sosai,dukka Dangin su Yar China farare ne yawanci gado Suka yo Yan Fulani ne usul Yar China ce tayi Kama da yan China Kalar Idonta da Dan shape din fuskar sai ta Zama Kamar ruwa biyu irin Babanta Dan China Babarta Yar Fulanin Nigeria Haka ta zama,kawayenta masu yawan jaraba gari Guda,wani gida me kyan gaske da girma ya sha tiles ko Ina a Nan ta sauki bakinta abinci iri iri na Yan gayu ta bayar aka yo Mata na saukar Baki,su Friedrice with chickens ta Sha hadin salat,ga Waina da Miya,sinasir,wani faten dankalin turawa da nama,Jullof rice,Dan Iyayin Yar China harda fura da Nono me yawan gaske an zuba a robobi kamar rufaida dink,gurasa ta Sha cabbage da Albasa da tumatur,harda Dambun shinkafa,alala,Tuwon shinkafa,ga lemukan roba da ruwan Roba da sauransu Yar China har makwaftan da suke mutunci sai da ta sanar musu Kar suyi girki ranar bikinta kowa yazo a Nan zaici ya sha.

Yar China sabo da surutu da tsokana kowa ya santa ta kwashi jama'a da yawan gaske,tana shiga wajen Iyalle taje tace Iyalle Kinga kwalliyata yanzu na dawo nayi sauri sabo da kar Ina can a daura auren ban sani ba,Iyalle tace an daura fa ga Salamatu Nan ta fada Miki,Yar China tace ai nayi tunanin Wasa take min au an daura Iyalle? Iyalle Tace kwarai,Yar China Fuska ta rufe tana kyalkyala dariya dangi suna ta dariya Ana kallon ikon Allah,Iyalle tace Umma salamatu na Miki Alkawarin dubu daya kafin ki tafi gida,Salamatu tace Yar banza fitsararriya abinci fa an Kai duk abinda kika ce wajen kawayenki,Habiba ta Ajiye na angwaye daban suna can gidan suna ta tsare tsarensu na Yan karya irinku can,Iyalle Tace gayu gayu ai mu akwai Harkar girma, Ana zafi Yar China ta dauki mufici tare da mikawa wata Yar Budurwa yar gidan Salamatu Yarinyar zata Yi 14yrs tace ungo Marsiyya duk inda nayi kina bi na a baya kina min fifita bana son kwalliyata ta baci tun kafin angwaye su zo.

Haka Yar China take yawo da yarinya tana Binta da fifita Wai ita Amarya,tuni Yar China ta Shiga gidan da Kawayenta suke Suka lullubeta da tsiya duk gasu Nan Yan matasa masu tarin kuruciya sai haukarsu sukeyi,Yar China ta dauki plate da cokali tayi kida rakacal...rakacal sai ta tsaya cik tace duk ku saurara kuji an daura Aure tuni babu wacce naji ta min Addua,ihu Suka saki yeeeeee....sai Yar China wlh yeeew.....Duk sun Sha gayunsu sai kuruciya amma ba karya sunyi kyau,Habiba tace me Dj yazo dama munce ana daurawa zamu fara cashewa har lokacin Kai Amarya,Yar China tace iceko me Speakers Bakwai din Nan ne yazo? Suka ae mana,yawwa so nake a gigita kowa na unguwar nan so nake yau a San Yar China amaryace,Habiba kuje a fara sakin kida me fasa kunne,da fatan kunci Kun koshi? Suka ce ae har mun shirya na angwaye a palon da Muka ware za a sauke su,Yar China ta leka katon palon me kujeru na Alfarma ga girke girke daban daban an shirya na gayu gidan wata ce suna mutunci da Yar China shi yasa ta Basu gidan.

Su dai kawayen Amarya suna ta rawa da danginta suna murgude murgude,Ana ta liki Amarya tana Jan aji bata fita ba tukun,Bangaren angwaye Kuwa duk sunje gidajen amare an gaisar da surukai lokacin Aamna gidan su Yar China tazo Driver ya kawota a Arniyar mota ta zuba kyau na gaske cikin wata Shadda ta kece raini maroon,kowa Binta yayi da kallo Kamar me,gidan ta shiga ta Gaida su Iyalle ta musu Allah Sanya Alkhairi,fita tayi aka rakata wajen Yar China ta isketa a wani Palo tana Shan ac Wai Dan kar kwalliyarta ta baci,ga me fifita da mufici tana gefe idan ta fita waje tana fifita Mata.

Aamna sai kallon Yar China takeyi tayi kyau fiye da tunanin me tunani Kuma a tunaninta ma Yar China ba Wani gyara kanta zatayi ba tunda taga kamar Bata da nutsuwa sai taga sabanin Haka Yar China ma kamar tafi duk Amaren yin kyau,shigarta da dinkinta ya birge,Aamna ko Yar gidan Gomna abinda zata Yi kenan,Bayan sun gaisa ta Mata Allah Sanya alkhairi,Yar China tace Aunty Balaraba dama Zaki zo? Gani kin ganni cewar Aamna tana dariya,Yar China wajen abincin ta nunawa Aamna tace ki zuba abinda kike so Aunty,Aamna tace na koshi,ai Yar China ba Wani tunani tace ai Kuwa karya ne wlh sai kinci duk Wanda yazo bikin Yar China sai ya koshi,Aamna a ranta tace Direct karya ma nake Yarinyar ta fini wauta Sanda Ina budurwa,Hannun Aamna Yar China ta rike tace nasan mu talakawa ne shi yasa baza kici abincin mu ba wallahi sai na fadawa Yaya Tawaga sabo da yasan irin zaman da zaiyi dake,Aamna ba shiri ta shiga bude abinci tayi mamaki komai na Yan gayu harkar girma,harda wata Green spaghetti ai Yar China tafi ma sauran Amaren yin abincin girma,dama bikin da kake sa rai bazaiyi armashi ba shike yin kyau,Wanda kake tunanin zaiyi Dadi Kuma sai kaga ba shine ba,Aamna dai taga zahiri Kuma taji tsoro tasan tsaf Yar China zata fadawa Tawaga idan Ahmad yaji Kuma tasan sauran bai iya Fushi ba,sai ta ebi gurasa,ta zuba dankali daban yasha nama, ta zauna taci da yawa tare da Shan lemo da ruwan,Yar china tace to kin taimaki kanki wallahi da Baki ci ba sai na Kai kararki wajen Oganki direct,Aamna tayi Dariya Tace na fita sul to,Yar China cewa tayi ai har cewa zanyi kin harareni Ni da Iyalle ta,Aamna tana dariya tace Allah ya rufa min asiri King wlh Bai Iya Fushi ba sai ki jaja min,Dariya Yar China tayi tace to ki kiyayi tabani wallahi sai na kulla Miki sharri Dan Baki Sanni bane bani da kirki ban San na gida ba,komai sanina da mutum ya min laifi baruwana cinnaka ce ni,Aamna tace Allah baki hakuri suna dariya Yar China tace muje yau sai kinyi rawa,ta ja Hannun Aamna Suka fita wurin Dj.

Suna zuwa wajen angwaye suna zuwa a motoci a Nan suka Sha kallon shagali sauran gidajen Amaren duk ba mutane ba kida kamar ba biki ba sabo da sunce auren yazo ba shiri,ai Nan Suka ga bataliyar Yan Mata an dau wankan sugar ba karya,sai ka kula matar aure baka sani ba kayi zaton Yan mata ne,su kansu bikin sai ya birge su,suka bige da kallo Ana ta rashin kunyar rawa,ga fararen mata na tashi sabo da Yar China danginsu ga Kawayenta na musamman sun Shiryawa bikin,Tawaga motarsu Daya da Jibson da Ahmad sauran Kuma su Brown ga wasu frnds na daban ma,Tawaga Yar Chinansa ya fara hangowa yaga Ana ta Mata fifita Ana take Mata baya ta rike Hannun Aamna gam,Dariya yayi yace Uhm kaga Ruhina can,abokai duk Wanda yaga Yar China akace amaryarce sai yayi Dariya tana ta hada hada,Fitowa sukayi Ana ga angwaye sunzo Ana ta kallonsu amma Ina Yar China biki yayi biki tuni ta kutsa Kai cikin filin rawar,aka tsaya da kida,Mc tayiwa magana abinda zaice da Yan bikin.

Ai Kuwa Mc yace Amarya tace tana yiwa kowa Barka da zuwa wannan bikin nata me Albarka,tace a fada muku a madadinta ita Amarya Sadiya Yar China da Angonta Aliyu Tawaga Uban tafiya duk Wanda yazo bikinta Bai ci abinci ya koshi ba baza su yafewa kowa ba,sannan Basu daukewa kowa rawa ba a wannan fili ko tsoho ko tsohuwa.

Dariya aka dingayi Wanda Suka San Yar China sun san zata aikata,angwaye suna ji Suka dinga dariya, Amarya aka Kira tsakiyar fili da angwaye,tunda Suka fito ake kallon matasan musamman Ahmad kamar Mata zasu cinye shi da kallo Nan take Aamna gaba daya farin cikinta ya dauke kishi ya kamata,Kamar zata Yi kuka,Ahmad Yana kallonta yayi Murmushi ta sake hade rai yasan dalilin,Yar China ma ta kula rada tayiwa Aamna tace ki saki ranki Dan Allah duk Nan wace ta fiki kyau? Babu me aure Miki Miji haba yau Naga mayyar miji,ba shiri Aamna ta saki ranta tasan halin Yar China yanzu sai ta tona Mata asiri.

Angwaye ne Suka shiga suna zuba Yan dubu dubu kowa da bajintarsa,ana kwashe kudi Ana ta yiwa Amarya liki,Amarya batayi rawaba ko kadan Wai aji take ja,duk Amarya me rawa bata da aji cewar Yar China shi yasa Kawai Hannunta Tawaga ya rike Suka tsaya a tsakiya Ana musu liki, ta yafito babbar kawarta Habiba da Hannu.
Habiba ta karaso filin tasan Shirin Kawai ta fara liki itama,Haka kawaye Suka shigo Suma,Tawaga Hannun Yar China ya riko ya Bata Yan dubu dubu itama tana lika masa,sai da suka gama Suka fito daga filin tare da tsayawa a jikin mota gaba Daya har Yar China.

Wata Yar Budurwa ce tazo wajen Yar China da Alama Yar uwarsu ce tace ke Yar China an damkawa Iyalle kudin sadakinki dubu dari cash,Yar China ta washe Baki taji kudin Sadakinta da yawa,Tawaga tayiwa rada tace dole na maka biyayya,sai ka juyani yanda kake so,sai abinda kace, su Ahmad suna ji radau sabo da kida sai anyi magana da karfi dole, suna ta dariya su yanzu Suka San Ana biki sabanin sauran Amaren.

Yar China tana ganin wata kawarta Yar Gayu tazo itama ta kashe kala an sauke ta a mota Yar China ta Bata hannu Suka tafa a Gaban angwaye tace shegiya ashe Zaki zo ai wallahi da na tanaji Rashin mutuncin da Zan Miki kwando kwando,Kawar tayi Dariya tace Yar China bikinki Guda yaushe Zan fasa zuwa ai ba Amana idan banzo ba,Wai an daura ne? Waye Angon a ciki Yar China ta tunana Tawaga tana kunya Tace gashi nasan dai ba snatching Zaki min ba,Gaisar da angwayen tayi itama kawar ba kunya Ana canja kida a Gaban mazan ta fara chashewa ta tafi har filin da rawa,Yar China Dadi ya kumeta tace shegiya Shamsiyya Mansur kina wuta...kina wuta,angwaye suka sheke da dariya,Aamna a ranta tace wannan Yar China duk Yan bariki ta Tara a bikinta sai kallon Mijina sukeyi ta koma wajen Ahmad makale ta hanashi sakat,Yar China ce ta taho da wasu kawayen Wanda yanzu ma suka zo su biyar tun a Hanya tace a fara zubar da girma a Nan dan Allah ya zaku bani kunya, ai Suma anga kawaye Yan school aka fara murna Ana Rungume juna Ana fitsara a titi.

Wata ce tazo itama aka sauke ta a dalleliyar mota anci Uwar gayu,Yar China tana magana a waya tana kina Ina ne Haka? Kawar Tace gani a bayanki Yar China ta juya ta ganta taje da tafiyarta dagwas dagwas suka runme kawar ta kalleta Tace Yar China Wai kece haka? Wannan uban kyan fa? Yar China tayi murmushi tace Amarya ce fa ai Dole nayi kyau da kyallin goshi,Suka tafa irin Shegun kawayen Nan ,angwaye suna ta Jin dadin bikin sai Suka ki tafiya,Jibson yace a Nan ake bikin,Brown yace wannan ta shirya ba Sanya,su Mashkoor da Bash ma Suka ce Wai sunce mu tsaya fa Za'a kaimu wajen cin abinci Bari mu gani, ita dai Yar China tana kusa da Angonta suna hira,tana cewa yau sai da nayi kukan murna harda Hawaye,Haka nake da jama'a ban sani ba? ai ko mutuwa nayi na samu wannan mutanen Kawai kuce Yar China tana Aljanna karka sake kayi min kuka,Kalli Yaya duk sabo Dani aka zo Kai amma nayi kokari,Tawaga yace gaskiya kinyi kokari ko mu mun yaba,ba Dole ba wane mutum ba Dole ku Yaba ba,ai biki ma Sai anjima da yamma ansha anko.

Angwaye suna ta Jin Yar China tana yabon kanta,wata kawar ce tazo da sauri tana zuba kamshi tace sauri nakeyi sai da Yamma Zan dawo,Yar China tace to matsiyaciya Zan Rama ne Jeki wallahi ai bikinki ya kusa duk abinda mutum ya min sai na Rama a Kan nasa,Dariya kawar tayi suka tafa cikin rada tace Yar China Haka naji sadakinki har dubu dari? Yar China ba sirri Tace wallahi nayi tsada Dan Ubanki dubu dari cas suna wajen Iyalle Yan dubu dubu je kice ta nuna Miki, kawar taja Yar China gefe tace suna jinki fa angwayen,to suji Mana da banyi tsadar bane Yar China ta furta ba ruwanta da wani rada.

Tawaga yace Aunty Balaraba ga matata Amana idan tazo a Dan dinga ganar min da ita,Aamna tace cab ai wallahi wannan tafi karfi na Kai baka santa bane wannan Kar take ganin kowa,Ahmad ya dinga dariya yaga Aamna ta tsorata da lamarin Yar China,Tawaga Yana ta dariya yace ai nuna Mata Zaki dinga Yi,Aamna tace yanda take ji da kanta tafi kowa ai Ni ta nuna ma Ni sa'arta ce dazu fa haka tace min sai ta zuga Ahmad Tace na harareta,daga magana direct Tace min karya nakeyi wannan ce zata tsaya na wani Bata shawara,Kai baka gani ba wannan Yar Chinan taka Kawai Dan yarinya ce amma Ni na gano Watarana ma Sai dai mu ta koya mana,Dariya sukayi Yar China tazo wajen tace Aunty zo mu tafi kin makale a Nan sai kace ke kadai ce me Miji muma fa matan auren ne,ko Kuma tsaya ga su Habiba Nan zasu zo.

Yan Mata ne na jikin Yar China suka Kai angwaye inda aka tanada Ana Bude palon kamshi da sanyi ya Dake su,cikin palon Suka gani an masa wata uban kwalliya na musamman da abubuwan kyale kyale Yana bada wasu colors, kidan soyayya na turanci na tashi kasa kasa, wasu hasken Fulawowi manya Yana kawo wuta kala kala tana rubuta
Sadiya Wed Aliyu

Abin sai ya birge kowa Aamna ta tsaya tana kallo cike da Sha'awa Nan tace Yar China tayi nisa ba Wani shawara da Zan bata,Yan matan Yan matasa ba ruwansu komai rawa komai rawa Basu da kunya irin Yar China ne ga Iyayin jaraba su a dole Yan Mata,sune sukayi Serving kowa abinda yake so,girkin ma ya birge su,Yar China Kuwa Tace Kar wacce ta zubawa wannan abinci tana nuna Tawaga,Itace ta zuba Masa da kanta harda wani durkusawa ta Mika Masa tare da cewa yau na fara Duty na,aka dinga dariya kuwa,ita Aamna Yar China kunya ma take bata gani takeyi idan itace baza ta iya katabus ba a Gaban mutane Haka maza da Mata masu yawa,Tawaga ya karba Yana murmushi,Bash yace Muna Shan kallo yau.

Tawaga sabo da kadawa Kashi miya harda bawa Amarya a Baki ta karba a kunyace Nan ne Kawai aka San Amarya taji kunya,tana cinyewa tace a Kara min,aka kece da dariya Ana yabonta taji kunya Ashe Bata ji ba,Tawaga yace okay ya Kara Mata ta lashe tace tun jiya banci komai ba fa,Tawaga yace ba Mayafi kike ta yawo? Yar China tace Ina amaryar ai Kuwa sai dai kayi Hakuri ka yafe amma bazan saka Mayafi ba na Bata kwalliyar Kuma,angwaye suna ta zabga Loma Ana Santi,Labarin bikin Yar China tuni yaje kunnen sauran Amaren ance Ana can ana rakashewa a can,Hafsat duk da Amarya ce sai ganinta akayi tazo da wasu kawayen nata.

Inda angwaye suke aka nuna Mata Bash yace wa ya Baki izini kizo nan,Dariya Hafsat tayi tace bikin Yayana nazo ni,Yar China tace na Miki kyautar dubu mutuniyar bayan biki kina bi na bashi,aka dinga dariya Yar China kowa ya birgeta sai ta Masa kyauta Tace ta bashi dubu bayan biki zata bayar,Tawaga yace zuwana nan naji da kunne na kinyiwa mutum biyar kyautar dubu kince bashi bayan biki Zaki biya yanzu har Hafsat ta shida? Yar China tace ai wajen mutum ishirin nayiwa kyautar dubu bashi ne Zan biya bayan biki Kaine sheda ko na mutu sai ka biya bashin Nan,Kuma Inshaallah Zan basu tunda na fada,Tawaga a ransa yace wannan kafin biki ya Kare zata ci min bashin dubu Hamsim ma naga alama,yace waye zai biya bashin? tace Kaine ai ko yanzu Ina da Rai Kai zaka biya,Tawaga yace to Indai kina so na biya Miki ki tsaya da kyautar dubunki Haka,Yar China da shagwaba Tace duk Wanda ya min abin bajinta Allah sai na bashi,su Jibson suna ta dariya Tawaga ya shiga Uku da biyan bashi,Aamna Dariya harda rike ciki tace wallahi Nima Ina zuwa Tace ta bani dubu Ina Binta bashi Kuma bazan yafe ba sai an bani,Ahmad Yana ta dariya ai sai sukaji wasu Yan matan sunce an Basu dubu wasu dari biyar,Tawaga yace Dan Allah ku yafe Mana,Yar China Kiri Kiri Ana kallonta ta shiga kyaftawa Kawayenta Ido Wai Kar su yafe tana makale musu kafada,Jibson Dariya harda kwalla,Ahmad yace duk wacce kika bawa kyautar Zaki iya ganeta? Yar China tace sosai ma,Habiba babbar kawa tace kawaye ma suna binku bashi ance baza mu zauna ayi siyen Baki da mu ba sai ku Bamu kudin siyen bakinmu kafin ku tafi,Kawaye Suka saki Guda wallahi hakane sister,Bash Yana ta dariya ganin Tawaga ya zaro Ido waje,Mashkoor Yana dariya yace ai an daina siyen Baki yanzu,kawaye Suka ce anayi mu Bamu daina ba suna gwalangwaso abinsu,Ahmad yace yanzu Ni a fara bani list din Yan bashi,Yar China ta dinga lissafi sai da aka lissafa mutum talatin cif harda Aamna da Hafsat Haka Ahmad ya bawa Yar China cas,Nan take ta mikawa Aamna ta karba tana Dariya,Ahmad yace My world ba Imani Haka?Hafsat ma ta karbe,Yar China ta kalli Kawayenta Tace ku kuci gaba da bina bashin sai na nutsu Zan Baku,ai kawaye suka ce Basu yarda ba,Yar China tace jaraba ku karba ta biyasu Saura dubu goma ta mikawa Habiba tace ki ajiye Zan karba

Hafsat tunda taga shagali itama sai ta samu wajen Zama,Haka sauran Amaren duk sun zo Humaira ce ta karshen zuwa aka dinga
hotuna har angwaye sai wurin 2pm Suka tafi,Dj ma Yar China ta sallame shi Tace da angwaye su dawo Karfe hudu Masu Algaita ne zasu zo suyi kidansu na sarauta,Ahmad yace Kun gaji sarauta ne Bamu Sani ba? Yar China tace ai Cousin din
Showing 108001 words to 111000 words out of 142807 words