Iyalle tayiwa Yar China magana akan ta nutsu Kar tayi hauka a gidan surukai amma Yar China Bata iya Shuru,har ciki Suka shiga tana so tayi kalle kalle a gidan sabo da ya hadu amma sai danne sabo da Iyalle ta tsawatar,da Sallama Suka Shiga,ai gaba daya taga Yan gida suna ta Fitowa da murna Yara suna ihu da tsalle ana Oyoyo Yaya Ana makalkale Tawaga,Yar China tana kallon ikon Allah,Hafsat Budurwar Bash wacce taci gayu cikin Arabian gown tazo ta tarbi Yar China tana murna sai kallon Yar China akeyi tayi Kama da Yan China sai dai ta fisu Hanci ita,Hafsat tace Yaya ka iya zabe kyakyawa fara,Yar China tace na gode ai haka ake ta cewa yayi dace naji dadina,Dariya Suka dinga Yi Yar China tana yabon kanta,Hafsat tace Kuma kinyi Kama da Yan China wlh,Yar China tace na fisu Hanci Kuma lips Dina da bakina ba irin nasu bane nifa cutata akayi da Yan Korea nayi Kama sunfi kyau Amma sabo da hassada ake cewa da Ni Yar China,Hafsa tace gaskiya kinfisu,ai Suma akwai masu kyau,ae ai irin masu kyan nayi cewar Yar China,Yaran kaf Suka dinga zuwa suna gaisar da Yar China tana amsawa,wani yaro Bai wuce 3yrs ba ya nacewa Yar China sai da ta gaji ta dauke shi tare da dora shi a cinyarta tana cewa to taho Sarkin nacin tsiya,Tawaga Ummansa ya Kira tazo Suka gaisa ta yaba da Yar China Bata da duhun Kai ga hira,Tawaga yace Hafsat shirya muje gidan Ahmad ku gaisar da matarsa,tana murna tace to.

Tare da Yar China da Hafsat ya tafi da su,Bash suna waya da Tawaga yaji ance da Hafsat budurwarsa za a tafi ai sai shima ya tafi gidan Aamna,can ya Iske Humaira da Brown Palo,Yar China tun a mota take cewa Nima a layin zamu zauna ko? Idan munje kusa da gidan Nawa ka nuna min na fara ganinsa,Tawaga yace to,sai da taga an shigo unguwa ta kirki Yar China Tace kar dai ka fada min cewar Nan ne Unguwar da Za'a kawo Ni,Hafsat Dariya take Kamar cikin zai ciwo,Tawaga yace Nan ne Mana,Yar China tace na haye,Ni Kam na gama hayewa na baya sai labari,Hafsat tace nima Nan za'a kawo ni abokaine Bash abokinsa,Yar China ta juyo baya tana kallon Hafsat tace ban mu tafa,Suka tafa Tace ba dai wannan Dan santalin ba? Hafsat tace ae da sauri,me Suma fa tafi ta Tawagana tsayi,Hafsat tace shi fa,Hafsat Tace Dan Allah ya kika ganshi? Yar China tace fessss,to shine cewar Hafsat,Yar China tace mun Zama kawaye daga yau,ga gidana ga naki,Idan Muka haifi yara idan zanje Unguwa sai na turo su gidanki,kema Haka ko? Hafsat tace sosai ma,Tawaga ne yace gaskiya kun dameni Kuma,Shuru Suka yi har ya Shiga Estate din ya nuna musu ko Ina,Yar China tace an kure karyar kudi a Nan,ayi ta Neman kudi ba a samu ashe kudi Yana Nan, to a Nan duk tsiyar kudi an gama kure shi.
Yar China harda saita sabuwar Wayarta tana ta daukan Hoto Wai zata nunawa Iyalle.

Tunda Suka nufi part din Ahmad Suka lalace a kallo,Yar China tace ba sai an fada ba Nan na babban kwaron ne,Hafsat tace ai na masu abin ne,suna Shiga Ciki sukayi Sallama aka amsa Aamna tana zaune tare da Ahmad,Humaira da Brown ga Bash a gefe Daya, Hafsat ce ta radawa Yar China karki nuna bamu waye ba muyi yanga Kar aga Muna kalle kalle kamar Yan Kauye Yar China suna tsakiyar palon amma ita ba sirri da karfi yanda kowa zaiji tace ban gane Kar ace daga Kauye muke ba? Ni wallahi bazan wahalar da kaina ba kallo na zanyi Kawai sai a hanani Allah ya min Ido ace bazan gode Masa ba ta wajen kalle kalle ba,ka gani Yaya zata hanani kallo Wai bazan kalli gidan Nan ba Yar China ta Furta da shagwaba,Tawaga yace wane mutum ai bata Isa ba matar babban Yaya guda yi kallon ki kinji,Ahmad dukkansu kallo Suka tsaya yi suna dariya Yar China ba sirri ta tonawa Hafsat asiri,a fili Ahmad yace tsigarallahu kenan Tawaga za a Sha fama,Yar China ce ta karewa palon kallo sai lokacin ta kula da mutane a ciki Tace salamuaikum bayin Allah ,Aamna ta Aamsa suna dariya,Lokacin Yar China ta kalle su ta juya ta Kalli Tawaga tace Yaya Tawaga ai Nasara Ne tsoronsu nake ji,Turawa ne,Tawaga yace baki ji suna hausa ba hausawa ne, Yar China tace turawa sai kwai dan Allah ku yo min kwai ko guda goma ne na kaiwa Iyalleta gobe ta soya Mana muyi breakfast me Dadi,Ahmad duk danne Dariyarsa sai da ya dara.

Humaira tace Ni Kam nayi kawa sa'ata,Yar China tace kaji Yarinyar Nan jibeki fa Nawa kike zakice wani shekarunmu Daya kalle ki fa ni da na Gama Zana waec Zaki ce Ni sa'ari ce,Aamna Suka dinga dariya Wai tayi Candy ita Humaira da take University ma,Brown ne yace Yaya Tawaga ku zauna,Dariya Suka saki Wai Yaya Tawaga.
Yar China tace to ku duk abokan Yaya ne bazan durkusa na gaisar daku ba wlh nasan Kun girmeni kuyi Hakuri Ina yininku ta Furta tare da Zama a saman kujera,Suka amsa Kuwa da fara'a,Ahmad tsokanarta yayi yace matar mu.

Yar China tace ba ruwana ban ce Ina sonka ba Kai dai da Allah ya maka kyau kaje da abinka Ni sai Aliyu Tawaga,Aamna tace Yar China kike ce mun balarabiya haskenki fa yafi nawa,yar China tace Alhmdllh saura kadan ai a Haifo Ni a zabiya Allah ya tsallakar dani, ku tace ku kunna Mana kallo mana,Ahmad ya kunna kuwa ya kamo India Yar China tace Kaini tashar hausa zalla inda aka san darajata da kimata kasar da Tawaga na yake Amma ka daukeni ka kaini India Ni ba Gunkiya nake bauta ba Sannan ba saniya ba, Ahmad da Tawaga ne suka Mike zasu fita,aka bar Humaira da Brown suna Hira harda komawa Daya palon,Bash da Hafsat aka barsu a Nan palon,Aamna ta ja Yar China wani bedroom.

Shigarsu ke da wuya sai Daddy da Mummy sukayi Sallama,sai Kuma ga su Ahmad suna dawo Duk Suka hadu a palo,Jibson ya shigo tare da Mashkoor,Aamna tana Fitowa ita da Yar China sai ga wani Mutum baki siririn gaske sanye cikin suit bakake ya shigo da Sallama,Daddy yace kowa ya nutsu ya zauna,kowa ya zauna sai ga Baba da Mama sun shigo,Baba Yana shigowa ya rafka Salati da karfi tare da furta Rahilu Menk???????Allahu Akbar,Rahilu Kaine ka dada bushewa ka tsotse haka? Rahilu haka ka dawo Kamar Dan gudun Hijira,Rahilu kalli wandonka yanda ya maka yawa,Wannan Hannu naka Rahilu Kamar Sanda,Mama tace wuya sai kace na zalbe,Aamna Karki ga Baku Yi Kama ba shine mahaifinki maza ebo Masa abinci ya ci da Alama yunwa ta gama dashi a Sudan,ku bashi yaci ya koshi,yanzu dama zaman da kakeyi a can ba Dadi kake ji ba? Nayi zaton ma kudi kayi ka watsar da yarka ashe wahala kake Sha Baba ne yake ta magana,Aamna ta kalli Wanda akace Babanta wani mugun bushashe.

Yar China bata San Kan zancen ba tace amma wannan daga Tanzania yazo ko? Baba yace Allah Miki Albarka yar nan kema Kya fada ko Kenya ko Tanzania ko Kuma Senegal,to a Haka Wai Balarabe ne larabci yake yi,Yar China kirji ta dafe tare da toshe kunnuwanta tana cewa bazan ji ba...bazan ji larabcinsa ba,ta bawa mutane Dariya amma akayi Shuru,Baban Aamna Yana Jin hausa Amma ba sosai ba kadan kadan, Yaji abinda suke cewa Dariya shima Yar China ta bashi ya murmusa,Wai baza taji larabcinsa ba.








Masu Sharhi Ina godiya,duk inda yayi ma mutum Dadi ya fada haka ake so




AsmaBaffa
10/26/21, 2:20 PM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵







NA KUDI NE







DUNIYATA AAMNA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.










101-105










Official









By
AsmaBaffa






Page naki ne

AUTA











Ahmad yana kusa da Aamnansa a zaune tare da rike hannunta,kasa kasa yace a Gaida Abbu mana My World ba'a Fushi da iyaye,Kallon Ahmad tayi idonta taf da Hawaye Kai ya girgiza mata Kar tayi kuka ya rada Mata a ajiye min kukan Nan sai anzo manta uwa,Murmushi tayi ba shiri,Ahmad ne ya juya harshe ya shiga suburbuda larabci Wanda ba kowa yasan yana ji ba,Baban Aamna yayiwa tare da Daddy dinsa Yana ,Abbun Aamna shima Yana yarensa cikin kwarewa,Baba yace shu'umi Rahilu akwai murya dama Indai kaji murya me dadi idan ka duba yawanci mummuna,Yar China tace kaji Larabawa Amma Banda Abbun Aamna bazan yarda Balarabe bane daga Tanzania yazo,Abbu ne ya kalli Aamna cikin Muryarsa wacce Bata fita sosai ya Furta Aamna ki yafe min,bani da bakin magana kawai ki yafe min,Yo a yafe maka ba'a San tsiyar daka shuka ba ka gudu,ko Kuwa can mun San me kakeyi? Cewar Baba.

Abbu ya kalli Baba yace Ni ban San dalilin da yasa na gudu na bar Aamna da Sumayya matata ba bani da dalili ban San me yazo kaina ba, ko me yasa hakan ta faru? Baba farat Daya yace Dan Iska ne Kawai Kai shine dalilin da yasa ka gudu algungumi Kai kamar na kwarangwal zaka ce baka San dalili ba sabo da Iskanci ya maka yawa,ai shi yasa aka ce a guji bawa bako 'ya aure,yanzu matanka Nawa da Yara? Baba ne yayi tambayar, Rahil yace Sanda na auri Sumayya matana uku itace ta hudun,bayan na samu labarin ta rasu Allah ya hadani da wata Yar libiya na aura,Baba yace Rahilu kaji tsoron Allah Wato Ashe ma munafuki kana Jin ta mutu ka Kara aure wato ka cike gurbi kenan zaka ce Allah ya hada ka da wata kaje dai ka kakai kanka Wai Kai wayo ko Dan muce kaddara ce to anki wayon,mu ka barmu a Nan kana can Kuna dancewa da Amaryarka,Dariya Baba ya bawa kowa Wai dancewa,Daddy yaji Dadi da Baba yake cin uban Rahil, Baba yace itama wacce ta aureka a Haka tayi asara mene abin so a jikinka Rahilu,Kuma har daga kasar libiya kaje ka auro ta karya kakeyi Yar wanke wanke da shara ce baza ta wuce Yar Niger ce taje Sudan aikatau ba ta rufe ka Tace Yar Libiya ce ita.

Inama tana Nan wajen na kure Yar banza yanzu nace idan ta Isa ta bani dutse dan Libiya na jefa a randar Aishatu maganin ciwon ciki,aka sheke da dariya,Baba shi baya Dariya da gaske yakeyin fadansa,Sannan yace to da ka Gama dancewar da matan naka Yara nawa Suka Tara maka? Rahil ya daga Kai Yana tunanowo,Cab Baba ya Furta suna da yawa kenan ya kasa irgasu,Rahil yace na Uwar gida Guda tara,ta biyu bakwai,Baba yace na hada Sha shida cif, Rahil yaci gaba ta uku Kuma guda shida,ta hudu Aamna kenan,sai wacce na aura bayan Sumayya ta rasu yanzu tana da uku,na hada talatin cif cewar wace Kuma me ciki yanzu take Shirin juyewa? Baba ya tambaya,Rahil yace Amarya ce,Dole wando yayi maka yawa Rahilu Nan gaba ma Sai dai idan ka koma saka jallabiya zalla Amma Riga da wando Ina tabbatar maka ka kusa rasa size din da zai maka dai dai,gashi turawa basa tazuge irin namu bare ka zamge kugunka.

Rahil ne yayiwa Daddy magana da larabci Wai ya gaji da masifar Baba zai yi tafiyarsa inda ya fito,Daddy ya tabbatar Rahil bashi da Imani yanzu wato Dole ma aka Masa yazo,Haushi yasa Daddy da hausa ya fadawa su Baba me yace ,Baba yace au haka kace ma? Yar China ce tace dan Allah Baba ku bashi abincin yaci ni Allah tausayinsa nake ji,Aamna ce tayi magana Tace na yafe maka koma mene kaje Kawai tunda dama Dole aka maka,kallon Aamna Rahil yayi rin mamanta sak,murmushi yayi tare da Furta na gode yarinya ta,Mama Tace rufe Mana baki wani yarka me ka kawo Mata tsaraba tun daga Sudan ko Dan lallensu baka kawo Mata ba domin ta dinga yiwa mijinta kwalliya ko Yar muhallabiya babu gata can tana tashi a can a banza,Baba yace sai ka dakko wani bushashen jikinka ka taho zikau zikau,Kiran Sallah aka kwala na Magrib,Daddy yace muje ayi Sallah mu dawo a karasa abinda ya kawo mu,Alwala sukayi gaba Daya su mazan suka fita masallaci Matan kuma Suka Yi a gida.

A hanyar dawowarsu Baba ya kalli Rahil Dariya taso kwace Masa yanda ya ganshi Yana tafiya kamar Yana tausayin kasa,Baba yace Rahilu kayi tafiyarka sosai kasa fa ba kyaleka zata Yi ba Matukar ka mutu aka binne ka matsar Nan sai ka shata,Sai kallon Rahil yakeyi Dariya tana kamashi,Baba yace Rahilu da gani kana ji a jikinka,a cikin yaranka ka kawo min da daya na rike maka shi,Rahil yace to Zan baka wallah,Baba ya sheke da dariya tare da dafa kafadar Abbu yace Rahilu anji wuya Dan gandal uba to bazan rike ba tunda baka da mutunci kai ai wallahi sai dai wuya ta kashe ka Ni Nace ka auri matan kana can kana Dancewa da su kana danno Yara duniya sannan kace na rike maka,Aamna ma da muka rike Allah ya karba,Daddy yace ai bazan Bari ma ka karbi wani Dansa ba wa yace ya tara Yaran,shi ga ayu to Kai ka jawa kanka,Baba ya sake dafa kafadun Rahil yace kayi Hakuri Rahilu Ina ci maka Fuska Kaine ka jawo.

Kafin su koma gida su Aamna sun shirya kayan ciye ciye a palon sai abinda ka zaba,abincin Suka zagaye Yar China Tace Ni Zan yi Serving kowa,haka kowa ta zuba Masa abinda yake son ci,Baba yace Ni bazan zaba ba komai Ina ci a zuba min komai zanci akwai waje me fili a cikina,Yar China tace ashe Muna iri daya da Kai Baba,kema haka kike? Baba ya tambaya tace ae komai Zan cinye,kin birgeni cewar Baba,Yar China tana zuwa kan Rahil ta cika Masa plate kamar zai zubo abincin har wani tsiri yake Yi a plate tace ci ka koshi Abbu in Allah ya yarda kafin ka koma Sudan gidan jiya ka danyi bulbul,idan ka koma sai kowa yace America kaje,mu Nan ba yunwa akwai abinci Kuma Abbu ba ruwanka da Yaranka bare su cinye maka rabonka,Baba yayi Dariya Yar China da tsiya take yace da zai yarda yayi wata Guda a Nan Ina tabbatar muku kafin ya koma can sai ya saka Leda a kafarsa kafin ya cire wandonsa sabo da kiba,Rahil ya kalli abincin da aka zuba Masa yace bazan iya cinye wannan ba ai ko quarter bazan ci ba,Ni ba Jaki bane ya sa spoon ya Dan kwashi ganyayyakin Vegetables yana ci sai fruits.

Baba ya kalle shi yace Rahilu wa zaka ji kunya a nan kaci abinka karka zo kana dana sani,Wai mu zaka kife ai da ganinka an San baka Jin dadin rayuwa,Wai Kai nufinka Balarabe ne? Rahil yace sosai ma,Kana cutar kanka Kuwa mu idan sama da kasa zata hade baza mu yarda ba,asalinka Dan Kenya ne,Rahil ya Bata Rai har da buga plate da cokali cikin hausarsa wacce bata fita dai dai yace Allah kiyaye Ni...Ni... hadani da Kenya... baka ganewa Sudan can... ni Sudan Yana daga Hannu sama.

Baba Yana cin nama Yana dariyar gwarancin Rahil,Rahil harda cewa Dan an rike Masa yarinya za a dameshi,shi idan hakane a bashi yarsa ya tafi da ita,Baki su Baba suka bude yace gata Nan dauke ta ku tafi idan ka isa,a ka'ida ma Rahil Kara ya kamata mu kaika kotu Amma Muka Yi maka alfarma,Rahil ya Bata rai,Baba jinjina Kai yayi yace wannan da a Isra'ila yake harbe mu zaiyi,Yar China ce tace Kuma jirgi ya hau yazo Nan?
Showing 99001 words to 102000 words out of 142807 words