ga Kamalu kin ci Masa mutunci ya gudu shima,Jollof din shinkafata wacce ta rigada tayi sanyi ta bushe ita Aamna ke ci su Mama suna ta mata fada har ta Gama,ta cire kayan jikinta gaba Daya ta wanke tare da shanya su a daren,Wanka tayi da ruwan zafi tare da Shirin bacci ta kwanta ta bar Zuhra tana chatting da masoyinta .

Dalleliyar mota ce ta gaske wacce a kalla ta miliyoyi ce,ta danno cikin wani katafaren gida na Gagara,Gida ne Wanda ya amsa sunansa,Babu abinda babu a ciki,motoci ne zasu Kai takwas a gidan Wanda suka gaji da haduwa ga tsada,farare Guda hudu a jere bangare daban Haka ga wasu kaloli daban,Machine ne Guda Uku kala daban daban masu tsada harda Keke na masu kudi su biyu,Gidan Ya gaji da tsaruwa ga flowers ko ina,idan ka Shiga gidan baza ka so Fitowa ba,Kalar gate din ma na daban ne,ba ko Ina ake ganin Irinsa ba a kasar Haka furniture sai dai ko gidajen Gomnoni, Wani Matashi ne ya Bude motar baka Daya shigo da ita,Fitowa yayi da kyar Wow wani Fari ne tas kamar Balarabe har wani ja yake kamar ka taba shi jini ya fito,dogo ne Amma ba can ba,gashi shi ba Mai kiba ba baza ace Kuma siriri ba,Fuskarsa me dauke da hancinsa zarkadede ba irin me tsayi da yawa ba,Sumar Kansa baka wuluk dauke da wani mayen Aski irin na Yan duniya,an kwashe gefe da gefe an yanki wani waje siriri an Kona shi tare da maida shi Fari tas,Sajensa me kyau luf luf me dauke da Dan gemunsa cas,idanunsa Dara Dara farare tas suna wani lumshewa,kowa ya kalli wannan matashi yasan ya Gama gajiya da haduwa,Naira da Hutu sun zauna a jikinsa,Jikinsa na maza Wanda suka amsa sunansu maza,sanye yake cikin wani Crazy Jean me tsada gaba Daya wandon a farfashe yake ruwan toka,da wata T-shirt me Rabinta Fari Rabi Kuma Blue,Takalminsa da agogonsa masu tsada,Yatsansa sanye da zoben Azurfa,da kyar yake takawa ga takama ga aji Amma Kuma Yana tangadi da Alama yayi shaye shaye ya gaji,Yana dafa bango Yana tangadi AHMAD kenan a Haka har ya Isa katafaren palonsa tare da fadawa saman kujera ko Takalminsa Bai cire ba ya kwanta Haka Yana sambatun maye shi kadai har bacci ya kwashe shi.

Tunda ya fara bacci gab da Magriba Bai tashi ba sai da gari ya waye sannan Rana da hasken gari yasa ya Bude lumsassun idanuwansa a hankali,Kara ya saki kadan Jin jikinsa a gajiye,da kyar ya iya tashi a hankali ya haura samansa Direct toilet ya shige ya Dade Yana wanka dake akwai tsafta,Bayan ya fito daure da Towel jikin mudubinsa ya nufa turaruka ne da mayuka na maza masu tsadar gaske,Lotion me kamshi ya shafa tare da fesa Body Spray a jikinsa sannan ya dakko sabuwar jallabiya me tsadar gaske fara sal Amma ta Dan tsangale Masa baya sa wacce zata Kai Masa har kafa sabo da Damunsa takeyi,Turaruka ya fesa sannan ya dauki wayarsa me tsada Yana latsawa,a hankali cikin tafiyarsa ta Isa da takama ya sakko kasa ya Bude kofa ya fito sanye da wani flat shoe fari sal shima Yana tafiya a hankali ya bi ta wani corido gaskiya gidan Nan ya Gama haduwa tiles din kasan gidan na tsakar gida fari da Baki ne ko Ina sheki yake Yi da walwali,Me Gadinsa ya hango Yana karasa gyara gidan Yana kida da bakinsa Yana rawa Yana aikinsa,Ya Dade a tsaye Yana kallonsa,Abin Dariya ya bashi mutum shi kadai Yana kida Yana Waka Kuma Yana rawa duk shi Daya, murmushi ya saki kadan tare da girgiza Kansa ya juya ya koma inda ya fito.

Har yayi nisa sai ya dawo ya Kira me Gadi Musa,da sauri Musa ya dago yace Oga tare da takowa da gudu yazo gabansa yace Ina Peter banga ya gyara ciki ba Sannan ba Abinci,Oga ai Peter ya tafi kasuwa yace abincinka Yana kitchen yace sauri yake yi,Ni gaskiya Oga Ina tunanin yafi a dakko mace yar Aiki wacce zata na maka girki da gyara maka ciki tunda Ni Ina kula da Campun,Ogan yace ba Campun ake cewa ba Musa Compound,Kuma Ni bana bukatar mace yar aiki,Ni bana son mace ta rabe ni,duk abinda zai sa na hadu da mace bana kauna,Musa ya zaro Ido yace Oga Mata sune Jin dadin duniya duk wata nutsuwa da Namiji zai samu tana jikin mace,Baki Ogan ya tabe yace Allah ko? A wajen wawaye ba,gwara naci abincin Gardi akan naci na mace,Karka sake furta kalmar Nan mace a gaba na,idan ba Haka ba Kora ce tukucinka,Musa yace an Gama,Kayi Hakuri Ranka ya Dade Namiji gwara nace Namiji,macen banza Banda Mum dinka Oga,Baki ya tabe ya juya da Gadara ya wuce,Abincin Peter ya Bude yaga Bai Masa ba,da Kansa ya shirya Girkinsa da lafiyayyen tea dinsa ya karya sannan ya dauki key din mota yayi waje,Yau da wata mota Ruwan toka ya fita kirar Benz.

Washe gari Aamna wanka tayi tare da Shiryawa tsaf cikin kayanta Riga da wando sunsha wanki da guga,After Dress ta Dora a Kai tare da yafa Mayafi,ba Wanda ya kalle ta a cikin Iyayenta Balle Tace Za'a Bata wani abinci dama yanzu basa kulata,ko ta gaishe su basa amsawa,Sallama ta musu ta tafi,Mama Tace yarinyar banza ace tasan Burin mu Bai wuce mu Aurar da su ba Amma Taki fitar da Miji abin kunya kanwa zata Riga Yaya aure duk ta tsufa a gida Allah wadaran Dan Riko,shekara ashirin da Hudu ai ba Wasa bane,mu duk da a cikin birni muke muna Nan da akidar mu ta Iyaye da kakanni na auren wuri Amma kash Yaran namu musamman Aamna ta Gama watsa Mana kasa a Ido,marikinta Bai da Buri sai na Aurar da su,ai mutuncin ya mace gidan Miji Amma ba komai Aamna wahala da azaba ma Sai ta sa kin fito Mana da Miji,kin daina Jin dadin gidan Nan kwata kwata,yanzu Zan canja Taku wajen gana Miki azaba duk da Kamar mahaifiyarki ce Ni dole wahala tasa ki fitar da Miji,Zuhra kuwa Shiryawa tayi tuni tayi Kari me kyau Ana ta nuna Mata gata da kauna ta tafi makarantar Boko Wato Secondary school sabo da sun kusa yin candy.

Ahmad Bai tsaya ko Ina ba sai gidan Mashkoor inda Suka Fi Zama suna shaye shaye a gidan,can ya Iske abokansu su Biyar Mashkoor, Abdul Tawaga,Jibril Jibson,Bashir Bash, Mubarak Brown sai shi Oga Mai gayya me Aiki Ahmad King,Yana zuwa ya Iske su a zaune a Garden suna zaune a kujeru ga karamin Table an zube kayan maye na shaye shaye kwayoyi da giya iri iri ga Sigari taba da Wiwi,Kirari suke Masa Suna The King...Our King,shi Kuma Yana uban Gadara Abdul Tawaga ya Daga Masa kujerarsa ta tsakiya Kuma kujerarsa ta mulki ya zauna tare da Balle kwalabar Giya ya Shiga tiltila Kamar ya samu ruwa,Bash ya kunna Wiwi Yana zuka ga wasu kwayoyi Daya hada a cikin wani ruwan giya Yana korawa Yana tiltilo hayaki ta Hanci ta Baki cikin kwarewa,Tawaga Yana Aswaki Yana cijewa Yana karkace Baki yace Our King....Sweet Boy,The Handsome King,Fresh Boy, shi kuwa King ya kalli Kansa yace Na me....Na me My Guy,Look at my skin color....
Mubaraq Brown yace Handsome King,Mashkoor Yana wani tangadi a zaune yace Our King ka huta baka hura hayaki sai ruwa Kawai kake bulbula sai kwaya,King ya wani girgiza Kai alamar ya fara daukan chaji shima yace,Hayaki sai dai na shaki na Titi My Guy, Mashkoor yace Look King akwai wata yarinya tayi Fuck Up,the Girl done Mess up man, Wai Ni Ina sonta Tace Banda hankali wani yaro Rabiu Yana Nan malamin makarantar Islamiyya ya kwace min ita,King Yana lumshe Ido duk ya fita a hayyacinsa ya karkace bakinsa gefe Daya irin na Yan shaye shaye cikin kakkausar da mayen muryarsa yace She must Collect,Dole ta karbi Certificate na abinda ta aikata,Na yarje muku kuci mamanta,shi Kuma Yaron za a tare shi dole mu bashi Sample,Sumarsa me laushi ya yamutsa,yace guys gobe Mommy da Dad zasu shugo garin Nan Karku zo gida na sai bayan sun tafi,Abdul yace Confirm,No wahala,Jibril Jibson ya Mike Yana tangal tangal yace ya za ayi ace baza mu zo gidan King ba,The sweet Boy,Cikin zafi da daga Murya King Ahmad yace hey What's up man Ina magana kana magana kana hauka ne? I'm sorry cewar Jibson ya Fadi a kasa Yana mayensa,da ganinsu kasan talakawa ne Ahmad shine me kudin shike musu komai,Haka Mashkoor Yana da kudi shima Amma ba Wani da yawa ba,Sai Abinda Ahmad yace shine King dinsu,duk wani rashin mutunci da sukeyi a gari shine yake daure musu gindi sai da sa hannunsa akeyi,Ba Wanda ya Isa ya nuna su da yatsa,Dai Dai ne Basu San da zamansu ba musamman Ahmad King din Wanda ya fita daban sabo da Naira da hutu,suturarsa Kawai abin kallo ce,Dukkansu baza su wuce 30years ba zuwa 34years,Ahmad 34yrs yake cif.

Washe gari da Yamma su Mashkoor da abokansa gaba dayansu har King din nasu Ahmad machine sababbi suka hau kowa da nasa Kuma duk King ne ya Siya musu kowa da nasa King shine a gaba suna binsa a baya sun kure Masa gudu sun biyo Hanya duk Wanda Bai matsa ba sai dai su bige shi ba ruwansu,sabo da an sansu Ana ganinsu ake kaucewa,Can layin da Islamiyayyar take suka tsaya Suka Parker machinansu,King shine kadai ya zauna a saman nasa suna ta Masa Kirari suna Our King,Fresh Boy,Sweet Boy,shi Kuma Yana ji da Kansa,Suna Haka sai ga malamin Islamiyya ya taho zai wuce matashi da shi Yana tafiya cikin nutsuwa Baki da shi,Tare shi Mashkoor yayi tare da cewa Yawwa ga dan Iska ya Furta tare da tallafe Masa keya,King ya Mike cikin maye yace kana gaba na kana tsaye,Robar Lemo Wanda ciki hadin kwaya ne a ciki Yana Sha ya daga ya tsiyaya wa malamin Islamiyya a kansa,Nan suka rufe shi da duka Wai yayiwa Sarkinsu magana a tsaye,Wata Mahaukaciyar mota ce me kyau da tsada ta taho a hankali,Mommy da Yar Autarta Humaira sai Daddy Mijinta a baya gaba Kuma Kanin Ahmad ne Saddiq da matarsa Mufida a Gaban mota suna tafiya, Saddeeq shi ke tuka motar,Daddy yace ai Kinga Ahmad din ma gashi Nan da Yan Iskan abokansa,na gaji da zuwa Kaduna akan Yaron Nan wallahi,Na rasa wannan masifa data sameni,Kinga Ni yanda suke dukan wani,Kanwar su Humaira Tace ga Yaya can da kayan maye a hannunsa, Saddiq ya tabe Baki tare da cewa kalli Askinsa Ana ganinsa anga Dan Iska,Mufida matar yayan Tace kuyi Masa Addua Kawai.

A wajen Suka Yi parking sai tsawar Daddy dinsa yaji a Kansa Ahmad Mene Haka? Baka da hankali ne,duk suna mota ba Wanda ya fito sai Mummy da Daddy,Daddy ya tashi malamin makaranta Wanda ya ci duka da gudu ya arce Yaron,Su Mashkoor suka kame a Gaban Daddy tare da Sara Masa kamar suna Gaban wani Soja,Zaga Daddy da Mummy suka shiga Yi suna musu Sannu da zuwa Wai Nan murna ce da girmama Iyayen Ogansu,Bash kuzo mu Basu kariya Guys ba Wanda ya Isa ya daga Musu yatsa a Birnin Kaduna kaf.

Tsaki Daddy ya ja Yana Jin yanda suke wa Ahmad Kirari,Wandonsa ya kalla wani shegen crazy an Masa daga daga,Askinsa ya kalla yace kalli yanda ka maida kanka Ahmad, Dariya ya Shiga Yi ta mahaukatan Yan maye,Mommy Tace Ahmad Dina meke damunka muje gidan da kake,Daddy yace shiga mota mu tafi,Wani fareti ya shiga Yi a Gaban Daddy Yana dariya cike da maye Yana karkace Baki yace No...no Ni a bike Dina zanzo kasan Ina Jin dadin bike Dina Kawai kuje zanzo daga baya,Tsawa Daddy ya daka Masa shiga muje,Amma ko a jikinsa sai ma Dariya da ya Shiga kyakyatawa irin ta basawa Yana kallon Daddy din da Mommy,Dole Haka Suka shiga mota Suka tafi shi Kuma shi da Abokansa suka take musu baya a machine suna tukin ganganci Dan Ahmad harda dage kafa Daya ya daura ta can sama Yana tuki da kafa Daya,Har katafaren gidansa Suka shiga sannan abokan daga bakin Gate Suka tafi gida abinsu shi Kuma yayi Horn me Gadi ya Bude Musu Gate,Bayan sun Shiga Suka firfito da akwatunansu,Wani handkerchief ya daura a wuyansa ya tsaya a Gaban Mommy Dinsa Yana zagata cike da maye Yana cewa Mummy...Mummy....Momma....You are looking Good ya furta tare da rungumeta yace Ina sonki Mummy,rokonsa ta fara Tace Dan Allah ka nutsu Ahmad,Da karaji Daddy yace Mene ne kike rokonsa, why are you Begging him,Dan ubansa tunda bashi da hankali sai yayi ai,Why...why...Daddy Ni dama fa ba tun yau ba nasan baka kaunata,musamman idan ka saka wannan farin Glass din naka sai ka dinga kwana idan anyi Nan sai kayi can,Ido Daddy ya zaro Yana kallon rashin kunyar Ahmad,Kaninsa Sadeeq ne yace ka canja wallahi Yaya,Cikin karaji ya tasowa Saddeeq Yana ce Masa Kai dalla gafara Ina yayanka zaka min fada,ko Dan kaga munyi Kai Daya Ina da gemu kana da gemu shine zaka rainani Kai wuyanka ya Isa yanka ko,Ka dai gyara halinka,Tafiya yayi zai Mari Saddeeq Mummy ta rike shi tana rokarsa yayi Hakuri, Humaira ya riko tare da Rungume ta yace kanwata kin girma,ya school? Tana Dariya Tace nayi Candy Yaya,Wow ya Furta tare da dagata sama ya ajiyeta suna Dariya,Matar Kaninsa ya kalla Mufida nutsatsiya kyakyawa yace matar mu ya gida fatan wannan shashashan yana kula Dake? Dariya Mufida tayi Tace sosai ma,yace Good muje ciki matar mu ke kadai ce tawa a gidan Nan,kishi ya Kama Saddeeq ganin Ahmad Yana shaye shaye tunaninsa har Mata yake bi sai kishi ya kamashi yace kaje kayi aure wannan matata ce Ni Daya ka daina cewa matarmu yawwa,Stupid Boy Kawai Ahmad ya furta Suka jera da Mufida suna Hira duk da a maye yake Amma Yama Saba Bai fiye buguwa da yawa ba, Sadeeq da Sauri yazo ya shiga tsakiyarsu ya rike Hannun matarsa ya janye ta da karfi,Baki Ahmad ya tabe ya Rungume Humaira Suka Yi ciki.

Bayan sun huta sunci abinci Daddy yace da dare Yana neman kowa za ayi Meeting zasu fadawa Ahmad dalilin zuwansu yanzu ma again, Har dare yayi Ana jiran Ahmad Amma tuni ya bar gidan Yana can suna shaye shaye har 1am Bai dawo ba sai kowa ya hakura yayi bacci,Da safe ma Ana ta jiransa har sun karya Shuru Bai dawo ba,can sai gashi a bige ya Fado palon ya tafi taga taga zai Fadi sai ya cije ya Dage Yana bude Ido da kyar Yana Rufewa ya fada saman kujera shirim kusa da Daddy yace An tashi lfy? Ina....Ji...ji..jinku.....m....me.....yaaaaaa....ya...kawo ku Kuma yanzu Kun wani sake dawo min gida...na tuna ance jiya za ayi meeting yanzu gani Ina da abin Yi ku Fadi meke tafe daku har zuwa gidana? Daddy ya zaro Ido yace au gidan ka ne ma? Gidana kace gidanka? Yace gida nane Mana Kai ai Temporary Owner ne Nan gaba mutuwa zakayi naci gado,Ran Daddy ya baci yace gidan Nawa? ni da gidan gida ka gaje min gida?aikin uban me kake Yi? Kaki nutsuwa,Mummy Tace Ahmad Dan Allah ka tsaya ka nutsu kaji abinda ya kawo mu,Ina jinku Mana ku fada,Kaninsa Sadeeq ya tabe Baki,Humaira Tace Addua zaku Masa please,Ita Mufida ita tunda auro ta akayi Bata cikin wacce zata Shiga matsalar Family tana bedroom.

Daddy yace kana ji na Ahmad? Yace Yeah,yace so nake ka bar Nan ka dawo Lagos kazo mu koma inda nake da Zama can Lagos Ina so Zan maka Visa mu tafi London gaba Dayan mu,akwai Company na Dake can kayi Handling dinsa kayi Aiki a can ka dogara da kanka,kullum sai dai na cika maka account da kudi kana kashewa a banza,ya kace?Ahmad yayi Dariya yace kasan amsata Mana Daddy Ni bazan je ba wata kasa da zanje Kuma Ni bana son Lagos a Nan gidana Zan zauna a Nan Zan mutu,Daddy yace to gidanka ne? Ni da gida na,Mummy Tace Dan Allah Ahmad ka bimu mu tafi kaga London ko Turkysh ko Kuma a Nan kasar Nigeria sai kayi Aiki an baka company kyauta ka dogara da kanka Kaine fa babban Danmu Kai ya kamata ace ka nutsu,kalli kaninka ya rike nasa a Lagos Yana aikinsa gashi da Degree da Masters Kai kuwa Degree daya ma da kyar muka samu ka karasa a Russia,Ahmad yace kunga fa Ni ba inda zanje Kawai ku daina Bata bakinku mutanen da basa son bakar fata ku Kun damu da su kuje kuyi harkarku,kuyi rayuwarku nima nayi tawa,yawwa kunji ba inda zanje ya tashi Yana tangadi ya haura sama,ya barsu a Nan cike da Alajabi yafi karfinsu.Daddy bakin ciki ya Kama shi ya juya kalli Mommy tare da galla Mata Harara yace Kinga danki ko kin ga abinda kika haifa ko? Mummy Tace au da nane ma Ni Daya? Daga Nan suka fara cacar Baki.

Aamna ce ta fito tsakar gida sanye da wani gajeren wando ko gwiwa Bai ba Milk color,da Yar rigarta t-shirt dark Blue,Hannu biyu ta zuba a cikin aljihunta tana tafiya tana yan ga,Cinyoyi da kafafunta lukutaye,Mama ce ta Bude Baki Tace Yau me Zan gani? Aamna kece yau kika Yi wannan shigar ke da bakya so aga jikinki yau me Zan gani na Shiga Uku Kamar Namiji, Malam fito ka gani,Kuma wandon ma na Yan Ball ta saka wani katon buje,Aamna saman bakin rijiyar tsakar Gidan ta zauna daram tare da Harde kafafu,Baba ne ya fito da sauri shima ya Bude baki,yace kwaya kika Sha? Nan fa gidan haya ne ga maza Wanda da matansu,Aamna Fuska ta bata tare da Furta naga Alama a gidan Nan magauta sun min yawa,Magauta sun sani a gaba Ana so aga baya na,to Zan dauki mataki
Mama kirji ta dafe Tace Aljanu ne da ke Aamna? Tace Ni yawwa da ace akwai Sigari a kusa ma yau
Showing 3001 words to 6000 words out of 142807 words