da Mata ba mayaudara ne zata yaudari abokinsu,daya palon suka koma.

Wurin Magrib Aamna Tace tafiya zanyi dare ya fara,Fuska ya bata Yana Zaune ya saki wani jiki Yana ta shagwaba kamar Yaron yaye ya turo Baki gaba Yana wani motsa Kansa yace Ni ban gaji da kallonki ba idan kika barni Ni kadai Zan Zama......sai ya canja muryar Yara Kuma da Waka yace Lonely....... Lonely.....oh....lonely.....Dariya Aamna keyi kamar sabon kamu,Tace kasan Mama zasu min fada fa...lokacin Mashkoor ya fito zai dakko lemo yaji abinda Aamna Tace karaf yace wannan Yafi Mama power a kanki ko a wajen Allah Shi yake da iko a kanki ba wata Mama ko Baba ba,kin Gama Raina shi Yana aurenki ki dawo gidan Mana idan gaskiya kika kulla a ranki,Ahmad ne ya cire ta kalminsa da sauri ya wulwulawa Mashkoor zai kwada Masa, Mashkoor ya goce takalmin ya Fadi a kasa,Tafiya yayi da Niyyar cin uban Mashkoor Amma Mashkoor ya gudu wancan palon,Tsaki Yaja yace yi Hakuri muje na ajiyeki a gida to.

Machine dinsa ya hau Aamna ta Haye itama ya fisgeta Suka tafi,a Kofar gida ya sauke ta sannan ya koma gida.
Da masifa ya Shiga wajen su Mashkoor yace wallahi idan Naga Wanda ya sake Yiwa My woman magana sai naci ubanku,iskancin banza, Mashkoor yace kayi hankali baka San Mata ba,idan Aunty Balaraba gaskiya ta kulla a ranta ta dawo gidanka Mana kuyi rayuwar aure,Taya zata tafi Kuma Tace tana sonka Taki dawowa inda kake, wallahi kabi a hankali mata Basu da Imani Tam,Ahmad Tsaki ya ja yace Ni ance maka Zan Mata Dole ne idan tana so da kanta zata dawo ka daina damunta,Tawaga yace shike Nan mun kyale ku yanzu Abinda ya kawo mu Baban Mubaraq Brown ne ya kawo mu.

Ahmad yace me ya faru Yana kallon Mubaraq,Mubaraq Brown da Muryarsa ta Yan kwaya yace Guys jiya Ina Shiga gida Wai na kure Hajiyanmu ta kulle kanta a daki tana ta Rusa kuka kaiii...abin fa ya caja min Kai,nace Hajiya me ya faru Tace ai tsohon Nan ne zai Mata kishiya,Tawaga ya daki Cinyar Ahmad yace abin haushin My Guy wata bazawara ce mijinta ya mutu ya barta da Yara biyar,Wai gaba Daya zai dakko ta ya aure ta da Yaran,Ahmad yace Uhm da ace ta daina Haihuwa to da sai muce yayi taimako ya tallafi marayu,ya kamata dama a dinga kula da marayu Ana samun masu Hali suna daukan nauyi kaga da an rage masifu,Jibson yace Kai Bari masu kudi sun daina taimako tunda Ummati ta rasu kwananta ashirin yau babu Wanda ya tallafamin da ko Sabulun wanki sai ku abokaina,Brown yace Dan Allah a duba matsalata,Sukayi Dariya Tawaga yace kaga a hasashe idan Ya auri me Yara biyar ta taho da su gidanku kaima Babanka idan da tsawon Rai a hannunsa zata haifi Kamar biyar ko shida kaga a lissafi Shida ga biyar Sha Daya kenan,Brown ya dura Ashar yace a Tara da mu Yaran Hajiya Guda tara,Ashirin cib cib cewar Jibson,Suka sheke da dariya.

Ahmad yace kaga ko zaben Shugaban kasa kuka fito iya gidanku sai ku kayar da Jam'iya Guda ko kusa Jam'iya ta lashe zabe,Dariya Suka dinga yi, Mashkoor yace idan a Iya shida Amaryar ta tsaya kenan ai yanzu Mata sun daina wata Tara kafin su Haihu,Ahmad yace Musamman idan da Abinci kaga idan zaka bawa Mace abinci taci ta koshi ta samu nutsuwa ai wallahi duk buga kwallo sai cikin raga,Jibson yace sai dai kaji a goalll.....idan ka sake ma duk kwallo Daya a biyu ko Uku take Yan Uku Yan biyu za ayi ta zubo maka,Suka kyalkyale da Dariya, Mashkoor yace kutmar dosan Uwa idan aka sake kayiwa matarka family planning na shekara Hudu Dan karta Haihu idan Allah yaga dama sai ka Gama tsarinka sai tazo Karo maka Yara cikin farko ta Haifo maka Yan Uku ko Yan hudu ko Yan biyu ta maka Yan biyu sau uku a jere,kaga shekarun da Bata Haihu ba Ashe Tara maka yaranka akayi Hhhhhhh suka sake sakin Dariya..

Ahmad yace wallahi ta sake ta Haifo Yan hudu har abada ita da Haihuwa ko dai ta tsaya ayi planning na kirki ko tayi gidan ubanta,Tawaga yace gaba Daya tsoron aure nakeyi sabo da wannan,Ina son Mata Amma ko Dan wannan jarabar Haihuwar tasu Daya ta ishe Ni,sabo da kowacce sai ta zube nata,idan kana da kudi ma Mata ma har gasar Haihuwa sukeyi sabo da aci gado in ka mutu, Mashkoor yace Kai Sarki Kaine zaka iya korar Aunty Balaraba Dan Tace zata Haihu? Inda ka susuce me zaka iya ai sai abinda taga Dama,Ahmad yace to sai na dinga amfani da Condom ba shike Nan ba,fashewa wani yakeyi cewar Jibson,Ahmad yace to idan baza tayi planning dinba Ni sai naje ayi min a kashe kwayoyin Halittar yaran Dan Uwatasu kaga inta buga kwallo ba cin ball na dawo Dan Arsenal kawai kwallo ba ci gaba,Suka dinga dariya.

Ahmad yace Amma yanzu a kiyayi Mata ba irin Iyayenmu bane na da,Indai mace zata samu shinkafa taci ta koshi,ga dankalin turawa,ga nama,doya...kaga doya ka guji bawa matarka doya naji ance tana sawa a dinga haifar 'Yan biyu 'yan Uku,Hhhhhh Suka sake sakin Dariya Ahmad yaci gaba da cewa ku daina Dariya gaskiya ne,yawan Shan Madara,da jarabar kwadayin mata su dinga girke girke to yanzu Mata sun daina wata Tara dauke da ciki ai wata shida shida suke Haihuwa yanzu,shekara Biyu Yara uku,Brown yace Ni yanzu a dawo wajen Baffa na,Ahmad yace ai Babansa Yana da Rai,Brown yace kwarai Ina da kaka a raye,gaskiya Kai Dan gata ne har wani Kaka ne da Kai Bai mutu ba? Bash ya tambaya,Ahmad yace wajen kakan zamuje lallai a dakatar da auren Nan yaran sun Isa,idan sunki yarda sai mu koma Kan bazawarar Baffa a cikinmu wani zai shigar Kamala mu dinga zuwa zance wajenta.

Kaga zata ga yaro sabon jini me zatayi da tsoho shike Nan ta daina son Baffa,Dariya Suka Yi harda ihu, Mashkoor yace King Ni za a Bawa wannan fannin,Ahmad yace no Jibson ne zaiyi kaga Jibson shi a cikinmu dama Yana kula Yan Mata Sarkin yaudara ne, Jibson yace ai wallahi na yaudari Mata sunfi dari Kuma abin haushin duk Wanda na yaudara ban taba samu nayi ko Sex da su ba,a duniya sau Biyu nasan na taba Sex da wata guntuwar yarinya me Kama da kofin shayi Me Hannu,King yace ku kyale ma wani Kakan Brown baza su yarda da mu ba, Kawai mu fara Shirin zuwa wajen Bazawara,Kai Brown ka Nemo Address din gidansu da sunanta.
Brown yace naji kanne na suna cewa sunanta Sameera,Tawaga yace kwanon cin abinci kenan Sameera fa tab,Bash yace daga yau sunanta kwano babu wani Sameera kwano kawai,suka tafa.

Tunda Aamna ta koma gida ta kasa sukuni Kawai Ahmad take tunani da Kuma sha'awarsa Tace yanzu ko Dan Romance Haka akeyi,yanzu saurayi da Budurwa ma basa zance su tashi lafiya mazan yanzu sai Allah ya shirya,Amma Miji Guda na kwanta a jikinsa na tashi wani garau da shi Anya Ni mace ce kuwa,Wata zuciyar ce Tace to Mene yaje da jikinsa,tana wannan tunanin bacci ya kwashe ta,Washe gari da Sassafe Ahmad ya Kira Aamna tana dagawa ko gaisawa Bai Bari sunyi ba ya marairaice tare da furta Dan Allah nazo na ganki yanzu? Ba Zama zanyi ba Kawai bakin gate Zaki leko Dana ganki Zan wuce to sai kazo ta furta tare da mikewa da sauri ta fada wanka a gurguje ta shirya cikin wata silk Yellow and red doguwar rigar material,Powder ta shafa da lipgloss ta fesa turaruka duk Dan a birge shi,Mayafi red ta yafa sai gashi ya kirata a waya yace fito na zo,da sauri ta fito Mama da Baba sai gani sukayi tayi waje da sauri ko kulasu Bata Yi ba tana ta kamshi,da Murmushi ta fito,ya kalleta sosai ya sake leka fuskarta Yana zuba murmushi yace kwalliya kika Yi min? A'a dama nayi abata cewar Aamna da karya,Yace Ina Zaki je to?
Tace dama Hospital nake so ka kaini,Me ya faru da ke ya furta a tsorace Tace wata takarda Zan karbo,Yace to kin shirya Tace ae yace hau mu tafi,kafadarsa ta dafa sannan ta hau suka tafi.

Suna zuwa da Mamaki sai Aamna ta ja Ahmad Office din Doctor Tace Likita gamu a rubuta Mana Tests din da zamuyi na medical checkup,Ina so cikin Nan nasa ta nuna cikin Ahmad Tace a Bincike min shi sosai,koda,hanta,Huhu da sauransu duk a tabbatar min da lafiyarsu,Haka jininsa ma ko Ina a Masa test,Dan kar yaji Haushi Tace harda Ni Nima ayi Mana tare,Doctor yace to Nan take ya rubuta musu tests ya turasu Lab,Ahmad baiji komai ba tunda tana so Bai San manufarta ba sai ya bita Suka je aka ja jininsu sannan aka musu scanning ko Ina Kamar yanda Aamna ta bukata,Dake private ne Nan take Likita yace ku jira Kawai result ya fito ku tafi da abinku,Zama sukayi Ahmad yana rike da Hannunta,kudin ma shi ya biya komai,sai wurin Bayan 12pm aka ce suje su karbi Result ya fito,Suna karba Suka shiga Office din Likita Suka zauna,Likita ya fara Bude na Ahmad ya Gama duba kowanne yace Kaga Kai Alhmdllh Allah ya taimakeka lafiyarka kalau,komai naka Normal ne baka da wata matsala gaskiya,Yace gashi Genotype dinka AA ne shima,Ahmad yace na sani ai Ni Ina ganin Likita duk shekara Ana duba Ni,Aamna taji kunyar abinda tayi zarginta shaye shaye ya Gama illata Ahmad,Ahmad cikin kuri ya bigi table din likita yace Doctor duba Mana nata mu gani Kuma mutum idan ba lafiyayye bane yaci ubansa a Nan wajen, Doctor ya dinga dariya shi da Aamna Wato da Aamna yake kenan.

Doctor ya bude na Aamna yana dubawa yace Alhmdllh kema lafiya kike Amma kina da matsalar Cold Bladder sanyin mafitsara Wanda Infection ne ya haddasa,Maganin ciwon Sanyi Za'a rubuta Miki Kuma sai kin dage kafin ya warke,sai Genotype dinki AS ce ke Wato carrier,Kinga Allah ya taimakeki mijinki AA ne baza ku haifi me Sickler ba Kun tsallake rijiya da baya, Doctor yace Kai kana mijinta ya akayi sanyin be Kamaka ba? Ahmad yace Amarya ce fa ai Bata tare ba,Gidan ne ba a karasa hadawa ba shi yasa nace tayi zamanta a gidansu sai an Gama,Kuma ka Iya Hakuri? Ahmad yace ae Mana Kuma kullum sai naje zance,yanzu ba gashi hakurina ya taimakeni ba da yanzu ta shafa min asosa,Dariya Aamna tayi Tace zaka ga Asosa wallahi.

Likita dai maganunguna ya rubuta Mata masu zafi,Ahmad suka je aka siya, Allura za a Mata ta kwana biyar,yau za ayi Daya Kamar zatayi kuka,Ahmad ne ya riketa Kam aka Mata a Hannu,Aamna harda kukan shagwaba na ganin Miji na kusa, Suna Hanya a machine yace Wai ke Baki da kawayen kirki ne sai wannan banzar Siyaman? Aamna Tace ai Siyama bani da kamarta ita take dorani a hanya me kyau,Take doraki a keken bera dai wannan ce ta kirkin? Fushi Aamna ta fara Wai ya tsani kawarta.

Lokacin suna zuwa kusa da wani masallaci anyi Kiran Sallah,Aamna Tace tsaya kayi Sallah a jam'i,tunda tana so sai ya tsaya a masallacin sai ya tsaya, tana waje ya Shiga ciki a Jam'i yayi Sallah yau,Yana Fitowa tana ta murna,Hararta ya Yi yace Sallah 12:30pm Bata Nuna ba,Kin jawo Nayi Sallah tun tana Danya sharaf,Aamna Dariya tayi Suka tafi ya ajiyeta a gida Yana ta Fushi.

Zai tafi ta tsaya Tace ba ko Sallama? Kansa ya dauke ya kalli can gefe,zuwa tayi da sauri tana Dariya ta riko Hannunsa,Idonsa ya rumtse sabo da har kwakwalwarsa yaji wani yarrrrr, Kiss ta manna Masa a Bayan hannun Tace I love you,da sauri ya kalleta yace da gaske? Kai ta daga Masa tana murmushi,Sakkowa yayi daga machine tare da rungumeta yace I love you too,a kunne ta rada Masa idan anyi Kiran sallar la'asar kaje masallaci Kuma ka Dan zauna kaji Wa'azin liman Naga masallacin kusa da gidanka Ana wa'azi bayan Sallar la'asar,Ahmad Bai kulata ba ya hau Machine ya tafi gida.
Zaune suke a gidan Ahmad,Tawaga,Jibson,Bash da Mashkoor,Kiran Sallah aka kwalla,Ahmad ya mike zumbur yace My world Tace naje sallah yau,Kirji Tawaga ya dafe Yana zuka Wiwi yace what....me zanji? Sallah ka manta mu Bama Sallah sai ta Nuna ligigif? Dariya Mashkoor yayi yace ai kwana Nan za a bashi limancin masallacin Unguwar, ku tashi muje muje ai muma ba arna bane Dan uwarka King cewar Bash.

Tafiya suka Yi tare gaba dayansu,Gaf da za a Tada Sallah sukayi Alwala sai kallonsu akeyi sabo da kitson Ahmad da gyaran gashin su Jibson kadai abin kallo ne,Ahmad ne kadai da Yar tsangalalliyar jallabiya fara Amma duk cikinsu daga me 3qtr sai me Creazy jean,sai dai kana gani kasan ba kazamai bane Yan iskan Yan gayu ne Kawai jikinsu suna kashe Masa kudi,Limamin Unguwar yasan su musamman Ahmad Bai taba ganinsu a masallaci ba sai yau Kuma Suka hau sahun gaba shu'umai,.

Bayan anyi Sallah an idar masu Zama Jin wa'azi Suka zauna har su Ahmad,Yau sai liman ya fara wa'azi akan Karin aure,ko wanne Namiji yayi kokari ya Kara aure,Ahmad ya kunna recording a wayarsa ya ajiyewa Aamna tunda itace Tace yaji wa'azi Kuma yayi Aiki da shi gashi ya fara da Jin falalar Kara aure mutum ya auri mace sama da Daya.
Malam yace idan Namiji Yana talauci zai iya Kara aure Allah zai Iya Buda Masa sanadiyar wannan auren,Tawaga ne ya daga yatsa Sama yace Ina da tambaya Malam,Malam ganin irinsu Nan take yace Ina jinka samari,Tawaga yace cikin darajaka da kankan da Kai tare da mutuntuwa Malam karya kakeyi.

Baki Malam ya bude ya kallesu Jibson yace kwarai kuwa katuwar karya ma,cikin Yaran Malam wasu Suka Mike da Niyyar tarewa Malam,Malam ya dakatar dasu tare da kallon Tawaga yace Kai bani hujjarka da kace ba Haka bane,ka daina gyarawa wani ba Haka bane Kawai karyace malam,ba hadisi ko Aya na karyata ba Kawai abinda ke faruwa,Babana kafin ya mutu talaka ne Haka Kawai karambani yasa ya Karo aure ai kuwa talaucinsa ya karu,Gomnati Watarana ta bada tallafin dubu dari ai sai Baba ya sake Karo ta Uku da kudin talauci ya sake dannowa gidanmu karshe wahala ce ta Kori matan biyu aka bar Mamata yanzu Yaran suna Nan rututu shi Kuma ya rasu an bar min nauyi sannan kace wani Ana samun Budi,ga mutane Nan yanzu da yawa ko mace Daya ya aura sai kaga duk ya fara lalacewa wahala ta isheshi yana dana sani.

Jibson yace ance Wai Malam ko matashi Niyyar aure yayi Allah zai Buda Masa ya kawo Masa yanda zaiyi yayi auren? to Ni Malam Niyyar aure nayi shi yafi sau dubu sannan yanzu zancen da nake maka Zuciyata a kudurce take da Niyyar aure Amma kwandala bana samu abokaina su suke daukan nauyi na sannan kazo wani kace,Bash yace Kai Malam yanzu ba irin da bane rayuwar yanzu daban take ku San abinda Zaku dinga fada,wancan satin naji wani malamin yace idan matashi baida aikinyi Kar ya sake yayi Aure sabo da rayuwar yanzu,Haka Rannan wani yace Mata Kar su sake su auri mara sana'a,yanzu Kai Kuma kace ayi sama da biyu,Ahmad yace da Allah ku dinga duba littatafai sosai kafin ku fadawa jama'a wani abu,Ya za a dinga zuwa Ana Raina Mana hankali mun rasa inda kuka dosa wannan yace kaza wannan yazo ya karyata.

Malam ya kalle su yayi Dariya yace Dana fara Wa'azin ai sai ku Bari na Kai Aya,da sai ku tsaya bayan na Gama fadar falala ai zanzo nayi bayani akan Kuma wannan matsalar da kuka ambata Amma sai kuka rigani,Dariya Tawaga yayi yace karka zo Mana da gyara Malam Kawai mun kureka ka zugo ta yawwa,Kai ku tashi mu tafi Sallah Kuma da Muka bika Allah ya baka ladan Jan Sallah Amma wa'azinka 0/0 baka ci ba,Suka Mike suka fice.

Liman sallamar mutane yayi yace gobe zai Dora daga inda ya tsaya ya fita da sauri,Liman hamshakin me kudi ne Dan kasuwa ne na gaske,Su Ahmad ya dakatar a wajen masallaci suna tafiya,Tsayawa sukayi Liman yace cikinku duk ba me aure?Ahmad yace Ni ina da shi Amarya ce Bata tare ba Amma ta kusa,Yace mashaallah ai Kai na sanka a garin Nan har mahaifinka na sani,Ahmad ya tabe Baki,Jibson ya kalla yace Kaine kace kayi Niyyar yin aure baka ga Budi ba ko? Jibson yace kwarai kuwa,Liman yace to kaje ka Nemo yarinya Ni Kuma na tsaya maka har gidan Zama kyauta Zan baka aikinyi me tsoka Kuma Zan maka komai na auren,Jibson yace Malam karfa ka min Alkawarin Yan siyasa baza kaji da kyau ba,Malam yayi Murmushi sabo da yasan Basu San shi waye ba,Karfa ka bashi gida irin na talakawa talak idan irinsa ne ka rike abinka Bamu shirya aure ba sabo mu mun tsara Dole matanmu suji dadin duniya shi yasa Muka hakura da Aure muna talauci jira mukeyi sai munyi kudi cewar Mashkoor,Bash yace yawwa kaji dai Malam,Malam yace cikinku ma idan akwai Wanda yayi Niyya ya fada,Tawaga yace Marayu kannena sun ishe Ni ma Ina Ni Ina aure banyi Niyya ba, Mashkoor yace Ni kuwa Muna da Hali ra'ayi ne banyi ba,Banga wacce ta min ba,Malam yace Ina da Yara kaje ka gani idan da wacce ta maka a ciki, Mashkoor yace rabani da Yar malamai tazo tayi ta zunduma min Hijab a gida,idan nayi magana ta jawo Aya gwara wacce ta rike izu biyu na Sallah Yar jahila jahila Haka,Dariya suka bawa Malam yace duk Sanda ka shirya kazo ka gani dai, Mashkoor yace bafa zanzo zance gurin yarka ba ta malamai Dan Hannu bazan rike Mata bare Yar runguma a fara min wa'azi ai sai
Showing 57001 words to 60000 words out of 142807 words