Miki har tallafo Kirjinta takeyi min,da badan Ni Allah yasa nace sai ke ba,zuciyata Bata taba son kowa ba sai ke,bana sha'awar kowa sai ke da tuni kinji kida magwan,ai ko Malam ne ta dinga Masa abinda ta min sai ya manta da karatunsa,Aamna tace yanzu da baka so na da yawa da shike Nan sai ka so ta? Ahmad yace ai tuni ma Zan karba,Dan Adam ne fa zuciya ce Bata da kashi,yanda a lokacin ma ba Wani tsoron Allah ne Dani ba lokacin Ina shaye shaye ai sai dai Kuma kiyi kuka ki hakura to Allah ya taimakeki bana layin Mata ni,ki kiyayi kawaye wlh maza su ba kowanne aboki ne ke canja su ba amma Mata ba Uwar da kuka Iya sai gulma da cin Amana.
Ni dai kayi min Alfarma kaji...ta karasa zata Yi kuka,it's okay zanyi Inshaallah Zan dauke shi Aiki sannan za sa shi a inda zai samu Albashi me tsoka Inshaallah ki dauka anyi an gama but sabo da ke ba Dan ita ba,Rungume shi tayi tana murna tace thank you King,I love you tare da hade fuskarta da tasa,Tace gobe su Mummy zasu koma yaushe zamuje Lagos ne? Nima Ina so Naga gidan surukaina,Zamuje ne verysoon,Suna Hira har bacci ya kwashe su.
Washe gari da Yamma su Mummy duk sun Gama Shirin tafiya sabo da tasan Idan Suka yiwa Humaira Sallama tasan kuka zata musu sai basu sanar Mata ba gaba Daya da kawayen Suka tattara zuwa airport,Ahmad yaje rakasu Suma,sai da suka je airport Daddy ya riko Hannun Ahmad yace ya naji Shuru ne? da me fa Daddy ya furta da shagwaba,Daddy yace ba score har yanzu? Ahmad Yar kunya yaji yace Daddy verysoon,Nasiha ya sake masa sosai sannan suka Yi Sallama ya Rungume Mummy yace zamu Zo verysoon da My World,Marar kunya a Gaban Nawa cewar Mummy suna dariya gaba Daya ya musu Addua ya tafi Suma Suka Shiga jirgi abinsu.
Aamna yau ma Yar China Kawai ce Bata girki ita ta kaiwa lafiyayyen lunch da kanta taje ta Iske Tawaga ya duka a kasa Yana rarrafe Yar China tana bayansa Wai jaki jaki yake mata,Gashi ta daure Masa Ido da bakin kyalle,Yar China Bata sakko ba tace Aunty Balaraba kin ganni ajiye abincin an gode,Tawaga ya cire kyallen Yana Shirin cewa Yar China ta sauka tace ja muje sai ka kaini can bangon,Aamna tana ganin Haka ma Yar China ba kunya gareta ba ta juya ta tafi gida ma kawai,Karatun Qur'ani tayi sosai tayi Adduointa kasancewar me gidan baya gida Yana can shirye shiryen fara zuwa Office.
A saman Sallayar Bacci ya kwasheta har after 5pm ya dawo tana bacci Bai tashe ba ya wuce yayi wanka,Abinci yayi serving Kansa Yana ci Yana Santi har ya gama,sai da zai wuce masallaci ya tashe ta,tana tashi Tace Sannu da zuwa yanzu ka dawo? Murmushi yayi yace tun 5:20pm ,lallai nayi bacci Sannu da zuwa abinci fa? Naci tun dazu nayi wanka kije kiyi Sallah zanje masallaci,Okay ta furta sannan ta Mike ta wuce toilet.
Sai Bayan Kwana Uku Jibson ya fito Shar da shi har ya wani canja,su Bash suna ta Masa dariya ana tsokanarsa,Ranar ne Kuma Ahmad ya fara zuwa Aiki Office,ranar Daddy ya Sha Kira a waya komai kafin yayi sai ya Kira a waya,sai 5pm ya nufo gida gaba Daya ya gaji Kamar an Masa duka abinka da ba'a Saba ba,Yana yin wanka Abinci yaci ko masallaci Sallar Isha bai iya zuwa ba a gida yayi Yana idarwa ya kwanta sai bacci,Ganin Haka Aamna ta gyara Masa blanket ta koma main Palo tana kallo sai ga Sameera taci gayu tare da Jibson Kamar Wanda zasu je wani party,Aamna tace Ango da Amarya Allah yayi fitowarku sai kace wasu kaji masu kwanci,Jibson suna wani zuba kamshi ya Sha shadda ita Kuma wani material ta zuba Malam peach,Jibson yace Ina mutumina? Aamna tace bacci yakeyi yanzu Bai Dade da dawowa daga Office ba Bai Saba ba sai bacci,Jibson yace ai Dole muma kafin mu Saba sai munji jiki,Hannun Sameera cikin nasa sai kunya take ji tana murmushi Kawai,Aamna tace ke Sameera Ni bana son kunyar Nan shi yasa Yar China ke birgeni da itace da yanzu Muna zuba Hira,Jibson yayi Dariya tare da furta ai wannan da kika ganta authentic ce, genuine and Lovable,Dariya Aamna ta dinga Yi tare da furta yayi kyau,suna ta Hira Yana ta wani koda Sameeransa.
Bayan sati biyu da bikin su Yar China duk sun Hada kansu suna zaman su lafiya sun Zama kawaye lokacin Kuma Saura kwana daya daurin auren Siyama,Hashim ya Kama gidan Hayarsa me kyau harda gate yasha tiles dai dai na rufin asiri,Iyayen Siyama ba laifi Kaya me kyau Suka Mata da Aamna akayi ake komai,ta bada gudunmuwa na kudi sosai da shi ma suka Yi kayan kitchen,Washe gari Saturday Amarya tayi kyau sai sheki takeyi ta Sha lalle da gyaran gashi 11am aka Daura Auren Siyama da Hashim,duk su Ahmad sunje group dinsu,Ango burinsa ya cika sai murna yakeyi ga albishir da Aamna ta Masa na karbar takardunsa an bashi Aiki zai daina aikin wahala,Da kwarinsa yake komai,Siyama Amarya dai ba yabo ba fallasa ta hakura Haka,Zuwa Yamma aka Kai Amarya abinta tana can yau ta hadu da Sarkin karfi cewar Baba Wanda shima ya Halacci daurin auren,Haka Mama taje bikin.
Aamna Kuwa da dare Ahmad ya tura driver ya dakko Masa matarsa,Suna Hanya Aamna tace Musa tsaya Amai nake ji, Musa da sauri yayi parking tare da mikawa Aamna bakar Leda har biyu yace Hajiya Yi anan sai ki jefa a kwalabati ai Aamna ko kula Ledar Bata Yi ba ta fita waje tare da tsugunawa ta Shiga sheka Amai Kamar zata fito da hanjinta,Musa ya Kira Ahmad yace Oga Muna dai dai sabon masallaci ka ganmu Hajiya ba lafiya gata tana ta Amai na tsorata fa Oga tun dazu take Amai yaki karewa,Ahmad gabansa ya Fadi yace me taci a gidan bikin? Karfa su kashe min Mata sauri ka kaita Hospital kafin na karaso,Sai da Musa ya jira Aamna ta gama tas ya Bata ruwan Roba ta wanke bakinta sannan ta shiga mota tana Nishi tace muje Musa naji sauki,Musa yace Oga Yana hospital yace na kaiki can,Aamna itama abinda takeji a jikinta kullum ya isheta Tace muje to.
Suna shiga Likita ta gani ta fada musu abinda take ji,Dake private ne Nan aka Mata wasu gwaje gwaje,tana jiran Result Ahmad ya shigo da sauri daga shi sai 3qtr da t-shirt fara,Zama yayi a inda take zaune ta jingina da bango tare da lumshe Ido,Ahmad yace Sannu My World,me kika ci a can? Aamna tace daga ganin Alala sai nayi sha'awa na ci Shikenan na fara Jin Amai,Ahmad yace Oh....me ya kaiki cin wani alalar biki kema,Ana zaune lafiya idan so kike Yi ai sai ki dafa da kanki.
Doctor ne ya karbi result din gwaji ya duba nan yace ranka ya dade na tayaka murna matarka ciki ne da ita na wata biyu, Ahmad murna tasa yayi mutuwar zaune ya wani Bude baki Yana murmushi,Takardar ya karba a wani slow ya duba,Aamna ya kalla da fara'a ya rike kafadunta tare da girgiza ta sosai yace I make it my world,Haba Ni San Ina buga game din Nan dai dai ah ki tayani murna na samu first score,kallon Doctor yayi yace Likita mace ko namiji? tsaya karma kace min Namiji Baby girl ce ko? Zanyi Yar Budurwa kwana Nan,Ya kalli Aamna yace ki dinga Mata irin Calabar Nan tawa ta da kin tuna? Ai kullum da ita Zan dinga fita sai duniya tasan King yayi 'ya,Likita ya Bude Baki Yana kallon Murna Ahmad ya mike ya Hana Kansa sukuni gaba Daya, Doctor yace Dan Bamu waje Zan Mata wani gwaji,Ahmad yace ban Gane na baku waje ba? Ina mijinta wallahi baka Isa ba nasan latse latsen Nan da kukeyi zaka Mata ka Kira mace ta mata,sabo da ka Mai Dani gara ka kalli matata one in million na barta ka saki wannan shegen labilen naku ka latsa mata kafafu da ciki baka Isa ba bada Ni ba.
Likita yace Allah ya bada Hakuri ya Kira mace tazo ita tayi abinda ya dace ta basu shawarwari da Maganar zuwa awo etc.Aamna karar murna ta saki da sauri Kuma ta rufe bakinta tare da furta au na manta,Ahmad yace Adana ta sai munje gida,Hannunta ya rike Suka taho a hankali,Musa yace ya maida motar gida,tsohon me gadin Ahmad an Kara Masa matsayi ya tashi daga me Gadi ya koma Driver sabo da Amana irin ta Musa,tun kafin su koma gida Ahmad yace a shirya yau akwai party a gidan,Su Jibson duk Suka Zama ready Suka tafi da matayensu sashen Ahmad suna Jiran dawowarsu,Kafin ma Ahmad ya dawo Su Jibson an tanaji lemuka wannan karon babu Shan barasa,Tare da Aamna Suka shigo,tana rike a hannunsa,Ahmad ba jira yace a goal,Suma Kamar Yan siyasa Suka amsa da a goallllll......a goal....suka ce a goallllll......Yar China tace na Gane zancen,Ahmad yace na Zama Daddy matata tana da ciki na 2mnths tafi suka fara raf raf raf.....Jibson yace music .. Bash ne DJ ya danna,Su dai matan Dariya suke ta Yi,Yar China harda cewa a kashe kida sai na fara rera Mata wakar Dana tanaja,aka tsaya Nafeesat tace Muna jinki,Yar China ta fara Waka wai me ciki turtsi bulli.....me ciki turtsi bulli,Tawaga yace a amshe mata Yana Tafi suka ce Suma Me ciki turtsi bulliiii me ciki turtsi bulliiii....Tace ta kasa Zama,Tawaga yace turtsi bulli harda tafi sauran har Ahmad Dariya Kawai suke yi,Yar China taci gaba da cewa tsaiwa ta gagara....Turtsi bulli....Tawaga ya sake Amsawa,Aamna tace wannan ai wulakanci ne wallahi Zan rama, Ahmad ta kalla wannan tijarar daka min fa,Cikin murna Bash ya Danna kida Aamna sabo da kunya guduwa tayi ta kasa Zama sun Dade suna shagali suna ta tsare tsare.
Ahmad harda cewa a Ina za a Kama ayi suna? Humaira tace Kai Yaya ko kunya,Hararta yayi tayi Shuru tana dariya,Hafsat Tace ba Wani suna an daina yanzu,Inji uban wa? Cewar Tawaga zamu samu karuwa baza muyi murna ba sai mun kashe kudi,Nafeesat tace Ni dai nice me kula da me jego,Yar China Tace Muna wajen Bikin suna mu Allah ya sauketa lafiya,Ahmad yace Halina Dake hankali Yar China,ba Wanda yayi Addua sai ke,party fa kace za ayi cewar Mashkoor,to naji an Gama kuje Kun korar min ita sabo da kunyarku,Jibson ne ya fara mikewa ya rike Sameeransa zai tafi Ahmad yace gobe karku manta akwai zuwa Office,Allah ya kaimu suka tafi Yar China kin tashi tayi tace Allah bazan koma da kafata ba sai dai ka goyani,Abu me sauki cewar Tawaga ya goyata Kuwa Suka tafi Yar China akwai son wasa Kamar me.
Washe gari Ahmad waya ya Kira Mummy ya sanar Mata ta dinga Murna tana bawa Daddy labari,su Saddeeq da Mufeedansa sai murna sukeyi,Basu Dade ba Kuma ya dauki Aamna Suka tafi Lagos,can ta Sha kallon kudi satinsu Daya Suka dawo,lokacin Kuma Ahmad yana Shirin tafiya da Aamna da Baba Sudan suje gano Rahilu,Baba ya rike wuta sai anje da shi,Kuma ya kamata aje da Baba sabo da shi ya rike Aamna,Baba ranar da Ahmad yaje ya sanar Masa ya Zama cikin shiri bayan an Masa passport,Baba yace Nima ka siyo min Sut (suit) irin ta Rahilu da ita zanje Masa Nima,Ahmad ba musu ya nemowa Baba size dinsa kala Uku,yace da jallabiya shima sai ya saje da Rahilu a Sudan.
Ranar da zasu tafi Aamna harda Shan abaya baka,Ahmad shi dai kana Nan Kaya yasa Yan ubansu,Baba kuwa harda sa jallabiya fara yayi Nadi da rawanin larabawa,Baba yace nasan mutanen Sudan ma tun a jirgi zasu fara Yi min larabci su Aamna suna ta dariya Mashkoor ya ajiyesu a airport Basu Dade ba jirginsu ya daga,Baba yace wayyo kunne na ya toshe wani dummm nake ji ice ko kamfanin mu na Najeria be? Basu iya jirgi me kyau ba,Ana ta yiwa Baba Dariya,duk ma'aikaciyar data wuce sai Baba yace baiwar Allah abincin jirgi ko baza a Bamu bane sai dai suyi ta kwantarwa da Baba hankali suce za a bayar idan lokaci ya cika,Wata Yar Budurwa ta fito cakwas cakwas itama ma'aikaciyar jirgi ce ta dafa kujerar Baba tare da cewa Baba a sa Belt,Baba yace yau Naga fitsara da gani ba'a kulla abin arziki ba ace ma'aikatan jirgi gaba Daya Yan Mata fella fella suke yawo suna kashe ma Ido sabo da a koya min fasikanci idan gaskiya ne a zuba maza Mana su dinga dakawa pasinja tsawa wallahi Baku da halin arziki kunyi asara an maida ku hotiho Ana talla daku a sararin samaniya,sai kunyi sama sosai sannan kuke tafka tsiya wallahi da Allah kuke bada mu ba,sai Dariya akeyi a jirgi Baba Yana ta masifa har aka kawo abincin jirgi.
Baba yace aikin banza shinkafa ce da nama Baba ya cinye nasa ya dauke na Aamna ya cinye,Ahmad ma ya bashi nasa ya cinye Baba yace abinci Kamar na Yaron Yaye Haka dama jiragan suke wannan rowar mutum ya biya kudi a bashi abinci naira Hamsim a dubu goma.
Baba Yana ta murna ya fita kasar waje zaiga Sudan yankin Larabawa,sai da suka sauka a jirgi Suka Shiga lafiyayyar Taxi Suka shigo har wata state,Baba yace me Zan gani? Sahara nake gani fa Ahmad,me Zan gani Haka? Yo wannan ai gwara naje Kano Kuma Sudan din ne? Aamna tana ta da dariya,Baba yace cab Dole Rahilu ya Shiga Uku a Haka amma Yaran wasu masu kudin suke Mana Iyayi Ana wallahi Yana can Sudan Yana karatu,tana Sudan tana karatu,ai wlh gwara Kayi Ado bayero iniversity (University) Ahmad Yana so ya dan rike ko Aamna amma yasan Baba.
Suna tafiya a mota Baba yaga wani Dan fari Yana tafiya a titi Baba yace wannan da gani bako ne shima baiyi Kama da su Rahilu ba duk yanda akayi daga Seria yazo gashi Nan a koshe bulbul,Driver dai suna ta larabci da Ahmad Yana Kiran Rahilu Yana Basu Address,Baba ya kalli wani Symbol kato Ana tallan omo Klin,yace Ashe Daya muke da su kaga jaraba Klin a Nan inama Aishatu tana Nan Sarkin ta'adi tazo ga mutuminta a Nan ma,Baba shi kadai yake surutunsa har Suka sauka a wani gida Kato me bene Hawa biyar, Aamna tace Baba anzo gidan Abbi na kaga gidan me kyau,Na Haya ne uban wa yace Miki gidansa ne,?Ahmad Yana jinsu dai suna Fitowa a taxi sai ga Rahilu ya fito sanye da jallabiya wata baka,Baba yace kaga bakin mutum ga bakin Kaya Rahilu manyan gari wuya kamar na zalbe,Rahil da fara'a ya tarbesu ya dauki akwatin Ahmad Suka nufi ciki,wani Palo yasha adon Larabawa shi aka kaisu,Babba yana kallon gidan Yana Kallon Rahilu yace Yan karya an iya tsara gida,Matar Rahilu ce ta fito wata balarabiya fara tas,ta zauna sai da Ahmad Suka yi maga suka gaisa su Baba basa Jin yaren,Wata ce ta fito itama fara ce Amma ba Kal ba irin dai Bata fi farin mu na Yan Nigeria ba,bayan sun gaisa itama ta Mike tayi ciki,gabansu aka cika musu da Abinci iri iri na Larabawa,Baba yana kallo,wani kwano me kyau ya bude yaga kubewa Danya Guda Guda a cikin kwano da wani ruwa tsululu Yana yauki ya Sha tafsrnuwa da kayan Hadi,Wani kwanon ya bude yaga wani Abu shi kamar Tuwon Zuma da Dabino,Rufewa yayi ya Bude wani kwanon yaga miyar ganyen kabewa,Can Kuma wani tuwo ne Kamar na madara har da Cheese,Ga Fruits iri iri,Baba yace Rahilu Ina shinkafa inda Muka Fi wayo,Dan Iskanci kasan wannan ba abincin mu bane na awaki ne zaka sa a kawo mana,kalli kubewa Guda Guda, Rahilu Yana murmushi yace yanzu shinkafa zata Zo harda lemon Tsaki,Karka sake ku matsa min lemon tsami salon na barke da zawo.
Suna zaune sai ga wata shinkafa taji Hadi da hadin salat,Sai ga kaji an kawo,Baba yace yanzu naji zance Baba ya sauka kasa ya shiga cin Abincinsa Suma su Aamna suka gyara Zama tayi Serving Ahmad,Bayan sunci sun Sha suka Yi Sallah sannan aka kirawo Yaran Rahilu Suka dinga gaisar da su,Dake suna makaranta suna Jin turanci sai suka dinga magana da Aamna,Baba yace mu Kuwa sai kallo Allah wadaran rashin Boko,Sai dai Kawai Baba ya dinga cewa Hey...Hey....Ahmad Yana ta dariya a zuciyarsa yanda Baba yake ta aikin Furta Hey ga Yaran da yawa,Yaran Rahilu basa Bari suyi baccin kirki sabo da Hayaniya, Baba cikin dare kullum sai ya tsine musu Wai sun hanashi bacci,yace Rahilu Dan Iskan banza ya dinga dirkawa Mata ciki suna ta zazzago yara Haka kamar zomaye.
Masauki me kyau aka Basu Aamna cikin Yan uwanta Mata ta shiga,washe gari Kuwa Daya gidan Rahil Suka je Suma Mata biyu da Yara da yawa Ahmad yayi Larabci ko turanci Aamna ma Haka Baba Kuwa sai Hey kawai,Nan ma kwanansu Daya aka raka su wajen Dangin Aamna na uba sannan wani babban matashi Mahmood shi ya dinga fita da su Aamna yawo suna ganin gari suna pics,Baba duk inda akaje sai yace ayi Masa pics shima,Ana dauka zai ce da Aamna maza dorani a yanar gizo duniya ta ganni a Sudan,Rahilu ya Gama tsorata da cin mutuncin da Baba ke Masa amma wannan lokacin sai yaga Dan kadan ya masa,kwana hudu tsakani Ahmad ya kafe shi gida Za'a taho Rabonsa daya kwanta a jikin matarsa kwana hudu kullum tana wajen Yan uwanta shi bazai iya ba,Baba yace Kai Nima na gaji da garin Nan mutane kamar konannu kowa baki sai Larabcin tsiya akan me,Aamna ita tana Jin dadin haduwa da Yan uwanta sai Ahmad ya yini Bai ganta ba,ai Kuwa Yace gida,kwanansu biyar Suka dawo gida Nigeria Aamna tana ta faman Fushi da shi har Bash ya dakko su a Airport aka sauke Baba a gidansa
Showing 126001 words to 129000 words out of 142807 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43 Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48