King cewar Bash,King a hankali yace Kun san dai yanda nake son Yarinyar Nan ko? Suka ce ae,Yace Kuma kunga yanda ta nuna min kauna,Suka ce ae Mun sani,yace to Kuma dai Kun ganni kalata ba kowa ke samun Irina ba ko? Suka ce ae,yace Kuma nine King,Suka yes Mana,yace kunga irin yanda nake fama da ita ta dawo gidana Taki Amma na hakura na barta sabo da Ina jira ta Gama abinda zata Yi sai ta dawo,to Wai duk Ashe Tace ba Sona takeyi ba Kawai ta karbi soyayyata Dan ta canja Ni na shiryu na daina shaye shaye,Ihu Suka saki,Bash yace that girl?,Yace yeah,yanzu Ni kudi ne da zata canja Ni? Suka ce a'a,yace to Tace canja Ni Kawai zata Yi na dawo mutumin kirki,Tawaga yace Yarinyar da Bata da ko nonon kirki ga Yan Mata Nan suna rubibinka Amma Aunty Balaraba zata maka Haka?
Jibson yace Ni dama Sam ban yarda da ita ba,Kawai ka bamu Dama mu tozartata a garin Nan, Mashkoor yace sai Dana fada maka kayi hankali da Mata yanzu ka bamu Dama muci ubanta,Ahmad yace Kuna ji na? Suka ce ae,yace ku bar min case din Ni zanyi Handling dinsa sabo da matatace baza ku Shiga zancen ba ku barni da ita,Shuru sukayi suna jimami kawai suna Kora shaye shayensu.
Aamna kuwa kwana tayi tana Rusa Kuka ko gajiya Bata yi,Baba ma da yaji labarin yafi Jin tausayin Ahmad akan Aamna,lallashin duniya Aamna Taki hakura Sai Kiran Wayar Ahmad takeyi yaki dagawa,a daren ta kirashi yafi Sau dari,Daya gaji ma kashe wayar yayi gaba Daya.
Sharhi sharhi fans.
AsmaBaffa
10/26/21, 8:53 AM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵
NA KUDI NE
DAN GIRMAN ALLAH KARKI FITAR DA NOVEL DIN NAN.
DUNIYATA AAMNA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.
Ranar Bai iya ko gyangyadi ba bare wani bacci Yana ta tunani,saman bed dinsa Kawai ya dawo ya kwanta shi kadai yasan irin radadin da yake ji a ransa,Aamna ma tana rike da waya Haka bata Yi bacci ba Haka gari ya waye,washe gari da safe ba yanda Mama batayi da ita ba akan taci abinci Amma Taki ci ko wanka Bata Yi ba sai kuka Kawai,Hijab ta zura ta tafi gidan Zuhra,tana Shiga gidan Zuhra tana mopping Aamna ta fada jikinta tare da fashewa da sabon kuka,Zuhra taji tausayinta Tace Aamna kiyi Hakuri Kar wani ciwon ya shigeki,Aamna tana kuka Tace Ni ya dawo, Taya Zan huce ya yafe min ya dawo?, Zuhra ta kalleta yanda dare daya ta firgice,Zama sukayi a saman kujera Zuhra ta Shiga lallashin Aamna da kyar ta samu ta daina kukan Amma duk da Haka idan ta Lula tunani sai sabon kuka.
Bangaren Ahmad kuwa Shaye shayen ma idan yayi baya Jin dadinsa ko kadan Haka ya hakura sannan Sallah Bai fasa zuwa masallacin ba,abokansa kuwa gaba Daya Suma sun tsaya cik sabo da halin da abokinsu ke ciki,suna ta tayashi bacin rai,barinsa suka Yi shi kadai sabo da kadaicin yake bukata,kwance yake shi kadai Yana tunanin mafita sai ga Jibson ya shigo tare da Siyama wacce taci shegen gayu,a saman kujera Suka Iske Ahmad Yana kwance Yana tunani duk ya fita a hayyacinsa,Jibson ya kalli abokinsa da tausayawa yace King gata fa Kawai ka so wannan tunda Aunty Balaraba ta ki ka,Ahmad fuskar Nan ba Rahma ya kalli Siyama yace Jibson Haka za ayi,Jibson ya fita abinsa ya rage daga Siyama sai Ahmad,tana ta faman karairaya tana fari da Ido,ta durkusa a gabansa Tace Ina sonka Ahmad,na Dade Ina kaunarka Matukar zaka so ni ba abinda bazan maka ba,har kaina Zan Iya mallaka maka,Ahmad kwata kwata hankalinsa baya jikinsa Haka Yace ba damuwa Ina sonki kinyi tashi ki tafi, gobe Jibi 10am kizo,Siyama farin ciki ya kamata harda godiya,Tsaki Yaja yace Jeki sai jibi,tashi tayi tana murna ta tafi.
Kamar Yanda yace Jibi sai ga Siyama 10am ta wani dau wanka duk ta matse jikinta ta zo,Ahmad ya fito sanye da Jallabiyya Suka fita a motarsa har bakin shagon Aamna lokacin Mama sun gaji da kukan Aamna gwara ma tazo shagon ko ta rage tunani,Aamna tana bakin shagon tare da Zuhra suna magana kawai taga motar Ahmad tayi parking a Bakin wajen,Fitowa yayi sai taga Siyama ta fito tare da rike Hannun Ahmad,har Gaban Aamna suka karaso ransa a bace ya kalli Aamna Yace kalli ya kika gani Yarinyar da tasa kika wulakantani kalle ta yanzu har gida take bina tana rokata akan na so ta,har gida take zuwa lokacin kina gidana take Neman na so ta,akanta kika min Haka to gashi roko na takeyi na sota,Siyama murna ta koma ciki Bata Yi zaton tona mata asiri zaiyi ba,Tace Honey ya Haka zaka Tona min asiri,Zuhra da Aamna Suka saki Baki galalala,Tsawa Ahmad ya dakawa Siyama yace ke dalla rufe Mana Baki,Baki da hankali amfani nayi da ke sabo da tana gadara kekawarta ce ta gari,kece me Bata shawara,kallon Aamna yayi yace Dan kince Baki so na cikin minti Daya zanyi mata kala kala Wanda zasu so ni,idan nayi Niyyar saurarar Mata cikin mintuna Kamar Riga Haka Zan na canja su,ke tunaninki har mace ce,Siyama ranta ya baci ta juya cike da borin kunya ta bar wajen sum sum.
Wata dalleliyar motar ce ta tsaya a jikin ta Ahmad,budurwa ce fara Yar gayu ta ko Ina tayi karshe ta karaso tare da tsayawa a Gaban Ahmad Tace Sweetheart kazo mu tafi motarka Zan Shiga kasa Musa ya maida min tawa ita a gidanka,Ahmad ya kalli Aamna yace kin gani idan kin kini cikin lokaci kankani Zan samu Wanda suka fiki komai,ya nuna Budurwar yace wannan idan Ilimi kike takama PhD ne da ita sannan me kudi ce ke gidanku ko Tyre ta mota Kuna da ita? Me kukeyi in Banda Siyar da citta,Ahmad Kamar Bai San Aamna ba Haka ya tsaya ya ci Mata mutunci tas sannan ya samu zuciyarsa tayi sanyi,Budurwar Yar gayu ita ce ta rike Hannun Ahmad suka tafi,Aamna tana tsaye sunyi mutuwar tsaye da Zuhra sai Hawaye da ya wankewa Aamna fuska,Kuka ta barke da shi me karfi lokacin da taga Ahmad sunja mota sun tafi,Zuhra Tace ya Miki kyau Aamna Kinga abinda nake fada Miki,Baki ji me yace Miki ba in a minute zai iya canja Wanda suka fiki kala kala,Mata rubibin irinsa sukeyi Kuma gaskiya ne,yanzu kalli dalleliyar Budurwar data ke like Masa,kalli kawar taki Siyama da kike takama da ita,itace ta Kai kanta tana rokonsa ya so ta,amma a gabanki me Tace? Aamna cikin kuka Tace Bazan yafewa Siyama ba,Kina gani Zuhra ya tafi gidansa da wannan kyakyawar Budurwar gidansa shike Nan kwana zasuyi tare,Zuhra Tace mene damuwarki tunda kince ba sonsa kike ba canja shi zakiyi,Aamna ta sake fashewa da sabon kuka Tace wallahi.....Zuhra....Ina sonsa......Ina....sonsa...I love him....I love him....Siyama ce take nuna min Illar auren me shaye shaye shi yasa zuciyata ta kasa tsayawa,to ai gashi ita yanzu ta nuna Miki iyakarki,tunda Dan shaye shaye ne shashasha Mene Zaki damu? Aamna da Matukar bala'i Tace Ahmad Dina ba shashasha bane ta ja tsaki tayi cikin Shagon tana ta uban kuka,Zuhra tana ta dariya ta bita ciki Tace to kiyi Hakuri Yana sonki har yanzu Bai daina ba ai kinfi ma wacce yazo da ita kyau,kin fita komai,Aamna Ido yayi jajir Tace gashi Nan ya tafi da ita gidansa,Ni wallahi komawa zanyi gidan Mijina duk Ni na cuci kaina,Zuhra tana ta dariya Tace wallahi karki koma yanzu yanda yake Fushi da ke kika je zai iya Miki Illa gwara ki Bari ya huce,Aamna Tace da abinda yake min ba gwara kullum ya dinga min Bulala Hamsim ba,Zuhra tana Dariya Tace au yanzu dukansa ma sonsa kikeyi?Aamna Tace ae dadinsa zanji Indai ya hakura to yayi ta duka na kullum har durkusawa zanyi na gode Masa.
Suna zaune wata tazo siyan Citta Aamna tana ta tunanin Ahmad sai ta zuba Mata barkono,sai da ta karba Tace citta fa nace,Aamna Tace au na manta sai ta juye ta zuba mata kanunfari,Matar Tace Citta fa tunanin me kikeyi Haka ne,Sai Zuhra ce tazo ta karba ta zuba Mata,wani yazo ya siyo Wani Boxers sai Aamna ta karbi kudin dari biyar ne Kuma dari biyar din ya Bata Amma sai ta irgo dari takwas ta bashi tace ga canjinka lokacin Zuhra ta tafi shi kuwa mutumin ya sani Amma ya karbe abinsa yayi gaba.
Kusan kwana Uku Aamna duk ribar Mama ta tafi Aamna tana ta yin aringizon kudi.
Yau ma da safe zata hada tea a kitchen sai ta dakko gishiri ta saka a madadin sugar sai da ta kurba ta feso da shayin waje sai taga gashiri ne,gaba Daya Bata cikin hayyacinta.
Ahmad Kam abokansa suna zuwa suna ebe Masa kewa,Jibson ne ya shigo ya same su tun kafin ya zauna yace ku fara Yi min jaje, Mashkoor yace na me? yace ku tausaya min suka ce Mene? Jibson yace Jiya kafin na kwanta bacci 9:30pm, Allah yaji Kan Sameera me Hannun kwano badan ta mutu ba sai Kawai na dinga ganin fatalwarta a kaina,tsorata nayi na Kira Wayarta a daren tunanina ta rasu ne an binneta tayi min fatalwa.
Sai kuwa ta daga tace ita kalau take Nan na gano mayya ce zata kamani nayi Mata fata fata nace Kar ta sake na sake ganinta a Ido na,Dariya suka dinga Yi,Jibson yace Kasurgumar mayya ce ban sani ba,na Kai kaina babu dama na Dan kebe Ni kadai sai ta dinga min fatalwa, Jibson yace yanzu ma Haka Ina ganinta a idona,Bash yace ko dai so ne? Jibson yace Bazawarar Allah kiyaye,Idonsa ya Shiga murzawa yace gata tazo... tazo bazan lamunci wannan ba idan na gaji Kara Zan shigar kotu Mayya ta kamani,Tawaga yace Wai da gaske kake?yace ae Mana, Mashkoor yace kirata a waya muji,Jibson ya dakko waya tare da Kiran Sameera,bugu Daya ta daga.
Yace ke Kwano Mene Haka bana son wasan da kike min,gaskiya na daina ganinki Maganar gaskiya Ina daga Miki kafa Zan kaiki Kara akan me Zan dinga ganinki,ko bacci nayi sai kizo min Mene Haka Dan Allah Ni bana so Gaskiya,Dariya Sameera tayi ya dameta da zargi Wai ita mayya ce Bayan ita Bata San komai ba,tsokanarsa tayi Tace Yau Danwake kaci ko? Tsoro ya Kama Jibson sabo da Tabbas yau Danwake kannensa suka Yi a gidan Kuma sai da yaci ya fito,da sauri ya kashe wayarsa su Tawaga Suka dinga dariya Jibson yace ba abin Dariya bane wannan wallahi Danwake naci na fito idan ba mayya ba Taya tasan naci Danwake? Gaskiya a Nemo min maganin mayu wallahi,Bari Brown yazo Dan Uwarsa ya sa munje wajen Mayya,Suna ta dariya Bash yace Ashe duk wankan da muke dauka a banza tana kallon Hanjin mu me muka ci,Jibson da sauri yace Kuma ranar tuwo naci kaga zata kalle Ni a banza Ina cin tuwo,da ace nasan Haka ne ai Kwai da nama zamu ci idan munje ta ganmu Yan gayu,yanzu ta ganmu cikinmu duk tuwo,Bash yace kyaleta anjima zamu je kaza zamu siyo muci muje Suka ce Haka za ayi su Ahmad suna jinsu suna ta dariya,Amma Ahmad duk da Haka hankalinsa Yana wani wajen.
Da Yamma su Jibson kazar kuwa Suka siyo Suka ci harda Shan Yogourt,Bash yace Bari na Kara da Biscuits sabo da ta ganmu muma ba baya bane,Jibson yace Apple zanci Ni Haka Suka dinga Ciye ciye su Tawaga suna ta dariya,yau da Sameera ta shigar da su Palon Baki kallonsu tayi Tace Bari na kawo muku lemo ko da yake nasan kunyi ciye ciye da yawa,Bash da sauri ya kalli Jibson,Jibson tsoro ya kamashi yace Wai ke Kwano Taki da ita aka haife ki ko kuwa siyanta kika Yi? Sameera ta Gama Gane shi Amma sai Tace me fa? Kasa fada yayi Dan kar ya ci Mata Fuska sai yayi Shuru kawai,Sameera ta fita a ranta tana ta dariya Bash ne yace ai ance ta bangaren Uwa tafi karfi Wala Allah ita a nono ta Sha,Abban Brown ne yazo zance yau ma yaga su Jibson Ashe Basu daina zuwa ba,Takaici yasa ya shiga palon shima ya nemi wuri ya zauna sabo da shima Abban Dan rigima ne baya tsoron abin kunya gashi ya makance Akan son Sameera,Su Jibson Suma suka ki tashi mirsisi sukayi,Abban Yana ta harararsu Suka share abinsu,Sameera ta fito tare da ajiyewa su Jibson lemo ta zauna tare da maida hankalinta wajen su Jibson,Abba ko Kallonsa Bata Yi ba,kwafa ya ja ya Mike ya fice Kamar zaiyi duka.
Su kuwa sai magrib sannan Suka tafi.
Bayan Kwana biyu duka abokan Ahmad na kusa Mashkoor, Jibson,Bash,Tawaga da Brown wajen Ahmad Suka zo,Brown yace Ahmad ka shirya muje daurin auren Cousin Dina a Kano gobe,Ahmad yace a halin da nake ciki bazan iya binku ba ga motar Nan ku dauka kuje da ita koma Ina ne ai komai Nawa naku ne,Suka ce to ba damuwa,washe gari da Sassafe Suka shirya tare da tafiya Kano,Ahmad da Rana Yana kwance Yana ta tunani iri iri akan abinda Aamna ta Masa sai ga kiran Wayar Mashkoor sabo da shine Kawai Suka Yi waya yanzu yanzu,Yana dagawa akace masu wannan motar sunyi hatsari ayi sauri azo Kan gawarsu gaba Daya sun mutu na Daya motar ne babu Wanda ya mutu suna asibiti,Zumbur Ahmad ya mike tuni ya rasa inda zai sa Kansa,yanzu abokan nasa ne suka Suka mutu? Kayan dakinsa ya shiga watsi dasu.
Kuka Kawai ya fara ya rude Kawai Iyayensu ya Kira ya sanarwa kowa hankalinsa ya tashi ko wanne danginsa Suka tafi can inda akace anyi hatsarin,Shi kuwa Ahmad a rude ya Kira Mummy ya fada mata,Yana kashe wayarsa ya fita shima ya bazama,tare da Baban Jibson Suka tafi can hanyar Kano,Suna zuwa Suka hango Yan Sanda da mutane da yawa a wajen Ana ta zaro gawarwaki,motar Ahmad gaba Daya tayi fata fata,da gani yawan gawarwakin Ahmad ya Fadi ya sume yin duniya Bai farfado ba,da shi aka hada aka tafi Asibitin da Wanda Basu mutu ba,Daya motar ita bata wani lalace sosai ba da gani kasan a motar Ahmad sune Wanda Suka mutu Kawai.
Duka Emergency aka wuce da su,Mummy ce ta Kira Aamna tare da sanar Mata Tace kiyi sauri idan sun dawo ki je wajen Ahmad kar ki Bari ya koma shaye shaye,Ahmad Yana son abokansa wannan abin zai taba shi,kece kadai Zaki iya kwantar Masa da hankali,Aamna tana kuka Tace to Mummy.
Ahmad da kuka ya farka Yana Kiran sunayen abokansa Muryar Mashkoor yaji yace Kai dalla mace ne ka ganmu Bamu mutu ba wallahi raunuka Muka ji na Daya motar ne Suka mutu,Zumbur Ahmad ya mike Yana bin dakin Emergency da kallo yaga dukkan abokansa suna numfashi Brown dake Jan motar ya Dan fisu Shan wahala,Farin ciki ya Kama Ahmad yace ya akayi Baku mutu ba yanda motar Nan ta dagargaje Haka? Mashkoor yace ikon Allah wallahi,ai Watarana mutuwa ba a Nan take ba sai kaga motar da Bata wani ki jiki ba an mutu wacce tayi raga raga Kuma ba a mutu ba,Jibson yaji wuya duk jikinsu raunuka yace na daina shaye shaye daga yau na jiyo kamshin mutuwa,Tawaga cikin wahala yace yan kannena marayu da tuni an musu sakiyar da ba ruwa,Ba Baba ba Ni sun Shiga Uku wayyo Allah na tuba,Ahmad yace Ni yau wacce irin godiya Zan yiwa Allah,Bash yace kaje kayi ta Sallah,Iyayen su Jibson kowa kuka ya Kare sai murna da godiya ga Allah,Ahmad ya fadawa Mummy Basu mutu ba,Itama Mummy cike da murna ta sanarwa Aamna Tace Idan an dawo dasu asibitin Kaduna taje can lallai ta kula da Ahmad.
Haka kuwa Ahmad shi ya biya kudin Hospital,har Wanda Suka mutu ya Bawa Iyayensu tallafi,Transfer aka musu zuwa Kaduna private hospital Ahmad ya dau nauyin komai Dukkansu ba Wani rauni me wahalar warkewa Suka ji ba,Sameera a guje tazo Asibitin tana ta kuka a gefen bed din Jibson ita dai tana son Jibson a rayuwa,Jibson kallonta yayi kadan yanda ta tashi hankalinta a hankali ya daura hannnunsa saman nata Hannun dake saman cikinsa,Idonta da Hawaye tace ya jikin? Murmushi yayi yace da sauki Me Hannun kwano yau cuta tasa bani da kitse,namana ba maiko zaiyi ba yanzu ki tausaya karki lashi kadan,Dariya Sameera ta dinga yi,Ahmad Yana kallonsu yayi Dariya tare da zuwa gefen Jibson ya zauna yace Malam me zaka iya ci? Kannen Jibson ne Suka shigo da Abinci iri iri,Ahmad suka gaisar tare da Sameera duk da Basu San wace ba.
Jibson yace kaima kasan bazan wuce farfesun hanta ba Malam,Maye Ahmad ya Furta suna Dariya yace Sameera ki taimaka a bashi,Sameera ta zuba a plate Ahmad ya tallafa Jibson ya jingina da jikin pillow,Kanwarsa Fa'iza Tace wannan Surukar mu ce ne?Ahmad yace ae Kawai,sai murna sukeyi suna kallon Sameera,Sameera harda kunya,Jibson yace me Hannun Kwano a bani Mana yunwa,Sameera kuwa Fa'iza ta mikawa Wai ta bashi ya ci,Fa'iza Tace ai mu fita zamuyi ma kiyi aikinki suka fice tare da komawa Room din Mashkoor.
Sameera ta fara bashi a baki Yana ci suna kallon junansu.
Mashkoor Wanda duk ya fisu Jin sauki,Ahmad ya koma Room dinsa tare da kannen Jibson gefe Kuma ga yayar Mashkoor tana zaune,wata Nurse ce Yar kyakyawa fara Amma ba can ba ta Sha fararen uniform dinta Idonta dauke da farin Glass da Alama Hutu ya ratsata kana gani kasan ba talaka bace,baza ta wuce 22yrs ba,tana kamshi ta shigo ta kalli Mashkoor Tace ranka ya Dade maganinka fa? Fuska ya Bata yace Baku da Aiki
Showing 66001 words to 69000 words out of 142807 words

66-70
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
MAMU GALADIMA
BESTYNBEELAT
AISHA
MAMAN SAMHA
HAFSEE

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23 Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48